← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 96

Sashe 7

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya kawai yayi yana fita daga shiyan,dan yasan in dai ya zauna to fa yanzun zasu shiga yin zirga-zirgar a cikin falon,daga yan matan gidan har na makota masu shigowa,
Shi kuma tsakanin shi da mace sai niman tsari,
Shi sam basu gaban shi,basu burge shi,shi yasa duk wacce tayi kuskuren ya gano kina son shi,to kin shiga uku bashi ba raga maki,tsakanin ku harara,amma in kin iya takunki to zaku zauna lafiya,harma ku yi hira,to duk kuma randa yan iskar nashi ke kai,to ranar kowa a gidan kama kanshi yake hatta masu tsaron shi,ɗan shi mutum ne mai matukar sauƙin kai,bai da saurin fushi,ya nada fara'a,sai dai bai son rai ni,wani lokaci kuma haka kawai ranar sai kaga ya dauke wuta,wato ya gimtse fuska duk wanda ya mai to ranar ya shiga uku,domin ya iya bada punishment wanda duk girman mutum sai yayi kuka,shi yasa duk randa suka ganshi a irin wannan yayi kowa yake kama kanshi a gidan babba da yaro....

Yana fitowa daga part din kaka sai ga Direba, cikin girmamawa ya miko mashi wani karamin pos na mata da waya kiran iPhone"Ustaz gashi a cikin mota na gani"

Bai amsaba sai tsayawa da yayi yana kallon pos din tare da wayar "ina riƙe pos ne da zaka kawo min?

Dukar dakai yayi cikin girmamawa yace" Ba haka nake nufi ba,a yi hakuri,ina ganin na wannan yarinyar ce data shiga motarmu "

Ɗan shiru yayi yana nazari dan shi sam yama manta da wata ta shiga motar su dazu,ohh ya tuna,wannan mara kunyar yarinyar,wacce tace mashi maye,harda cewa ya gyara suman kanshi,

"Jeka dashi" Yace ma Direban,har kuma mutumin ya juya yana tunanin yanda zai yi da kayan,ko me ya tuna ohho,sai kuma yace "Kawo"
aikuwa da sauri mutumin ya kawo mai ya juya ya bar wurin cikin sauri dan karma ya canja ra'ayi.

Jujjuya kayan yake a hannu kafin ya nufe dakin shi dasu......

______Bangaren Biba kuwa...

🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*08*

*Na mai da Littafina mai suna a sama na kuɗi,tare da JAURO,idan kina son daya 300,dari uku,guda biyu kuma da Yar Tsanar Zinari tare da Jauro,dari biyar 500,ko wani daya dari uku*
*Hauwa Umar,Zenith Bank, 2284905309*
*ko katin waya na MTN,tare da turo shedar biya ta 08141644865*

A gigice ya shigo cikin gidan har yana cin tuntube sabar saurin da yake yi,
Ga masu aiki ta ko ina duk in da yabi sai gaida shi suke yi amma sam ba su bane a gaban shi,
Burin shi daya shine ya ƙarasa inda masu gidan suke,
Tunda ya taka ƙafar shi a babban falon gidan wanda daka ganshi kasan naira tayi kuka ya fara kwalla kiran sunan mutanen gidan daya bayan daya cikin tashin hankali,
"Mama! Mama!Abdulrahman! Yaya Abdulmajid! Ina kuke ɗan Allah ku fito! "

Daya bayan daya suke fitowa daka shiya mabanbanta a cikin falon,
Ita wacce aka kira da Mama wacce ke sanye da Hijabi dogo har ƙasa tare da carbi a hannun ta ne ta kalle shi,"lafiya Abdulmalik?

Kallon ta yayi,tare da kallon ƴan uwan shi maza dake tsaye suna jira suji ko lafiya,yake a gargitse haka,
A hankali ya buɗe baki ya kira sunan ta"Mama"

Amsawa ta kara yi tana kallon ɗan nata wanda yake cikakken saurayi kuma matashi wanda zai kai shekara ishirin da takwas,taga ya fashe da kuka tare da rungume ta,

Duk da basu san me ya saka shi kuka haka ba,amma sun san ba karamin abu bane zai saka shi kuka haka,dumin kuwa shine mai ƙarfin zuciya a cikin su,shine mai kwantar masu hankali a ko wani lokaci,tun bayan faruwar wani babban lamari a rayuwar su,wanda shi ne yayi sanadiyar sauya komai na gidan,ya mai da masu da gida tamkar kango wanda babu mutanen dake rayuwa a cikin shi,tun daga lokacin da suna rasa NURUL AINI,wato hasken idaniyar su,mai haska zukatan wannan Alhali gaba ɗaya,sunyi babban saken da ZINARIYAR da suke ji da ita tabar hannun su,wanda suke tunanin da wuya ta kuma dawowa hannun.

Abdulmajid da bai da wuyan kuka wanda shine Babban yayan su,ne ya zo ya rungume shi yana hawaye"Me haka Abdulmalik,so kake ka kara tayar mana da hankali,ɗan Allah na rokeka ka faɗa mana damuwar ka,ɗan uwan mu"

Dagowa yayi ya kalle su,yayin da wasu hawayen ke kara sauko mai a ido,dukar da kai yayi,sannan ya dago cikin matsanancin rauni yace"Mama na ganta,na ganta yau a garin Abuja "

Cikin sauri Abdulrahman ya kara so in da yake"wa ka gani! Wa ka gani yau a Abuja,pls ka faɗa mana"

A jiyar zuciya ya sauke me haɗe da kuka,"Yaya,wallahi na rantse Allah wannan karon naga Ummu Salma a garin Abuja, na....

Ganin ta tafi suuu tayi baya tana ƙoƙarin faduwa ne yasa da sauri suka tare ta suna kiran sunan ta a kidime,tare da taimaka mata suka zaunar da ita kan kushin,
Kiran sunan daya faɗa ta fara"Salma! Salma,dan Allah ku nimomin Salma kamin in mutu,akwai abinda nake son na faɗa mata,"riko hannun Abdulmalik din tayi"ɗan Allah ka taimake rayuwa ta Abdulmalik ka kai ni wurin Salma,waiyo Allah rayuwata bata amfana min komai ba sai aikin dana sani,na bi son zuciya na cutar da rayuwata da ta ƴa ta,na kai kaina ga halaka bayan nasan cewa halakar ce,ya zanyi da rayuwata,waiyo ya Ubangiji ka yafe min,ka yafe min na tuba"

Tsugunawa yayi a gabanta tare da zube guiwoyin shi a ƙasa yana zubar da hawaye mai ciyon gaske,"Mama ina niman gafaranki domin na kasa kawo maki ita,domin kuwa a Traffic na ganta,ko da na kira sunan ta muna haɗa ido da ita ta fita daga adaidaitan da take,na yi niman ta a wurin banganta ba,kwanana biyu a kullum a wurin nake yini ko Allah zai sa na ganta amma banganta ba Mama"ya faɗa yana kifa kanshi a cinyar ta.

Dafa kafadar shi Abdulrahman yayi"karka damu Abdulmalik,ko da ace zamu zagaye garin Abuja,insha Allah in dai anan Ummu Salma take sai mun ne mo ta,"

"Kwarai kuwa" Cewar Abdulmajid,domin kuwa sun san dole zai kasance cikin damuwa,duk cikin su yafi shakuwa da ita sosai,

"Mama ɗan Allah ki bar kuka haka,kin ga kada Dady ya tashi yaga idonki ya kumbura haka zai damu,idan kuma yaji batun Salma kin san me zai iya faruwa, pls"

Hannu tasa tana sharewa wani na zubowa "na kasa tsayar dasu,a ko wani lokaci ƴar uwar ku na cikin rai na,tunda tabar gida dai dai da sakon daya ban taba manta taba,a ko wani numfashi na cike yake da nadama,da dana sani,ji nake da za'a dawo da lokaci baya,da ban haɗu da miji kamar mahaifinku ba,da dana haɗu dashi dana ki amincewa dashi,kila da kaddarata bata zo a haka ba," Dago kai tayi ta kalle yaranta maza dake zagaye dasu,"a lokacin da kanwar ku ta faɗa min damurta,a matsayina na uwa kamata yayi na nima mata mafita na gari,sai na bata shawara akan tabi ta hanyar da nake bi,!a lokacin kun san me tace min kuwa?

Duk kallon ta suke cikin tsananin sanyin jiki mai haɗe matsanancin damuwa irin wanda yake tafiya da kuzari,

A lokacin kuka ta fashe dashi tare da rungumeni,tace min Mama kina ban tsoro,wannan kamar ba Mama na ba,dan Allah ki dai na faɗin haka kina ban tsoro,

Da wannan hannun nawa na ture ta,na ce mata sai ta nimar ma kanta mafita da kanta,amsar da ta ban shine,na yi dana sanin zuwa duniya a matsayin ƴar ku,da Ace Allah yana ba ya'ya zabi su zabi iyaye,Mama da ban zabe ku keda Dady a matsayin iyaye naba,na kwammace a haife ni a cikin ahalin da basu da komai sai sun fita sunyi bara sannan su ci dani,ba zan taba bi ta hanyar da kuka bi ba ke da Dady,Allah ya isa tsakanin ke dani,da kuma wanda yake a matsayin uba a gare ni,Ubangiji shi zai min hisabi daku ta yanda kuka kawo ni wannan duniyar,:

Wannan shine maganar kanwarku dani na karshe,Abdulmalik na tabbatar da haƙƙin ta ba zai bar ni ba,maganarta gaskiya ne,ban cancanci zama uwa ba,dan Allah ku gafarce ni"ta faɗa cikin matsanancin kuka tare da haɗe hannun ta wuri ɗaya.

Dukkanin su rungume ta suka yi suna masu kwantar mata da hankila,domin kar hawan jinin ta ya tashi,
Da kyar dai suka samu ta yi shiru,yayin da kowannensu ke fama da kuka zuci,domin kuwa Ummu Salma farin cikin su ce,ita ce Nurul Kalbi a gare su.

Jin wani ɗan ƙara ne yasa duk suka dago,
Mikewa tayi tsaye,tana ɗan share fuska,"ina ga mahaifinku ya tashi,muje ku duba shi"

Duk bin bayanta suka yi,suka bi ta cikin wani korido a falon in da yasa dasu da wani karamin falon wanda akwai wani dakin a cikin sa,dakin suka shiga,in da wani farin mutum ke kwance a kan gado an daura mai abun jawo numfashi a hanci,sai na'urorin dake zagaye dashi masu nuna blood pressure,da temperature,sai respretion,din shi,

Duk zagaye shi suke yi suna mashi sannu,da ido kawai yake iya amsawa,yana bin su da kallo daya bayan daya,kafin ya saida idanun shi akan matarshi,
A hankali ya daga hannun shi ya mika mata,
Matsowa tayi tare da kama hannun shi ta riƙe,

Cikin dauriya ya ɗan daga abin zukar numfashi,a hankali ya furta "Salma,ta dawo"

Da sauri Abdulmalik ya maida masa abin a hancin shi,"Dady ka kwantar da hankalin ka zata dawo,insha Allah zata wo"

Mai da ido kawai yayi ya lumshe,bai ƙara ce masu Komai ba har suka bar dakin...

*Abuja*

Sai da ta sauka a Adaidaita sannan ta shiga niman pos ɗinta,
"Ohh, ya Allah,ina ganin na barshi a motar wannan mutumin," Tsaki taja,sannan ta karasa inda me gadi ke zaune,"Audu ka bashi dubu daya idan nashiga ciki kazo ka ansa"

"To Hajiya an gama" Daki kuwa ya shiga ya dauko dubu guda ya ba mutumin.

Ita kuma tuni ta shiga gida,

Dakin ta shige kai tsaye tare da ciro wani madaidacin akwati ta shiga zuba kayanta a ciki,
Chapter 7 · 0% Book details