← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 96

Sashe 57

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bin su ciki yayi sai da suka shaida ma Mama sun dawo kafin su shiga nasu falon dashi,

Tana gama cire kaya dakin su ta shiga bayan ta canja wani,zama tayi cikin su suka shiga yin hira,
Kallon Yusuf tayi "Ka iya game?

" Wani iri?
"Motal comebat"

Girgiza kai yayi"A'a "

"Yana da daɗi sosai bari na koya maka"

Jona TV tayi ta haɗa da kayan game,nan suka shiga bugawa tana yi tana nuna mashi,
Sai da lokacin sallah yayi sannan suka fita masallaci ita kuma ta shige daki,

Washegari tunda Asuba ƙarfe biyar kafin ayi sallah ta tashi bacci ko wanka bata yi ba ta buɗe ƙofa ta nufe shiyansu,bubbuga masu ƙofa ta fara da karfi tana kiran Ya Abdulrahman,ya Abdulmajid,ya Abdulmalik,haka ta shiga kira tana buda ƙofa wanda ƙaran haka ne ya tayar da Baba ya fito yana haskawa dan jin ko lafiya,
Ganin ita ce yasa yace"Gimbiya lafiya?me kike yi a nan yanzun"

Turo baki tayi cikin jin haushin kyale ta da sukayi tace"Baba yau fa Birthday dina so nake su bani kyautar karin shekara"

Dafe goshi yayi"My gimbiya yanzun fa ƙarfe biyar na asuba tayi,ko sallah ba'a yi ba,ki je ciki idan gari ya waye zasu baki "

"Ba zasu bani"

"I promise you zasu baki"

Juyawa tayi ta shige cikin shiyansu ta bar wurin,
Girgiza kai kawai yayi yana kwankwasa masu kofa sau daya tare da kiran sunan su,
Nan take kuwa sai gashi ko wanne yana buɗe ƙofar dakin shi yana fitowa,
Kallon su yayi"Amma kuna jin kanwar ku ko?

Hamma Abdulrahman yayi"Baba wallahi she is really Stoburn"

"Lokacin sallah yayi sai ku fito mu tafi masallaci"

"To Baba"

Koda suka dawo masallaci da zasu kulle kofa daga mai saka filo ya toshe kunne shi sai mai saka Earpis a kunne, dan kawai kar su ji damun da zata masu,
Sai dai fa duk da haka ƙarfe bakwai na safe na cika ta dauki katon sanda ta shiga bugun kofar su dashi tana kiran sunan su,
Ganin ba su da niyar buɗewa ne yasa da kuka ta nufi cikin gida dakin Mama wacce take kwance tana waya,
Kwantawa tayi kusa da ita tana cigaba da kuka wanda ganin haka yasa ta ajiye wayar"me ya faru?

"Mama su Yaya sun ƙi tashi su ban Happy birthday"

Kallon agogon bangon ɗaki tayi "ƙarfe bakwai yanzun,ki bari idan sun tashi zasu baki"

"Wancan karon ma haka suka min fa Mama,ni dai yanzun sun daina so na"

"Salma pls barci nake ji kin ji Sweet heart"

Sauka tayi akan gadon tana barin ɗakin ta shige nata ta kulle ƙofa,
Komawa tayi ta kwanta kan gado tana jin haushin abinda suka mata,daga haka barci ya ƙara kwashe ta,
Ba ita ta farka ba sai ƙarfe goma saura,banɗaki ta shiga tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga na Les ruwan ƙwai da fari,
Ba karamin kyau kayan ya mata ba,sai Mayafin data yafa,ta fito shar da ita yanda kasan wata Ƴar Tsanar Zinari,

Ji tayi an Kwankwasa mata ƙofa,dama kuma tana shirin buɗewa ne dan haka buɗewa tayi,
Ji tayi abu mai ƙyalli ya zubo mata a kai yayin da yannin ta ke tsaye a gabanta suna mata waƙar Happy birthday to you,
Duk irin yanda take jin haushin su ganin yanda suke murmushi da dariya yasa ba shiri itama ta saki dariya tana kama ƙananan fulawar dake sauka a jikin ta,
Hannun ta Abdulmajid ya jawo suka gangaro da ita ƙasa,anan ta tarad da Mama rike da katon cake tana jiran isowar ta an kunna kendu a jikin shi,

Karamin wuƙa ya mika mata ta amsa,suna mata waka ta yanka cake ɗin,
Mama ta fara saka ma abaki kafin ta shiga saka masu daya bayan daya,sai Yusuf dake gefen shima yana murmushi dan ba karamin burge shi suke yi ba ta saka mashi shima a baki.

Wannan shine asalin rayuwar su mai ɗauke da farin ciki da annashuwa,

A hankali shakuwa ke ƙara shiga tsanin su da Yusuf wanda take kira da Game partner saboda duk lokacin da yazo gidan suna tare suna buga game yana biye ma duk wani shirmenta,kamar yanda yannin ta ke mata,

Wata biyu da cikar ta shekara goma sha-biyar takardar nima mata jam'i ya fito a London wanda anan zata karanta Lauya na tsayin shekara biyu,

Koda Baba ya kawo mata takardar a maimakon yaga farin ciki shimfide a fuskarta sai damuwa daya hango,yayi tambayar duniya amma sai ce mashi take babu komai,karshe ma sai tashi tayi ta fito daga falon shi wanda a bakin ƙofar fita ne suka haɗu da Yusuf yana ƙoƙarin shiga wurin Baba,

Kallon shi tayi na sakan ni kafin ta ɗauke kai tayi wucewar ta,
A cikin yan watannin nan da yayi tare da su,ta lura ba karamin ji dashi Baba yake yi ba,yanda yake ma Yusuf ko su Yaya baya masu haka,idan har Yusuf zai ce yana son abu to cikin rawar jiki kuwa zai ɗauka ya bashi har ma fiye da yanda ya tambaya,
Shida iyayen shi Baba ya basu wani tankamemen gida wanda babu abinda babu a ciki,sannan ga Mota lafiyayye ya siya mashi,amma su yaya tun yaushe suke bin shi ya sai masu mota yaƙi sai dai duk inda zasu Direba ya kai su,

A babban falo taci karo da Yaya Abdulmajid,rike ta yayi"ke kuma tunanin me kike kina tafiya?

Kallon hanyar data fito tayi "na fara jin haushin Yusuf" Ta faɗa tana tura baki,

Kama baki yayi yana dafe kwankwaso"ke kuma da ya maki me?

"Kalli fa yanda yake shiga dakin Baba kai tsaye yanda kasan wani Baban shi"

Rankwashi ya sake mata a kai"to ai Baban shi ne tunda yaron aikin shine,kin ga ban son gulma je ki faɗa ma Baba masu karɓar sadaka suna waje suna jira "

Dafe kanta tayi tana bata fuska "ba zan je ba ka je da kanka" Ta faɗa tana rugawa da gudu tayi hanyar dakin Mama,

Girgiza kai yayi "kyuya ko?zamu haɗu da ke" Ya faɗa yana wucewa dan sanar dashi,domin Al'adar shine yin sadaka a ko wani yamma,daga wurare ma mutane kanzo karɓar wannan sadakar nashi,shi yasa mutanen unguwar su ke girmama shi sosai,

Dakin Mama ta shiga da sallamah ta same ta a zaune kamar ko yaushe ita kenan yawancin lokaci cikin amsa waya,sam Mama bata gajiya da amsa waya,

Zama tayi kusa da ita "Mama"

Sallamah tayi da wanda take wayar ta juyo kanta"ya akayi Sweet heart?

Miƙa mata takardar tayi,

"Na menene?

" Na makaranta ne a London "

Nan take ta sake murmushi ta jawota ta rungume "Oh Sweet heart congrat yaushe ne tafiyar?

" Nan da sati biyu "

Ganin yanda tayi maganar cikin damuwa ne yasa ta ƙara kallon ta"me ya faru,ya naga kamar you ar not happy "

Ai kuwa kamar dama jira take ai mata wannan tambayar ta fashe da kuka wanda yi take ba kakkautawa,
Duk ta tashi hankalin Mama sai aikin lallashi take yi,
Da kyar ta samu tayi shiru ta natsu,
"Faɗa min meke faruwa"

"Mama ke kika ce duk abun dake damuna a should feel free to tell you"

Jinjina kai tayi"sosai ma faɗa min ko ma menene I will be here for you "

Share hawayen idon ta tayi da yaƙe dai na zuba.
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*57*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

"Mama ina ganin ina da karfin sha'awa"

Zaro ido tati cikin mamakin jin abunda yarta ta faɗa "Ƙarfin sha'awa kuma Salma?

Shiru tayi ta dukar da kai tana murza ƴan yatsun ta,

Ajiyar zuciya ta sauke tana ƙoƙarin saisaita kanta" Ta yaya kika san haka,i mean ya kike ji a jikin ki?
Ganin taki cewa komai ne yasa ta riƙo hannayen da take murzawa "ba na ce zan taimaka maki ba,dan haka faɗa min "

Dan rintse ido tayi ta buɗe,tana jin kunyar yanda zata faɗa,sai dai ba ta da wanda zata ni ma shawara ne sai ita Maman,domin duk rashin kunyar ta ba zata iya tunkarar daya daga cikin yannin ta maza ta nime shawarar shi ba,ko yanzun ma abun yana son yafi karfin ta ne "Idan har zan kalli wani namiji na kan ji tsigar jiki na yana tashi,sai kuma in ji ina son in rungume shi,haka kuma idan na kalli film naga mace da namiji sun yi Kiss ji nake kamar na samu wani kusa da ni da zai min,jiki na sai ya dinga kaikayi ta ciki wani lokaci har jikewa nake yi ta cikin pant di na,hankali na tashi yake"

"Har da yannin ki kina jin haka a kansu?

Da sauri ta girgiza kai" Su bana jin komai a kansu ko kaɗan "

Dan shiru Mama tayi tana nazarin maganarta tabbas sha'awar ne,to sai dai ya zata yi da ita,

"Mama baki ce komai ba?

" Salma tunani mafita nake yi"

"Mama ina da mafita"

Kallon ta tafi ta zuba mata ido na wani lokaci kafin tace "wani iri?

" Mama na yanke shawarar aure zan yi"

"Aure!aure fa kika ce Salma?yanzun ke har kinsan aure?

Dukar da kai tayi" Ni dai aure nake so "

Tama rasa me zata ce mata sai ido data zuba mata"shekaran ki nawa ma?

"Goma sha biyar"

"And you want to get marriage at this age?

Shiru tayi bata bata amsa ba,

"Answer me girl"

Kara marairaice fuska tayi"Mama ni dai duk hukuncin da zaki yanke dan Allah kumin aure "

Dafe kai tayi kafin ta kuma cewa"to wa zaki aura?

Kai tsaye ta bata amsa wanda sai da tayi dana sanin faɗin hakan domin tunda suke da Mama bata taɓa yi mata tashin hankali ba irin na yau "Mama Yusuf nake so,shi nake so na aura "

Wani irin zabura da tayi tare da faɗin "What" Sai da ta matsa baya,domin kamar abin yazo ma Mama a bazata ne,

"Yusuf fa kika ce"

Shiru tayi tana zazzare ido,
Chapter 57 · 0% Book details