← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 96

Sashe 12

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari da Asuba,tana barci taji wayarta na ƙara kamar zai fasa mata kunne,
Tsaki taja tana jawo wayar tare kashewa,
Ƙara kira aka yi,wanda sau uku tana kashewa,amma sai ƙara kira ake yi,
Ana huɗun ne dai ta ɗauka cikin jin haushin damunta da ake yi tace"pls abar ni in yi barci "

Daga ɗayan bangaren taji ance"tashi zaki yi ki fara gyaran falo ki daura abin kari "

Cire wayar tayi daga kunnen ta tana duba ko ƙarfe nawa ne "ƙarfe biyar dai dai yanzun"

Cikin tsananin gajiyawa da maganar tace"A'i ba zan iya ba barci nake ji"

"Dole zaki tashi domin haka aka tsara maki,dole sai kin shiga jikin mutanen gidan kafin ki samu ki cika aikin ki,dan haka tashi ki fara gyaran gida"

Ranar haka tayi kyaran falon har kicin tana hawaye,domin Allah ya gani ita wannan aikin azabtar da ita ake,sai da ta kammala har karin safe kafin ƙarfe bakwai,
Zuwa lokacin ji take kamar zata faɗi tsabar gajiya da ciyo da jikinta ke yi,
Ruwan Tea kawai ta iya sha sannan ta fito harabar gidan,
Kalle_kalle tayi,sai dai ba kowa a tsakar gidan,dan haka zagayawa tayi ta baya in da sai gashi tana hangar ɓangaren samarin gidan,
Karema tsarin jeren ɗakunan wurin kallo tayi,kafin naga ta nime wani dan dutse nisa kaɗan da wurin ta zauna,
Hannu naga tasa kasan hijabinta sai gashi ta ciro karan sigari ɗaya tare da abin kunnawa,
Tunda ta saka abiki ta fara zuka har wani lunshe ido take tana jin wani natsuwa na sauko mata,haba ta yaya za'ayi ace wani tabar shaye-shaye,ai gara kawai a cillata rijiya,

Jin kamar karan tafiya ne yasa ta dago kai a firgice ta na kallo wurin,
Sai dai cikin rashin sa'a idanun su ya faɗa cikin na juna,wanda ba ƙaramin firgita tayi ba.......

🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*14*

*Na mai da Littafina mai suna a sama na kuɗi,tare da JAURO,idan kina son daya 300,dari uku,guda biyu kuma da Yar Tsanar Zinari tare da Jauro,dari biyar 500,ko wani daya dari uku*
*Hauwa Umar,Zenith Bank, 2284905309*
*ko katin waya na MTN,tare da turo shedar biya ta 08141644865*

Cikin sauri ta maida hannun ta baya tana fuskewa,tare da ɗauke idanunta cikin sana,

Shima ɗauke idon shi yayi a kanta yana turo kofar daya buɗe ya shege tare da maidawa ya rufe,
Banɗaki ya shiga yayi wanka,sannan ya canja kaya zuwa riga da wando na ratsattsen shadda fari kar,sai ɗaukar ido yake,
Yana gama shiri ya fito daga bangaren su,ya nufe shiyan Ammi,
Koda yayi sallamah babu kowa a falon dan haka samun wuri yayi ya zauna yana daddanna waya,daga dukkan alamu abu mai muhimmanci yake yi,

Sam bata lura da mutum dake zaune a falon ba,da fari dogun tsaki ta fara ja tana rike Kwankwason ta,"waiyo Allah baya na,Allah ya tsina ma VIP,gara aikin komai da wannan"ta faɗa tana komawa kicin,

Jin tsinuwar da aka yi yasa ya dago kai dan ganin wacce tayi wannan lafazin a cikin gidan su,domin yasan tsunuwa ba ɗabi'ar su bace,sai dai ko da ya dago bai ga kowa ba,tsirama hanyar kicin din ido yayi na ɗan lokaci kafin yaci gaba da abinda yake yi,
Ammi ce ta fito falon domin ta san cewa da safen ne zai wuce dan zai gudanar da wa'azi a Jos,
Tunda ta hango shi zaune ta saki murmushi,wato dai ba zai shigo dakin ta ba,domin haka ɗabi'ar shi take,baya taɓa shiga dakin ta da sassafe haka,

Jin takun takalmin ta ne yasa ya ajiye wayar hannun shi yana mikewa,karasawa yayi inda take ya riko hannun ta yana sumbata,"Good Morning Ammi"

Shafa kanshi tayi"Morning Sweet heart,Allah ya Albarkaci rayuwar ka"

"Amin Sweet Ammi"riƙo mata hannu yayi suka zauna kan kushin,

Ɗan ɗaga murya kaɗan tayi ta na kiran sunan " Biba,Biba"

Da sauri ta fito kicin tana goge hannu tare da amsawa ta karaso in da suke tana amsawa,cikin girmamawa ta tsugunna "Mam gani"

"Ɗan Allah ki kawo ma yaro na kofin shayi, amma karki sa madara da Sugar,sannan kar kisa tafasasshen ruwa,ki yi amfani da wanda ya ɗan fara hucewa amma ba sosai ba"

"Yes Mam" Ta faɗa tana satar kallon shi,
Da sauri ta dukar da kai tana mikewa,a zuciyar ta tana raya,na shiga uku,ba dai wannan bane yaron matar nan oh young ustaz kenan,hakan na nufin akanshi da baban shi zata yi aiki, ya Allah gashi ta gwabsa tun a matakin farko,me yasa da ya zuba mata ruwan zafi bata haƙura ba,Allah ma yasa dazu bai ga tana shan sigari ba,kai data shiga uku in dai wannan aikin ya lalace a wurin Vip.

Ta gefen ido yake kallon ta tun lokacin da tsugunna a gaban Ammi har ta koma kicin,
"Ammi wace wannan? Ya tambaya yana cigaba da danna waya.

" Sabuwar mai taya ni aiki ce wacce kaka ta dauko "

"Ammi bana son ta,ki sallame ta,zan sa asamar maki wata mai hankali"

Kallon mamaki take mai,domin tunda take dashi wannan ne karo na farko data taba jin yayi magana akan al'amarin daya shafi cikin gida,dan haka ƙara maida hankalin ta tayi kanshi,tare da amsar wayar dake hannun shi wanda yake daddannawa ta ajiye gefe "yaro na,faɗa min,shin akwai wani abin ne,ko ta maka wani laifi nr?
Ɗan murmushi ya sakar mata ganin lokaci ɗaya tana ƙoƙarin shiga damuwa" Ammi na,ki kwantar da hankalin ki,babu komai,kuma bata min komai ba,kawai dai bata min bane Ammi,ban yarda da yarinyar ba,kamar akwai abinda take ɓoyewa "

Ajiyar zuciya sauke"batai maka ba,kuma kana zarginta "

Jinjina kai yayi.

"A ganin dana ma yarinyar ban fahinci wani abu tattare da yarinyar ba na damuwa ba,tana da kokarin aiki daidai gwargwado,na yaba da tsaftarta da kuma girkin ta,sai dai ban san Me ka hango ba a tattare da ita wanda yasa harka fara zargin ta,wanda ni ban hango ba,abin mamaki ban taba jin kace wani bai maka ba sai yau,ban sani ba ko zargin da kake mata ne yasa kace bata maka ba,amma dai na san kasan cewa babu kyau kace halittar Allah bai maka ba,kuma insha Allah dana kara samun sauki da yardar Allah zan sallame ta,tunda kaka ce ta kawo ta,dole nayi haƙuri da ita na dan wani lokaci,kuma ni ma zan saka ido a kanta "

"Insha Allah zan kiyaye Ammi," Kafin ya kara magana sai gata ta fito hannun ta riƙe da ƙaramin Tea plate mai dauke da ƙaramin kofin shayi,
Ajiye mashi tayi a gaban,ba tare data dago ba ta mike zata wuce,
Ji tayi ya ce ma mamatshi "ki yi hankali da ita,sannan ki fara kasa ido a kanta,da zaran kinga abinda baki yarda dashi ba dangane da ita ko da kaɗan ne,ki sallame ta,karki damu da kaka ta kawota,ni zanji da komai"

Iya nan wakai taji ta karasa shiga kicin,

Jingina tayi da kofar kicin ɗin,wato dai daga dukkan alamu da ita yake yi,zargin ta yake yi,kuma ya sanar da mamarshi,Allah yasa bai sanar da ita batun shan tabar ta ba,dole ta fara takatsantsan ta samu ta karasa wannan aikin,
Komawa tayi ta bakin ƙofar fitowa ta labe da kyau ta yanda zata iya jin me suke faɗi,

"Idan ka tafi yaushe zaka dawo"

"Nan da kwana uku insha Allah,domin a local government uku zanyi wa'azi a garin"

"Pls Suraj ka dunga saka kayan sanyi,domin kasan yanzun lokacin sanyi ne kuma Jos a kwai sanyi sosai,ka dunga shan ruwan zafi akai_akai,kar ka bari mura ya kamaka kasan yanda yake maka"

"Insha Allah Ammi"

Ɗan marairaice fuska tayi"gashi Abbu ku bai dawo ba,kai kuma zaka tafi ka barmu ni da kanwar ka,gabaɗaya in baku gidan baya daɗi,pls karka je ka daɗe "

Ɗan dariya yayi"karki damu Ammi,Abbu ma zuwa jibi insha Allah zai dawi,so karki damu,"

Murmushi ta sake tana ɗan daka tsalle kaɗan tare da dunƙule hannun ta"Yes "tafiya zai yi zuwa Jos kuma har na tsayin kwana uku gashi mai gidan ma baya nan," Waiyo daɗi, this is the right time da zan gama wannan aikin na bar wannan gidan kafin su dawo"
Cikin jin daɗi ta koma kicin dan karasa kife kayan data gama wanke wa,idonta ne ya sauko a kan inuwar mutum,
Ɗan tsayawa tayi jim,tana kallon inuwar,a hankali ta ƙarasa ta jikin windon tana jan labulen windon baya tare da lekawa,tabbas mutum ne ke a lebe a jikin windon,sai dai duk yanda taso ta iya hango wani abu dangane da wanda ke wurin bata iya ganin komai ba,
Komawa tayi ta tsaya tana nazari,kenan hakan na nufin labe ake masu,kenan dai ace ba ita kaɗai bace keda buri a akan wannan aikin,

Da sauri ta zagaya ta ƙofar kicin din ta fita,sai dai cikin rashin sa'a tana isa sai dai hangar bayan na miji tayi,to waye wannan kuma,lallai akwai matsala dole tayi sauri tayi komai kar ya zamana abin harin su ɗaya,
Koda ta koma ta samu harya fita,ita kuma Mam ta koma ɗakin ta,
Yanzun ta wata hanya zata bi ta samu ta fara shiga dakin Abbu kafin dakin wannan ɗan rainin hankalin,
Dole tana buƙatar sanin komai daga nan zuwa gobe,domin iya lokacin da take dashi kenan,gashi daga dukkan alamu wannan matar bamai bari a shigar mata daki miji bane koda ta hanyar shara.
Komawa tayi ta zube kan gado tana runtse ido akan dole sai ƙwaƙwalwarta ta fara aiki,

Yana fita daga falon bayan sun yi sallamah da Ammi,wurin parking ya nufa inda yana isa aka buɗe mai kofar mota ya shiga sannan aka maida aka kulle,
A hankali motar ya fara tafiya dan barin harabar gidan,
Jinginar da kanshi yayi a jikin set yana lumshe ido na wani lokaci,
Motar na gama barin gidan direbobi suka hau kan hanya da kyau,
Gani na yi ya saki wani lallausar murmushi na gefen baki,wanda ba karamin kyau yayi ba,duk da bansan na Menene ba,
Chapter 12 · 0% Book details