← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 96

Sashe 48

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan shine dare na biyu da ta ci kuka kamar rayuwar ta zai ɗauke a karo na biyu,komai sabo yake dawo mata a cikin ƙwaƙwalwarta,
Da fari komai gwanin daɗi,amma daga baya komai ya juya tun daga sanin wani ɓoyayyen gaskiya,ba zata taɓa manta ko ita wacece ba,duk kuwa da irin nisan da tayi da kuma kokarin da tayi,
Abu ne mai matukar ciyo sosai,mai kuma kona zuciya ya narkar da ita kamar bata taba wanzuwa ba a jikin ɗan Adam,
Tabbas tayi tunani me zurfi a wannan dare,ta kuma ɗauki darasi a mutuwar yar uwarta,shin ta koma in da ta fito ne ko kuma taci gaba da tafiya kamar yanda ta ɗauki kudiri a da.

Rufe karamin littafin dake hannun ta tayi tana ajiye biron a gefe,
Shafa bayan littafin tayi wanda aka rubuta *MY DESTINY* a jikin bangon littafin,

Kallon Agogon bangon dakin tayi wanda ya nuna ƙarfe Uku na dare,
Komawa tayi bakin gado ta zauna a kasa tana daura kanta a saman katifar gadon a maimakon ta hau ta kwanta,
Daga haka ne bacci barawo yayi awan gaba da ita ba tare data shirya ma hakan ba.

🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*48*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Washegari tana tashi wanka tayi sannan tayi sallah ta koma ta kwanta tana jawo wayarta ta buɗe data,
Bansan me take yi ba amma daga dukkan alamu abu mai muhimmanci take yi,wanda tana yi tana duba agogon dake makale jikin bango lokaci_lokaci saboda ƙarfe goma na safe za'a fara gudanar da nashi shari'ar,
Dan haka sai ƙarfe tara sannan ta tashi tayi break Fast wanda tasa aka kawo mata tun dazu,

Number Alhaji Mansour ta kira tana sanar dashi ta kammala ya turo mata direban sa yace zai mata aiki,
Nan yake sanar da ita ai mutumin yana harabar Hotel din yana jiranta tun ƙarfe takwas na safe,
Kashe wayar tayi ba tare data damu da mai godiya ba ta fito,
Tsayawa tayi a babban harabar Hotel din tana kallon manyan motocin dake farke a wurin,

Ji tayi daga bayanta ana fadin"Hajiya barka da fitowa "

Juyowa tayi ta kalli mutumin wanda bai wuce sa'ar yayanta ba,sai dai bata ce mashi komai ba,

Da hannu ya mata nuni da inda wani lafiyayyen mota ruwan ƙasa ke parke "Hajiya ga motar can"

Bin bayan shi tayi ba tare data jira ya buɗe mata ba ta saka hannu ta buɗe gidan baya tayi zamanta,
Shi kuma buɗe mazaunen Direba yayi ya ta da motar suka fita farfajiyar Hotel ɗin,
"Hajiya ina zamu tafi?

" High court"ta bashi amsa a taƙaice tana kwantar da kanta jikin kujeran motar,

Kunsan yanayin Goslow irin na Legos dan haka ko kafin su isa har ƙarfe goma da rabi ake nima,koda suka shiga koton an daɗe da fara gudanar da shari'a,

_____Acikin koto kuwa ba'a bari wasu mutane masu yawa sun halarci cikin ba,daga dangin Yarinyar sai kuma nashi dangin,wato su Pa dasu Abbu,Dady,sai Nadiya dake ma su Kaka Video kai tsaye suna kallon abinda ke wakana acikin koton,
Haka suma bangaren iyayen yarinyar suma suna da masu kwashe masu,sai dai su kai tsaye suke daurawa a shafikan su na yanar gizo wanda kowa zai iya kallon yanda komai ke gudana,

____A can gida Kano kuwa hankalin su duk a tashe yake,domin gabaɗaya daga manyan gidan iyaye da yara har Ammi a falon kaka suka haɗu suna kallon yanda Lauyan su ke jeho ma Suraj tambaya kuma ya hana shi magana sai dai kawai ya bashi dama in Eh ne yace eh,in A'a ne yace A'a,kuma duka da harshen Turanci suke magana,

Kaka ce ta fashe da kuka"kai Allah ya tsine ma wannan jikan bakin tuwo,ta yaya zai hana yaro magana "

Kuka Amira ta saka tana dafa Ammi dake kusa da ita wanda Allah kaɗai yasan meke gudana a cikin zuciyar ta"Ammi shi kenan yanzun sun kada yaya Suraj,jibi yanda suke zubo mashi tambaya "

"Ai daga ganin yanda wannan lauyan ke jeho tambaya kasan ƙwararre ne, kayar da shi ba abu mai sauƙi bane,gaskiya da wuya akai labari" Cewar Hajiya Saude,

"Koma dai menene karfin addu'ar mu na tare da Suraj Allah zai baiyana gaskiya ta inda basuyi zato ba" Goggon yara ta fada,

Dafa hannun ta tayi"me yasa zaki karaya tun yanzun,bayan ko asalin shari'ar ba'a fara ba "

Duk kallon mamaki suke mata,Ibrahim ne yace"Ammi amma ai har yanyi rabin shari'ar,idan kuma har aka kai karshe ba tare da wani kwakkwaran hujja ba shike nan mun rasa wannan shari'ar "

Nuna masa TV tayi"ai ba kai karshe ba,amma ka kalla ka gani"

"A'a wacece wannan ta shigo?ku kalla ga wata nan ta shigo sanye da kayan lauyoyi"
Duk maida hankalin su kan TV suka kuma yi,

_________*Legos*

Mai gadin bakin ƙofar babban Hall din ne ya buɗe mata ƙofa bayan ta nuna mashi I.D card ɗinta,
Jin an buɗe ƙofar ne yasa Lauyar dakatar da wasu tambayoyin da yake ma Suraj ɗin,

Taku take cikin natsuwa tana juyawa tamkar wata Ɗawisu,har ta iso dai dai in da take da damar tsayawa kafin ta cire gilashin dake Idanunta wanda ya kusa rufe rabin fuskarta ta rike a hannun,
(Kuyi haƙuri da yanda shari'ar zai zo domin bansan yawancin ka'idojin Kotu ba).

Daya daga cikin masunjojin kotu ne ya tashi"Hajiya shin baki san nan kotu bane da zaki shigo kai tsaye tamkar gidan ki?

Ba tare data bashi amsa ba ta maida fuskanta kan Alkalan dake zaune su biyu cikin girmamawa irin nasu tace"ina niman afuwa akan jimawar dana ni ban karaso ba,wanda hakan ya faru ne sakamakon cunkoson abun hawa,
Ni suna na *Ummu Salma Abdullah Lauyan wanda ake tuhuma*

To fa wannan shi ake kira kallo ya koma sama,

Nadiya ce ta dafa yayan ta tana kallon Pa"Pa wannan ai daughter Biba ce,matar Suraj "

Ɗan rankwashi yayan nata ya sakar mata"ba ita ba ce,ke dai ki yi shiru muji "

"Kina iya zama kotu ta maki uziri amma nan gaba ki ki kiyaye"

"Na gode ya mai shari'a" Ta faɗa tana zama a kujerar da aka tanada dan su,wanda ta samu lauyoyi biyu a zaune,

Lauyan dake magana ne ya cigaba da faɗin "Ya mai shari'a,kamar yanda na gabatar ma da kotu kwararan hujjojin na,ina rokon koto data yi gaggawar yanke ma mai laifi hukunci ba tare da bata wa kotu lokaci ba"sannan ya koma ya zauna

Alkalin ne yace" A sakamakon waɗannan hujjojin da Lauyan mai ƙara ya gabatar,koto ta duba kuma ta gamsu dashi,zata kuma yi amfani dashi wurin yanke ma mai laifi hukunci.....

Mikewa tsaye tayi tana daga hannu "ya mai girma mai shari'a,a matsayina na Lauyan wanda ake tuhuma ban yarda da hujjojin da Lauyan wanda yake kara ya bayar ba,sannan ina da tambayoyin da nake da bukatar na ma wanda nake karewa a gaban kotu sannan tare da ba da nawa hujjojin kafin a yanke hukunci"

Ji yayi kamar ya taso ya shake wannan yarinyar daga saman kujeran da yake zaune,wacece ita da zata bata masu shirin su,daga ina take,shi yasa yaso ya yanke hukunci kai tsaye amma ta katse shi,daga ganin kuma yanda take tana da kwarin gwiwa,domin babu alamar tsoro a tattare da ita ko fargaba,chief ya fada a zuciyar shi,wanda ba shi kaɗai yake raya hakan ba,yasan suna da yawa a koton masu tunani irin nashi,dan daga inda yake zaune yana iya hango bacin rai mai tsanani ƙunshe a fuskar Shugaba,
Babu yanda ya iya dan haka dole yace"Kotu ta baki dama"

"Na gode mai shari'a" Ta faɗa tana haurawa saman stage din da yake tsaye yana kallon ta tun shigowar ta,duk da ada ya fara cire rai akan zuwan nata,

"Malam shin zaka iya faɗa mana Asalin Sunan ka? Ta fada cikin kwarewa da harshen turanci,

" Suraj Abdul basir "

"Menene Alakarka da Jusica"

"Ba ni da wata Alka da ita,asalima ban santa ba"

"Idan baka santa ta yaya aka samu gawarta a cikin dakin Hotel din da kake zaune?

Zuba mata ido yayi na sakanni,yayin data kauda kanta daga kallon da yake mata,
" Ni ma ban sani ba,domin bansan da gawar ba sai da jami'an tsaro suka zo suka bincika "

Juyawa tayi gaban Alkalan "ya mai girma mai shari'a,ina son kotu tayi duba da waɗannan takardun binciken da likitoci suka gudanar a kan gawar,wanda ke nuna babu shafin hannun wanda ake zargi akan jikin Jusica,ko kuma wuƙar da aka yi amfani da ita wurin cire wani shashi na jikin ta,ina son koto tayi duba ga wannan ta kara nazari akan wannan batun"

Mikewa Lauyan su yayi"ya mai shari'a,Barista Ummu Salama ba ta da wani hujja da zata gabatar ma kotu,so kawai take tayi ma kotu wasa da hankali ta kuma bata ma kotu lokacin "

"Ina da dama da zan fada duk abinda zan faɗa kuma kotu ta saurare ni a matsiya na Lauyan under Section 10 a kundin littafin lauyoyi,"

"Kotu ta baki dama,Barista Wale ka kiyaye"

Dole ya koma ya zauna yana hararanta,ƙarama da ita tana ƙoƙarin maida masu da aiki baya,

"Yamai shari'a ina rokon kotu ta Bani damar yi na shugaban yan sanda na wannan yanki tambayoyi?

" Kotu ta baki dama"
Nan matsinjan ya fara shelan mutumin kafin katon Bayaraben ya fito yazo ya tsaya gaban kotun,

"Ya sunan ka?

" Suna na Akintola "

"Malam Akintola ko zaka iya faɗa ma kotu ta yaya ka samu labarin cewa akwai Gawa acikin wannan Hotel din a kuma dakin da wanda ake tuhuma yake ciki"

"Eh na samu labari ne daga kiran dana samu"

"Muna bukatar jin daga waye ka samu kiran?

Ɗan shiru yayi kamar mai nazari kafin yace" Nima ban san ko waye ba kawai dai number ne ya kira ni ya faɗa min,ni kuma naje domin na tabbatar shine na samu abinda na samu"
Chapter 48 · 0% Book details