← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 96

Sashe 96

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

A ta bakin titi ya tsaya ya tsiya masu sannan suka kara kama hanyar gidan shi dake unguwar Bosso Lokos,
Dama kuma ta san gidan,
Yana parking a harabar gidan ya buɗe ya fito sannan ya buɗe in da take,kamar wata karamar yarinya haka ya dauke ta ba tare daya dire ta ba har cikin daki saman gado ya zaunar da ita,

Fita ya kuma yi ya shigo da akwatin kayanta ledar kuma ya kai kicin,yayyanka fruit din yayi ta yanda zata ji daɗin sha sannan ya dauko,

Tsayawa yayi rike da tire a hannu yana kallon yanda ta jinginar da kanta jikin gado idanun ta a lumshe alamun barci na son ɗaukarta,

Murmushi ya samu kanshi da saki,domin aduk sanda ya tuna gudan jinin shi na tare da ita sai ya ji wani irin farin ciki mara misaltuwa tare da ƙaunarta na ratsa zuciyar shi,
Ajiye tire din yayi a hankali sannan ya taka zuwa in da take,
Zube guiwowin shi yayi a kasa ya tura hannun shi cikin rigarta yana shafa marar ta,

Ɗan zabura tayi tana sauke ajiyar zuciya tare da kyara zama,
"Sorry na tsorata ki"

Bata ce mai komai ba sai kokarin cire hannun shi tayi daga cikin ta,

Tashi yayi ya hau kan gadon gaba ɗaya ya jawota kan gadon yana kwantar da ita tare da karasa cire mata karamin kyalen dake kanta,
Rigarta ya tattara ya mai da shi saman kirjinta tana saka hannun shi a tsakanin siket dinta ya jawo shi kasa,

Tsira ma shaffen cikin ta idanun yayi,yana kure in da yaga ya ɗanyi tudu kaɗan idanu na kusan mintuna goma kafin a hankali ya kai hannun shi sai tin wurin yana dan shafa wurin,sai kuma ya duka ya sakar mata Kiss a wurin,yana kankame ta hanyar zagaye hannun shi gabaɗaya ta bayanda kanshi kuma saman cikin ta"Allah ya Albarkaci rayuwar ki,ya faranta maki kamar yanda kika faranta min,ya yafe maki kura-kuran ki har abada ya saka Aljanna ce makomar ki"

Hannu tasa ta shiga shafa lallausar suman kanshi"ya kuma barni tare da kai har karshe rayuwata "

Da sauri ya sake ta yana dagowa "da gaske kike kina son Allah ya barmu tare?

Jinjina mashi kai tayi tana rungume shi tare da saka kuka" Dan Allah ka yafe min akan duk abinda na maka,nasan na faɗa maka maganganu marasa daɗi wadanda Allah zai iya tuhuma ta,na maka alkawarin ba zan sake ba dan Allah ka yafe min"

Shafa bayan ta ya shiga yi"shiii ya isa haka,ni dama ban taba rike ki a raina ba,na san kuma idan nayi haƙuri komai mai wucewa ne zaki fahimta,dan haka tun tuni yake yafe maki"

"Ni dai kace ka yafe min"

"Na yafe maki duk abinda kika min da kuma wanda zaki min nan gaba,Allah ya yafe mana baki daya"

Ƙara rungume shi tayi"na gode Zauji "

"Kin tabbatar ni din Zaujin ki ne?

" Kai rayuwata ta ce"

Sunbatar goshin ta yayi yana sauko da ita,tare suka sha fruit din sannan ya mai da kayan kicin,

Ranar tare suka yi kwanan farin ciki,babu wani da ya shiga tsakanin su sai dai kyakkyawar runguma daya mata har gari ya waye,

Haka washegari ko tsinke bai bari ta dauka shi yake mata komai har ta wanka shi ya mata ya shirya ta,
A ranar ta ga wani abu wai shi tarairaya,ko kwakkwarar motsi tayi sai ya tambaya mai take so,
Jirgin yamma suka bi zuwa Abuja daga nan suka tafi London,

Da yaba Ammi takardar Sikainin din ta gani har da kukan farin ciki ita da Grandma,
Kwanan ta biyu tare dasu ya zo ya dauke ta ya maida gidan shi dake nan bayan dogon gargaɗi da bayani daga Ammi akan ya rinka binta a hankali,

Rayuwar ta koma tamkar na wata Sarauniya,domin ta ko wani bangare ba karamin kula take samu ba,har balle da cikin ta ya kai wata biyar lokacin ya fito sosai kana ganin shi,

Sau biyu ta zo Nigeria a lokacin bikin yanninta sai kuma lokacin da Amira ta kammala makaranta,a nan Kano a dakin Goggon yara ta sauka,
Dawowar su da sati biyu aka rataye Pa,Allah sarki rayuwa shi kuma a inda nashi babin ya kare kenan,

Bayan wata huɗu sai gashi Allah ya sauke ta lafiya in da haifi ɗan ta namiji mai matukar kama da mahaifinshi,tun a Asibiti yama danshi Huɗuba da Abdulbasit wanda zasu rika kira da (Abid) kasancewar sunan mahaifinsa,
Grandma da Ammi har da Kukan murna,wannan dama shine burin su,
Tunda aka haifi yaro sun dauki son duniya sun daura mashi,har balle Ammi ko ƙara bata yi sai tace ai yayan ta ne,

Yan Nigeria ma sun zo Suna ciki har da Maijiddarh,Allah sarki ita ma da nata cikin,sai fatan sauka lafiya,
Sai da sukayi sati ɗaya sannan suka dawo da goma sha tara na Arziki,domin sunje gidan Arziki sun ga inda aka gaji Arziki a bar Arziki,

Sai da tayi Arba'in bayan haɗi da tsumi na musamman da Ammi tai mata sannan ta bashi matar shi suka koma gidan su,cike da sharadin kullun za'a kawo mata Yayanta ta ganshi,
Ganin yanda Suraj din ke yi masu zarya a gida kamar zai sace ƴar mutane,

Randa ta koma kuwa data shiga hannun shi sai da tayi har sai da idanun ta suka kumbura,saboda ya nuna mata tsakanin ta dashi babu sassauci,domin kwanakin daya ɗauka yana haƙuri sai da fanshe shi,
Sai da komai ya lafa sannan ya rungume ta yana aikin lallashi,
"Ke rayuwata ce Bebin,ba zan iya rayuwa ba babu ke,ina mai rokonki da kiyi haƙuri da ni da kuma halina,ban taba jin haka game da wata mace ba face ke,shi yasa bana iya riƙe kai na a duk lokacin da nake tare dake"

Shafa fuskar shi take yi tana jin wani shaukin shi na kara taso mata"kai din jarumi ne a cikin jarumai,a duk lokacin da naso nuna jarumta ta a gabanka sai naji ni ba kowa ɓace face YAR TSANAR KA wacce zaka juya kayi yanda ranka yake so da ita,ina matukar Alfahari da kai"

Mumushi ya saki wanda ya bayyana fararen jerarrun haƙoran shi,yana ƙara matso da ita jikin shi"soyayyarki kullum takan narka tunani na acikin shaukin iske goben rayuwata a tare dake, tamkar jini ina da bukatar a ko da yaushe ki kasance a cikin jiki na,
Sabanin haka kuma,hakika zan azabtu sau lokacin da yawa,
Haka kuma da soyayya nauyi ce ga jiki,tabbas dana roƙi Allah ya hukunta jiki na ya zamo mafi nagarta iya dauka domin kada na bada rauni yayin tafiyar da soyayyar ki,
Kece ƙaddara mafi daraja wacce farashin ki baya taɓa faduwa a rayuwata,kullum hauhawa kike sama tamkar shekaru na Bebin,ina matukar son k....

Haɗe bakin su tayi wuri ɗaya domin ƙwaƙwalwar ta ba zata iya jurewa sauraron waɗannan tausasan kalaman dake fitowa bakin shi ba,masu saka ta jin shaukin soyayyar shi dake kokarin fasa kinjin ta ya fito,
Cire bakin ta tayi cikin nashi tana haɗe goshin su wuri ɗaya"ina matukar kaunar ka Zauji"

Kara hade bakin su yayi yana jawo masu bargo,

Ni ma kuma ganin haka yasa na fito dakin tare da jawo masu kofa ina ma Abid fatan samun kani a wannan daren.

*Alhamdulillah ina ma Allah godiya da ya bani ikon kammala wannan littafin na yar tsanar zinari a wannan lokacin a kuma wannan ranar, abin kirkin dake ciki Allah ya bamu ikon amfani dashi,wanda bai da amfani kuma Allah ya yafe mana kura-kuran mu Amin*

Sai mun haɗu a sabon littafi na mai suna *Ayi dai mu gani* wanda zai zo a matsayin na kyauta,wato free book.

Godiya ta musamman ga paid group din YAR TSANAR ZINARI, na gode da haƙurin ku Allah ya sadamu da Alkahiri Amin...
Chapter 96 · 0% Book details