← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 96

Sashe 8

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummita ce ta shigo,dan su gaisa,sai dai ganin yanda take haɗa kaya a akwati cikin sauri ne yasa ta tsaya tana kallon ta,"tafita zaki yi ne Biba?

ba tare data juyo ba ta bata amsa"Eh"

"Zuwa ina,ko wani aikin ne ya taso"

"Legos zan je,ina ga daga nan zan tafi England ba yanzun zan dawo ba"

Cikin sauri ta ƙarasa in da take tare da karɓar takalmin data dauko tana kokarin sawa a jakka,"Biba amma lafiya,tafiya cikin gaggawa haka,kuma ba aiki ba"

Dauko wani tayi ta saka"sauri nake yi,"

"To zan biki"

Kafin ta bata amsa ne wayar ita Ummitan yayi kara,
Dubawa tayi,wanda ganin me kira ne yasa da sauri ta saki hannun Biba data riƙe tana danna wayar tare da ƙarawa a kunne,
Kafin tayi makaga sai cewa aka yi"idan kina tare da ita ki bata "

Cikin sauri ta mika ma Biba wayar,tare da faɗin "VIP ne"

Bata yi niyar karba ba sai dai jin sunan da aka kira yasa ta amsa tare da karawa a kunnen ta,"ina jin"abinda tace kenan.

Daga ɗayan gefen kuwa sai cewa akayi"ki shirya a yau da yamma zaki bi jirgi domin zuwa Kano,akwai aiki mai muhimmanci da za ki yi a can"

"Akan waye? Ta tambaya.

" YOUNG USTAZ "............

*sai mun haɗu a paid group*

🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*10*

*Na mai da Littafina mai suna a sama na kuɗi,tare da JAURO,idan kina son daya 300,dari uku,guda biyu kuma da Yar Tsanar Zinari tare da Jauro,dari biyar 500,ko wani daya dari uku*
*Hauwa Umar,Zenith Bank, 2284905309*
*ko katin waya na MTN,tare da turo shedar biya ta 08141644865*

"Akan waye" Ta tambaya,

Ta ɗayan ɓangaren ne aka bata amsa da "YOUNG USTAZ"

Shiru tayi yayinda ta shiga tunanin ina ta taɓa jin wannan sunan,
Bata son tayi Stressing brain ɗin ta shi yasa ta kara tambayar"waye shi"

"Idan kin isa Airport akwai wacce zata baki wani envelope mai dauke da duk wasu bayanai na mutanen gidan wanda ya kamata kisani har da na shi"

"Zan iya tafiya da Ummita? Ta tambaya tana kallon Ummita wacce ke haɗe hannun ta alamun roƙo akan zata bita,

" A'a domin wannan karon aikin ya banbanta da wanda kuka saba yi,wannan aikin na musamman ne wanda idan har kika samu nasaran cika shi,na maki alƙawarin cikar burin ki a wannan karon,dan haka ke kaɗai zaki tafi,sannan karki dauki kaya ko daya,a airport din matar da zata kawo maki sako zata hado maki da kaya harda wanda zaki canja ki saka,sannan ki yi taka tsantsan Good lock"yana gama fadar haka yawar ya tsinke.

Kallon Ummita tayi wacce tayi shiru tana turo baki,dan taji a binda yace,duk da tasan yawancin aikin su da Biba tana matukar shan wahala wanda ba wata wahala bane daya wuce tsoro,saboda Biba yar kasada ce,tana iya siyar da ranta ta jefasu cikin hatsari dan cikar aikin ta,kuma sai tayi cikin ikon Allah kuma ta samu nasara.

Komawa tayi ta zauna kusa da Ummita,tana tunanin wani aiki ne haka zai turata wanda zai ce karta dauki ko wani kaya,
Ummita ce ta katseta wacce tace"ni kuwa ina na taɓa jin wannan sunan Young USTAZ"jujjuya kai ta shiga yi tana jujjuya sunan a zuciyar ta,ganin ta kasa tunawa ne yasa ta mike,zan fita amma zan dawo kafin lokacin tafiyar taki tayi.

"Uhmm" Kawai ta bata amsa tare da komawa ta kwanta,tana tunanin dole ta yi masa wannan aikin ko don samun cikar burinta ita ma.

duk yanda taso ta samu tayi barci kafin lokacin tafiyar ta tayi bata samu tayi ba har Ummita ta dawo tasame ta,
Tare suka shiga kicin suka yi girkin abinci,sannan suka yi wanke-wanke,
Sai da ta ci abinci kafin tashiga banɗaki tayi wanka,koda ta kammala shiryawa biyar saura,dan haka Ummita ce taja mota taimata rakiya har airport,
Sai dai bata shiga ba,anan bakin kofa suka rungume juna"ki kula da kanki,Allah ya bada sa'a "

"Amin,ke ma ki kula da kanki"

Sake juna suka yi "ta yaya zan iya samun ki a waya"

"Idan na sauka zan siya waya da sim zan nime ki"

Jinjina kai tayi"sai na jiki"

Juyawa tayi tashige ciki,yayinda ita kuma ta juya ta shiga,

Ta san cewa ba tada komai a hannun na tafiya daga ita sai karamin hand bag wanda ake ratayawa,

Ji tayi daga bayanta an taɓa ta,juyowa tayi,sai dai wata mata ce wacce fuskarta ke sanye da nikaf,wani Bag ta damka mata a hannun ta irin na matafiya mai ɗan girma,sai wani envelope fari tare da ta takardun jirginta,
Bata ce mata komai ba ta wuce,ita ma bata ko juya ka kalle matarba ta ta saka kanta gaba,kai tsaye banɗaki cikin Airport din ta shiga,buɗe jakkan kayan tayi domin ta ciro wani kayan ta canja tunda yace in ta iso ta canja kaya,
Sai da ta kammala ciro kayan jakkan kaf kafin ta tsaya tana masu kallo mamaki,wannan wasu irin kaya ne,ko dai matar nan tayi kuskure ne,amma kuma ta saba in dai har zata aiki ita ke kawo mata jakkan kalan kayan daya kamata ta saka a wurin aikin,
Ƙare ma kayan kallo take yi,wasu riga da zani ne kodaddu wanda babu yabo babu fallasa,sai riga da siket wanda bai wuce kala uku ba,suma kuma data ɗaga su wasu manya dasu babu daidai jikinta,suma kuma duk babu sabo,duk da a goge suke,
Kai ina wannan ba kayanta bane,dan haka ba zata saka su ba,idan zaje can ta san dole zai nime ta ko ta yaya ne kafin ta fara aikin,amma ba zata saka waɗannan summokaran ba, danƙa bata canja kayan ba ta dauki jakkan ta fito,
Duk wani abunda ya kamata tayi sai da tayi kafin a basu dama suka shiga jirgi,wanda in da zata zauna a first class ne,

Sai da ta zauna kafin ta dauko wannan Envelope din ta buɗe,paper dake ciki wanda aka naɗe ta ciro tare da buɗe shi,
A hankali ta fara karanta bayanai dake ciki,wanda the more tana karantawa the more ɓacin ranta na ƙara baiyana,
The worst part of it,shine wai a gidan malamai VIP ya tura ta aiki wannan karon,wanda zata tafi a matsayin mai aiki a cikin gidan,
Har da cewa ta saka wannan kayan ta kwantar da hankalin ta ba wanda wani ya saka bane,duka sababbi ne,an zuba masu wani abu ne wanda ya kodar dasu ya maida su tsofaffi,kuma dole sai tayi taka-tsantsan,karta kuskura tayi abinda zai yi exposing dinta,har da wani cewa dole tabar duk wani shaye-shayen da take yi saboda ba karamin gida zata je ba,dole ne ta dauko mashi abinda ya faɗa mata a cikin gidan ta.

Tunda take bata taba jin bacin rai ba akan aikin ta irin na yau,
wai yau ita Biba ce zata wani gida a matsayin ƴar aiki,
A gaskiya da ba dan jirgin su ya tashi ba da ba abinda zai hana ta sauka tace ta fasa wannan aikin,duk da tasan cewa bijirewa VIP ba karamin matsala bane domin shi ɗin mutum ne mai matukar hatsari.

Tafiyar ba wani mai dadewa bane suka sauka a garin Kano,wanda tana fitowa airport din taji an kira sunan ta,

Juyawa tayi sai ganin wata mata tayi fara tas wacce fatarta yaji bilicin ya gaji,sai taunar cingan take yi,
Kai da ganinta kaga yar duniya,

Karasowa matar tayi inda take tare da karɓar jakkanta,
"Biyo ni" Kawai tace mata tana yin gaba,

Bin bayanta tayi har wurin parking in da ta saka jakkan cikin wani adaidaita sannan ta shiga ta zauna,

Ganin haka ne yasa ita ma ta shiga,sannan mutumin ya tayar suka bar wurin,
Sunyi tafiya mai nisa kafin su isa wani unguwa wanda tun daga bakin layin zaka tabbatar da unguwar talakawa ne,ko ta ina ka juya hayaniya kawai kake ji yana tashi na jama'a,
Har kofar wani gida wanda bai da kofa ya, tsaya sannan suka fito,
Kuɗi taga ta ciro ta bashi sannan ta ƙara daukar jakkan suka shiga cikin wannan gidan wanda tunda suka shiga ta fara ganin ƴan mata kala-kala yara da manya wasu kallo daya zaka masu ka fahimce daga kauye suke,

Wani daki suka shiga daga cikin jirin ɗakunan dake cikin gidan,

Wata budurwa ce ta ajiye jakkan gefe ta fita wanda dama suna shigowa cikin gidan ta amsa,

Kare ma dakin kallo tayi cikin yanayi ta ɗan kyankyami domin sam gidan bai kwanta mata ba,ita macce ce mai tsafta da son gayu,dan haka gefe ta samu ta ɗan zauna,

Cire mayafin ta matar tayi tana wurgi dashi,ruwa ta dibo a kofi ta sha sannan ta ajiye ma Biba a gabanta,wanda ganin kofin ruwan kaɗai yasa ta fara jin tashin zuciya,

Zama tayi kusa da ita tana faɗin "wash Allah" Kallo ta tayi "kina jina,ki sake jikin ki domin sai nan da kwana biyu zaki fara aiki a gidan zuwa lokacin mun san dole zasu buƙaci mai aiki"

Bata rai tayi "kina nufin zan zauna a nan har na tsayin kwana biyu?

" Eh domin dole ne akwai wasu abubuwan da zan koya maki,da kuma karin bayani dangane da halin ko wani mutum na cikin gidan har zuwa bangaren da zaki yi aiki"

"Wai a matsayin mai aikin me zanje"

"Shara da wanke-wanke,wata kila harda girki"

Wani irin zaro ido tayi tana dafe kirji"shara! Ni Biba! Wallahi I hate it,na tsane shara, ta ina kuma na iya girki,? Hannu ta Daura a kai "this is the worst ever"

Dariya matar ta fashe dashi......

*waye VIP*
*Menene burin Biba*
*Shin masu karatu wani irin abu ne Biba zata je daukowa a gidan su Young Ustadz*
*wani irin aiki ne koma zata yi a kanshi*
*Shin zata samu nasara a kan matashin malamin namu*
*Zai gane ta kuwa*
*me zai faru a gidan*
*Shin tukunna ma zata amince tayi wannan aikin*
*wacece BIBA*
*Me Asalin ta da labarin ta,me ya fito da ita gida*
*shin zata koma kuwa*🤷‍♀️ ohhuuu,ni ma ban sani ba sai mun haɗe a *Paid Group*

Taku har kullum Jiddarh Umar🦚.
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Chapter 8 · 0% Book details