← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 96

Sashe 20

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Me kake nufi?
"Nasan komai,na kuma san kin warke,abu ɗaya kawai zai sa na bari ki tafi hutu saboda nasan baya ƙasa,ya tafi Sudan yin wani aiki tare da mahaifinsa,karshen watan nan zasu dawo,ina nufin nan da sati uku,kina da damar da zaki iya hutawa na sati biyu,domin jinyar mahaifiyar taki,ki tabbatar ya dawo ya same ki,sannan a wannan lokacin idan baki yi saurin cika min aiki na ba kome ya biyo baya ki yi kuka da kanki "

Cikin tsananin mamaki tace"ar you threaten me?

Kai tsaye ya bata amsa da"Yes"
Bai jira tace komai ba ya kashe wayar.

Kallon wayar dake hannun ta tayi,sabar bacin rai ne yasa ta buga wayar da ƙasa,me yake nufi,threatening ɗin ta yake saboda wani banzan aiki da bata masan amfanin me takardun zasu mai ba,sannan kuma duk halin da take ciki a gidan ya sani,to kodai ba ita kaɗai ɓace take mai aiki,
Tsaya ma tukun,ta ji yace ya tafi aiki Sudan tare da Mahaifinsa,bayan kuma ta san Abbu na gida,to wani mahaifi,Something is not right some were,tunda take aiki tare da VIP bata taba ganin yayi serious about wani abu ba kamar wannan aikin,
Komawa tayi ta zauna saman gado,ta shiga duniyar nazari,na farko shi dai ba Aljani bane,dole mutum ne,to waye shi,bata taɓa ganin shi ba,amma shi yasan komai game da ita,ta yaya,
Dafe kanta tayi,tana buƙatar sanin abubuwa masu yawa,amma kuma ta yaya zata yi hakan,
Ajiyan zuciya ta sauke tana jin kanta na daurewa,dan haka tashi tayi ta saka kaya sannan ta dauki Sim card ta jefa a jakka,
Ko da ta bar gidan ba wai ta tsaya a nan Kano bane,ko kuma tayi Abuja,kawai Jirgin Legos ta shiga dan gara taje can ta huta,in da anan suka hadu da Ummita.
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*22*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Kwanan ta biyu a Legos ranar sun dawo daga cin abinci tana zaune tana danne danne a Laptop sai saki take yi,mikewa zauna tayi ta dafe kanta,kallon Ummita tayi dake zaune tana kallo a TV sai faman dariya take yi,
Kiran sunan ta yi"Ummita"

Amsawa tayi ba tare data juyo ba,
Cikin jin haushi ta wurga mata filo,"dan Allah malama ki juyo "

Juyowa tayi tana bata rai ta katse mata kallo"gani"

Kyara zama tayi"ni kan baki ganin kamar akwai abinda bai tafiya dai-dai?

"A ina kenan?

"Wannan aikin da nake yi"
"Me kike nufi,kinsan wannan karon ba abinda na sani"

A jiyar zuciya ta sauke"da fari aiki akan Young Ustaz da Baban shi,sai kuma na fahimta mijin Goggon shi ya ɓace ba'asan in da yake ba,"

"Eh to ɓacewa yayi,is a normal thing"
Girgiza kai tayi"is not normal,Nafisa tace min Shamsuddeen ba yaron Ammi ba ne mahaifiyar sa sun rabu da Abbu,to shi kuma Ustazu fa?

"Yaron Ammi ne da Abbu mana"

"Kai ina da wata a kasa,ki duba fa ki ga,karshen magana na da VIP cewa yayi Ustaz ya tafi wani aiki da Baban shi a Sudan,kuma a lokacin Abbu yana gida"

"Oh Biba ni dai ban fahimci abun da ke kika fahimta ba,ni dai a gani na da ki bata lokacin ki wurin wannan bincike ba gara ki samar ma kanki mafitar da zai kai ga waɗannan takardun kawai,ayi a wuce wurin"

Dan shiru tayi,kafin tace "tabbas a kwai wani abu a kasa,yauwa kin ga matso ki gani" Ta faɗa tana nuna mata fuskar Laptop ɗinta,"kin ga anan sunan mahaifin sa Abu Sufyan,shi kuma yana amfani da Suraj Abdul Basir,waye Abdul Basir? Me yasa yake amfani da wannan sunan a maimakon Abu Sufyan?

"Ni dai Biba ki yi a hankali domin na lura wannan aikin ba kamar irin wanda muka saba yi bane"

Komawa tayi ta kwanta"in Allah ya yarda idan na koma da zaran ya dawo zan kammala komai na dawo,kin san wani abu kuwa"ta faɗa tana kunna Sigari,

"A'a sai kin faɗa?
" Da na kammala wannan aikin London zamu koma da zama,gaba ɗaya Nigeria ya ishe ni"

Ihu ta saka cikin tsananin jin daɗi ta taso ta rungume ta suna dariya,
"Shi yasa nake ji dake Aunty Biba,gashi Alhaji Mansur sai damuna da kira yake akan yaushe zaki dawo,"

"Kyale dan wahala,ni yanzun bata nasu nake yi ba,so nake kawai naga na kammala wannan aikin in huta"

"Ai kuwa sai dai ki yi hakuri dan wallahi na riga na tura masa Address din mu,idan baki ganshi yau ba kya ganshi gobe"
Haka dai suka cigaba hiransu,
Zamanta a Legos ba karamin daɗi ya mata ba,dan har bata son ta tuna cewa zata koma wannan gidan aikin.

Ranar da zata koma aiki har da Kukan zuci sai da tayi,dan ta san zata koma aikin shara kenan da wanke-wanke,.

Tana sauka a bakin Get din ta haɗu da A'i tsaye tana jiran ta,
Ganin tana ƙoƙarin shigewa ne yasa ta kira sunan ta,
Tsayawa tayi tana kallon ta,mika mata wani karamin waya tayi tare da karamin takarda,bata jira tace komai ba ta juya ta wuce,
Da kallo ta bita,kafin ita ma ta shige cikin gidan,
Sai da ta gaida Ammi wacce tuni ta ji sauƙi,sannan taje shiyan kaka ta gaida ita,sosai tayi farin cikin ganin ta,kafin ta koma shiyan su,
Fadawa tayi kan fado tana warware takardar da A'i ta bata,
"Karki zurfafa bincike,domin yana iya faɗawa kanki"

Ta maimaita maganar ya kai sau nawa,to me taje nufi da zai iya faɗawa kanta,
Nannaɗe takardar tayi ta saka cikin kayanta,
Amira ce ta zo ta faɗa mata cewar Ammi na kiran ta,
Fitowa tayi ta same ta zaune a falo,
Tsugunnawa tayi a gefe"Mam,gani"

"Alhamdulillah,dama so nake na sanar dake naji sauki,dama Kaka ta kawo kine domin ki taimaka min,kuma yanzun na warke,duk da ban jima dake ba amma naji daɗin aikin ki,Kaka tace na tambaye ki shin kina ganin zaki cigaba da zama damu anan ko zaki koma shiyan kaka?

"Zan zauna dake anan Mam," Domin ta san zama anan din ne zai fi bata damar sanin duk abinda take buƙata,

"Kin tabba ta?
" Eh Mam"
Murmushi tayi"shi kenan tashi ki tafi "
Godiya ta mata sannan ta koma daki.

Da yamma ne taje kaima Kaka Abinci ta ji suna magana Momy Saudat Mamar su Nurudeen,tana magana da Kaka cikin marairaicewa yayin da Aunty maijiddarh ke zaune tana sharan hawaye,
"Kaka nasan fa kinsan abun da ke wakana a tsakanin Suraj da Maijiddarh,gabaɗaya taki kula kowa,ta nace sai shi kaɗai take so,duba ki ga yanda duk tabi ta lalace,na rasa yanda zan yi,duk wani hanya da zata bi ta samu shiga a wurin shi ya to shi,ko kiran shi tayi a waya baya ɗagawa,taki cin abinci ba ta da aiki sai kuka"

"To ni yanzun Saude me kike son nayi mata?

" Kaka Suraj yana jin maganar ki,kome kija faɗa kai zai amince,ni wallahi tsoro ma nake kar yaje can wurin wa'azin shi wata ta samu nasaran aure shi,tunda matan ma yanzun da kansu suke kawo mashi tallan kansu"

"Kinsan dai shi ba yaro bane ballantana na takura akan sai yayi abinda nake so,ita maijiddarh ta hakura mana,ko ta samar ma kanta mafita amma ni dai kam ba zan iya mai magana ba"

Kuka ta fashe dashi tana rarrafawa gaban kaka"ni dai Kaka ki yi wani abu kai,ni ba zan iya auren kowa ba in ba Yaya Suraj ba,dan Allah ki taimake ni"

Shafa fuskarta tayi"ya isa haka,bari ya dawo za'a san abun yi"

Rungume kaka tayi babu kunya,tana mata godiya kafin su fito shiyan,
Da sauri ta labe ta ƙofar gidan dan ta cikin gida ba wurin da mutum zai labe,

Suna fitowa tsayawa suka yi a ƙofar gida,Momy Saudat ce tace"ya kama mu ƙara dagewa akan wannan lamarin,domin na lura da take_taken Goggon ku,so take ta saka Khadijah a wannan lamarin,dan haka wannan karon idan ya dawo ki yi duk yanda za ki yi alakar ku tafi na da ƙarfi,bana son ya tsubuce mana"

Tsaki taja"Momy kin san halin Yaya Suraj yanda kika san mai zuciyar dutse haka yake,duk yanda mace za tayi ba ya daga kai ya kalle ta,shi yasa wani lokaci take ban haushi "

"To ko zaki hakura?
Zaro ido tayi" Rufa min Asiri Momy,wane ni,ai ba irin Suraj bane ake hakura da shi,Allah dai ya dawo dashi lafiya,amma wannan karon dole salon zai canja"

Da haka dai suka tafi,in da suka bar ta cikin tsananin mamakin su kuma,
Ganin tana kokarin faɗawa tunani ne yasa ta watsar da lamarin ko ma dai menene gara ta cika nata aikin ta bar gidan.

Ana gobe zai dawo Ammi ta saka suka shiga kyaran gida,duk da dama ko'ina a kyara yake ko yaushe amma na yau na da ban ne,
Ita da kanta taje ta kyara mai dakin shi,bata bari ko Amira ta shiga ba,

Ranar da zai dawo ma basu fara shirya abinci ba sai da akayi sallah Azahar,zuwa ƙarfe hudu da rabi gar sun kammala,
Wanka tayi ta nime wuri ta kwanta tana karanta littafin girkin da A'i ta bata,tana kuma tunanin hanyar da zata bi domin samun shiga dakin shi.
Chapter 20 · 0% Book details