← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 96

Sashe 84

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin firgita na Dago kai ina kallon shi,ba kowa bane face mijin Goggon yara,wato Habib mijin kanwar su,
Na tsorata da ganin shi,saboda babu abinda ke haɗa ni dashi sai gaisuwa,

Cikin kwantar da murya yace ki yarda dani ni nasan komai tun kafin auran ki,ni cikakken dan jarida ne,kuma aboki ga mijin ki sai dai ganin hanyar daya zaɓa ne yasa bama shiri dashi,

Cikin kuka nace ya taimaka min na gudu na koma garin mu,bana son zama dashi,

Dariya yayi sannan yace lallai ashe so kike ki mutu ke da dan ki,domin duk in da kika shiga a wannan duniyar sai sun nimo ku saboda wannan takardar,sai dai daki tura makiyin ki nisa ai gara ki jawoshi kusa,ki zauna tare dashi ta hakan ne kawai zaki iya tsira,idan har kin amince zan taimake ki"

Da wannan shawarar na yarda domin ba ni da hanyar daya wuce haka,a kuma wannan ranar na samu labarin mutuwar su da fadawar Ummi doguwar suna,
Nayi kuka na tashin hankali wanda naji kamar na kashe kaina nima,sai dai idan na tuna Suraj dole nake dakatawa,ni ce silar komai,ni najawo komai,idan da ace ban amince da waɗannan hotunan da na gani ba kula da hakan bata faru ba,
Habib shi ya bani shawara kar na ce zan je na zauna tare da Ummi in zauna tare da Safwan kin dinga bibiyar rayuwar shi ina tara hujjoji ta yanda zan san duk wani mai hannu a ciki,in kuma raini dana,
Ana cikin haka ne wata rana ya kira ni akan nazo wani wurin hutawa na same shi,to anan ne na iske shi da wata mata da yarinya yar shekara biyar suna zaune,gaisawa muka yi da matar har na dauki yarinyar ina mata wasa da tambayar me sunan ta,nan matar wacce daga gani kasan yar duniya ce ta bani amsa da Salma,ko minti biyar basu kara ba naji tace mai su sun tafi Minna sai ya zo,
Bayan wucewar ta ne nake tambayar shi me haɗin shi da irin waɗannan matar,shine yake bani labari a kan matar matar aure ce,sai dai shi ya aikata babban kuskuren da bai taɓa ɗauka zai yi shi ba a rayuwar shi,ita taja hankalin shi suna tarayya tare,sannan wannan yarinyar da nake gani yar shice,sunan ta Ummi Salma,anan ya bani Address din garinsu da gidan da suke,
Cikin jin haushin abinda ya aikata nace masa me yake buƙata nayi da wannan address din,a lokacin murmushin yayi mai tattare da damu yace,kawai dai na baki ne saboda wata rana,ko da bana nan komai daɗewa dan Allah ki duba ta,ba sai ta san komai ba game dani,amma dai bana son tayi rayuwa irin na mahaifiyarta,daganan ya bani wani karamin Envelop,wannan duk wani abinda na bincika ne na kuma samu,sai dai kina iya ci gaba da bincike daga in da na tsaya,
Ko godiya ban mai ba tsabar haushin tarayya da matar aure da ya fadamin yayi na wuce,wannan shine gani na dashi na karshe shima domin tun daga lokaci shima aka ni me shi aka rasa,wasu suce ya gudu ne saboda matar shi,wasu suce ya mutu me a wani wuri,Allah kadai yasan abinda ya faru dashi,

Bayan faruwar haka dole na ajiye duk wasu makamaina na mai da hankali wurin ganin na inganta rayuwar Dana ta yanda zai zamo jajirtacce,domin ba zan iya faɗan ni kaɗai ba,ina bukatar matayi,sai dai kowa ba abun yarda ba ne,
A lokacin da Suraj ya kammala karatu a lokacin muka soma fuskantar wani matsalar domin ta ko'ina aiko mana da yan leken asiri ake yi,sai dai ina saka shi yana iya baƙin ƙoƙarin shi wurin kauce masu,
Ana haka wata rana za shi wa'azin Niger State na roki alfarman akan ya duba min Yar Habib na bashi Address din da ya bani,
Bayan yaje da kwana biyu sai gashi ya dawo min da labarin sun tashi daga wannan Address din amma yayi ƙoƙarin ganin ya same su,kuma a ranar aka ɗaura ma yarinyar aure,har ma ya taho min da hoton ta,nayi farin ciki sosai,sai lokacin ya tambaye ni wacece ita,ban faɗa mashi komai ba na dai ce mashi wata ce,ganin ban son faɗa mashi ne ya bar maganar,

Bayan wani lokaci sai gashi wata rana ya kawomin wani post da su ATM card sai kwalin sigari,cikin yanayin kokonto ya nuna min,Ammi wannan kamar yarinyar da kika sa nayi bincike a kanta,
Amsa nayi na duba,tabbas ita ce,sai dai ganin wannan sunan ta Biba yasa na ni ma na shiga kokonto,na dai karɓi kayan na bar maganar,
Na samu labarin cewa suna ƙoƙarin kawo mana wani mai aikin dana bincika sai na gane ita din ce zata shigo,a nan ne nasa shi ya fara min bincike akan ka,har na gano tabbas ita ce,
Ta gefe ɗaya kuma na gane ba kowa bane yake turo su face Abbu Safwan,shi ne VIP,shine ke saka su komai,sai dai shima kuma yana da Oga,sannan da haɗin bakin danshi Shamsuddeen,dashi aka haɗa baki wurin yi ma Suraj sharrin kisa a legos,sannan da taimakon shi wurin yin munakisa Suraj ya auri Biba,duk da saka hannun shi,sannan Abbu Safwan yana tare da matar shi mahaifiyar Shamsuddeen,amma a idanun duniya gani ake sun rabu,yanzun haka duk wani shaida daya kamata mu haɗa mun haɗa har da na hatsarin daya faru da Ummi,na gode.

Kara_kara_kara,ai kuwa zan so kuga yanda koto ya rikice,kowa kallon dan uwan shi yake hankali tashe,yayin da dage gefe ɗaya kuma zufa ya shiga jika wasu,wannan ba kamar koton Nigeria bane,wannan suna amfani ne da karfin hujja da dokoki,

Ta gefe ɗaya kuma tunda ta dukar da kai take hawaye,domin tabbatar bata taba tsammanin kaddara zai kai ta nan ba,mahaifinta shine mijin goggon yara,sannan Abbu shine VIP sannan shi ya kashe Ummi ta,tabbas sai yanzun ta tuna shine ya buga mata ƙarfe a kai,sakamakon haka yasa ta manta komai daya faru a wancan ranar sai wayarta wanda tace Suraj ya nima,
Dago kai tayi ta kalli in da yake........
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*84*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

"Daya daga cikin Alkalan ne yace ko zamu iya ganin shaidun da kuke dasu?

Suraj dake zaune a gefe ne ya tashi ya mika kudi mai dauke da duk wani baya nai da suke buƙata,video din shi sakawa a kayi yayin da komai ya fara baiyana kamar film,duk wani shiri da suka gabatar da abinda Pa ya shiya,shi ne silar komai shi kuma ya Daura su akan hanyar da suke,

Kotu ne ta bukaci in akwai mai magana acikin su sai yayi,

Abbu Sufyan ne ya fito cikin hawaye ya fara magana,tabbas nasan son zuciya shi ya kai ni ga wannan halin da nake ciki,Pa abokina ne tare dashi muka yi karatu a can Sauth Africa,shi ya nime taimakona tare da nuna min hoton Hafsat,ni kuma tunda na ganta da kuma jin irin kudin da zan samu na amince da aikin,tabbas na aikata kuskure wanda nasan baza taba yafe min ba,nasan da zaran mun koma ba ni da damar da zan sake ganin ta har na nime tafiyarta duk da nasan ba yafe min zata yi ba,ina rokon gafaran ku"

Cewa akayi ko Pa yana da magana,
Shi babu alamun dana sani ko dar tare dashi,sai cewa yayi"ai Baba shi ya ja maki domin shi yara nuna banbanci tsakanin ni da ke,ni da nake namiji ne yasa bai Bani wannan kyautar ba sai ke,dan haka ko yanzu na fito sai na ga bayanki,kuma Diamond yana wuri na ba zan taba fadar inda yake ba"ya karasa faɗa yana nuna Grandma,

Cikin kuka Nadiya ta mike"ni na San inda yake zan faɗa komai zan fada maku in da yake,Pa na yi dana sanin kasancewar ka mahaifi a gare ni,tana gama fadar haka tabar Koton da gudu tana kuka,

Mai shari'ar ne ya buga wannan sandar yana fadin a natsu,
Ganin yanda Pa ke kiran sunan Nadiya da fadin sai ya kashe ta idan ta faɗi wani abu,

Sai da aka natsu sannan yaci gaba da faɗin "abisa ƙwararrun hujjoji wannan Koton ta yanke ma Pa hukuncin rataya,tare da mukarrabansa,
Shi kuma Abbu Sufyan saboda haɗa hannu dashi zamu mika shi ga hukumar kasar shi domin ta zartar masu da hunci shi da Danshi,
Sannan hukuma zata yi ƙoƙari wurin ganin ta dawo ma da Dr Aisha dutsen Diamond din ta na gado,

Daga Su Nurudeen dasu Dady duk kuka suke yi ganin yanda aka saka ma Abbu Sufyan sarka,babu tonon asiri da yafi wannan,
Da sauri Dady ya karasa in da Ammi ke tsaye" Dan Allah Ammi ki yi hakuri a sassauta ma Dan uwan mu,ki yafe masa"

Kallo data taimasa ta kauda kai,"ku bari idan na dawo Nijeriya zamu magana "

Tana gama fadae haka ta shiga tura Grandma a keken ta suka bar wurin yayin da Biba ke biye dasu a baya.

Tunda suka isa gida ta shiga daki kulle kofa ta kwanta tana faman rusa kuka,zuciyar ta zafi yake yi,ji take kamar ta samu wani abu wanda zai gusar mata da hankali ta sha,ba tada komai sai dai kuma ta riga ta tuba ga Allah,ranar haka ta yini idanun ta sun kumbura saboda kuka gaba ɗaya bata cikin walwala,ko da Ammi ta aiko akan ta sauko su ci Abinci cewa tayi ta ko shi,ganin har yamma bata fito bane yasa ta shigo dakin da kanta,
Zama tayi a bakin gado in da take kwance,sai dai ba bacci take yi ba,
Shafa kanta tayi"kina fushi ne a kan kin faɗa maki da nayi?

Girgiza kai tayi hawaye na sake saukowa daga cikin ramin idanun ta,

"To faɗa min menene?
Chapter 84 · 0% Book details