Sashe 93
Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Banki ta abinda ka faɗa ba,sai dai ka sani yawancin mata sun fi son ko da yaushe kana faɗa masu cewar kana son su,kuma suna da matukar muhimmanci a rayuwar ka,ta yu ita matarka tana ɗaya daga cikin irin jerin waɗannan matan,amma kuma kai saboda wani ra'ayi naka baka taɓa faɗa mata cewar kana son ta ba,ko ka taɓa?
Girgiza kai yayi" Ai naga ita ba yarinya bace"
Dafe kai yayi yana dan girgiza shi "Oh My God!Suraj,ni fa abin da nake ta kokarin in faɗa maka shine su mata komai girman su da tsufan su tamkar yara haka ƙwaƙwalwar su take,suna son su ji ana faɗa masu cewar su masu kyau ne,kamshi na da daɗi,idan sun yi kwalliya kuma ace sun yi kyau,sannan a fada masu ana son su,suna son kalamai masu daɗi da kwantar da hankali,kamar yanda suke son kayan daɗi,idan har zaka iya saukar da kai to ka gwada "
"Kana ganin hakan zai yi amfani?
" Idan har ita mai ra'ayin soyayya ce to hakan zai yi amfani "
"Ka yankar min tiket na Kano"
"Kano kuma?ko dai Niger?
" A'a ina son in je in duba Kaka ne"
"Shi kenan".
*washegari*
Kamar yanda ya faɗa mashi kuwa haka yayi dan zuwa ƙarfe goma na safe jirgin su ya tashi daga nan Legas zuwa Kano,
A gidan shi ya sauka,sai da ya huta zuwa Azahar sannan ya nufi gida,
A bakin Get ya haɗu Nurudeen,tsawa yayi ya bashi hannu suka yi musabaha,
Tambaya shi yake"yaushe ka dawo?
"Dazu,ya garin?
" Lafiya qlau,hala wurin mutuniyar kazo?
Dan murmushi yayi"kasan dole sai ana yi ana leko ta"
"Gaskiya kam,to mushiga ciki"
Tare suka jera suna dan tattaunawa har shiyan kaka,domin yanzun duk sun zubar da makaman su,saboda sun san yanzun ko kusa shi ba abin rainawarsu ba,dan nasabarshi ma har yafi nasu,
Ba karamin daɗi Kaka ta ji ba har da hawayen farin ciki,dukda ta san yana yawan shigowa ya dubata,amma ta ji kewar shi saboda a da kullun ai suna tare in dai ba ya tafi wani wurin ba,ko yayi tafiya zuwa wa'azi,
Goggon yara ce ta shigo dauke da kulolin abinci a hannun ta,ajiyewa tayi tana faɗin "kai kuma yaushe a gari?
Cikin girmamawa kamar ko yaushe ya shiga gaida ita,
Amsawa tayi tana fadin bari a zubo maka abinci,
" Ai kuwa dama yunwa nake ji,gashi kaka ko ruwa bata Bani ba"
"Ja'iri ai daɗin ganin ka ne yasa ni sha'afa,jin ga zubo mashi"
Da waya kuwa ta zuba mashi,yana cikin ci ne Salman ya shigo,sabar ɗokin ganin shi saura kaɗan ya barar mai da abinci,
"Wai kai yaushe za ka yi hankali?
" Yaya ai in ina ganin ka ba zan taɓa yin hankali ba"ya faɗa yana zama kusa da shi,
Girgiza kai kawai yayi yana kallon Nurudeen da ya mai da hankalin shi wurin daddanna waya,"yaushe ne bikin naka"
Dagowa yayi ya kalle shi"Malam da saura,dan har yanzun bamu gama daidaitawa da yarinyar ba"
"To kadai yi ƙoƙari,so muke ka yi Azumi da mata bana"
Tabe baki yayi,
"Ina Ibrahim ne?
" Yana wurin aiki"
Goggon ce ta katse shi"ina yarinya ta?
Ya san wacce take nufi"tana Minna"
"Gaskiya dai ta kamata ta dawo dakin ta haka,kun yi magana da ita kuwa?
" Eh gobe zani can din ma"
"In dai har zata dawo ka kawo mana ita"
"Insha Allah"
Ya jima sosai suna hira kafin ya masu Sallamah akan zai fita zuwa anjima zai dawo,dan so yake yaje gidan yari ya duba
Abbu.
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*93*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Ba tare da wani matsala ba yana zuwa Gidan Yari aka bar shi ya shiga har zuwa wurin da suke ganawa da baƙi,
Zaman mintuna biyar zuwa bakwai yayi sai ga shi ya shigo,
Mikewa tsaye yayi har sanda ya kara so,
Cikin girmamawa kamar ko yaushe ya gaida shi,
Amsawa yayi cikin sanyi murya yana zama kanshi a kasa,
Shima zama yayi suna fuskantar juna"Abbu!"sai kuma yayi shiru ya rasa me zai ce,Abbu Sufyan mutum ne da yake matukar girmamawa kodan son da yake ma Ammi,ko dan daurashi da yayi akan tarbiya na gari,sai dai lafinshi babba ne,laifin kisan kai ba karamin abu bane,
"Ka yafe min Suraj!nasan na aikata kura-kurai masu yawa a rayuwata waɗanda a matsayina na masani,na take sani na nayi abinda nake so,na bi son zuciya,gashi a in da na ƙare" Ya fada yana fashewa da kuka,
Duk yanda zuciyar shi takai ga motsawa yaki yarda ya zubar da hawaye,sai dai idanun shi da suka yi ja,
"Ni na yafe maka Abbu ko dan Kanwata Amira,amma ka sani Allah baya yafe laifin wani sai in shi yace ya yafe maka,
Mutanen da kuka kashe fa yaya za ku yi dasu?waɗanda kuka yi sanadiyar mutuwar su fa?iyalansu da kuka saka cikin halin damuwa,zullumi da bakin ciki fa Abbu?yaya za ka yi da nasu haƙƙin?"furzar da iskar bakin shi yayi,"Na roki Ammi da Grand ma,akan su yafe maka,sun yafe maka,domin rashin yafe maka ma babu abinda zai kara masu ko sai ma ya rage su,naso ace ko da sau daya ne ta zo ta ganka kamar yanda ka roka,sai dai taki yarda,ni kuma ba zan iya tilasta mata ba,"
Kuka yake yi sosai,wallahi_wallahi har ga Allah yayi nadamar abinda ya aikata,
Mikewa yayi"ina maka fatan samun sassauci daga wurin Allah"
Ya juya ya wuce,duk da ya so ya duba Shamsuddeen sai dai ba zai iya ba,saboda zuciyar shi ya riga yayi sanyi da ganin yanda Babban malami kamar Abbu Sufyan ya tafka babban kuskuren da yanzun yake kuka da na dama,lallai duniya budurwar Wawa ce,sai yanzun ya kara yarda da maganar Hausawa.
Sai zuwa Yamma ya koma Gidan Kaka,in da anan take sanar dashi ai Maijiddarh za tayi auren wata mai kamawa,zata auri daya daga cikin Alarammomin da suke fita dasu wa'azin,mutumin matan shi biyu ita ce ta uku,
Hajiya Saudat kamar za tayi hauka tsabar tashin hankali har da yaji,
Amma babu wanda ya kulata da kanta ta gaji ta dawo,
Addu'ar samun zaman lafiya kawai ya mata,
A daren ne da zai wuce yaba Salman kyautar makullin mutar nan nashi,ai kuwa tsabar daɗi har da kukan farin ciki,duk wani ahali na gidan da ya samu labarin wannan kyautar sai da ya jinjina ma Suraj.
Washegari jirgin safe yabi zuwa Minna,
A gidan shi ya sauka,sai zuwa da yamma sannan ya shigo Bosso,
Yaro ya aika aimasa iso,
Tana jin sunan wanda aka faɗa tace maza ace ya shigo,
Yana shigo har ƙasa ya tsugunna ya gaishe ta,
Cikin jin daɗi ta amsa tana nuna masa babban tabarmar data shimfida masa har da darduma,a gindin icce,kasancewar ana ɗan taɓa zafi a garin,
Tambayar shi take ya mutanen gida,cikin sakin fuska yake amsa mata,
Dama ta riga ta gama girki,dan haka zubo mashi lafiyayyen Gurasa tayi a plate wanda yaji kayan haɗi da ganyayyaki kabeji,salat,karas,har da yankakken tumatur,ga dakan kulin yaji tafarnuwa da citta,
Ai kuwa sake jiki yayi yaci sosai dan har ya manta rabon da yaci irin wannan abinci,gaskiya yayi missing Ammi,
Ganin ya cinye ne yasa Kaka tace ko a kara mashi,girgiza kai yayi yana Hamda,
Kasancewar ta mace mai surutu gata da iya jan mutane da hira yasa cikin lokaci kankani ta saka ya sake da ita,hira suke sosai har da dariya,
"Mutuniyar taka ta fita motsa jiki,yau da kyar na nasamu na korata tabi Hulaira,kullum ba tada aiki sai kwanciya,idan dare yayi kuma ta hana kowa bacci wai jikin ta na ciyo,
Shi yasa na tura su Tudun Fulani can kusa da Dam,gidan yar kanwa ta Mariya,maman Hafsat da Haidar,"
"Ko ba tada lafiya ne dai Kaka"
"Kyale ta shegen taka ne kawai,yau kuma akwai labari"
Ko gama rufe baki ba tayi ba sai ganin ta sukayi ta shigo babu ko sallamah ta shiga cilli da takalman ƙafarta,da dingishi ta karaso ta dauke ruwan goran dake gaban shi ta ƙafa kai,sai da ta shanye tas sannan ta ajiye goran,
Aunty Hulaira ce ta shigo tana kyalkyalan dariya,
"Ke kuma me haka zaki shigo ma mutane gida babu sallamah?
Dan waiwaigawa tayi ta jawo kujera ta zauna kusa da kaka tana mika mata ƙafa" Danna min ƙafa "
"Ko uwa ki bata Hulaira bata isa ba balle ke"
Ai kuwa kafin su ce me sai hawaye sharr ta fara,
Salati kaka ta saka"ke Hulaira zo ki gane min ikon Allah,Suraj kalli lalaci irin na matarka me aka mata yanzun take ma mutane kuka?
Ita sai lokacin ma idanun ta ya sauka a kanshi daya zuba mata ido,ai kuwa harara ta zuba mashi tana ci gaba da matso hayawan ta,
Aunty Hulaira ce ta maso"me ya same ki?
"Aunty ƙafa ta kamar zai karye ciyo yake min,gashi kaka taki ja min kafa"
"Taso muje na ja maki"
Girgiza kai tayi"ba zan iya ba,"dan tsakani da Allah ji take ƙafafun ta kamar basa jikin ta,
Kwanun dake gefen ta ta jawo tana buɗewa "Kaka kin yi mana gurasa kuwa?
Girgizar kai kawai Aunty Hulaira tayi tana amsa gaisuwar ta da Suraj yake yi,
Ganin gurasa a kwanu yasa ta saki murmushi" Ina Balango yake"
"Ai baki ban kuɗi ba"
Ture kwanun tayi tana turo baki "to ni dai ba zan ci gurasa ba babu tsire ba"
"Eh,ai kuwa gurasar mu za tayi auki"
Cikin sanyi murya yace "muce na siya maki"
Hararanshi tayi"bana so"
"Ai kuwa kin ma kanki domin babu me siyo maki"
Mikewa yayi "kaka zan tafi sai zuwa anjima"
"To ɗan Albarka sai ka shigo,dan Allah ka din ga haƙuri da ita na ga ko gaisheka ba tayi ba,ita wannan cikin nata da jarabar masifa yazo mata"
Da sauri ya jiyu yana kallon ta,kamar zai yi magana sai kuma yayi shiru bai ce komai,