← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 96

Sashe 73

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dayar ce tace"to me yake yi a asibiti?

"A jiya aka kawo matar shi ba ta da lafita daga Legas,amma kunsan wani abun mamaki?

Duk girgizar kai suka yi,

" A jiya da daddaren ya siya wannan Asibitin a kan miliyoyin kudi,ya kuma ƙara ma duk wani likita dake aiki a wannan Asibitin Albashi,duk da akwai kayan aikin da za'a ma matar shi aiki sai da ya kara yin odar wasu daga ƙasashen waje sababbi na zamani wadanda a kanta za'a fara aiki dasu,kunsan irin farin cikin da duk wani likita dake Asibitin nan yake ciki saboda shi?maganar gaskiya munji daɗin kawo wannan Zinariyar matar tashi wannan Asibitin,dan haka daga yanzun duk inda kuka gan shi ya zamo abin girmamawa a wurin ku,domin mutane da yawa zasu amfana saboda shi"

Dayar ce ta rungume hannu a kirji cikin shauki take faɗin "waiyo Allah ina ma ace ni ce wannan matar tashi,dana tsula tsiya a duniya"

"Sai kuma Allah yayi ko me sharan gidan shi baki zama ba,com on Jare kuxo mu tafi"
Bin bayanta suka yi suna masu fadar abubuwa da dama a kanshi,yayin da shi kuma ko sanin suna yi bai yi ba.

_____daga bakin kofar suka tsaya suna kallon kanwar tasu dake wance bata da maraba da gawa face ta hanya daya wato numfashi wanda yake fita a hankali,

Hankalin su ya tashi sosai da ganin halin da take ciki,duk yanda suka so su daure ma zuciyarsu kasawa suka yi,sai da suka dinga zubar da hawaye yayin da abubuwa masu yawan gaske ke dawo masu a ransu game da rayuwar su na baya daya shuɗe,lallai dan Adam ba abakin komai yake ba,
Basu jima sosai a wurin ba yace su tafi domin ko da ma sun tsaya babu wani abunda zasu iya yi mata,dan haka dole suka fito suka bar ta ba dan ransu yaso ba,

Yanzun ma a motar shi suke sai dai bai nufe Hotel din da suka sauka da suba sai gidan shi daya kai su,

Abdulrahman ne yace"Kanin mu nan ina ne"

Murmushi yayi jin sunan da ya kira shi dashi"nan gida na ne "

"Ai da ka maida mu Hotel kawai" Cewar Abdulmalik

"Ta yaya zaku zo har in da kanwar ku take ba tare da kun shiga gidan ta ba,duk da bata ciki na tabbatar zata ji daɗi idan tasan anan kuka sauka,ni ma kuma zanfi samun natsuwa"

Kallon juna suka yi suna sakin murmushin farin ciki,domin kan lallai sun yarda yanzun Ummu Salma tayi aure kuma ta samu miji,

Bin bayan shi suka yi har cikin babban falon gidan.

Duk zaunawa suka yi a falon suka kara kallon gidan,

"Ya su Mama " Ya tambaya,

"Kamar yanda ka roka akan kar mu faɗa masu tukunna shi yasa basu san mun zo nan ba"

"Dama nafi bukatar ku fara ganin halin da yar uwar ku ke ciki saboda ku zasu fi su iya jurewa"

Abdulmalik ne yace"kani ni kam kana min kama da wani malami bari dai ka gani"nan ya ciro wayar shi ya kunna video din wa'azin Young ustaz mika ma Abdulrahman yayi"kalla ka gani kamar har ta baci "

Amsa yayi ya kalli na wayar ya kalli shi yanda yake zaune yana kallon su hankali kwance,
"Shine mana,kanin mu ai kai ne ko? Ya tambaya domin son tabbatarwa

" Ni ne"

Mamakin su ne ya saka boyuwa ikon Allah,"To Babban Malami irin ka a ina ka haɗu da Biba gashi har kunyi aure"

Dan murmushi yayi"is a long Story,idan ta tashi zata faɗa maku"

"Allah yasa ta manta da komai ta yafe mana"Abdulmajid ya fada cikin damuwa,

" Karka damu Allah ya bata lafiya "
Duk da Amin suka Amsa,

Tambayar shi suyi game da bayanin likita akan lafiyar ta,

Bai ɓoye masu komai ba ya sanar dasu har kuma da irin aikin da take buta,

"Abbas Mama ta faɗa mana lokacin Salma na da shekara biyar a duniya tayi fama da ciyon koda sosai wanda sai da cire Mama daya aka saka mata"cewar Abdulmalik

"In dai har Salma zata samu lafiya a shirye muke damu bada Kodar mu domin a saka mata" Kanin mu,dan Allah ka mai da mu Asibiti likita ya gwada mu ya gani a cikin mu duk na wanda ya mata a shirye muke damu bada har ta da jinin da take bukata"

Shiru yayi dai ba tare daya basu amsa ba tamkar dai mai nazarin kalaman su.
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*73*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Sai zuwa yamma sannan suka kara komawa Asibiti domin a gwada su,dan lokacin da Dr ya basu kenan.

Abdulrahman ne ya fara shiga aka gwada shi,su kuma suna zaune a babban ofishin likita suna jira,sannan da aka kammala yi masu gwaje-gwajen daya kamata sannan suka koma gida dan sai zuwa gode sakamako zai fito,

_______A gidan kuwa,suna barin shiyan Kaka part din su suka shiga,
Zama tayi sharaf saman kushin tana sauke numfashin takaicin mahaifiyar nata,

Itama zama tayi kusa da ita"yanzun ya zamu yi"

Cikin jin haushi ta juyo tana fuskantar ta"akan me kenan?

"Akan wannan yaron mana Suraj,nasan kin San me nake nufi"

Ji tayi ranta na ƙara ɓaci "yanzun ni Momy me kike son in yi ne,ina ce tun farko sai da na faɗa maku ina son shi haka nan,amma ke da Aunty Atika babu irin zagin da baku mai ba,har da Marina sai da kika yi,bayan ni na hango ma kaina irin rayuwar da baku hango ba,gashi a karan banza kun saka wata yar aiki cikin daula,sannan yanzun kina tambaya ta akan me zamu yi? Mekewa tayi ta bar falon tana faɗin "sai ki san yanda za ki yi"

Da kallo ta bita baki buɗe "ki zo mu samu mafita" Sai dai ko kulata ba tayi ba tayi shigewar ta,

Dan shiru tayi tana nazarin maganar Kaka,in dai kuwa haka ne to dole ne Yusuf ya janye dan ko ana ha maza ha mata wallahi ba zata bari wannan daular ta wuce su ba.

_______karfe tara na dare ne suka kara komawa Asibiti tare domin jin sakamakon gwajin da aka yi.

Yanzun ma kamar dazu ne sune zaune a ofishin Babban likitan,sai dai wannan karon bashi kaɗai bane su uku ne,
Dan haka cikin kwantar da murya suka shiga yi masu bayani akan an samu jinin Abdulmalik zai dauki nata,batun koda ma haka na Abdulmajid zai mata,
Wannan bayanin ba karamin farin ciki ya saka su ba,

"Dr yanzun zuwa yaushe za'a gudanar da aikin?ya tambaya,

" Nan d kwana biyu,domin zuwa gode kayan da kayi mana oder zasu iso,dan haka sai mun tsaya mun kwada su yanda ya kamata"

"Babu damuwa Allah ya kaimu"

Da Amin suka amsa,

"Sai dai batun STEM Transplant zuwa gobe da yamma za'a yi mata shi,domin mun duba cigaban da aka fara samu ta wannan ɓangaren" Cewar ɗayan Dr ɗin.

"Babu damu a shirye muke a ko wani lokaci"

Daga nan suna fitowa gida suka koma domin Ammi ta kira akan ita ma tana hanya domin zuwa ta gana dasu.

Tun a harabar gidan suka shaida isowarta dan ganin baƙuwar mota a wurin parking,

A falon kuwa suna saka ƙafa wani daddadan kamshi na musamman ya ziyarci hancin,
Kalle_kalle yake a falon ganin yanda ko ina yayi fes,duk da falon a kyare yake a ko wani lokaci domin ma'aikatan gidan na ƙoƙari,amma gyaran mace dana namiji ba daya bane,
Fitowa tayi daga cikin hannun ta ɗauke da wasu hadaddun kuloli yayinda Bala ke biye da ita a baya shima yana dauke da sauran kayan,
Da sauri ya amshi kayan dake hannun ta yana murmushin farin ciki "Ammi sannu da zuwa"

"Yauwa har kun dawo"

"Umm" Ya faɗa yana ajiye kulan a table,

Cikin girmamawa suka shiga gaishe ta,
Amsawa tayi cikin dakin fuska tana nuna masu wurin zama,
"Ya kuka tsaya a tsaye,ku zauna mana"

Zaunawa sukayi "Ammi mun same ku lafiya"

"Lafiya qlau,ya iyayen naku"

"Suna nan lafiya"

"Ya jikin Baban naku,da sauƙi kuwa ko har yanzun sai a hankali"

Wannan karon kallon juna suka yi cikin mamaki,ya akayi tasan da jikin Baban su har haka,

Ganin sun dan shiga yana yi na mamaki ne yasa ta kuma cewa"karku damu hakan ba abin mamaki bane,domin na San iyayen ku shekaru ishirin da biyu data wuce"

Wannan karon ko Abdulmajid kasa ɓoye mamakin shi yayi"Ammi a ina kika san iyayen mu,sannan gashi kuma Ummu Salma tana auren danki,amma kuma baƙi taba niman itayen ta ba,ko dai dama kin riga kin San ko ita din wacece?amma baki nime mu ba?

Wannan karon kam murmushi tayi domin tambayoyin yaron sun mata,tana son mutum me confidence,"batun sani iyayen ku ba abu ne daya shafe kuba,wata kila nan gaba kadan ku na iya sanin a ina muka san juna,ita kuma Salma tun farko nasan ita din wacece,sannan maganar kiran ku ko maida ita gida kuma kun san ba abu bane da zai yu a wancan lokacin,domin zuciyarta bata gama karɓar kaddaran daya same ta ba,yanzun kuma da ta ji tana iya yafe maku ta karbe ku a matsayin ƴan uwa shine ta haɗu da wannan tsautsatin,shi yasa ma har Ɗa na ya kira ku domin ku ganta"

Duk shiru suka yi domin sun kasa tabbatar da manufar wannan matar,sai dai koma menene zasu jira har sanda ƴar uwar su zata farfado,

Nuna masu abincin dake gabansu tayi"kuci abinci kar yayi sanyi"

Cikin natsuwa suke cin abincin har suka kammala,
Mikewa tayi tana kallon su"ku kwantar da hankalin ku insha Allah ƙanwar ku zata samu lafiya,sannan ku dauka tamkar a nan gida kuke"

Haɗa baki suka yi wurin faɗin "mun gode"

Sallamah ta masu yayin da Suraj ya rakota har bakin mota inda Direbanshi dama ya dauko ta shi kuma zai maida ita,
Chapter 73 · 0% Book details