Sashe 21
Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da ta gaji zata gudu sannan yace ai Bai dawo ba Amma ance gobe ko jibi zai dawo Amma fa babu Guarantee, bacin ran ya tunzura Farida tace ai Kuwa baza ta hakura ta yafewa Farooq ba Wanda ya Bata Mata ganin Dan sarki sabo da Haka ta shiga Bincike da Neman Ina Manal ta kaisu,ai Kuwa taci sa'a ta samo gidan,har wajen Baba me kayan Miya Farida taje, Bayan ta gaisar da shi da ladabi Tace Baba nasan ka Gane Ni ko? Baba yace kwarai Yar Uwar Manal ba,Farida tace to Baba kana ta jawa kanka zunubi,ya za ayi ka bawa fasikai wajen zama? To wallahi ka Sani Manal Bata da Aure ka bincika kaji,ba mijinta bane karya take,ba mutuniyar kirki bace Mazinaciya ce,a Kauye ma cikin shege tayi shine aka turo ta birni Yayanta Yazed ya zubar Mata da ciki,Baba yace Amma Yarinyar Nan ta cuce ni,tsakanina da ita sai Allah ya isa,dama Ni tunda Naga Yaron ban yarda da shi ba,nayi Dana sani,Farida tace kaje wallahi ka koresu irinsu ne suke yiwa Yaran Unguwa fyade,sune masu lalata Yaran Unguwa,Amma Manal tun a Kauye karuwa ce,Rannan ma tunda ta bar gida ba a sake ganinta ba sai bayan sati biyu,Baba ransa ya baci yace muje yarinya yau sai naci zarafinsu sai na Tara musu jama'a sai nasa Yara sun musu Atile da kasa da ruwan duwatsu,Gidan Baba Suka wuce ya sanarwa Matarsa komai itama matarsa ta dinga Salati Tace Bari na dakko mayafina da Ni za a je koresu shedanun banza.
Lokacin Kuma Fuzail ya kalli Manal suna cin abinci tare yace kiyi min alkawari ko Mai wahala komai runtsi Zaki zauna tare Dani,ki min Alkawari ko a wanne Hali Zaki aureni,kiyi min alkawari baza ki sake saurarar wani Namiji ba ko waye sai Ni Daya sannan ki kular min da kanki,wannan gangancin taimakon da kika Yi Mana a zamanin Nan na yanda kasar Nan take ciki abin a yaba Miki ne,Amma daga kaina karki sake gangancin yin makamancin irin wannan taimakon ko da kuwa Mutanen karairayewa sukayi kada ki taimaki uban wani,daga kanmu an rufe Kofar taimako irin wannan,Manal tana Dariya Jin son Kai irin na Farooq.
Ameer mamaki yakeyi Wai Fuzail ne Haka,Yana jinsu Yana cin Abincinsa,Manal Tace nayi alkawari gaba Daya Inshaallah,Nima kamin alkawari duk runtsi zaka so ni Kuma baza ka kula wata ba sai Ni, Fuzail yace Inshaallah nayi alkawari zanci gaba da sonki har abada Manal,ke mutum ce,ke abar a so ce,sai da suka Gama alkawarinsu sannan Suka cinye abincinsu,Naman ya dauka yasa a bakinsa tsakanin hakoransa ya tallafe kanta a hankali tare da sa Mata Naman a Baki Kamar wasu tattabaru,Basu taba yin hakan ba sai yau,suna taka tsantsan Amma sai ji sukayi an banko kofa an shigo gaba Daya da Yara da manya,kowa ya saki Salati,Baba yace ga zahiri na gani,Manal ya nuna da yatsa yace Allah ya Isa tsakanina Dake fasika,ai Manal tunda taga Farida tasan me zai faru,Farida ta kalli Farooq shekeke Tace kwarto ihuuuu anji kunya kwarto eho jama'a,Fuzail ya Kalli Farida ransa a bace matuka yace Wai me na Miki a rayuwa ne? Sabo da Ni talaka ne shine kike min Haka? Ribar Nawa kika samu yanzu Dan kin Sa an Mana ihu? Farida tace idan kunyi zuciya kuyi kudin Mana waye ya hanaku, wallahi duk Randa na auri prince Dina sai Kun yabawa aya zakinta a duk inda kuke a garin Nan,Manal Yan tarkacen kayan su ta Hado kaf ko tsinke Bata Bari ba tana Fitowa ta kalli Fuzail da Ameer tare da kyafta musu Ido,a fili Kuma Tace Baba ku fito Nima yanzu a Kofar gida Ina da shedar da Zan kafa Kuma wallahi idan na fiku gaskiya sai na kaiku kotu Kara an bi min hakki na,wallahi kunji na rantse kuzo muje na nuna muku abinda kuke zargi, Baba Bai tunanin wani abuba yace muje Naga shedar gantalalliya Allah wadaran halinki sai kin kafa sheda na gani Dan Ubanki,naci dake Ashe fasikai nake tallafawa,Manal aka biyo su yuuuu da Yara suna jira a bada Umarni su fara ihu da ruwan duwatsu,Suna fita Fuzail da Ameer Suka sulale Suka Sha kwana lokacin mutane gaba Daya hankalinsu ya koma Kan Manal.
Manal tana tafiya kusa da titi tana cewa ku biyoni wallahi na fiku gaskiya Yara da wasu manyan har Farida Ana Binta yuuuuuu lokacin ma tuni Ameer ya tare Napep sun shiga inda Manal ke tafiya Suka nufo da Napep.
Ai kafin su karaso ta arce da gudu da kayanta,Ihu aka dauka Ana jifanta Allah yasa Me Napep yaci birki ta shige Ana fisgo rigarta Fuzail ya rike ta sosai Yana yiwa me Napep Tsawa yayi sauri ai Kuwa ya fisga da karfi Saura kadan su kife Allah yasa Suka hau Titi kafin kace me sunyi nisa.
Sai lokacin Manal ta saki Ajiyar zuciya tare da sakin kuka,tayi karfin Hali ta shiga tashin hankali da tsoro Allah yasa Basu ji Mata rauni ba,Fuzail lallashinta ya dinga Yi har tayi Shuru,sai da sukayi nisa sannan me Napep ya tsaya da Umarnin Fuzail,Ya kalli Manal cike da so,marairaicewa yayi tare da komawa Kalar tausayi yace My love ya Zama Dole yau mu tafi Kinga Dan Uwan namu yayi waya yace Yana garin Nan sun dawo shi da Iyalinsa,yace muje gidansa mu zauna tare kafin Nan gaba mu fara sana'a sannan sai mu koma Kauye na siyar da ragowar gonar gado na nazo muyi aure,na matsu Naga kin Zama matata,Zan samu na Kama gidan haya a daura Mana aure,Manal zata Yi kuka ya fara lallashinta yace ki koma idan Yayanki ya dawo zanzo na kaiki kiga Yan Uwana Dake Kauye da Kuma Dan uwanmu Wanda yanzu zamu koma gidansa da zama sannan sai na kawo kudin aure ko?,Manal tace na yarda da Allah na yarda da Kai Farooq Dan Allah karka yaudareni kasan Ina sonka ka dawo da wuri,yace Inshaallah,fita tayi da kayanta a katuwar leda ta Basu kayan gwanjonsu ta dauki nata sannan sukayi Sallama Hawaye Yana bulbulowa Manal Bata son rabuwa da Farooq dinta.
Tace bazan yafewa Farida ba nasan makircinta ne,Fuzail Wayar Dake hannunsa ya Bude ya sa Mata wani sabon layi sannan ya Mika Mata Wayar ta karba,yace ki rike Wayar Nan Zan dinga kiranki a ciki kinji,Manal tana Hawaye da shesheka Tace to Kai Kuma fa? Haba Dan uwanmu zai bani wata,Tace to na gode Allah ya Kara arziki,Ameen ya furta,Ameer ya zaro dubu biyu ya Mika Mata yace ungo tun Rannan aka bani sadakarsu a Hospital kiyi amfani da su,Manal tayi godiya sannan suka Yi Sallama me Napep Yaja kenan Fuzail yace wait da sauri.
Me Napep ya tsaya cak da sauri Fuzail ya fito ya taka Gaban Manal ya jawota jikinsa tare da Rungume ta sosai,Manal ta sake fashewa da kuka a jikinsa yace so kike Kar na dawo na aureki da wuri? Kinfi so muyi ta Zama babu aure? Manal ta girgiza Kai yace to kije gidanku ki jirani Zan dawo na aureki okay? Kai ta daga tana goge hawayenta Suka rabu shima Kamar yayi kukan.
Allah yasa ka dawo da wuri na hadaka da Yaya na,Bafa Kauye Zan tafi ba Ina garin Nan ko sati bazanyi ba Zaki ganni.
Suna rabuwa gida ta koma Direct tana shiga da shirgin kayanta Farida da Hajiya Suka dinga sheka uban dariya sabo da Murna,Ran Manal ya dugunzuma amma Bata su take Yi ba rabuwarta da Farooq itace ke damunta.
Bangaren Farooq Kuwa suna barin Manal wasu dalla dallan motoci na Alfarma Guda uku suka shiga Daya biyu suna take musu baya har zuwa Guess House din da Suka Fara zuwa kafin su fito gari da farko,Machine din da suka Yi Hatsari Fuzail ya hango anyi parking nasa,Dariya yayi sosai Yana Fitowa ya nufi inda Machine din yake tare da Dan dukan machine din da hannunsa ya furta na gode ka birgeni,bazan bayar da Kai ba sai ga mutum me daraja,Ameer yace lallai ka zare Prince Fuzail,Ciki Suka shiga su biyu bedroom kowannensu ya zaba ya shiga shi daya,Ameer toilet ya fada ya shiga darje jikinsa kamar me.
Fuzail Kuwa a bakin bed ya zauna tare da murtukewa ya dawo Fuzail dinsa na asali sannan ya cire uban gashin Daya saka tare da gemu da sajen Daya Kara a saman kan nasa,Kyawunsa zalla ya bayyana,Izza ta dawo da Gadara ya shiga wanka ya Dade Yana kalailaitarsa sannan ya fito,tare da Shiryawa cikin wasu kana Nan Kaya farare tas,Pencil jean da rigar me dogon Hannu Yar gajera,ya zuba kyau Kamar me gashin Nan ya Sha gyara Yana sheki,Bangaren Ameer Kuwa wata Jallabiyya yasa maroon, Lafiyayyen abincin da sukayi order Suka Fara ci suna Santi,Fuzail Kamar zai cinye har plate din yayi irin Hausar Manal yace yaushe Rabon duniya da ayyaraye,Kai talauci masifa ne just one week Zan mutu ahhh.....Dariya Ameer ya dinga Yi shi dai zai ga rigimar da za ayi kafin Fuzail ya auri Manal,Fuzail Naman Nan ya dinga ci yace kaza Dadi wallahi,Ameer ya rage tasa amma Fuzail ya dauke ya cinye kazar Yana Santi ya Dade Bai ci ba,yace Saura kadan idan na nayiwa mutum Baki ya kamashi sabo da Rashin cin nama,Ameer yace Kai dai ka sani Duk Manal ce ta koya maka iskancin Maganar Nan,badan Haka ba gidan Ubanwa kasan Wanda ya Dade Bai ci nama ba idan yayiwa wani bako ko tsinuwa tana kamashi?Dariya sukayi.