← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 96

Sashe 70

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rike hannun ta yayi"ba kiyi komai ba Ammi,kin yi ne dan ki taimaki rayuwar ɗan ki,and na tabbatar da she will understand you,fata na yanzun Allah ya bata lafiya"

"Amin ya haiyu ya kaiyum "

Ya tsanshi biyu ya saka a cikin idanunshi yai gashi ya ciro wani dan abu kamar leda fari tas wanda ya hade da kwayar ido,baka iya sammanin ya saka abu a ido,buɗe wani karamin contena yayi ya saka wannan ledar idanun guda biyu, wanda nan take asalin kwayawar idanun shi suka baiyana,
Rufewa yayi ya mika ma Ammi"komai yana cikin nan,yanzun abu ɗaya ya rage mana mu kammala haɗa hujja "

"Shima dab muke da cimma shi,sai dai ya maganar iyayenta?

Busar da iska yayi yana shafa fuskar shi" Ada nayi tunanin kiran kiran su,amma dai yanxun ina ganin gara mu bari idan an yi aikin ta samu lafiya"

"Eh hakan yayi,yanzun yaushe zaka koma Asibitin?

" Sai bayan Sallah Magrib"

"Ok Allah ya kai mu"

Da Amin ya amsa yana tashi,

Daganan gidan shi ya nufa inda anan su Bala suka saka sabon kukan murnar ganin Ubangidan nasu.

*Bayan wasu Awanni*

Yana fitowa masallaci ko gida bai koma ba ya wuce Asibiti,
Yana yin parking mota kiran Dr na shigowa wayar shi,
Ɗauka yayi yana karawa a kunne,
Daga ɗayan ɓangaren yace"kana ina sir Suraj?

"Gani a cikin Asibiti"

"To kayi sauri ka same ni a ofishi na"

Ba tare daya ce komai ba ya sauke wayar,yana karasa shiga cikin Asibitin,

Yana isa ofishin ƙwanƙwasa kofar yayi domin mutumin ba Musulmi bane,
Umurnin shiga aka bashi sannan ya shiga,
Nuna mashi wurin zama yayi"zauna"

Zaunawa tayi"ina fatan babu wani matsala?

"A'a da sauƙi dai,dama jini muke nima saboda aikin da za'a shiga da ita,shine nake son na tambaye ka,shin a saka mata jinin siyarwa,ko kuma a family za'a samu wanda zai yi donating blood"

"In dai wannan ne babu damuwa zan yi donating blood dina saboda ni (O-) negative ne"

"Yauwa to yanzun zamu tafi LAB domin a fara ɗiban jinin ka a duba,sai a duba nata jinin ita ma"

Mikewa yayi"to mu je,yanzun saura awa nawa a shiga aikin"

"Saura dai mintuna talatin"

Tare suka jera har Lab din in da anan ka ja jinin shi suka fara gwadawa,shi kuma yana zaune a reception,har suka je dakin da take suka dibo jinin ta,

Yana dai zaune yana danne _danne a wayar shi yaga wanda yazo ya dibi jinin ta ya fito da sauri,kafin wani lokaci kuma sai ga wasu manya daga yan Lab din sun zo sun shiga,
Yana dai zaune yana lokacin_lokaci yana duba agogo,a haka sai gashi har an kwashe kusan mintuna ishirin,
Likitan da zai mata aiki ne ya ga anje an kira tare da wasu likitocin ma,
Hakan ne yasa a jiye wayar a gefe yana tunanin ko lafiya,gashi lokaci na ta kurewa,

Dr Daniyal ne ya fito jiki a sanyaye yazo in da yake,

Shima yana ganin shi ya mike tsaye,

Dafa kafadarshi yayi"mu je Lab akwai abinda nake son nuna maka "

Jinjina kai yayi yana bin bayan shi "da fatan dai lafiya?

Bai bashi amsa ba har suka shiga ciki,sai dai ba ta inda aka diba jinin shi ba ne,wannan wani madaidaitan falo ne,mai dauke da kujeru sai kuma likitocin dake zaune a wurin su uku ko wanne fuskar shi dauke da damuwa,

Nuna mashi wurin zama sukayi ya zauna,

Sannan daya daga cikin su ya fara magana kamar haka"Malam Suraj Abdulbasir,matarka ita ce Ummu Salma Abdullah "

"Haka ne"

Ajiyar zuciya likitan ya sauke"muna son mu sanar da kai cewar cuta ba mutuwa bane,sannan duk wani cutar da Allah ya saukar dashi sai da ya saukar da magani,sai dai wani lokaci kafin mu fahimce maganin ne sai ya dauke mu shekaru masu yawa,"

Katseshi yayi"ka fada min meke faruwa kai tsaye "

Daukar Rimot din wani karamin TV yayi dake jikin bango ya danna,sai gashi wasu irin abu na yawa a cikin TV,kamar dai a saka mai a cikin ruwa yanda yanda yaje rabewa yana hadewa,

Nuni ya mashi da TV"wannan shine gwajin jinin Matar ka da muka yi,wanda ya tabbatar mana da tana dauke da *LEUKEMIA* *CANCER OF THE BLOOD* wanda ya nuna a cikin jinin ta sakamakon kwajin da muka je yi tsakanin jinin ka da nata.

🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*70*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Gabaɗaya karamin falon shiru ya ɗauka na sakanni yanda kasan babu mutane a cikin shi,
Sai da suka ƙara maimaita mai maganar ganin kamar baida niyar cewa komai,
"Rayuwa da mutuwa duka na Allah ne,nasan cewar tun daga lokacin da aka hallicci ɗan Adam Allah ya riga ya dibar masa iya numfashin da zai shaka a rayuwar sa,
Bai isa ya kara ƙofa da ja daya bane" Dago idanun shi yayi wanda suka sauya daga farin da suke zuwa wani yanayi da baka isa ka fassara halin da zuciyar shi ke ciki ba,yanayi ne da duk wani bawa mai tawakkali da karfin imani kan tsince kansa a ciki a duk lokacin da wata masifa ko jarabawa ta same shi.

"Hakan na nufin lokacin rasa ta yayi?

" A'a ba haka lamarin yake ba Sir Suraj,wasu mutane sun dauka da zaran ance mutum na dauke da ciyon Cancer shi kenan lokacin mutuwar shi yayi,abun kuma ba haka yake ba,yanzun an samu cigaba a duniya fiye da yanda mutum ke tunani,kullum sababbin lamari ƙara fitowa suke yi,ka ga kamar na Matar ka,ya zama matsalarta biyu ne,wanda nake ganin idan har muka shawo kan matsalar zata samu lafiya ta koma dai-dai kanar da"

Ganin bai ce komai ba ne yasa yaci gaba da bayani kamar haka,yana matsar da hoton dake jikin TV zuwa wani,

"Wannan hoton Kidney ta ne,wanda ya nuna mana saboda rashin functioning yanda ya kamata ya janyo wannan Leukemia ɗin,
Ɗan Adam yana iya amfani da Kidney daya kuma ya rayu,to sai dai ita dama a sakamakon binciken da muka yi ya nuna an taba mata aikin Kidney har an cire daya,da daya take amfani,wanda shima yanzun ya samu matsala ta sanadiyar shan kwayoyin da take yi ko wani lokaci,sannan da shan taba,ma'ana Sigari,duk da illar sigarin ba sosai bane dan bai kai kwayar da take ci yawa ba"

Hannun yasa yana shafa gaban goshinshi da yaji yana mashi ciyo lokacin daya,ba tare daya dago ba yace"me abin yi yanzun?

"To da farko dai dole muna buƙatar wanda zai iya Donating blood cell,sai ayi abinda ake kira da *STEM CELL TRANSPLANT* kafin nan kuma ita kuma za'a mata *Chemotherapy* is to kill the blood forming cell,
Idan har an kammala an samu nasara,sannan ne zamu mata asalin Surgery na kai da kuma Kidney Transplant"

"Yaushe ne za'a fara gudanar da aikin?

" Eh aikin ba shine matsalar ba,matsalar shine wanda nasu cell din zai dace da juna wanda zai iya bata kyauta ko kuma dai a siya,sai kuma batun Kidney,duka ba abu bane mai sauƙin samu nan kusa,dan haka dai zamu cigaba da daurata a cikin Coma har sanda za'a mata aikin in an samu"

Mikewa tsaye yayi"na gode "ba tare daya jira cewarsu su ba ya fito daga ɗakin,
Har yayi taku uku yaji an kira sunan shi,
Ji yayi kamar ba zai tsaya ba,sai kuma ya juyo,da sauri Dr din ya karaso in da yake" Wucewa zaka yi"

"Umm" Ya bashi amsa yana kauda kai,

"Mu je ka ganta"

"No"ya faɗa kamar mai ciyon baki,

Cikin mamaki yace " No fa kace,I thought you care so much,kuma zaka so ganin ta"

"Zan iya tafiya,domin inada abun yi"

Kasa ba shi amsa yayi,sai ma rakashi da ido da yayi har ya bulle ma ganin shi,
Shifa a nashi tunanin yanda yaga ya nuna damuwa sosai a Legas a ranar farko da aka kawota,hankalin shi a tashe,sai yake tunanin zai iyayin komai domin ita,yanzun ma yana tunanin wannan maganar da suka faɗa mashi sai sun rike shi,amma sai gashi yana nuna kamar abin bai dame shi ba,shifa bai gane ba,
Ganin kanshi na ƙoƙarin kullewa ne yasa ya gyaɗa kai yana wucewa.

Yana fitowa daga cikin Asibitin kai tsaye wurin parking mota ya nufa inda ya ajiya Motar shi,ji yake zuciyar shi na mashi wani irin zafi da raɗaɗi,a maimakon daya shiga ya tayar da motar ya wuce,sai kunna AC da yayi ya rufe Glass ya haɗa kai da Sitiyarin motar,
Ya dauki lokaci mai tsayi a zaune a cikin motar da ana tunanin samun mafita wanda aƙalla yayi awa daya zaune kafin ya yanke shawarar da zuciyar shi yafi tsayawa a kai kafin ya tada mota yabar Harabar Asibitin,
Kai tsaye gidan shi dake Sultan Road ya nufa,
Yana shiga daki zama yayi a baƙin gado yayin da hannun shi ke riƙe da waya ya tsura ma wata number ido kamar mai shirin tantance wani abu,

Ajiyar zuciya ya sauke a karo na ba adadi kafin ya danna number cike da fata iri-iri,
Sai da wayar yayi Ringim sau biyu sannan aka ɗauka da Sallamah,

Amsawa yayi cikin muryar nan nashi mai matuƙar sanyi,"Ina magana ne da *Abdulmajid* ?

"Eh dashi ne,pls waye ke magana?

Shiru ne ya ratsa wayar na ɗan wani lokaci wanda har sai da ya ƙara maimaita tambayar kafin ya buɗe baki kamar wanda aka tilasta yace" Kana magana ne da Suraj Abdul basir "

Tun daga nan ban kuma sanin me yake faɗi ba saboda yanda yake magana a hankali,
Sun dauki lokaci mai dan tsayi yana magana kafin naji yace"Sai kun iso "ya sauke wayar ya koma ya kwanta yana lumshe ido,wanda Allah ne kaɗai yasan me ke gudana a ran shi.
Chapter 70 · 0% Book details