← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 96

Sashe 19

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ya kai hannu yana kyara mata suman tare da shafawa yana kallon tushen suman don son tabbatar wa ko nata ne,
"Dibo ruwa da towel ki zo kina shafa mata,bari na dauko Alurai wanda zai taimaka mata" Ya karasa faɗa yana barin dakin da sauri,
Shi dai tana tsaye rungume da hannu yana kallon dun abinda suke yi,sai dai bai ce masu komai ba,

Ba jimawa kuwa sai gashi ya dawo da kayan aiki,cikin kwarewa ya mata duk abinda ta kamata ai mata,
Ganin yana ƙoƙarin zama bakin gadon ne yasa yace"Malam tashi mu tafi zasu kulle ƙofa "

"Ka tafi kawai idan zazzabin ya sauka zan wuce"

"Ba dai ka mata abinda ya kamata ba?

" Sosai ma kuwa"
"To tashi mu tafi bana son cin musu" Ya fada yana ƙara gimtse fuska,dan ya fara lura da take_taken shi.

Ba dan yaso ba ya mike ya nufa kofa harda juyowa ya kara kallon ta,gaskiya wannan Ustazun ya kwabsa mashi,shi da yaso ya zauna yata kalle ta.

"Mu je ki kulle ƙofa" Ya fada yana yin gaba,
Da sauri Nafisa ta bishi ta kulle kofofin shiyan,

Cikin ikon Allah kafin wani lokaci zazzabin ya sauka,ta daina rawan sanyin,
Washegari da safe ta ji sauƙi tunda har ta ita tashi tayi sallah,sannan taje ta gaida Kaka wacce ba karamin jin daɗin ganin ta tayi ba,sannan ta koma daki ta kwanta,

Kamar yanda suka saba daukar karatu a shiyan kaka dun safiya yauma haka ne,sai dai Yaya Nurudeen ya riga kowa shigowa,shida bai cika zuwa ba,
Sai kalle_kalke yake ta ina zai hango ta,ganin sun fara karatu ne yasa ya mike ya doshi dakin Nafisa,
Ji yayi muryar Kaka ya dakatar dashi"ina zaka"

Shafa kai ta fara ya nuna mata dakin Nafisa "zan dubo mai jiki ne"

"Dawo ka zauna dan yanzun ta bar nan,jikin da sauƙi dan har tayi sallah ta kuma zo ta gaida ni,sannan bana son na ƙara ganin irin haka"

Ya gane me take nufi wato bata son ya kara cewa zai shiga dakin.

Ba dan yaso ba ta dawo ya zauna,can kuma ta tashi ya fita,dan ya lura kaka ba raga mashi za tayi ba,har balle ta gano ƙudirin shi akan yarinyar.
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*21*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Misalin karfe takwas da rabi na safe ta tashi tayi wanka da ruwan ɗumi,sosai ta ji daɗin jikin ta,Nafisa ce ta je shiyan Ammi ta karbo mata kayanta,riga da zani ne na Atamfa wanda rigar ya saukar mata har guiwa sai zani,

Kasancewar ranar sati ne babu aiki kowa na gida,shi yasa duk ranar ashiyan Kaka suke karin safe,sannan suke cin abinci dare,
Shi yasa ma yau duk suka hadu Ana cin abincin safe,
Hauwa'u ce ta shigo da sallama,gaisawa suka yi har da Kaka,
"Ga wuri ki zauna,Nafisa kawo mata abin kari"

Zama tayi tana murmushi domin ba karamin burge ta suka yiba,"kaka na koshi,na gode,"

"Nafisa kira mata Habiba"

Da to ta amsa tana mikewa,
Jimawa kaɗan sai gasu sun fito tare,tana biye da ita a baya,
Duk da kayan jikinta sun mata yawa zani kuma leɓe daya yafi daya tsayi,ga kuma ɗan kwalin da yafashi kawai tayi akai bata Daura ba,amma ta fito shar da ita,fuskarta ya ƙara haske,yayi fayau da shi,
Nuna mata kusa da ita tayi"zauna a nan "zama tayi tana gaida su,
Wasu sun amsa wasu basu amsa ba,
Tambayar ta matar da ta ji an kira da Hauwa tayi" Kin yi karin safe"

Jinjina mata kai tayi"eh"

Kaka ce tace"Zainab jeki shiyan Ammi ki anso ledan magunguna "

"To kaka"ta faɗa tana fita,
" Wai nikam ina Surajo yake ne ko yau ba zai karya ba ne?

"Na dai ga kofarshi a kulle" Cewar Salman.

Zainab ce ta shigo da leda a hannun ta mika ma Hauwa'u,
Amsa tayi ta ciro magunguna ta shiga nuna mata yanda zata sha,
Allura ta ciro ta shiga haɗawa,"zamu shiga daki sai na maki Allura zuwa yamma kuma zan dawo sai na maki daya"

Numfashi ta sauke sannan ta mike tsaye,kallon kofar fita falon tayi,"ina so in je in gaida Ammi,bari in na dawo sai ki yi min"ta faɗa tana nuna ƙofa,

"Da dai kin tsaya sai na maki dan sauri nake zani wurin aiki"

Tana kokarin yin magana ne kaka tace"ku shiga daki na sai ku yi "

"To Kaka" Cewar Hauwa'u tana mikewa,
Ba dan ta so ba tabi bayan ta,
Mintina biyu tsakani,sai jin tashin ihu suke,sai kuma gashi ta fito da mugun gudu ɗan kwali a hanu tayi waje,yanda kasan wacce kura ya biyo,
Duk da kallo suka bita,
Kafin Hauwa'u ta fito ɗakin riƙe da Allura a hannu,tana kiran sunan ta,
Kaka ce ta dakatar da ita daga ƙoƙarin binta da take "lafiya?me ya faru?

Tsayawa tayi tana dafe ƙwanƙwaso" Wallahi nima ban sani ba kaka,amma ina ga duk yanda akayi tsoron Allura take yi"

Yamutse fuska Aunty Maijiddarh tayi"sai dai in iskanci amma me abin tsoro ga Allura"

"Wallahi kuwa,ke dai bari kin San idan mutum ya samu wuri babu tsiyan da ba zai shuka ba" Cewar Khadija,

Ibrahim ne yace"na ga dai Uwar faɗin ma haka take "

Kaka ce ta dakar dasu"bana son rashin girmama abinci,wannan ba ɗabi'a mai kyau bane kana cin abinci kana surutu,

Sallamar shi da suka ji ne ya jawo hankalin su,
Niman kusa da kaka yayi ya zauna,
Da sauri Aunty Maijiddarh ta taso tazo tana kokarin zuba mai kunun kyada dake cikin fulas,da hannu ya mata alama akan ta dakata,
Jiki a sanyaye ta tashi ta koma wurin zaman ta,

Gaida shi Hauwa'u tayi ya amsa,a takaice,

"Zainab maza ku tashi ku kira min Habiba ta bar yarinya tana zaman jiranta"

Turo baki tayi"kaka to ai ita ba ƙaramar yarinya ba ce,kawai ita Hauwa'u ta yi wucewar ta jiki magayi,idan ta ji jiki da kanta zata nime a mat...

Haɗa ido da suka yi dashi ne yasa ta kasa karasa maganar daje bakinta,cikin sauri ta tashi ta fita,

Da kanshi ya zuba kunun a kofi har sai da ya kusa kammalawa sannan suka shigo wai basu ganta ba bata shiyan Ammi,
Dan haka kaka tace Hauwa'u ta wuce Nurudeen zai karasa mata Alluran,wanda hakan ba karamin daɗi ya mashi ba.
Sallamah ta masu ta wuce,

Yana kammalawa tashi yayi ya fita kaka ce ta dakatar dashi"ina zaka kuma baka ci kosai ba"

"Sauri nake saboda yau zamu tafi wa'azi Nijar"

"Yanzun zaku tafi?

" Sai zuwa anjima amma yanzun akwai in da zanje ne"

"To Allah ya tsare hanya ya dawo da kai lafiya,"

Da Amin ya amsa,sannan ya wuce.
Har ya saka katin kofa sai yaji kamar yana jin motsin mutum,
Dan haka juyawa yayi,sai dai bai ga kowa ba,hango gefen zani yayi,
Dan haka a hankali ya taka ya isa in da take zaune a ta lungun dakin su,ta makale ta haɗa kai da guiwa,
"What are you doing here?

Baki ta buɗe tana ƙoƙarin saka ihu,domin ba karamin tsoro taji ba,
Ihun ya makale ne sanda taga wanda ke tsaye a gabanta,
Dafe kirji tayi tana sauke numfashi,
Cikin jin haushi ta turo baki" Shi ne zaka ba mutum tsoro"

Jin kamar takun tafiya ne yasa ta juya baya,Salman ne ke ƙoƙarin bude nashi kofar,
Kokarin yin magana yake yi,yaji an riƙe mai ƙafa gam,
Juyo da kallon shi kanta yayi,ta tsugunna yanda kasan me niman gafara,gashi ta wani marairaice fuska yanda kasan kyanwa,sai wani rau_rau da ido take yi,"dan Allah karka faɗi in da nake"

Jan kafar shi yayi"me yasa?

"Bana son Allura"
"Bout you are so big to say that"

Shagwabe fuska tayi"ni dai dan Allah karka faɗa ma kowa"

Jinjina kai yayi,ya juya ya wuce abin shi,
Mintuna kaɗan sai ga Ibrahim da Aunty maijiddarh,sai Bilki,
Kawai sai ganin mutane tayi tsaye a kanta,
Ihu ta kurma yanda kasan wacce za'a yanka ta mike tana ƙoƙarin gudu,
Da sauri Aunty maijiddarh ta rukota,
Hmmm ranar sunga hauka domin kuwa da kyar suka kai ta shiyan kaka da kuka da ihu,duk yanda aka so ayi Allurar dole hakura aka yi aka kyale ta,dan har da cizon Nurudeen tayi a hannu,gabaɗaya ta hargitsa gida,dole aka kyale ta,

Wurin shan magani ba tada matsala domin ko banza ta ci kwaya balle kuma wannan,

Bayan sati ɗaya,
Sai da taji sauki sosai sannan ta koma shiyan Ammi,bayan kaka ta kira matan gidan tai masu kyakkyawar kashedi akan bata yarda ko da wasa a ƙara cin zarafin wani ɗan aiki a gidan ba,idan kuma aka kuma yi mutun zan haɗu da ita,
Wannan dalilin ne yasa ta dan samu sauƙi,dan bata shiga shiyan kowa sai na kaka,
Sai dai idan ta haɗu dasu a hanya,
Tsakanin ta da yaran gidan kuwa ko kallon banza,dan sai dai su zage ta amma bata gaida su,tunda ba girman ta suka yi ba,har gara Aunty maijiddarh,tunda taga wani lokaci tana da kirki,
Zaman gidan gabaɗaya ya isheta domin ko wanda zata yi aiki domin shi bata ganin shi tun wannan ranar daya faɗa ma su Nurudeen in da take,dan ta tabbatar da shi ya faɗa masu.
Ganin ƙafar Ammi da sauƙi ne yasa taimata karya akan zata ganin Mahaifiyar ta wai jikin nata ya tashi,
Cikin tausayawa ta amince mata sannan ta haɗa mata tsaraba sosai,har da kaka,

Ranar da zata tafi ne ta fito wanka kenan sai gashi taga shigowar kira a wayar ta,duk da babu suna kuma yawancin lokuta da numbobi mabanbanta yake kira amma ta fahimce me kira,
Dan haka ɗauka tayi,
Abu na farko da yace shine"me yasa zaki tafi?

Shiru tayi tana mamakin ta yaya akayi yasan zata tafi bayan ko A'i bata san da maganar tafiyar ta ba,
"Ina buƙatar hutu" Ta bashi amsa.

"Ba dai akan dan abun da ya faru ba?
Chapter 19 · 0% Book details