← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 96

Sashe 55

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jinjina kai yayi"dan Allah ka yi min ƙoƙarin kar ta rasa komai nata,ka yi min Alkawari "

"Na maka Alkawarin zan yi iya kokari na,kai ma sai ka dage da addu'a"

Hannun shi Dady ya yawo suka fito"tunda har tana karkashin kulawar likitoci kuma ba zasu bari a ganta ba,ya kamata kaje gida ka yi wanka ka huta"

"A'a ba zan iya tafiya ba Dady"

"Ba nason musu tashi muje"

Suna fitowa suka hadu da Hashim da sauri ya karasa in da yake"me ya faru dazu,wa ya aikata mata haka?

"Ban sani ba nima,amma abu ɗaya na sani shine daga Kotu dazu ina tsaye sai gashi tazo ta same ni wai na bi wancan bakin motar,shine na bi su har wani unguwa tace nayi parking a gefe zata shiga ta fito,

Daganan dai Nasan ta shiga amma bansan me ya faru ba sai ganin ta nayi ta fito da gudu wasu maza na binta tana shiga mota ni kuma naja,shine tace na kawota wurin ka akwai maganar da zata fada maka,iya abinda na sani kenan "

Lumshe rinannun idanun shi yayi ba tare da yace komai ba ya juya ya buɗe mota yashiga,in da Dady ke jiran shi,wallahi wallahi duk mai hannu a cikin wannan lamarin koshi waye ba zai taba barin su ba,domin idan har ta sanadiyar shi wani abu ya same ta ba zai yafe ma kanshi ba,
Dafe zuciyar shi yayi dake mai zafi,idan har ya tuna rabuwar su da kuma abinda ta mai a jiya sai yaji hankalin shi ya ƙara tashi,
Har Dady ya tayar da mota yace masa yana zuwa,kiran Hashim yayi "Ina jakkan ta,a wani Hotel take zaune?

" Ba Hotel take zaune ba a gidan Oga na take zaune"

Cikin mamakin daya kasa boyuwa yace"gidan oganka kuma"fuskar shi na nuna wani yanayi,

"Eh amma shi yana Abuja ita kaɗai ce a nan," Nan ya faɗa mashi sunan unguwar da number gidan,sai jakkan ta daya miko mashi,

Jan motar Dady yayi suka bar Asibitin zuciyar shi cike da tunanin me take son ta faɗa mashi.

Suna shiga Hotel din Dady ya amsar mashi makullin daki kusa da nasu ya bashi,

Wanka yayi ya sauya kayan jikin shi,
Sannan ya kunna wayar shi da suka mai da mashi,

Number Ammi ya duba ya danna ma kira,
Ai kuwa makar dama jira take yi ta dauka da sallamah,

Sunan shi ta kira domin son tabbatar da ko da gaske din shine"Suraj "

Ji yayi idanun shi sun cika da hawaye"Na'am Ammi"

"Alhamdulillah,Allah na gode maka Alhamdulillah, yau zaku dawo ko?

" Umm um "ya faɗa yana share hawayen shi,

Dan shiru tayi kafin tace" Me ya faru,na yana ji kamar kana kuka,why are you Crying?

"Ammi tsoro nake ji"

"Nasan duk abinda ya girgiza wannan zuciyar har ya samu nasarar tsorata shi ba ƙarami ba ne,faɗa min me ya faru ?

" Nan ya shiga sanar da ita abinda ke faruwa har karshe kamar yanda Hashim ya sanar dashi"

"To su waye ta gani ta bi,me kuma ya faru a cikin gidan,me take son ta fada maka?

" Ammi koma dai menene ba karami bani na tabbata"

"Gobe zan zo insha Allah zan biyo jirgi,sannan ka kwantar da hankalin ka insha Allah zata ji sauki za'a dace"

"Allah yasa Ammi" Daganan sallamah suka yi ya kashe wayar ya kwanta,sai dai duk yanda ya so yayi barci ko ya huta kasawa yayi,dan haka tashi yayi ya jawo jakkan ta ya buɗe,hannu ya saka a ciki sai gashi ya ciro wayar ta,sannan ya zazzage jakkan gaba ɗaya saman gado,
Takardu ne a ciki sai man baki da sauran kayan kwalliya dai na mata,sai makullin gida, mai da komai yayi cikin jakkan ya adana,
Ranar bai samu yayi bacci ba domin kukan shi da godiyar shi ya rinka mikawa ga Allah,
Ba ya so ya rasa ta ko ta rasa wani ɓangare na jikin ta,

Washegari ma ko kafin su Abbu su tashi bacci shi har ya wuce Asibiti,sai da suka duba dakin shi a kulle shine suka kira shi ya sanar dasu ai tun ƙarfe bakwai na safe yana Asibiti,

Abbu ne yace"ka kuwa karya "

Dan shiru yayi kafin yace"yanzun zan karya dan na ga akwai wurin cin abinci a asibitin "

Cikin yana yi na dan faɗa faɗa yace"kasan ƙarfe nawa yanzun kuwa?

Kallon agogon hannun shi yayi wanda ya nuna ƙarfe goma da rabi na safe "Sorry Abbu"

"To ka dai dinga kiyayewa muma gamu nan zuwa"

"To sai kun iso" Ya faɗa yana sauke wayar,

Lekawa yayi ta glass din dake tsakanin su a I.C.U,tana kwance yanda kasan gawa babu ta inda take motsi sai na'urorin dake aiki a kanta wanda har saman kanta aka mammanna wasu karafe ƙanana,

Ji yayi an dafa shi daga baya,
Juyawa yayi,ganin Doctor ne yasa ya sauke numfashi,
"Kana son ka shiga ka ganta?

Girgiza kai tayi" Ba sai na shiga ba"

"Ka tabbata?

" Umm,yaushe za'a shiga aikin?

"Nan da ƙarfe biyar na yamma"

Lumshe ido yayi ya buɗe waɗanda yake ji sun mai matukar nauyi "ina fatan dacewa"

"Da yardar Allah"

"Zan je na dawo zuwa anjima"

"Ba damuwa ranka ya daɗe"

Juyawa yayi ya wuce,sai da ya je yaci abinci sannan kai tsaye ya wuce unguwar da Hashim ya mai kwatance,har ƙofar gidan kuwa aka kaishi,

Da makullin daya dauko a jakkan ta dashi yayi amfani ya buɗe har cikin falon,

Sai da ya gama ƙare ma falon kallo wanda yake tsaf sannan ya shiga dakin da ya gani a buɗe,

Daga dukkan alamu a nan take kwana,dan ga dakin nan da kayan ta har a saman kushin,daga dukkan alamu bata kyara dakin ba ta fita,
Gaban madubi ya tsaya wanda ke dauke da man shafawarta sai turarukan jiki,
Daukar daya yayi ya buɗe ya fesa a iska ya lumshe ido yana shakar ƙamshin,tabbas shi ta saka shekaran jiya data zauna a jikin shi,

Wani takarda mai ɗan girma ya gani a saman madubin,bangon littafin ya ja hankalin shi har ya shafa littafin,

Haka kawai yaji yana son buɗewa yaga me a rubuce,
Bin umarnin zuciyar shi yayi ya buɗe wanda shafin farko kyakkyawar rubutunta wanda yake jere bisa tsari yaga an rubuta *MY DESTINY* ( *Kaddarata* )da manyan harafi,
Ya dau sakanni yana mai maita sunan a zuciyar shi kafin ya buɗe shafi na biyu,
Abinda ya gani a rubuce ne yasa ya mai da takardar ya rufe ya ɗauka sannan ya rufe gidan ya koma Hotel din daya sauka,
Yana shiga daki hawa saman gado yayi ya zauna tare da kara buɗe littafin wanda daga dukkan alamu tarihin asalin rayuwar ta ne a ciki wanda shi kanshi zai so yaji wacece asalin Biba da kuma Ummu Salma,me alakar dake tsakanin suna biyun nan,menene ya faru da rayuwar su da kuma kaddaran dake bibiyar su.....

🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*55*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Shafi na biyu daya bude a cikin littafin,ya shiga bin abinda ke rubuce daki daki makar haka:A ranar Laraba sha biyu ga watan Agusta shekara ta dubu biyu da ishirin da huɗu,da misan ƙarfe goma na safe,iska ne mai matukar daɗi ke kadawa yayinda tsuntsaye ke tashi daga wannan bishiyar zuwa wannan,ta gefe ɗaya kuma idan har na kalli gajimare abin na matukar kayatar dani,saboda ina son kallon sararin samaniya ko dai lokacin haɗari ko kuwa lokacin da taurari ke baiyana,na kan tsince kai na cikin tsananin farin ciki kamar yau,
Tafiya nake ina juyawa yayin da kaina ke kallon sama,sabanin sauran mutane dake tafiya suna kallon gabansu ko gefe,

Ji nayi cikin zafin nama da karfi an jawo ni baya,wanda sai da nayi tangal_tangal kafin na tsaya da kafafuna,
Cikin masifa ya fara faɗa "wai ke wata irin yarinya ce da magana daya baya mata,ta yaya zaki saka kai a Titi ba tare da kin duba ba,kalla yanzun saura kaɗan mota tabi ta kanki amma ko sani baki yi ba"

"Na sani Mana yaya"

"Kin sani shine zaki shiga titi haka?

Dafa shi tayi" To me yasa zan wani damu da kallon Titi ba yan ina tare da ku"

"Me kike nufi"

"Ga ka ga Yaya Abdulmajid,ai kune ido na bana bukatar yin amfani da nawa"

Karamin tsaki ya ja yana jinjina shirme irin na Ummu Salma "

Jan kunnen ta yayi da ƙarfi "ai kuwa shi yasa baki gajiya da faɗawa kwalbati"

Ihu ta saka tana kiran sunan "Ya Majid"

Da sauri wanda aka kira da Majid din ya juyo yana sallamar Abokan shi da suke tare ya karaso in da suke"me ya faru "ya tambaye dan uwan nashi dake ke rike da kunnen ta har yanzun,

" Sauran kaɗan mota ya bige ta"

"Kai kana ina har mota zai bige ta,hankalin ka na ina,shi yasa nace ai ka bita a baya kana kallon hanya," Kwace ta yayi"sake ta ai duk laifin ka ne"

Buɗe baki yayi yana bin su da kallon mamaki,duk da wannan ba shine bane karo na farko ba,in dai zata fita sai an haɗa ta da wani a cikin su,saboda tsabar kanta bai iya tsayawa wuri daya,idan kuwa ka bari taji ciyo ka shiga uku ko a wurin mama da sauran su,

Yana biye dasu a baya har suka shiga cikin unguwar su wanda yake na matsakaita ƙarfi ne,
Tunda suka shiga layin su duk inda suka gifta in da akwai manya a wurin sai sun gaida su,
Su kuma suna amsawa cikin sakin fuska,

Da haka har naga sun doshi Get din wani makeken gida wanda kaf unguwar babu gida mai girma da tsaruwa irin shi,
Kwankwasa karamin ƙofar gidan suka yi sai gashi mai gadi ya fito ya buɗe masu,
Chapter 55 · 0% Book details