Sashe 41
Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abu kamar wasa babba magana ya kara zama gagarumin magana,domin kafin ka sani gaba ɗaya maganar ya zagaya Nigeria har ta inda baka yi tunani ba,har ta gidan TV da gidajen Rediyo duk in da ka kunna labarin dake zagayawa kenan har ta da social media an haɗa hoton shi dana gawar.
___A lokacin da Shamsuddeen ya shigo cikin tashin hankali yake nuna ma Ammi hoton nan take ta yanke jiki ta faɗi sumammiya domin ko Awa daya basu yi da gama waya dashi ba yake sanar da ita ya sauka lafiya shine kuma yanzun za'a ce haka.
Ita da Kaka dole Asibiti aka kai su domin an yayyafa ruwa amma basu farka ba daga dukkan alamu doguwar suma suka yi.....
*Tofa wasa farin girki*
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*41*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Tunda ta kammala cin Abinci bayan sallah Isha'i take zaune a falo tana buga Game a waya,badan komai ba dan ya ɗebe mata kadaici,ita ba gwanar kallo bace,haka kuma social media sai tayi kwana da kwanaki ba tare data hau online ba,
Ji tayi an buɗe ƙofar an shigo da gudu ana kwala mata kira"Hajiya!Hajiya"dan sam bai lura da ita zaune a falo ba,ita har ma ya bata tsoro,
"Bala lafiya?menene haka?
Jikin shi rawa kawai yake yi yayinda hawaye bibbiyu ke suka daga cikin idanun shi,
Tsoron tane taji ya fara tasiri har cikin zuciyar ta,domin bata taba ganin shi a haka ba,cikin wannan halin," Menene? Ta kuma tambayar shi a tsorace,
TV ya nuna mata da hannu,"Mai gida!Oga"
Ji tayi gaban ta ya yi wani irin mummunan faduwa,wanda ba zata tuna ranar data ji irin shi ba,"wani abun ya same shi ne?
Shi bai masan ta ina zai fara fahimtar da ita abinda ke faruwa ba,dan haka cikin sauri ya dauki rimot dake ajiye a teble ya kunna TV wanda kamar dama jira ake a kunna magana ya ɗauka, yayin da matar ke kan sanar da cewa"Shi dai wannan shahararren Malamin wanda matasa ke masa laƙabi da Young Ustadz an kama shine Dazu da misalin karfe takwas da kwata yana ƙoƙarin tsirewa bayan ya kashe matashiyar budurwar ya kwakwale idanun ta da harshen ta,wacce har yanzun ƴan sanda basu gama kammala bincibe ba akan wacece ita wannan matashiyar sannan wani alaƙa ne a tsakanin su,
Yanzun haka dai shi mai laifi yana hannun hukuma domin zanga-zangar da matasa garin Lagos suka tada akan sai hukumar ta mika mashi su sun kashe shi,
To masu kallon mu duka_duka anan muka kawo karshen labaran mu sai kuma kun jimu gobe domin jin yanda wannan Al'amarin mai matukar girgizawa zai kasance domin yanzun haka malamai suna kan tattaunawa akan wannan lamarin"
A tsaye take amma ji tayi wani irin gizo yana rufe mata idanu,bata iya ganin matar da kuma hoton shi dake gefe tare da gawa,
Ragab ta faɗa kan kushi,ta dai ga bakin Bala na motsi yana hawaye amma kuma sam bata jin me yake faɗa,
Ruwa masu sanyi a kofi ya miko mata,
Ganin ba tada niyar karba ne yasa ya ɗauki hannun ta ya Daura mata kofin a sama,dan ya gama alama ita ma kamar ƙoƙarin suma take yi,
Ganin yana mata alama da hannu a kan ta sha ruwan ne yasa ta kafa kai kuwa sai da ta shanye tas sannan ta mika masa Glass cup ɗin,
"Bala" Ta kira sunan shi,
Da sauri ya amsa,
Nuni tai mashi da TV"me matar nan ke faɗa ne,?
Kuka ya kuma fashewa dashi sannan ya shiga yi mata karin baya ni,yana kuma faɗin "yanzun haka yanda na samu labari mahaifiyar oga da kakar shi suna gadon Asibiti a kwance rai hannun Allah,ki duba Facebook zaki ƙara samun bayanai dan abun tuni ya zagaya ƙasa"
Duk da irin jirin da take gani wanda ba komai ya jawo shiba sai bugun zuciyar ta daya karu fiye da ka'ida sannan ga Shock da abin yazo mata dashi,"Suna wani Asibiti ne?
"Suna asibitin Nasarawa"
Dafa kushin tayi ta mike "mu je ka kai ni"
"To dauko Hijabin ki mu je"
"Doguwar riga ce a jikinta mai ƙauri kasancewar ana sanyi sai hula data saka,
Ba tare data bashi amsa ba ta fita daga falon tana dosar wurin a jiye motoci,
Ganin haka ne yasa da sauri yashiga kwalama direba kira,
Kokafin ya iso har ta zauna a mazaunin direba,hannun ta mika mai " Bani key"
Yana ƙoƙarin mika mata ne Bala ya amsa da sauri yana hararan shi"kana da hankali kuwa?a haka a wannan halin kake tunanin zata iya tuki da kanta "
Juyowa yayi ya kalle ta cikin kwantar da murya yace"Hajiya fito dan Allah a kai ki,kin ga dare ne ga kuma halin da Kike ciki,kuma ba lallai bane k gane Asibitin "
Fadin haka ne yasa ta fito ta koma gidan baya ta zauna,tabbas ya faɗi gaskiya domin hankalin ta baya jikin ta,duk da bata zauna tare da shi ba na tsayin lokaci ba amma ta tabbatar shi ba kalan mutumin da za'a ce yayi kisan kai bane,No way,babu ta yanda hakan zai faru,sai dai ita tun jin wannan labarin ta san Shiri ne mai matukar karfi,wanda fito dashi sai Allah,
Idan har suka yi nasara a kanshi,to tabbas ta san mutuwarta ce ta ke gabatota,
"Dan Allah ka ƙara gudu"
"To Hajiya"
Cikin mintuna kalilan suka isa katafaren Asibin,
Da sauri ta fita duk da bata san ata ina zata gansu ba amma ta tabbatar koma ta ina ne dole suna Emergency,
Cikin ikon Allah ma suna Shiga da Nurudeen suka fara cikin karo yana ƙoƙarin fitowa,
Cikin sauri ta karasa inda yake tana kiran sunan shi,
Ganin ta ne yasa ya dakata yana fuskantar ta,"ina su Ammi,ina kaka?meke faruwa?
Ganin yanda duk take a rikice yasa yace"ki kwantar da hankalin ki duk suna lafiya,mu je ki gansu "
Bin bayan shi tayi da sauri har suka isa wani kofar daki dake VIP world,in da anan taga sauran mutanen gida kowa ka gani hankalin shi a tashe yake,buɗe mata kofar dakin da Ammi take ciki yayi,
Da gudu ta karasa shiga tana rungume Ammi tare da fashewa da kuka,
Rungume ta tayi ita ma tana jin hawaye na saukowa daga cikin idanun ta,Allah ya gani tana matukar son ɗanta,bata fata wani abu ya same shi,kamar yanda aka samu nasaran mahaifinshi a samu nashi,
Ganin yanda take kuka ne yasa ta shiga shafa bayan ta,
Goggo ce data shigo ta dafa kafadar Ammi"kukan ya isa haka,kibar kuka ki kwantar da hankalin ki in sha Allah zai dawo domin yanzun haka Abbu da Dady sun kama hanya ko,dan babu Jirgi,amma duk da haka tafiyar mota zasu yi,da yardar Allah komai zai zo da sauki "
Cire jikinta tayi daga na Ammi tana rike hannun ta"Ammi tsoro nake ji,Allah yasa babu abinda suka mai,"
Gara ma yarinyar tana da sauran karfin da zata iya yin magana,ita tunda aka kawo ta Asibiti har yanzun ta kasa furta komai,
Ganin ƙarfe goma na dare yayi ne yasa Goggo tace"ya kamata ki tashi ki koma gida dare nayi"
Girgiza kai tayi"tsoro nake ji,kawai zan biku mu can gidan,tunda yanzun za'a ba da sallamah "
"Gama takardar sallahar,bari na taimaka ma Ammin Yara dan naga har yanzun jikin nata ba ƙarfi"
Tare suka taimaka mata har suka fito aka saka ta a mota suka nufi gida,
Har yanzun kuma bata yi magana ba,sai da suka tabbatar ta kwanta sannan suka ja mata kofa suka fito,
Goggo ce tace"ki yi ƙoƙari ki dinga shiga kina leka ta,ni zan kwana tare da Kaka,"
"To,sannan Amira bata shigo ba"
"Tana shiyana tare dasu Khadijah,nasan idan ta shigo zata damu Ammi da kuka ne,shi yasa nace tayi zamanta a can dan karta takura mata"
"To hakan yayi sai da safe"
"Allah ya tashe mu lafiya"
Har ta juya sai kuma ta dawo"yauwa,kema karki saka damuwa a ranki,duk da nasan hakan ba mai yiwa bane,amma ki yi ƙoƙari ki danne zuciyar ki,ki kuma taya shi da Addu'a Allah ya baiyana gaskiya,koma menene ya kawo mana ƙarshen shi cikin gaggawa,domin nasan Suraj bazai taɓa aikata haka ba "
Tunda take ganin matar bata taba tsammanin tana da sauƙin kai har haka ba,kawai dai dama can rashin fahimta ne,
"Na gode sosai Goggo"
"Babu komai" Ta faɗa tana fita yayin da ita kuma ta kulle ƙofar,
Ɗakinta nada ta shiga,inda take zaune a lokacin da take aiki,har yanzun komai na dakin yana nan,dan haka zama tayi abakin gado tana tunanin ta ina ya kamata ta fara fuskantar wannan lamarin,
Karan wayar tane ya dawo da ita daga duniyar nazarin da take kokarin faɗawa,
Ganin number kawai yasa gabanta ƙara tsinkewa,karo na farko da taji shakkun daukar wayar shi,
Ganin ya kusa katsewa ne yasa ta daga,
"Da fatan wannan hanyar zai maki?
" Wani hanya kenan?ina fatan ba kada hannu akan wannan labarin "ta tambaya ɗanta tabbatar,
" Kin ce baki san hanyar da zaki ja hankalin shi har ya faɗa maki inda takardun suke ba,shi yasa na matsar maki dashi dan kiji daɗin cika aikin ki cikin sauƙi "
"Amma me yasa sai ta hanyar kisa,kana ganin zai fito kuwa,batun kisa ba abu mai sauƙi bane"
"Wannan ba damuwarki ba ne,kawai dai kiyi abinda ke gabanki"
"Ina Ummita?
" Idan kin gama aiki da wuri zaki ganta "yana gama fadar haka ya kashe wayar.
Sauke wayar tayi a kunne tayi shiruu,yanzun yaya zata yi,sun riga sun samu nasara mataki na farko,ta tabbatar da zaran sun samu wannan takardar daga ita har shi kashe su zasu yi,tana buƙatar shi a raye idan tana son kasancewa a raye,dole ne sai ta kubutar da shi,tana buƙatar haɗuwa da shi sai dai dole zata jira zuwa nan da sati ɗaya taga wani mataki iyayen shi zasu ɗauka.