← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 96

Sashe 27

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shin ka tashi aure ne? Ko ince kana buƙatar aure ne?

Kallon mamaki ya shiga yi mata" Kamar ya? Ya tambaya cikin rashin fahimtar in da ya dosa,

"Tambayar dana maka shi nake nufi"

"Kai muke saurara ka bamu amsa kawai" Cewar Dady,

Numfashi yaja ya sauke yana ƙoƙarin daidaita kanta"A'a kaka,bana bukatar aure"

"Me yasa" Ta kuma tambayar sa,

"Saboda ban shirya ma hakan ba"

"Ko da baka shirya ma hakan ba me zai hana ka fara ajiye daya a kusa da kai,na tabbatar da yanzun kana bukatar haka"

"Ta yaya nake buƙatar hakan?sam aure baya gabana yanzun"

"Na fahimta,amma me zai hana ka yarda cikin satin nan a aura maka yar uwar ka Maijiddarh"cewar kaka,

Wannan karon baki buɗe yake kallon su," What? Why? Sai kuma yayi shiru tuna waye Dady a wurin shi da kuma wurin Maijiddarh,domin mahaifinta ne,duk cin fuskar shi ba zai iya yi a gaban shi,amma me dalilin kaka na dauko wannan zancen,

"Me ka ga" Dady ya kuma tambaya,

Shiru yayi gaba ɗaya ma ya rasa me zai ce,
"Kai muke saurare"

"Ayi abinda ya kamata" Ya faɗa kasan makoshi,
"Ina iya tafiya?

Cikin sakin fuska gaba ɗaya suka amsa mai da "eh"tunda sun samu amsar da suke so,

Ganin ya fita ne yasa Kaka sakin murmushi" Alhamdulillah tunda ya amince,yanzun abinda nake so sai a fara gudanar da shirye-shiryen tunda yau Lahadi nan da kwana biyar sai a ɗaura auren kowa ya huta"

Zuciyar shi wasai domin yasan matarsa yau sai tayi rawar daɗi "to amma Kaka wani hanzari ba gudu ba,yaya za'ayi da batun ita wannan yarinyar,kinga bai kamata ma kwata_kwata su dinga ganin juna ba"

Dan shiru tayi kamar mai nazari kafin tace"babu damuwa akan haka,domin nan da kwana biyu zan sallame ta,tunda ita Ammi din ma taji sauƙi"

"To shikenan bari naje dan a fara shirye-shiryen da wuri"

"To Allah ya maka Albarka"

Da Amin ya amsa cikin tsananin farin ciki.

Yana fita shiyansu kai tsaye ya nufa,anan yake sanar da iyalan shi kyakkyawar labari wanda sai da Maijiddarh tayi kukan farin ciki,
Kafin kace me tuni gida ya hargitse da murna,

Ammi ita ma Kaka ke nasar da ita hukunci data yanke,duk da abin bai mata daɗi ba ko kaɗan kuma ya kona ranta haka ta hakura ta ke sakin murmushi ba tare data nuna damuwarta ba,amma a ranta ta san duk inda yake yanzun baya cikin walwala,

Aunty Atika Maijiddarh ta kira tan sanar da ita abinda ke faruwa,cikin wayar ta shiga zuba ihun farin ciki,tana taya yar uwarta murna,
"Ki ce tun yau na fara kiran ki da Hajiya Maijiddarh"

Dariya tayi"kai Aunty Atika "
"Dama ina da ƙawa yar Sudan bari na kira ta na maki bukin gyaran jiki"

"Ai kuwa da kin taimake ni"
"Ke dai ki jira gamu nan zuwa"
Daga haka ta sauke wayar tana kuma niman number kawayen ta domin sanar dasu,

Itama a bakin Amira ta ji batun Bikin,duk da taji abun a ranta wani iri,amma sai kara ɗaukar ƙuduri tayi akan kafin bikin ta samu abin harinta ta bar gidan,can su kara ta abin su,

Tun daga lokacin da aka sanar da wannan bikin basu kara samun hutu ba domin yanda ake ta faman gyaran gida ana sake sabon fenti shiya_shiya,

Kuma tundaga lokacin daya shake mata wuya basu kara haɗuwa har yau da ya rage saura ƙwanaki uku bikin shi,

Kira ne na gaggawa ya shigo wayar ta daga VIP,sai dai bansa me yake faɗa mata ba amma abu ɗaya kawai naji tace shi ne "me kake nufi da yau Kaka zata sallame ni a aiki" da ganan kuma sai naji tace"yanzun? Sai kuma ta ajiye wayar,
Kallon Agogon bango tayi,wanda ya nuna ƙarfe goma na safiyar ranar Talata,
Riga da Siket ne a jikinta wanda ya zauna mata cas ajiki dan kayan ma har yaso ya dan matse ta,dan Amira ce ta bata,kuma ta dan fi Amira kiba kaɗan,
Bata iya saka ɗankwali ba dama kuma sumanta ta kama shi da ribbon ne,dan haka hijabinta mai dan jirma ta saka ta fita tare da daukar wannan katin na buɗe ƙofa ta nufi shiyan mazan gidan,
Tana zuwa ba tare da shakkun komai ba tayi ammafi da katin wurin buɗe ƙofar ta shiga kanta tsaye,ba tare data damu data kulle kofar ba,

Kallon ta yake rike da goran ruwa a hannun shi,kamar yadda itama take kare ma shi kallo,

Wannan karon babu riga a jikin shi,gaba ɗaya tana kallon farar fatan jikin shi,wanda yake a cike ko ina yake,yayin da alamun ƙarfi ya gama bayyana a jikinshi wanda Kirjinsa babu ɗigon suma ko dis,

Ganin kallon da take masa ne yasa cikin tsananin bacin rai wanda ya nunka wanda yake ciki ya nufota a hargitse,"wai ke wata irin jahila c....

Kafin ya karasa faɗa ta shire hijabin jikinta ta yar haɗe da ribbon wanda yayi sanadin saukowar sumanta har gadon bayanta,
Yana isowa daf da ita kafin ya ƙarasa faɗin abinda ke bakinsa sai ji yayi ta shige jikinshi tare da bashi kyakkyawar runguma tana haɗe bakinsu wuri ɗaya,

Duk yanda yaso ya kwace bakin shi acikin nata ta hana shi ta hayan kin bashi dama,wani irin tsotsa take ma harshen shi,yanda kasan wacce bata San dawa take tare ba.......... 🤭

🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*29*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Duk yanda ya so ya kwace bakin shi a cikin nata ta hana shi ta hanyar ƙin bashi dama,
Wani irin tsotsa take ma harshen shi yanda kasan wacce bata san dawa take tare ba,

Cikin zafin nama da jarumta ya dago ta daga jikin shi,wannan ne karo na farko a rayuwar sa da mace ta samu galaba har haka a kansa,kuma wannan ne karo na farko daya taba ɗaga hannu ya Mari wata mace kamar yanda bai jira komai ba ya sauke mata lafiyayyen Mari a saman farar fatan fuskarta,

Hannu yasa ya shiga goge baki tare da jawo tulin Tissue paper ya shiga goge bakinsa dashi,sam hankalin shi baya kanta yana kan yanda zai yi ya taimaka ma kanshi ta hanyar goge najasan data saka mashi,

Daukar hijabinta tayi fuskanta fes cikin farin cikin halin da taga ya shiga"ina fatan yanzun na tabbatar maka da ƙwarin gwiwa ta? Ta faɗa tana daga mashi gira daya,
Juyawa tayi ta shiga takawa a hankali har wani rausaya take yi tsabar farin ciki,sai da takai bakin kofa sannan ta kuma juyowa"Excuses me"

Juyowa yayi da rinannun idanun shi ya sauke a kanta,wanda ita kanta sai da gabanta ya faɗi,amma tsabar tsaurin ido irin na Biba sai sakin murmushi tayi tace"you Smell nice "tana gama fadar haka ta kashe mai ido daya tare da barin ɗakin,wanda Allah ne kaɗai yasan irin juriyar da tayi wurin gudanar da wannan aikin,dan zuciyar ta tsabar zillo ji take kamar zai fito ta baki,dan haka tana fitowa dakin bata jira komai ba ta kwasa a guje sai shiyan su,tana shiga daki ta kulle kofa ta saka Key,
Jingina tayi da jikin ƙofar ta na sauke numfashi ɗan ji take makar biyo ta zai yi,zamewa tayi ta zauna a wurin tana tunanin makomar ta,idan har yau Kaka ta kore ta a gidan ya makomar aikin ta,me kuma makomar rayuwar ta.

Gabadaya he is speechless yama rasa me ya kamata yayi,ji yake makar yayi hawaye tsabar bakin ciki,
Yanzun kenan duk tattalin kanshi da yake yi ya tashi a banza kenan?domin ita ce mace ta farko data fara sumbarta shi,tuna ranar daya fara ganin ta tana shan Segret yayi,da kuma kwana uku da suka wuce,ai nan take yaji hanjin cikin shi ya murda,cikin hanzari ya shiga bayi ya fara kwara Amai tamkar zai amayar da hanjin cikin shi.

*Bayan Awa Biyu*

Gabaɗaya ta tashi hankalin Aunty Atika da ta zo gaishe ta,saboda tana shigowa ta isketa zaune tana faman rusa kuka,kuma tayi lallashin har ta gaji taki faɗa mata meke faruwa,
"Dan Allah Kaka ki faɗa min me ke faruwa,wai ko dai rasuwa aka yi?

Fyace majina tayi da tissue paper" Yanzun nan ki kira min yaran nan gaba ɗayan su"

"Wasu yara kenan kaka?

" Ki kira min Mustafa da Abbu Sufyan da Amadu,ke kowama na gidan nan ki kira min shi yanzun nan babba da yaro ina son ganin su"

"Too,Allah dai yasa ba wani abu bane" Daukar wayar ta tayi ta shiga kiran su daya bayan daya,waɗanda ma basu kusa duk cawa suka yi ga sunan zuwa.

Kafin wani lokaci ahalin gidan babba da yaro sun halarta a wannan falon,kowa hankali a tashe ganin yanda tsohuwa ta tashi hankalin ta,gashi kuma sai kuka take yi,
Da yar dai su Goggo da Hajiya Rahama suka samu tayi shiru,

Dagowa tayi ta kalle ko wanne su,sai dai bata ga mutum ɗaya ba,"Ina Sirajo? Ta tambaya tana kallon Nurudeen,

"Na kira shi yace gashi nan zuwa"

Jinjina kai tayi"Salmanu, Zainabu,Hadiza,Khadija, Bilkisu,Amira,ku tashi ku tafi wannan maganar da zan yi ba naku bane,na iyayen ku ne da yanyin ku"

Nanfa suka shiga turo baki dan wallahi ba haka suka so ba,amma ba yanda suka iya dole suka fita,

Kallon Maijiddarh tayi"Je ki kira min Habiba"

Tashi tayi tana ƙoƙarin fita sai gashi ya shigo,sanye yake da farar shadda a jikin shi,yayi matsifar kyau sai kamshi yake zubawa,sai dai ko kaɗan fuskar shi babu fara'a kuma ya ɗan faɗa kaɗan,dan fuskar shi ya nuna ramar da yayi,

Sallamah yayi sannan ya gaida iyayen nashi,ya zauna kusa da Ibrahim,

Tunda Maijiddarh ta sanar da ita kiran Kaka gabanta ke matsanancin faɗuwa,wanda ta san bai rasa nasaba da rasa aikinta da zata yi,
Sai dai ganin irin taron dake falon ne yasa tsoron karuwa,dan haka bayan ta gaida su wadanda zasu amsa suka amsa sannan ta koma gefe ta rakube.

Maida kallon ta kan shi tayi"Sirajo "ta kira sunan shi,domin tunda ya shigo ya zauna kanshi a duke yake,
Chapter 27 · 0% Book details