← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 96

Sashe 78

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Busar da iska yayi yana lunshe birkitattun idanun shi da lokaci ɗaya suka canja daga farin da suke zuwa yanayin jaja,kallon idanun shi ma kaɗai ya isa ya sanar da kai irin tafasar da yake yi a ciki,

"A'a I am ok,nan da mintuna goma jirgin mu zai tashi,idan na je can zan ci gaba da ganin likita domin na ma Grandma alkawari"

Duk shiru suka yi ba dan sun so ba"dan Allah kayi haƙuri"

Dan murmushi ya sakar masu ganin yanda duk hankalin su ya tashi,

"Karku damu babu wani matsala"ya fada yana kiran waya akan a kawo mashi wani riga,yana gama canjawa ya mike ya masu sallamah,

" Mu je mu raka kanin mu"

Gyaɗa mashi kai kawai yayi,tare suka fito har wurin parking,yana ƙoƙarin shiga mota ya dakata yana juyowa "dan Allah kar a kara barin shi ya shiga inda take"

Tare suka saki murmushi domin sun fahimce wanda yake nufi, "karka samu damuwa"

Koda ya shiga motar ma jin jinginar da kanshi yayi yana rintse ido tare da dafe wurin,sai dai duk irin raɗaɗin da wurin yake masa idan har ya tuna kalaman Yusuf akanta sai yaji raɗaɗin zuciyarsa ta shafe wannan,
Cikin kankanin lokaci suka isa Airport,
Niman wuri yayi ya zauna yayin da daya daga cikin security din shi ne ke kokarin kammala masa abinda ba'a rasa ba,

___________Asibitin kuwa,
Suna ganin motar ta bar harabar Asibitin suka koma ciki,sai dai wannan lokacin ɗakin da take ciki suka nufa kai tsaye,

Jin shigowar su ne yasa da sauri ta shiga share hawayen da ke idanun ta,

"Umm hmm kukan rabuwa da masoyi ake yi?Abdulmalik ya faɗa da sigar zolaya,

Zama kusa da ita Abdulrahman yayi yana mika mata waya" Karɓi ki kira shi "

Dago jikakkun idanun ta tayi a kanshi"waye ?ta tambaya kamar bata gane wa yake nufi ba,

"Mijinki,domin sun samu matsala da Yusuf yanzun nan,kuma ya tafi ranshi a matukar ɓace duk da bai nuna ba,sannan ki faɗa masa ya kula da kansa dan Allah sosai"

Kallon mamaki take mai yanda yake zaro mata zance"to me yasa zan faɗa masa haka?

"Saboda mijin ki ne,kuma akanki komai ya faru,ni dai sam hankali na bai kwanta ba da yanayin da yake ciki"

"Yaya to ni baka ga yanayin da nake ciki bane na bacin rai,ai Allah ne ma ya kama min shi" Ta faɗa tana juya masu baya,

Ranshi ne yaji ya fara ɓaci dan haka cikin yanayin fada_faɗa yace"kin san halin da yake ciki kuwa,wai me yasa har yanzun ba zaki nuna mana cewar kin yi hankali ba,mijin ki ne fa,karki saka raina ya baci dake a yanxun "

Kukan da take kokarin rikewa ne ya kucce mata,ai kuwa nan ta shiga rerawa,domin abin ya mata yawa a cewar ta,ga mari ga tsinka jakka,bayan yanzun ya gama gasa mata maganar banza,sannan kuma shi dan an bata mashi rai sai su zo suce sai ta kira shi,

Dafe goshi yayi yana mikewa tare da barin ɗakin,
Abdulmajid ne ya dawo gabanta tare da rike mata hannu,
Cikin kuka tana ƙoƙarin kwace hannun ta daga cikin nashi tace"kunfi son shi yanzun a kai na"

Share mata hawaye yayi "ke din yar uwarmu ce,abin Alfaharin mu,ki sani babu wani wanda muke so sama dake,kawai dai ba muso son da muke maki ya rufe mana ido ya hanamu dauraki a kan hanya madaidaiciya,shi din mijin ki ne,wanda ya samu rauni saboda ke,ki sani abinda ya maki ba kowa bane zai iya yi maki shi a rayuwa,ko da kuwa mu da muke yannin ki,shi yasa ba mu so ki yi wani abun da zai nuna rashin godiya ko girmamawa a gare shi,dan Allah kiyi yanda muka ce"

Turo baki ta shiga yi"me yamin wanda ku baku min ba?kuma bancin haka ai kome yayi ni ban sa shiba"

"Na dai ji,amma dan Allah ga wayar ki kira shi,"ya faɗa yana daura mata waya a hannu ya tashi suka fita shi da Abdulmalik,

Share hawayen fuskarta tayi tana jan hanci,bala'in haushin shi take ji,Allah ma ya gani zata kira shi ne kawai saboda su ba dan shi ba,

Kiran number dake saman wayar tayi,sai da yayi ringin biyu sannan aka ɗauka,

Ji tayi cikin sanyin murya wanda yafi na ko wani lokaci sanyi yayi sallamah,

Ɓoyayyen ajiyar zuciya ta sauke tana kumbura baki tare da amsawa ciki_ciki kamar wacce aka shake ma mako shi,

Shiru yayi bai ƙara cewa komai ba yayin da yake sauraren yanda take sauke ajiyar zuciya akai akai,

"Har yanzun baki gama kukan ba ne? Ya faɗa a hankali tamkar mai raɗa,wanda da ba dan wayar tana akan kunnen ta bane da bata ji me yace ba,

" Baka kai matsayin da zan maka kuka ba"

"Abinda kika kira ki faɗa min kenan?

Ji tayi wani abu mai kama da ɓacin rai ya mata tsaye a wuya,ta rasa wani irin raini hankali Suraj ke dashi,
Cikin jin haushi tace" A'a,sako na kira na faɗa maka,wai ance in ce ka kula da kanka"tana gama fadar haka ta yanke kiran ba tare data jira jin ta bakin shi ba dan karma ya ƙara sako mata wani abun bacin ran,

Jin ta katse kiran ne yasa ya sauke wayar yana dan lumshe ido"marakunyar ƙarya"ya faɗa a ranshi yana mikewa jin an sanar da lokacin shigar su jirgi yayi........
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*79*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

*Bayan Kwana biyar*

Tun daga wannan lokacin bata ƙara saka shi a ido ba har yar yau da aka sallame ta,

Suna cikin motar da zai maida su gida sai gani tayi sun doshi hanyar gida kaka

Da sauri ta juyowa"Yaya ina ce Airport zamu wuce daga Asibiti?

"Me zamu yi a Airport?Abdulmalik ya mai da mata da tambayar,

" Gida mana,ina ɗauka Minna zamu koma a yau"

Wannan karon Abdulrahman ne ya bata amsa"mijinki ya buƙaci da a maida ke wurin mahaifiyar sa kafin ya dawo"

"To ku kuma fa?

" Mu yanzun haka jirgim mu na kasa zuwa ƙarfe hudu zamu wuce"

Aikuwa kamin ya gama rufe baki ta fashe da kuka tana kankame hannun shi"ni dai wallahi ban yarda ba,babu in da zaku je ku barni,kafar ku ƙafa na,babu in da zan zauna ni gida zan je,"

Shafa kanta yayi shima yana jin babu daɗi a ranshi,dan maganar gaskiya yaso su wuce da ita,sai dai ba zai iya rokon Suraj wannan alfarmar ba,ya lura yana da dalilin yin haka,sannan ko wannan Alfarmar daya masu na sake kasancewa da ƙanwarsu ai ya masu,
"Ki ƙwantar da hankalin ki,ai ba cewa akayi ba zaki je gidan ba,cewa yayi ki jira shi idan ya dawo sai ku taho tare"

Girgiza kai ta shiga yi tana cigaba kuka"ni dai a'a,yaushe ma nasan sanda zai dawo, Yaya dan Allah ku tafi dani,ina son in ga Mama da su Baba dan Allah "

Yanda take kuka kuma duk sai ta tashi hankalin su,nan suka shiga lallashi amma sam ta nuna bata san da wannan yaren ba,

Koda motar tayi parkin a harabar gidan fita kawai tayi wuce shiyan Ammi ta bar su nan tsaye sake da baki suna kallon ta,

Ko da ta shiga falon Amira ce kawai zaune dan ita ko lura da ita bata yi ba ta shige dakinta na da tana kullo kofar har da saka key tana ci gaba da kuka,

Ya Abdulrahman "baka ganin ya kamata muma Suraj magana yayi haƙuri ya bari mu tafi da Salma?

" Me yasa?

"Wallahi ta bala'in bani tausayi,na tabbatar da tana jin kewar su Mama ne sosai kuma ta saka ran da ganin su"

Ajiyar zuciya ya saukar"ba zamu bari son kanmu yayi tasiri a zuciyar mu ba,na tabbatar tunda ya faɗi haka yana da dalili,kuma tunda har ya iya kawomu gare ta na tabbatar da zai kai ta gare mu ita ma,dan haka mu ƙara haƙuri"

Ganin wasu yan mata na ƙoƙarin geftawa ne yasa ya dan daga murya kaɗan yana faɗin "Assalamu Alaikum"

Juyowa suka yi suna amsawa,

"Muje su mana jagora cikin gidan"

Kallon samarin dake doso su suka yi "Bilki kamar yannin Biba"

"Ta yaya kikasan ko sune?

" Saboda ban manta fuskar na tsakiyar ba"

Kallon shi da kyau Khadija tayi tana dan mun tsinin ta"ya haɗu "

Juya ido tayi tana "ke ba haka nake nufi ba"

Suna karasowa,gaida su suka yi kafin tace "wa kuke nima?

Abdulmajid dake tsakiya ne ta bata amsa" Ko zaku mana jagora zuwa wurin kaka"

"Eh babu matsala mu je"

Suna baya ƴan matan na gaba har shiyan Kaka,

Tsayawa suka yi a ƙofa har sai da suka shiga suka nimar masu izini wurin kaka,

"Wai ku shigo" Cewar Khadijah data fito,

Ita kaɗai ce a ɗakin sai su Balki da ke ciki tare da Nafisa,suma suna cikin gaisawa da Kakan suka fito suka wuce daga dukkan alamu wani wurin zasu,

"Ya masu jikin?ta tambaya,

" Duk sunji sauki Kaka,dan ita Salma ma ina ga tana shiyan Ammi"

"Hakan yayi Allah ya ƙara masu lafiya"Abincin dake gabansu wanda Nafisa ta kawo ta nuna masu" Kuci Abinci "

"To Kaka mun gode" Sun san halin tsofaffi basu son su baka abu kaki ci,dan haka suka buɗe kulolin wanda lafiyayyen dambun shinkafa ne a ciki yaji kayan haɗi,

Dama shi Abdulmajid yana matukar son dambu,dan haka ko suka ci kaɗan shi ya karasa sauran sannan ta kora da ruwa,

Dariya kaka ke masa ganin yanda ya keta santin dambun,har da tambayarsa ko a karo masa,
Yace ta ko shi,

Sun dan jima a gidan kaɗan sai da suka bata labarin duk abinda ya faru,sai dai kuma ba komai suka faɗa mata ba saboda wannan sirrin Ahalinsu ne,wanda suke fatan ya kasance a binne har abada,

Sai dai basu ɓoye mata batun auren Yusuf da ita Salman ba,
Chapter 78 · 0% Book details