← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 96

Sashe 76

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali suka ta kowa suna karasowa in da take zaune,gabaɗaya durkusa suka yi a gaban ta suna masu fashewa da kuka,
"Dan Allah ki ga farcen mu Salma,tabbas mu masu laifi ne a gare ki,ki yafe mana a matsayin mu na ƴan adam ajizai"

Kara share hawayen idonta tayi,lokaci ɗaya kuma tana sakin murmushi tare da dafa hannu su dake saman nata,
"A wancan lokacin naji babu dadi sosai musamman idan na tuna wadanda nake tunanin zasu kasance bango a gare ni,su suka fara watsamin kasa a ido,sai naji na ƙara tunzura da son na kuma yin nisa daku sosai, nisa irin wanda kona waiwaya babu abinda zan gani,sai dai cikin ikon Allah sai gashi na dawo farko,sai dai dan Allah ina roƙon ku akan abar abinda daya wuce,zai maida shi tamkar wani mugun mafarki ne dana taɓa yi a cikin barci na,kuma na tashi,dan Allah karku kuma niman yafiyata "

Gabaɗaya duk rungume ta suka yi suna masu hawayen farin ciki,

"Ina Abdulmalik?

" Nan suka shiga bata labarin ai shi ya bada koda aka saka mata dan haka yana ɗayan dakin na kusa da ita"

"Yaya amma ya akayi kuka san inda nake?

" Ai mijinki ne ya kira Abdulmajid ya faɗa mashi in da kike,sannan yace in zamu zo karmu zo dasu Mama saboda halin da kike ciki,koda zamu faɗa masu mu fara barin kiji sauƙi "

Wannan karon ko mamakin ta ne ya kasa boyuwa "ta yaya aka yi ya sanku har ya san number Ya Abdulmajid,sannan ya kira?

" Ya ce mana ya san komai akanki har da dalilin barin ki gida"

"In ji shi"

"Tabbas haka yace ranar da muka iso garin nan"

Shiru tayi kawai yayin da zuciyarta ta shiga tunanin dame_dame ya sani game da ita da yake kiran ya san komai game da ita,

Katse mata tunani Abdulrahman yayi da fadin "mijin ki mutumin kirki ne,ya karbe mu hannu bibbiyu,ban taɓa tunanin Allah zai haɗa ki da mutumin kirki irin wannan Salma,ya san mutunci da dattako,muna fatan Allah ya bar ku tare"

Bata bashi amsa ba sai ma cewa da tayi"ina yake?

Hannu Abdulmajid ya saka a Aljihu ya ciro wani Emvelop ƙarami ya mika mata"yace idan kin tashi a baki"

Amsa tayi tana warwarewa,tsirama rubutun shi ido tayi,yanda suka kwanta sosai a jikin takarda gwanin ban sha'awa,: *Assalamu alaikum,ina maki fatan samun lafiya mai ɗorewa,tafiya ya kamani,ki kula da kanki*:

Kara kallon wasikar tayi tana kara juyawa ko akwai wani rubutun ta baya da bata karanta ba,ganin babu komai ne yasa cikin yatsine fuska tace"Yaya iyakar wasikar kenan?

"Eh"

Cikin jin haushi ta dangwaran da wasiƙar a durowar wurin,

Kallon juna suka yi suna tambayar juna da ido ko lafiya,

Jin hayaniya na tashi daga bakin kofa ne yasa suka fita dan su duba ko lafiya,

Ganin wanda ke tsaye ne yasa Abdulrahman kallon Abdulmajid "ya zamu yi dashi"

Murmushi yayi yada dafa kafadarsa tare da faɗa masa wani maganar a kunni wanda banji ba sai gani nayi shima ya saki murmushi "to ai ba komai"

Kallon security wurin sukayi"ku bar shi ya shigo domin shima dan uwa ne"

Shi kanshi kallon mamaki yake masu domin bai taba tsammanin jin haka daga bakin suba,ji yayi wani sanyi ya lullube shi.
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*77*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Hanya suka buɗa mashi"shigo mana,ka kuma tsaya kamar wani baƙo "

Murmushi yayi yana karasowa cikin ɗakin "na gode"

Jin muryar shi kaɗai ba ƙaramin saka mata bugun zuciya yayi ba,dan har sai da taji kanta ya sara,
Kamar yanda take kallon shi shima haka yake kallon ta,yayin da abubuwa da yawa suke dawo masu,

Wani irin abu ne taji ya sauko ya tsaya mata a zuciya,kauda kai tayi gefe,ji take kamar ta ɓace ta bar wurin,bata son tuno wasu abubuwan da suke dawo mata,sai dai tunda har ya kawo kanshi gare ta a wannan lokacin,bai kamata ta nuna gazawar ta ba,zata tayi amfani da wannan damar wurin nuna masu jiya da yau ba ɗaya bane,

A hankali ya karaso baki n gadon da take,harshen shi har tuntuɓe yake yi wurin faɗin "Partner ya jikin naki?

Sai da tayi tamkar ba zata kula shi ba kafin ta amsa " Alhamdulillah "

Ji yayi duk ta kara mashi kwarjini,sai yake jin shakkar yi mata magana kuma,dan gani yake tamkar ba Salman daya sani shekara biyar baya bane,wannan ta daban ce,duk da akan gadon jinya take da ka kalle ta kasan ita din macece mai aji,

Ganin ko kallon in da yake ba tayi ba yasa cikin sanyi jiki ya koma ya zauna kan kushin kusa da Abdulmajid da suka yi tamkar basu san da zaman shi ba,

"Abdulrahman nace ba,amma idan ta ji sauki zata koma Minna ne tare damu ko?

Wani kallon banzar ya watsa mashi" Ban sani ba amma gaka gata ai kana iya tambayarta "

Juyawa yayi ya kalle ta sai kuma ya dauke kanshi ba tare daya ce mata komai,

A hakan sai da suka yi zaman mintuna Ishirin babu wanda ya ƙara cewa komai,asali ma dakin kamar babu kowa acikin shi,
Jin yanda ya tsargu ne yasa ya tashi "zanje na dawo anjima" Babu wanda ya bashi amsa har ya bar ɗakin,

Juyowa tayi kansu"Yaya"

Dukansu lokaci ɗaya suku amsa suna juyowa,

"Kar a ƙara barin shi ya shigo"

"Me yasa? Abdulrahman ya tambayeta,

" Kodai har yanzun kina son shi ne? Abdulmajid ya ƙara jefa mata wani tambayar,

Ji tayi zuciyar na wani irin tafarfasa da suya,ta ma rasa wani amsa ya kamata ta basu,dan haka komawa kawai tayi ta kwanta ta juya masu baya ba tare da tace masu komai ba,

Kollo juna suka yi suna tabe baki,

Har sun cire rai akan zata sake yi masu magana,sai cewa tayi"yaushe yace zai dawo?

"Waye?

" Suraj"

"Ina ce ya fada maki komai a cikin wasiƙar,'

Juyowa tayi daga kwancen da take,cikin shagwabe fuska tace" Yaya,ni dai in kun dai na sona ku tashi ku tafi"

Makale dariyar dake taso masu suka yi,
"Oh Sorry ba haka bane,ta yaya zamu dai na son hasken idaniyar mu,Kin ga bai faɗa mana komai ba illa fada mana cewar tafiya ta kama shi,sannan ya bamu wasika mu baki"

"Amma shine baku hana shi tafiya ba?

Wannan karon ko buɗe baki suka yi suna mata kallon mamaki,

Ganin kallon da suke mata ne yasa ta kyaf_kyafta idanu tana ɗan turo baki gaba," To me yasa zaku bari ya tafi ya bar ƙanwar ku a kwance rai a hannun Allah?

"To me zamu masa?

" Well I don't now kawai dai naga bai kamata bane,sannan ko irin ku tambaye shi yaushe zai dawo baku yi ba,I am disappointed with you gay "

Da hannu ya nuna ta"you..

Maida kanta tayi ta kwantar tana kulle ido,

Ganin daga kulle ido bacce ya kwashe ta ne yasa suka fito suka komawa wurin Abdulmalik,

*Bayan Sati Ɗaya*

Alhamdulillah jiki ya fara warwarewa dan har ta fara dan takawa,sai dai abubuwa da yawa sun faru koma dai in ce suna kan faruwa,domin kullun sai Yusuf ya zo Asibiti sai dai ba mai hana shi shiga wurin ta,amma in ya shigo kuma babu mai kula shi har ya gaji ya fito,ba zai sa gobe kuma yaki dawowa ba,

Kamar yanda suka ma Kaka Alkawarin zasu je,basu samu zuwa ba dan sun roki Suraj ya basu number ta kuma ya basu,Abbulrahman ne ya kira ta da kanshi,ya bata haƙuri akan idan Salma da Abdulmalik sun ji sauki zasu taho tare,
Ta yarda kuma tai masu fatan samun sauƙi,

Ta bangare Ammi kuwa kullun sai ta zo ta dubata,sai dai kamar yanda bata ce ma Biba komai ba haka ita ma bata ce mata komai ba,jira kawai take ta kara samun karfin jikin ta lokacin zata ji daɗin fuskantar kowa,

Babu ma abinda ke bata haushi irin rashin jin Suraj,ko a waya bai nime ta ba,sai dai kawai wani lokaci taga suna waya da daya daga cikin yannin ta,amma ko irin da wasa yace a bata bai yi ba,ai kuwa tana kule dashi,kuma zasu haɗu,dan jira ce take dashi.

Washegari da safe tunda ta tashi tayi sallah ta koma ta kwanta,
Cikin barci take jin kamar dariya na tashi sama_sama ne yasa a hankali ta shiga buɗe idonun ta,sai dai bata juyo in da suke ba,
A hankali take jin wani irin kanshi mai matukar sanyi yana mamaye hancen ta,wanda take da tabbacin a jikin mutum ɗaya ne kawai take jin irin wannan kamshi,
Lumshe ido tayi ta buɗe tana jin yanda bugun zuciyarta ke kara karfi wurin harbawa,
Kasancewar ta juya masu baya ne yasa basu san da farkawarta ba,a hankali ta juyo tana fuskantar su,
Su huɗu ne zaune a cikin kujerun dake zagaye a tsakiyar wani dan madaidaicin charting table,
Hira suke yi cikin kwanciyar hankali wanda daga dukkan alamu hiran ba karamin daɗi yake masu ba,dan sai sakin murmushi suke yi,wani lokaci ma har darawa suke yi,

Tunda take dashi zata iya cewa bata taba ganin dariyar shi ba,murmushi ma bazata iya tuna when last ta ganshi yana yi ba,

Gani tayi ya kara mata tsayi duk da a zaune yake,fuskar shi ta ƙara haske da kyau musamman yanzun da yake dariya,wani lokaci ma har tafawa taga sunayi da Abdulmalik dake zaune a gefen sa,

Tun dazun yake jin alamun ajikin shi ana kallon shi,

Ita kuma data ga kamar zai kallo in da take sai ta lumshe ido da sauri,

Wannan karon shammatar ta yayi dan sai da ya bari ta gama sake jiki sai kawai sintar idanun shi tayi cikin nata tsamo_tsamo,
Chapter 76 · 0% Book details