← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 96

Sashe 68

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*rayuwata ba ta da wani amfani tunda ni ƴar zina ce,Gara na karar da rayuwata a hanya,gara nabi wasu mazan,sai dai ba zan taɓa haihuwa ba,balle na haifi ƴar da zata maimaita irin abunda mahaifiyata ta aikata,ni ma kuma na aikata,na yi Alkawarin ba zan kara waiwayar su ba har a bada*

Ban shiga harkar bin maza a tsiyace ba,ba kuma ko wani namiji nake bi ba,na canja suna na daga Ummu Salma zuwa BIBA,
Da Abuja na fara,a haka aka Bani kyautar gida,in da anan nake zaune,na fara ma manyan mutane aiki ne shekara biyu data wuce,ina samun manyan kuɗaɗe,
Ana haka ne na haɗu da Ummita,wacce ita kuma kishiyar uwa tai mata Asiri ta sakata bin maza,a haka ta samu ciki shine mahaifinta ya kore ta,
Yarinya ce mai hankali,muna zaune tare muna gudanar da rayuwar mu,ita ta kasance min ƴar uwa,ina son Ummita sosai.

VIP ya fara bani aiki shekara daya da ya wuce a waya,ban sanshi ba,sai dai shi ya sanni,
Yana biya na kuɗi sosai a lokacin,domin ba ni da wani damuwa dashi,
Sai dai wannan karon ya bani wani aiki mai matukar wahala da hatsari,
*daganan ta fara rubuta duk wani abunda akai mata wanda ya mata dadi da wanda bai mata dadi ba a gidan su*

Idanun shi ya tsaya a in da ta rubuta *Yau Suraj ya ce min ina dauke da kazanta a jiki na!shi bai san gaba ɗaya ta kazanta bace?Umm,maganar shi ya min ciyo sosai,har ma nayi kuka,shi bai sai komai ba game da rayuwata,wama ya fada mashi ni Mage ce,Suraj Mugu ne,bayan yasan ina tsoron maciji shine zai fitar da ni dakin shi*

Shafi na karshe a cikin littafin shine in da take faɗin *Ummita ta mutu,sun kashe ummita,ba ni da kowa yanzun!sai dai ba zan taɓa kyale su ba sai na ɗauki fansa ko da zan rasa raina,na riga nama Ummita alkawarin wata rana zan maida ita gida,me yasa zata tafi ta barni*

*idan har Suraj ya fito a yau ina son ya rubuta min saki na domin na tafi,ina son na bar rayuwar su,na karasa fadana da kaina,idan har na samu nasara,zan koma gida bayan shakara Biyar,ina son na ga fuskar iyaye na,ina son na tambaye Mama ko Allah zai sa ta gane waye mahaifina,ina son nayi nasara a wannan shari'ar*

*Ammi ta san ko ni wacece,ta san abinda ban sani ba game da kaina,me ta sani a kaina,ina son in sani*

*cigaban labari*

Rufe littafin yayi yana sauke ajiyar zuciya,"za mu yi nasara tare,ba zan taba rabuwa dake ba Ummu Salma,domin ke wata bangare ce na rayuwa ta "

Jin karan wayar shi ne yasa ya zaro shi daga cikin aljihu,ganin number Ammi ne yasa ya ɗauka da sauri,

"Suraj muna Airport mun sauka lafiya,a wani Asibiti Kuke?

Shi sam yama manta da batun zuwan ta,wannan labarin ya dauke mai hankali" Ku tsaya Ammi gani nan zuwa"

"To kayi sauri dai"

Yana sauke wayar ya dauki littafin sannan ya jawo kofar ya kara kullewa,ya kulle gidan sannan ya nufi Airport rike da takardan a hannu.

Yana isa ita kaɗai ya samu a zaune tana jiranshi,
Karasa kusa da ita tayi yana yi mata sallamah,

Amsawa tayi tana mikewa tsaye tare da rungume shi,shima bai yi kasa a guiwa ba wurin maida mata da kyakkyawar runguma,
Sai fadin "Alhamdullah" Take yi,
Sake shi tayi tana shafa fuskar shi,da wurin idon shi in da yayi dan baki alamu duka ne yasa wurin baki ko buguwa"kana lafiya?

Sumbatar hannun ta yayi"ina lafiya amma,sai dai kuma ita din bansan me zai faru da ita ba,ba na son ta rasa komai nata"

"Da Allah muka dogara,na tabbatar da ba zai taɓa zamar damu ba,yanzun muje ka kai ni in duba ta"

"Ammi ki bari na kaiki ki huta"

Girgiza kai tayi"muje dai kawai,domin hankali na ba zai taɓa kwanciya ba har sai na ganta"

Ba yanda ya iya dole Asibitin suka tafi tare,

Da Abbu suka fara haɗuwa wanda ba karamin jin daɗin ganin Matar tashi yayi ba,dan ba karamin kewarta yayi ba.

🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*68*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Bai damu Suraj din dake wurin ba sai ma rungume ta da yayi"barka da isowa"

Dan dariya tayi tana kokarin zamewa daga jikin shi "yaron mu na kallon" Ta faɗa cikin raɗa,

Shima cikin raɗan yake ce mata"shima ta matar shi yake yi"

Jin muryar Dady na kyaran murya ta bayan su ne yasa ya sake ta da sauri yana dan waskewa,

Dariya yayi"sannu da isowa Ammin yara,tunda baki ganmu ba"

Cikin jin kunya ta kara gaida shi"sannun ku da Ƙoƙari,Allah ya biya ku"

"Ki dai na fadar haka domin shima Suraj ai ɗan mu ne,yanzun dai sai dai mu yi fatan Allah ya tsare na gaba,sannan ita kuma matar shi Allah ya tashi kafadar ta"

Duk da Amin suka amsa,

Abbu na riƙe da hannun ta har bakin ƙofar I.C.U in da take ciki,
Shima yana tsaye ta Glass din yana kallon ta,yayin da zuciyar shi keta ruwaito mashi abubuwa da yawa a kanta,

Dafa kafadarsa tayi"insha Allah zata ji sauƙi "

Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon ta"I Hope so"

"Yanzun me likita yace?

" Yau za'a mata aiki,amma na roƙi Alfarma ko za'a iya maida ita Kano,in ya so sai ayi aikin a can, ni ko nawa ne zan ɗauki nauyi,domin ina ganin hankalin mu zai fi kwanciya,sannan zata fi samun kulawa"

Jinjina kai tayi "tabbas kayi tunani,yanzun me suka ce,hakan yai yu?

"Eh amma zasu amfani da private jet ne na wannan Asibitin sai a tafi da ita," Rike hannun ta yayi"kiyi haƙuri Ammi na baki wahala"

Girgiza kai tayi"duk wahalar da zan sha bai kai kashi ɗaya ba cikin wanda kake fuskanta,buri na dai shine Allah ya tashi kafadar su"

"Amin"

"Ammi muje ki ci abinci kafin lokacin tafiyar mu tayi"

"Da yake yau Alhamin ina azumi"

Murmushi yayi "haka ne Ammi na manta"

Abbu ne ya karaso,dan dama yana barin ta tare da Suraj suka fita da Dady"lokacin tafiya yayi "Ammi gashi kina isowa zaki juya"

"Babu komai"

"Yauwa to mu je,domin ke zaki bimu ne mu tafi tare,shi Suraj sai ya biyo jirgin Asibiti da mara lafiyar"

"To ba damuwa" Dan juyawa tayi "tunda na iso banga Pa ba dasu Nadiya?

" Nima tunda muka rabu a kotu ba mu haɗu ba,sai dai ya kirani yake shaida min wani uzirin gaggawa ya taso masu zasu tafi,sannan yace na faɗa maki yana tayaki murnar fitowar Suraj,amma in sun samu lokaci zasu dawo"

"To ba damuwa Allah ya tsare"

"Amin" Suka amsa.

Tare suka fito daga cikin Asibitin ya masu rakiya har wurin parking suka shiga mota sannan ya koma cikin Asibitin.

Yana shiga ya samu har sun canja mata kaya an kuma Daura ta a wani gado suna ƙoƙarin fitowa da ita,
Da sauri ya ƙarasa in da suke,yana rike hannun ta da yaga ya sauko,
Lumshe ido yayi ya buɗe yana sauke numfashi kafin ya maida mata hannu saman cikinta yana gyara rufan da aka mata da wani tsaftataccen zanin gado,

Ko a cikin jirgi yana zaune kusa da ita yana karanto mata addu'o'i,
Kusa da ita ya zauna yana tsura ma kyakkyawar fuskarta ido,yana kallon yanda numfashin ta ke hawa da sauka ta cikin oxygen,
Hannu yasa a hankali ya shafa gefen fuskarta,yana ƙara jawo mata hular kanta wanda ya dan zame kaɗan aka ganin lallausar sunan kanta wanda yake baki kirin ya kuma kwanta sosai.

Daya daga cikin likitocin da suke cikin jirgin ne wanda duk abinda yake yana kallon shi yana murmushi yace"you Love her a lot"

Shima murmushi ya sakar mashi kawai ba tare da yace komai.

Ƙarfe Biyu na rana tai masu ne a cikin garin Kano, wanda kai tsaye a cikin babban Asibitin su jirgin yayi Landing,

Wasu manya daga cikin Asibitin wadanda suka san da zuwansu su suka tsaya suka tare su,har aka shigar da ita dakin da ya kamata aka saita komai sannan suka fito,

Babban likitan da zai yi aiki ne ya dafa kafadar sa"Abokina ka kwantar da hankalin ka,ka je gida ka huta domin kai ma daga dukkan alamu kana bukatar hutu,karka ka bari Stress ya yarda kai,domin kai kaɗai ne zaka iya kula da matar ka,shi yasa nake son yanzun kaje gida kayi wanka ka huta ka ci abinci sannan ka samu isasshen bacci,tunda sai karfe tara na ayi aikin nata,mun matsar da shi ne saboda tafiyar da muka yi,ka ga kafin lokacin ka huta harka dawo"

Shi kanshi yasan yana buƙatar hutu,domin tunda ya fito wannan abun ya faru da ita bai samu natsuwar zuciya ba,"na gode sosai Doctor,zan tafi amma dan Allah idan wani abu ya taso ka sanar da ni "

"Karka damu"

Daganan yana fitowa abin hawa ya tara ya kaishi har ƙofar gida,Allah yasa duk mutane suna cikin masallaci suna Sallah dan ba'a idar ba,
Shigewa cikin gida kawai yayi bayan ya sallami mai Adaidaita, ,nan ma ko da ya shiga bai ci karo da kowa ba har ya buɗe dakin shi ya shiga ya maida ƙofa,
Tsayawa yayi yana ƙare ma dakin kallo,
Komai a gyare yake tsaf,sai Ni'imtaccen kamshi ke tashi,wanda ya san wannan aikin ammi ne,tunda kullun da kanta ke shigowa ta kyara ɗakin,
Idanun shi ne suka tsaya a daidai tsakiyar falon,
Wani tunani ne lokaci ɗaya yazo ya gilma ta zuciyar shi, wanda ya saka sai da yaji tsigar jikin shi na tashi,
Ba komai ya tuna ba face ranar data sumbace shi a tsakiyar falon,
Da sauri ya shiga kiran sunan Allah,yana ƙoƙarin kauda wannan tunanin daga zuciyar shi,
Chapter 68 · 0% Book details