← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 96

Sashe 14

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon matar tayi ido cikin ido babu alamun tsoro ko dar a tare da ita"suna na Biba,ina aiki ne a ma Ammin Amira"

"Waɗanda kike ma aiki basu faɗa maki matsayina dana ƴaƴana bane a wannan gidan?

" Ba'a faɗa min ba"
Saukan wani lafiyayyen mari taji a lafiyayyen fatar fuskarta mai taushi wanda nan take shaidan yasunta biyar suka fito kwance a fuskar ta,
Nuna ta tayi "amma daga dukkan alamu baki samu tarbiyya daga wurin iyayenki ba,to ki sani idan har bikida tarbiyya ni nan zan tarbiyantar dake, wawuya,jahila,dakikiya kawai,fitar min a shiya,karna kara ganin kafarki a shiyana"

Idanun ta sunyi jawur na azaban Marin da tasha wanda tunda take a ba a taɓa Marin ta ba sai yau,
Bata son ko kaɗan ta nuna gazawarta ta hanyar zubar da hawaye,shi yasa ta juya kawai zata fita,

Dakatar da ita tayi "ke,zo ki basu haƙuri"

Juyowa tayi,ta kalle yaran da ake cewa tana ma haƙuri,girgiza kai tayi ta kalli goggo "Never" Ta fadin haka ta bar falon,
Juyawa tayi ta kalli ko ina,nima take ta samu inda zai fi mata sirri domin amayar da abinda ta hadiya,
Ta gefen ɗakunan samari ta samu dakali ta zauna,

Hawaye ne ya fara zuba a hankali a hankali,kafin kuma ta rufe bakinta tana fashewa da kuka mai taba zuciya tana gunji,wanda da kaji yanda sautin kukan ke fita kasan cewa wanda ke yinshi tabbas kuka ne na kadaici da kuma tuno wani abu mai ciyo a rayuwarka irin wanda ka kasa mantawa dashi,
Babu abinda ya mata ciyo irin kiranta da jaka, tunkiya,da wannan yarinyar tayi, sai mamarta data kira ta da Jahila,kalmar mara tarbiyya bai mata ciyo ba,domin ta san tun daga lokacin data saka kafa tabar gida,tun daga lokacin ta fita a jerin masu tarbiyya,

Duk gatan da suke takama suna samu,to wallahi bai yi koda rabin gatan da take dashi ba,ilimin da suke takama suna dashi na Boko idan suka ji a inda tayi karatu da abinda ta karanta sai kusa haɗiye zuciyar su da mamaki,haka kuma ilimin Addini,sai dai kawai ta ajiye su a gefe ne kawai domin basu da amfani a gare ta,domin tayi Alkawarin duk abu abu wanda ta sanadin iyayenta ta same shi to ta ajiyeshi har abada,ko da menene.
Domin koma yaya ne su suka hallakar da rayuwar ta,kai,bama tason ta tuna komai dangane dasu har a badas
Ta sanadin su gashi waɗanda basu kai matsayinta ba suna wulantata,

Tayi kuka sosai wanda sai da fatan idon ta ya kumbura,idanunta sukayi jawur,
Ta kwashe kusan mintuna talatin kafin ta fito wurin dan komawa shayansu,

Tana fitowa shi kuma yana jawo kofar dakin shi ya wuce,wanda daga dukkan alamu cikin sauri yake,
Taga lokacin da yake kokarin saka katin buɗe ƙofar shi a aljihu,sai da cikin rashin sani katin ya faɗi, shi kuma bai lura ba ya wuce,

Ganin ya wuce ne yasa da sauri ta karasa ta dauki katin tana jujjuya shi,
Wani irin murmushi ne ya subuce mata wanda nan take ta manta duk wani damuwa daya shiga zuciyar ta a shin mintunan nan,
Rungume katin tayi a kirjin ta,tana murmushi,sai kuma ta ciro ta kai baki ta sumbata,tare da lumshe ido jin ta shaki wani ni'imtaccen kanshi "mugu,kai Allah na gode maka,ko na komai in dai na samu na dauko na ɗakin shi a dakin Abbu bazai min wuyan samu ba" Karrama rungume katin tayi wanda tana zuwa ta saka a na'urar,nan take kuwa kofar ta buɗe,
Cikin sauri ta shiga ta maida ƙofar ta kulle,
"Wow" Ta faɗa tana kallon tsarin falon yanda yake a tsaftace,ko ina sai kamshi yake tashi,
Ta jima tana kalle_kalle a dakin kafin ta shiga aikin take mashi kaya,wanda tundaga falon har zuwa ɗakin barcin shi bata ga komai ba,
Wani fitowa data jawo a dakin barcin shi,babu komai aciki face damin kuɗi wanda a kalla taga na Country biyar a ciki,harda daloli,
Maida durowar tayi ta kulle ba tare data ko taba ba,
Cikin mintunan da basu wuce goma sha-biyar ba ta gama hargitsi komai na dakin harta zanin gado a wurge yake a kasa amma bata ga koda alamar abinda take nima ba,
Ji tayi ranta ya baci,so take ta ƙara dubawa,sai dai kuma ta riga taja lokaci,
Dan haka ta yanke shawarar ta fita kawai wata rana zata ƙara samun dama,
Kar ya zo ya Kamata,

Kallon dakin tayi yanda gabaɗaya ta fitar dashi kamannin shi,
Girgiza kai tayi,data tsaya kyara mashi dakin ya kamata,Gara ta gudu ai ba zai san ko waye ba.

Da wannan shawaran tayi amfani ta doshi kofa domin fita,sai dai tana saka kati kofar ya shiga key ya kulle bam,
Ƙara kwada sawa tayi bayan ta juya katin ko bata saka dai_dai bane,
Sai dai ga mamaki ta duk yanda tayi domin kofar nan ta buɗe taki buɗewa sai ma nuna mata key da yake yi,
Tun tana yi da wasa har ta fara tsorata ta hau jan ƙofar tana tura shi iya karfinta ko zai buɗe,
Sai dai ina kofa ko motsi bai yi ba,
Tsoron ta daya,yanzun idan ya kamata me zata ce mashi ta zo yi dakin shi,ƙila ma asirin ta ya tonu,
Wasa_wasa tana cikin wannan halin har awa daya ya shige,har gashi na biyu na ƙoƙarin shudewa,
Ga uwar yunwa da ke addabar ta kamar hanjin cikinta zai tsinke,
Nan lamarin ya wuce tunanin ta ne yasa kawai ta zauna nan bakin kofar tana fashewa da kukan nadamar shigowa dakin tare da kife kanta a jikin ƙofar tana rusa kuka............
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*16*

*Na mai da Littafina mai suna a sama na kuɗi,tare da JAURO,idan kina son daya 300,dari uku,guda biyu kuma da Yar Tsanar Zinari tare da Jauro,dari biyar 500,ko wani daya dari uku*
*Hauwa Umar,Zenith Bank, 2284905309*
*ko katin waya na MTN,tare da turo shedar biya ta 08141644865*

Tun tana yi da ɗan ƙarfi har ta koma yi a hankali daga nan barcin wahala ya ɗauke ta wanda bata masan iya adadin lokacin data ɗauka ba,

_____koda suka je suka dauko Abbu a filin jirgi zuwa gida,ya daɗe a shiyan Amme suna hira,har Abbu yayi wanka suka ci abinci tare,sai wuraren ƙarfe daya sannan ya fito ya nufi bangaren su,yana jin Ammi na aiken Amira akan taje ta dubo mata Biba tun dazu bata ganta ba,Abinci ma sai tare da ita Amiran suka lalaba suka yi tunda ba makaranta,

Ganin ya laluba aljihunshi bai ji katin buɗe ƙofar shi bane yasa kawai ya saka numbobi ya buɗe ƙofar dashi,

Yana tura ƙofar yaga ya buɗe kaɗan sannan kamar a kwai abu mai dan nauyi daya tare kofar wanda ya hana shi buɗewa yanda ya kamata,
Yana sako kafar shi bayan taku biyu,yaji kafar shi ya sauka a kan abu mai laushi,
Da sauri ya daga kafar yana matsawa baya a tsorace dan Allah yasa bai gama sauke kafar shi ba,duk a tunanin shin ajikin mage ya saka kafar shi,shi yasa yaja baya yana kiran sunan Allah,dan ba karamin tsoron mage yake ba.

Tsayawa yayi cikin tsananin mamakin ganin ta a wurin yana kallon ta,ya kuma kalli kofar,ta yaya ta shigo ne,ta ina,

A hankali ya saka kafa ya tsallake ta,
Jin yanda ta sauke wani ajiyar zuciya mai ƙarfi irin wanda ke nuna mutum yana cikin kuka barci ya dauke shi irin shi tayi,

Hakan ne yasa ya juyo ya kalle ta ba tare da yayi niya ba,
Idon shine wannan karon ya sauka akan fuskar ta,wanda yasha mari,ganin kamar shaidar hannu a fuskar ne yasa a hankali ya kara taku ɗaya daga inda yake zuwa gare ta,
Tsura ma fuskar ido yayi,tabbas shaidar mari ne wanda ga alamun kwanciyar yatsu biyar nan a faran fatan fuskar ta,sai kuma idanunta da suka kumbura,

Dauke idon shi a kanta yayi wanda nan take kuma suka kara sauka akan yanda falon ya canja kamanni ba kamar yanda ya fita ya bar shi ba,
kalle ta yayi ya kalli falon kafin ya shige dakin shi,in da ya iske nan ma haka ɗin ne,
Dafe ƙwanƙwaso yayi yana nazarin ɗakin kafin ya fara tattara duk wani abunda aka cire daga muhallin shi yana mai dawa daidai,ganin lokacin sallah Azahar ya gabato ne yasa yashiga bayi yayi wanka,dan daga masallacin yana son ya fita ne.

Daga inda take kwance kamar wacce aka tunatar da inda take haka ta Mike a firgice,ba tare data tsaya gama wastsakewa ba ta tura ƙofar dan ganin ko zai buɗe,sai dai cikin tsananin sa'ar ta sai gashi kofar ya buɗe,
Ai bata jira komai ba yanda kasan wacce aka kora haka ta tashi ta fita da gudu tana sauke ajiyar zuciya,

Ba tare data Ankara ba kawai sai ji tayi taci karo da mutum,tana kokarin faɗuwa shi kuma ya torota yana maida ita tsaye a kan ƙafafun ta,

A hankali taji muryar shi yace "ki dinga kula,ki daina guda ɗan bashi da amfani"ya fada yana kare mata kallo,dan gaba ɗaya a hargitse take,gashi ko ɗankwali babu a kanta,ga ido a kumbure,

Kallon shi kawai tayi ta saka kai tana yin gaba,dan yanzun bata shi take ba,duk da ta gane shi,wato Shamsuddeen ne.

Binta yayi da kallon mamaki,kafin ya kalli ƙofar dayaga ta fito,

Baya son zuciyar shi ta raya mashi wani abu,amma kunsan yanda zuciya take,har ya kai bakin kofar dakin shi,ya juya yayi kofar dakin Suraj,
Yana tura ƙofar yaji ya buɗe,dan haka shiga yayi,
Tsayawa yayi yana karema falon kallo kafin idon shi ya sauka a kan ɗan kwalinta dake yashe ata bakin kofar,
Shiru yayi ya zuba ma ɗan kwalin ido,
Sai kuma yaji yana son ya shiga cikin dakin,

A hankali yake takawa har ya isa bakin ƙofar ɗakin,
Kiran sunan shi yayi"Suraj "
Chapter 14 · 0% Book details