← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 96

Sashe 29

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba tare da yace masu komai ba ya mike ya bar falon,kamar yanda suma basu ce mai komai ba sai bakaken maganganu da wasu a ciki ke jifan shi dasu,
Yana fitowa bai koma dakin shi ba da kyar ya samu yakai kanshi wurin Parking ya buɗe mota ya shiga,
Ganin hakan ne yasa daya daga cikin direbobin gidan yazo ya shiga yana tambayar shi ina zai kai shi,
Da kyar ya iya furta kalmar "gida"
Ya gane inda yake nufi dan haka jan motar yayi suka bar gidan,
Yayin da yake jin numfashin shi kamar zai bar gangan jikin shi.

Kuka ta fashe dashi tana zama anan bakin kofa,to me ke shirin faruwa kuma a rayuwar ta a karo na biyu,Aure! Aure fa!dama abinda VIP ke nufi kenan da yace ta je tayi kissing din shi kuma ta bar kofa a buɗe,
To waye ya shigo ya ɗauke su hoto,dama ya shirya ma hakan kenan,amma ai baya cikin tsarin aikin su,baya cikin yarjejeniyar su,
Cikin sauri ta lalubo number shi a wayar ta tashiga kiran shi,sai da ta kira sau takwas ba tare da kakkautawa ba kafin a ɗauka,
Kuka ta fashe dashi"me haka! Me haka! Wannan fa baya cikin yarjejeniyar mu,kokarin aura min shi ake yi,gaskiya a canja wani hanyar "

Daga ɗayan bangaren yace"kina da wata hanyar ne daya fi wannan,?

Shiru tayi"amma kai ai ba zaka rasa ba"

"Haka ne,shi yasa na zabar maki da wannan,domin shine hanya mafi sauki da zai kaiki ga kammala wannan aikin cikin kankanin lokaci"

"To auren fa?

" Biba me yasa kike abu kamar ba wayayyiya ba,auren ai na baki ne tunda baki son shi,da zaran kin kammala aiki da kaina zansa ya sake ki"

"Ni dai ba na son wannan hanyar,domin ka sani a rayuwata babu abunda na tsana sama da Aure,ta sanadin aure komai daya faru dani ya faru,ta sanadin wannan kalmar na gano abinda bai dace nasan dashi ba har abada,idan sai da aure zan cika wannan aikin to na ajiye,na janye"

Wani irin shegen dariya ya fashe dashi,irin wanda da ka jishi kasan irin na rashin imani ne"dama nasan irin haka na iya faruwa,shi yasa na shirya ma wannan ranar Biba,ina ga har yanzun ba kisan da wanda kike aiki ba,ai tunda kika fara aiki dole ne saikin ƙarasa,ko kina so ko baki so,bari na tuna maki,ina kika bar ƴar uwar ki Ummita,"ya fada yana ƙara sakin wani dariyar,

Gabanta ne ya faɗi "me kake nufi,ina Ummita?

" Karki damu,tana hannu na cikin ƙoshin lafiya a yanzun,amma ban dai san daga nan zuwa nan gaba ba idan kika cimin musu,kina iya rasa ta,domin a wurina hakan ba komai bane,dan haka rayuwar ƴar Uwar ki yana hannun ki,idan kin ga dama ki yi wasa dashi idan kuma kinga dama ki cece ta tahanyar kammala aikin dana saka ki"

Idan ranta yayi baki to ya baci"idan har wani abu ya samu Ummita ba zan taba barin ka,sai na binciko ko kai waye naga bayan ka "

"A'i zata zo yanzun domin mun riga mun shirya wadanda zasu tsaya a matsayin iyayen ki,idan kinga dama ki nuna abinda zai sa a zarge ki,Gara ki kwantar da hankalin ki kiyi komai cikin natsuwa domin nasan babu abinda zaki iya" Yana gama faɗar haka ya kashe wayar,

Ihu tayi na bakin ciki tana haɗa wayar da bango,nan take kuwa ya tsarwatse,
Dukawa tayi a wurin ta shiga rusa kuka ko zata ji sanyi a zuciyar ta,wannan wani irin ƙaddara ce haka,idan har ta rasa Ummita bata san Me kuma ya rage tayi ba a rayuwata ta,ina zata samu mafita,wani irin tunani ya kamata tayi,
Kuka take sosai na rashin sanin mafita.

A falo kuwa Kaka ce ta bada number A'i aka kira ta Goggo tai mata bayanin komai,ita ko harda kuka,tace masu yanzun zata sanar na mahaifinta,kuma komai yazo da sauƙi tunda yayan mahaifin Biba aman Kano yake anan kuma yake sa'ar shi,

Daganan ne taro ya watse inda mazan suka nufe masallaci dan lokacin sallah Azahar yayi,
Mata kuma kowacce ta koma shiyan su.

Ko da A'i ta iso gidan Ana daf da kiran sallah la'asar dan ta bata lokaci ne wurin koya ma wadanda suka yi haya yanda zasu yi idan sun zo nan ɗin,

Cikin mutumci suka gaisa da Kaka kafin ta nuna Mata dakin Nafisa da Biba ta koma,

Ko da ta shiga a kwance ta same ta idanunta a buɗe tana kallon ƙofa,
Ganin shigowar A'i ne yasa ta tashi da sauri tazo ta rungume ta tana fashewa da kuka "A'i dan Allah ki taimake ni! Ki taimaki rayuwa ta,ya ɗauki Ummita,idan wani abu ya same ta ba zan iya yafe ma kaina ba!

Hannu ta saka mata a baki alamun tayi shiru,zaunar da ita bakin gado tayi,sannan ta maida kofa ta kulle, wayarta ta buɗe ta cire batir sannan ta zauna" Ya saka tiraka a waya ta duk abunda muka faɗa yana iya ji"
Share mata hawaye tayi"nasan haka zai fara,kuma abinda yafi haka ma yana iya faruwa idan shi ne,"

"Me kike nufi A'i"

"Shi mutum ne mai matukar hatsari,yanada wayau sosai da basira"

"Ta yaya zan iya taimakon ƴar uwa ta,ki taimaka min"

"Ki yi hakuri Biba,ban San ta wace hanya zan taimaka maki ba,amma kuma bari na faɗa maki abunda baki sani ba,kila nan gaba hakan na iya taimakon ki"

Rike mata hannu tayi"ki faɗamin koma menene"

"Bake kadai ce kika fara aiki a wannan gidan ba,kafin ke a kwai mutum shida,acikin su babu wacce tayi nisan da kika yi suke barin aiki,sai dai da sun fito da kwana biyu ake niman su a rasa,sai bayan wasu ƴan ƙwanaki ake tsintar gawar su a wuri mabanbanta"

Zaro ido tayi cike da tsoro"me hakan ke nufi?

"Kashe su yake yi saboda suntsan komai,kuma kema ina mai tabbatar maki idan har baki kammala wannan aikin ba zai iya kashe ki,haka kuma idan har kika kammala masa aikin shima ba barin ki zai yi ba"

A tsorace tace"to me ya kamata nayi,idan na kammala a kashe ni idan ban kammala ba akashe ni,to me zan yi kenan na tsira,ba na son na mutu a hannun wani?

"Hanya daya ce kawai zaki iya bi domin ceton kanki dana ƴar Uwar ki"

"Dan Allah ki taimaka ki faɗa min A'i"

Ajiyar zuciya ta sauke "saboda ina ƙaunar ki tun ganin farko shi yasa na yanke shawarar taimaka maki,sai dai ban sani ba ko abinda zan faɗa haka ne,? Sauke numfashi ta kuma yi" Ki yarda ki aure Suraj,domin shi kadai ne wanda zai iya taimaka maki,shi kadai ne wanda yasan Asalin waye suke takun saƙa dashi,domin ni kai na bansan waye VIP ba,amma ina da tabbaci a kan shi ya sani,
Ko ta halin yaya kar ki taba dauko abinda ake buƙata,domin da zaran kin miƙa naki ya ƙare,haka kuma kar ki taɓa kin daukowa,kar ki bari ko ta halin yaya VIP ya zargi wani abu,ki ci gaba da nuna kina kan aiki,
Sannan akwai wani gagarumin matsala da zai taso ma Suraj,wanda ba lallai bane ya rayu,abu ɗaya kawai nake son na sanar dake,shine ko ta halin yaya kisan yanda zaki taimaka masa ya rayu,domin fa idan kika bari suka samu nasarar kashe shi to lallai zasu samu damar cimma manufarsu sannan kema su gama dake ko kina so ko baki so,
Dan haka daga yanzun sai ki fara tunanin ta hanyar da zaki tseratar da rayuwa uku"

Tunda uwata ta haihota duniya bata taba shiga tashin hankali da ruɗani ba irin wannan "A'i wani irin matsala ne wannan da zai taso"

"Gaskiya ba na ce ba,domin bansan me suke shiryawa ba,amma nasan koma dai menene to ba ƙarami bane,zai iya kaiwa matakin da za'a rasa rayuwa"

Ganin yanda ta shiga damuwa ne yasa ta dafa kafadar ta"ki kwantar da hankalin ki,na tabbatar idan har kika natsu,kika kuma bi komai daki_daki zaki iya cin nasara "

"A'a matakin cin nasara ta sufili 0 Zero ne,ba ni da kwarin gwiwa da jarumta"

"Idan kika tuna mahimmanci rayuwar ki data ƴar Uwar ki su zasu kasance maki kwarin gwiwa"

Ajiyar zuciya ta sauke,amma Allah ya gani gabaɗaya ƙwaƙwalwar ta ya toshe,ta yaya zata iya fuskantar wannan Ustazun ma,ta san yanzun haka duk inda yake ji yake kanar yaga bayanta,

"Ni zan wuce amma zuwa anjima zan dawo kafin a ɗaura auren"

Jinjina kai kawai tayi,dan ba zata iya ce mata komai ba,tana kallo har ta fita ta jawo mata ƙofar.....

*yanzun aka fara*
*Jiddarh 🦚ce*
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*31*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Tun daga farkon shigarsu layin Sultan Road Jami'an tsaro ne ta ko ina wanda hakan ne zai tabbatar maka da unguwar bata ƙananan yara ba ce,
Tunda Direban daya dauko shi ya shigo layin Jami'an ke tsare shi domin duba wanda ya dauko,domin da mota daya ne suke,kuma sun san duk wanda yake layin da kuma number motar su,da ya tsaya ya sauke glass sun hango wanda ke Hakimce a cikin motar suke Sara mai su basu hanya,

A bakin wani haɗaɗɗen bakin Get din wani gida ya tsaya,wanda ni kaina da badan nasan ba yanda za'ayi a ajiye gidan kwali iska bai dauke ba da nace wannan gidan ba hannu ya gina shi ba,
Gani nayi Get din ya buɗe da kanshi kafin direban ya shiga da motar ciki,nan ma Get din ne ya kulle kanshi,
Chapter 29 · 0% Book details