← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 96

Sashe 63

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan dakatawa tayi tana share fuskarta" Eh,"

Rungume mahaifiyar nata tayi tana dariyar farin ciki,
Suna fitowa bata ko kalli in da kakar nata ke zaune ba ta saka kai zata fita,ji tayi tana faɗin "A sauka lafiya,Uwar soyayya"

Dan juyowa tayi kaɗan tana dariya kafin ta ƙarasa fita daga gidan,

Direban daya kawo ta shi ya mai da su gida,
Tun daga lokacin basu kara tayar mata da zancen shi Yusuf ba,sai dai sun sake mata fuska sun koma tamkar babu abinda ya faru,Baba kawai ke sanar da ita cewar sun yi magana da iyayen Yusuf sati mai zuwa za'a daura auren su,washegari kuma zasu tafi London din tare,
Ranar farin ciki kamar zai sheketa,ƴan uwanta sun tayata murnar samun muradin zuciyar ta,amma Mama ko kallon in da suke bata yi ba,kuma har ya kasance yau da ya rage saura kwana uku ɗaurin aure Mama bata ce mata komai ba dan gane da gyaran jikin amare da ake yi,

Aunty Hulaira ce ma ta kira ta take ce mata ko an gama bata magungunan mata data karbo kuwa,

Tace ita ba abinda aka bata,in ba maganin sanyi ba da Mama ta bata,

Taga bacin rai sosai a fuskar kanwar Maman nata,dan haka bin bayanta tayi ta tsaya a ƙofa bata shiga ba ganin yanda ita Aunty Hulaira ta shiga dakin Mama a hassale,

Tana ji take tambayar Mama"Aunty Fatima ina maganin dana siya ki ba Salma"

"Wani magani? Ta tambaya,

" Na kayan mata"

"Oh yana nan"

"Me kike nufi da yana nan,kin san irin kudin dana kashe domin hado waɗannan magungunan kuwa,sannan ace yarinya biki har saura kwana uku ba'a fara bata komai ba,haba sai kace wacce ba tada gata,ke in ba zaki bata ba Bani su nan na fara bata"

Girgiza kai tayi"shi yasa tun farko na ce maki karki siya,amma baki karɓi shawarata ba,Salma ba zata sha wannan maganin ba"

Katse ta tayi"zata sha mana domin abune da zai taimaka wurin ɗaga darajar mace"

"Ba zaki gane me nake nufi bane Hulaira,Salma bata dace da shan maganin mata ba,domin idan har tasha ina mai tabbatar maki za'a samu babban matsala irin wanda bana fata,ko yanzun ya ta kare,da kanta fa take sanar da ni irin karfin sha'awar da take dashi,to ina ga tasha wani kayan mata,"

"To ai hakan abu mai kyau ne,kin ga su sabbin aure ne,sannan suma mazan yanzun ba haka suke zama ba,idan tasha sai kiga komai yazo masu yanda ya dace"

Dafe goshinta tayi,domin ta tabbatar idan zata kwana yi masu bayani ba fahimtar ta zasu yi ba,"na maki alƙawarin idan aka kaita ɗakinta da sati biyu ba tare da an samu wani matsala ba to da kaina zan kai mata kayan matar har inda take,na maki alkawari amma dan Allah karki kuma cewa komai "ta faɗa da alamun roƙo,

Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi" Shikenan ba damuwa na yarda dake,sai dai dan Allah Aunty Fatima ki cire komai a ranki dangane da wannan aure kawai ki masu fatan zaman lafiya,da samun ya'ya na gari"

Maganar ta na karshe ne ya sata ɗan yin murmushin takaici "Ya'ya,Umm,to!Allah ya basu masu Albarka"

"Yauwa ko kefa,Amin"

Da hakan zancen ka kare suka dauko wani hira,

Ita kuma juyawa tayi ta wuce tana tunanin dalilin da zai hana Mana bata maganin yanzun har sai nan da sati biyu wai kuma shima in ba matsala,Umm ta rike maganin ta domin ita kam tuni suka yi ciniki da wata mata a online mai sai da kayan mata yau kuma kayan zai iso tun daga Sokoto,in ita ba zata gyarata ba ai Gara ta gyara kanta.

🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*63*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Duk wannan haukar da take yi tun daga farko har zuwa yau da yake ɗaurin auren ta basu taɓa yin waya da Yusuf ba,komai Baba ke mata,dan haka ita abun be dameta ba,

Ranar Sati da misalin karfe goma na safe aka ɗaura auren,wanda ya samu halarta manyan mutane daga wurare daban-daban,domin a garin Minna mahaifinta ba ɓoyayyen mutum bane,
Kasancewa yanda auren yazo da kuma yanda yan uwan basu so yasa ba'a yi wani program ba,sai gagarumin Dinner da Baba ta shirya masu a Lebo Kutigi,da karfe takwas na dare,

To fa shine suka haɗu a cikin motar da aka shigo ɗaukarta dashi da zasu tafi wurin Dinner,
Tayi shiga na Alfarma,tayi kyau na ban mamaki,yanda kasan ba a kasar Nijeriya ba,kasancewar ta Fara tas,yayin da kayan dake jikinta na doguwar riga ya kasance ruwar toka mai haɗe da dan karamin hijabi,shima Kot ne a jikin shi ruwan toka,
Tunda aka buɗe mata marfin mota ta shiga aka maida aka kulle,ta juyo tana fuskantar shi,domin bata San da wani irin fuska zai tarbe ta ba,

Shima ita yake kallo kamar mai nazarin wani abu,kafin kuma lokaci guda ya sakar mata da murmushi,ya mika mata hannun shi alamun ta riƙe,

Wani irin ɓoyayyen ajiyar zuciya ta sauke tana daura hannun ta a saman nashi,
"Kin yi kyau sosai Beauty"

Juya idanun ta tayi cikin tsananin farin ciki tace"na ɗauka ba zan samu irin wannan tarbar daga gareka ba"

Sumbatar hannun ta yayi "nariga nama Mahaifinki Alkawarin zan kula dake na mai dake gimbiya a gida na"

"Kana nufin Baba?

" Eh Baban mu,Kin San yanzun ya zama namu har da ni"

Dariya ta saki cikin jin daɗi,
Da haka suka isa wurin Dinner aka gudanar da komai cikin kwanciyar hankali da wadata,aka kuma rabu cikin Arziki,yayin da suka yi sallamah da mutane da dama domin gobe da safe ƙarfe takwas jirginsu zai tashi zuwa London.

Sai da ya ajiye ta a gida sannan shi kuma direba ya mai da shi gida,
Har ta yi wanka ta kwanta dan lokacin ƙarfe sha-biyu na dare ake nima sai gashi ta ji an turo kifar dakin ta,

Daga kai tayi ta kalle ta,ganin wacce ta shigo ne yasa ta mike zaune tana kiran sunan ta"Mama"

Dan murmushin yake ta sakar mata tana zama kusa da ita,

Kallon mahaifiyar nata tayi yanda idanun ta suka kumbura alamun ta ci kuka,to ko ita da take amarya ta lura ba tayi kuka ba kamar yanda Mama tayi,
Shafa kanta tayi"ba kiyi barci ba?

"Tanzun na fito wanka shi ne na kwanta"

"How was the party?

Murmushi ta saki" Komai ya tafi dai-dai "

"That good"

Dan shiru sukayi na dan lokaci,kafin ta katse shi tun da faɗin "gobe d safe zaku tafi"

"Eh haka Baba yace"

Ajiyar zuciya ta sauke a karo na ba adadi "Nasan ba lallai bane gobe na samu lokacin da zamu yi magana shi yasa na shigo yanzun dak da Nasan kin gaji"

Girgiza kai tayi "is ok Mama ina ji"

Lumshe ido tayi ta bude kafin ta fara da kiran sunan ta,"Ummu Salma"

Kasa amsawa tayi sai zuba ma Mama ido da tayi

"Ina son a ko wani lokaci ki dinga tunawa kina da Mahaifiya mai ƙaunar ki,da yanni maza masu son ki,kina da Ahali masu matukar kaunar ki,ko me zai faru dake ki dinga tunawa dasu kuma zasu tsaya maki a ko wani hali,idan har kina niman wanda zaki fadama damuwarki ni mahaifiyar ki ina nan,zan saurareki na kuma baki mafita,"

"Mama wani abun zai faru ne?ta tambaya cikin dan yanayi na tsoro,

Rike hannayen ta tayi" Babu abinda zai faru,kawai dai ina faɗa maki ne saboda karki manta damu,
Abu na gaba,shine mai muhimmanci,Salma banda bincikan mijiki,karki cika bincike akan lamuran shi,ki yi hakuri da duk abinda kika gani domin ke kika zaɓa,kuma dauriya da juriya da dauke kai ya zama dole a gare ki,a duk lokacin da kika ji zuciyar ki na rayo maki wasu abubuwa ki yi sauri ki kama kiran sunan Allah domin shi kaɗai ne zai taimake mu,"

Shiru kawai tayi tana sauraren wannan nasiha na Mama wanda kwata_kwata bata gane kanshi ba,bata gane in da ta dosa ba,ita a nata tunanin nasiha ya kamata ta mata akan yanda zata kula da tsafta da girki da kuma kyaran jiki ta yanda zata rinka dauke hankali mijinta,sai gashi tana mata Nasiha kamar wacce zata shiga rayuwar kunci,

Ganin irin kallon da ƴar nata ke mata ne yasa ta kuma shafa kanta"na San yanzun baki gane mai nake nufi ba,amma a hankali zaki gane,ki kwanta ki huta sai da safe"ta faɗa tana sumbatar ta agoshi,

"Ok Ma," Ta faɗa tana gyara kwanciyar ta yayin da Mama ta kashe mata wutar dakin ta fita.

Washegari suna idar da sallar Asuba Baba ya haɗa su daku har da yannin ta ya masu nasiha akan su rike zumunci,su haɗa kan Ya'yan su,koda yana da rai ko beda rai,
Kallon Salma yayi cikin zolaya yake faɗin "Gimbiya idan kin haihu wani suna zaki saka ma ɗan ki"

Dariya tayi tana juya ido"Baba idan na haifi ɗa namiji zan saka masa sunan Muhammad,saboda sunan Manzon Allah,kuma suna yana tasiri sosai akan yaro "

"Laa to ba zaki saka suna na ba"

Da sauri Mama tace"A'a tunda har suna na tasiri akan yaro ai Gara dai Muhammad ɗin,"

"Mama to ai sunan Baba ma yana da kyau,tunda shima sunan ɗan Manzon Allah gare shi,Abdullahi"

Girgiza kai tayi tana canja zancen"to idan mace ce fa"ta tambaye ta,

"Umm,to zan saka mata Nana Habiba,ina son sunan sosai"

"Sai na kira ta da BIBA"

Dukan wasa takai masa"kai Yaya Abdulmajid me kuma Biba,ni Nana Habiba nace "

"Kunga ni idan na yi aure sunan Mama da Baba zan saka ma yara na"

"A'a,bamu bukatar haka,kawai ku saka masu wani sunan amma ba namu ba"

Bata fuska yayi"Mama"
Chapter 63 · 0% Book details