← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 96

Sashe 56

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko asalin cikin gidan abin kallo ne ba sai na tsaya faɗa maku ba,
Tana ganin sun shiga cikin gidan ta fisge hannun ta da gudu ta karasa cikin falon gidan tana kiran sunan Mama babu kakkautawa,

Cikin sauri ta fito daga kicin hannun ta rike da Cokalin miya,
Dafe Kwankwaso tayi tana kare masu kallo,
Itama dafe kwankwaso tayi tana kallon Mama tana kyafkyafta ido,ganin Mama na ma Ya Abdul majid signal akan ya kamo mata ita ne yasa ta zabura zata gudu dakin ta,duk bin bayanta suka yi yayin da suka shiga zagayen falon suna dariya,har Mama ta samu nasarar kamata a ɗaura a kafaɗa tayi kicin da ita,
A wannan lokacin shekara ta goma sha huɗu a duniya,ba ta da wani nauyi sai tsayi,
Wurwurga kafa ta fara tana rokon Mama "dan Allah bana karki shigar da ni kicin,bana son kicin"

"Ni kuma bana son kira kamar wata batatta"

"Mama kiyi haƙuri ba zan kara kiran ki ba"

Direta tayi a gaban sink din kayan wanke-wanke, "ga aikin ki nan"

Turo baki tayi tana fashewa da kuka,dan ita a rayuwa ba aikin data tsana irin ace tayi shara tayi wanke-wanke,kallon Abdul Majid da Abdulmalik take tana mika masu hannu,

Dan marairaice fuska Abdul Majid yayi"Mama na taya ta?

Girgiza kai tayi "No"

"Pls Mama,let us help our little sister"

"Kuje ku kyara min dakin Baban ku yanzun"

Badan sun so ba dole suka tafi,
Ganin sun wuce ne yasa dole tayi shiru domin ta san a wannan lokacin Mama ba kula ta zata yi ba,
Dan haka Safar hannu dasuke amfani dashi wurin wanke-wanke ta saka sannan ta buɗe fanfo ta fara,

Kiran da aka ma Mama a waya ne yasa ta dauka tana barin kicin din,

Kamar jira suke ta fita sai ga Abdulmajid ya shigo "kawo safar hannu"

Zarewa tayi ta bashi,nan da nan kuwa ya shiga taya ta wankewa tana daurayewa har suka kusa kammalawa,
Jin takun tafiyar Mama ne yasa da gudu ya fita kicin din ya bar ta bayan ya cire safar,
Da sauri ta maida shi a hannun ta tana ƙara marairaice fuska,

Kallon kayan tayi ta kalle ta"ke waye yazo ya tayi ki"

Kumbura baki tayi"babu kowa"

Girgiza kai tayi domin tasan karya take yi,wannan saurin ba nata ba ne,

Sai da ta saka ta kammala ta wanke wurin sannan ta bari ta fita,

Ɗakinta ta shiga wanda ya ji ado da kayan more rayuwa irin na matasan yan mata waɗanda ake ji dasu,

Hayewa tayi saman kushin ta ɗauki wayarta tana buga game,
Ba adau wani lokaci ba sai ji tayi ana ƙwanƙwasa mata ƙofa,
"Come in" Ta fada da ƙarfi,

Turo kofar Mama tayi"ki fito ki ci abinci"

"Na koshi"

"Bana son jin haka maza ta so mu je"

Ajiye wayar tayi ta fito,ko da suka fito har yannin ta sun fito ko suna zaune sai Baba da shima shigowarshi kenan,
Da gudu ta karasa inda yake ta rike hannun shi"Baba na barka da fitowa"

Murmushi yake saki "barka mai gimbiya,da fatan kin tashi lafiya"

"Lafiya glau"
Zama suka yi a saman babban Darduma na falon,duk barka da fitowa suka mai,
Mama ce ta zuba ma kowa abincin kari,
Cikin natsuwa suke ci babu mai magana har suka kammala ita ta kwashe kayan ta mai da su kicin sannan mai aiki tazo ta wanke,

Dawowa falon tayi ta zauna a tsakiyar yannin ta,"Baba ina son in siya wani takalmi dana gani ana tallah a online "

"Nawa zai maki?

" Dubu hamsin "

"Zan tura maki,ke ma ban manta da Alkawarin mu ba"ya faɗa yana kallon Mama,

Kiran da aka mashi a waya ne ya katse su,
Sun dai ji yace" Shigo"

Ba jimawa kuwa sai ga wani matashin saurayi ya shigo cikin falon da sallamah,daga dukkan alamu shi din ɗan gidan matsakaita ne daga ganin yanayin kayan jikin shi,kana kuma iya saka shi a sahun talaka amma ba tubus ba,
Kyakkyawa ne baki ba laifi dan alokacin rashin kuɗi ya hana kyan shi fitowa,

Dukawa yayi ya tsugunna har kasa yana gaida su,Baba da Mama ne suka amsa mashi sannan ya gaida su da suke kallon shi dan ba Kasafai Baba ke bari wani ya shigo har cikin falon shi haka ba,

"Wannan shine *Yusuf*,shekaran jiya ya fara aiki a kamfani na na Suger"

Kallon yaron Mama ta kara yi,nan take fara'ar dake fuskanta ya ɓace "gaskiya wannan yayi ƙarami"

"Na dauki wadanda basu kai shi komai ba kuma sun iya balle shi,kuma a matakin manager zan Daura shi"

"Allah ba da sa'a ta faɗa tana mikewa tare da barin wurin,
Sallamar shi Baba yayi akan ya jira shi a waje yanzun zai fito.

Ranar ƙarfe hudu suka kuma zuwa islamiya wanda da ma hakan yake duk ranar sati da Lahadi sau biyu suke zuwa islamiya,
Tana zaune a aji ana karɓar hardansu na Kur'ani sai ga Malam babba ya aiko a kira ta,
Sai da malamin dake ajin ya karɓi hardan ta sannan ya bari ta fita,domin haka dokar su take,to yanzun haka tana izufi Arba'in da biyu ne a harda,
Tana shiga ofishin shi da sallamah ta gaida shi cikin Girmamawa,
Nuna mata gefen shi yayi"Me alaƙar ki da waɗannan "

Kallon su take daya bayan daya kafin ta zare ido tana kokarin karasa kusa da ɗayan,
Dakatar da ita yayi"baƙi Bani amsa ba"

"Malam wannan yaya na ne,sai wannan kuma saurayi na ne"

Kallon ta sauran Malam dake ofishin suka yi,
Daya daga ciki ne yace"kai jama'a lallai duniya ta zo ƙarshe,yanzun ke ƴar ƙarama dake har kinsan ki nuna wani a matsayin saurayin ki ba tare da kinji kunyar idanun mu ba?

Bata fuska tayi"Malam to ai naga ku kuke faɗa mana ƙarya haramun ne,yanzun kuma dan na faɗi gaskiya sai ace nayi rashin kunya?dama fadar gaskiya na zama rashin kunya lallai duniya ta zo karshe"ta faɗa tana dafe gemunta da hannu,

Dariya Malam babban yayi,dan yanda ta karasa maganar dole ya baka dariya,kallon su yayi"me ya hada ku faɗa a kanta"

Ɗayan yaron ne da bai wuce shekaru sha biyar ba yace"Malam muna hira ne a ajin mu shine kowa ke fadin sunan budurwa shi,ni kuma da aka tambaye ni na kira sunan ta,shine fa ya taso ya ƙoda min Mari wai akan wani dalili zan ce ita duburewa ta ce "

Maida kallon shi kan Abdulmajid Malam babba yayi"da gaske hakan ne ya faru?

Dukar da kai yayi "haka ne Malam"

"Yaya" ta kira sunan shi cikin jin haushin abinda ya aikata,

Dagowa yayi yana hararan ta"Do you tell me?

"Amma ai dama zan faɗa maka"

"To be mun ba"

"But I Love him"

"Sama da ni?

Lokaci ɗaya kuma ta saki murmushi ta tako har gaban shi ta rungume shi" Ai kai rayuwata ce,duk kuma abinda rai bai so ai barin shi yafi"

"Da gaske"

Jinjina mashi kai tayi "sosai,dan haka karka kara faɗa da wani"

Murmushi ya saki shima"good Girl "

Sake shi tayi"Malam kayi haƙuri yaya na bazai ƙara faɗa ba,"

"Ke ce bakin shi?

" Umm "ta fada maimakon ta cewa A'a,

Dan waro ido yayi" Umm"

Shiru ta mai dan wannan tambayar Malam Buhari ne dama kuma shi ba shiri suke yi ba,

"Ku biyo ni dole zaku karɓi hukunci domin makaranta ba wurin wasa bane,ba kuma wurin dambe ba ne"

Tashi suka yi suka bi bayan shi har ofishin shi,ganin ya dauko ƙato bulala ne yasa ba shiri ta shiga rokon shi akan dan Allah yayi haƙuri karya Duke yayan ta,

"Ki koma aji domin dole sai an hukun tasu".

🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*56*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Kin tafiya tayi ta tsaya a wurin har Malam Buhari ya dauko bulala ya shiga zuba ma Yaya Abdulmajid,a duk bulalan da zai sauka a jikin shi ji nake tamkar a jiki na yake sauka,shi ake duka amma ni make faman zuba kuka shi kuma yana faman faɗin "ya isa haka ai babu zafi ma,ki dai na kuka"

Shi kuma mugun malamin sai ƙara dukarmin yaya yake yi,
Jin irin kukan da nake yi har da hadawa da ihu ne yasa Malam babba ya fito daga ofishin shi yace dukan ya isa haka ya bar su,
Dole ya bar su badan ya so haka ba,dan yaran haka kawai suke bashi haushi saboda yanda yake ganin su ko yaushe a tare,
"Malam ban fa yi mashi wani bulala ba,kawai makirci ne irin na wannan yarinya ita kullun haka take in dai za'a daki daya daga cikin yannin ta sai ta zo ta tasa mutum da kuka kamar ana yanka su"

Murmushi Malam babba yayi yana kallon yanda take cigaba da kuka tana duba tafin hannun yayan nata,shi kuma sai cewa yake"ai hannun ba yamin zafi,ki bar kuka haka"

"Tashi ku koma aji"

Mikewa suka yi suka fita sai da ya raka ta har bakin ajinsu ya tabbatar ta shiga sannan ya koma nashi ajin,

Ko da aka tashi islamiya tare suka jero sun saka ta a tsakiya kamar ko yaushe,
Abdulrahman ne yace"wai ke yaushe zaki daina wannan fushin ne,na ga shi wanda aka daka har ya hakura amma ke sai fushi kike yi"

"Yaya wallahi malamin nan haushi yake bani,kome nashi na mugunta ne,amma bari sai nayi maganin shi"

"Me zaki mashi? Cewar Abdulmalik,

" Sirri ne"

"Don't just go and do anything stupid" In ji Abdulrahman,

Kin bashi amsa tayi sai ma ƙara sauri da tayi ta yi gaba ta bar su,dole da sauri suka bi ta,

A ƙofar gida suka haɗu da Yusuf yana zaune,
Yana ganin su ya tashi ya mika masu hannu suka gaisa,
Abdulrahman ne yace"me kake yi a ƙofar gida?

"Ba komai kawai dai na shigo ne mu gaisa Mama tace kuna islamiya"

"To ai daka zauna ciki,shigo mu je"
Chapter 56 · 0% Book details