← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 96

Sashe 83

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga lokacin sai muka samu sauƙin komai har sai da jikana Suraj ya kai shakara goma,

Wata rana na dawo gida daga wurin aiki na taradda Hafsat zaune a falona tana kuka,
Hankali na ya tashi dan haka da sauri na karasa in da take na rungume ta ina tambayar ta lafiya,
Cikin kuka take sanar dani cewar Abdul basit yana cin amanar ta ba zata iya zama dashi ba ya sake ta,
Jin wannan kalmar daga bakinta yasa hankali na yayi kololuwa wurin tashi,domin saki abu ne da ba'a taba yi ba a dangin mu,
A lokacin nayi rarrashin duniya amma taki hakura,na kira shi shima nayi tambaya har nayi fushi yaki ya fada min abinda ya faru,sai ma kuka da yake yi akan na riƙe ta tayi hakura ba zai iya rayuwa babu ita ba,

A lokacin da nayi kokarin kara bata haƙuri sai nuna min hotunan shi tayi wanda yake tare da mata cikin tsiraici,abin yasa zuciyata girgiza,sai kuma kalmar da ta faɗa na cewar idan har ina kallon ta a matsayin Ƴar dana haifa na saka ya sake ta,

Juyowa nayi gare shi,cikin mutuwar zuciya dana gangan jiki,sai dai kafin ince mashi wani abu,ya buɗe baki da kyar cikin kuja ya furta mata ya sake ta saki ɗaya,sannan ya tashi ya fita,tunda ya bar gidan bai ƙara dawowa ba,sai dai muna waya dashi lokaci-lokaci,bayan tayi Idda da watanni biyar wanda har lokacin muna tare kuma babu abinda ya canja a tsakanin,ta kawo mana wani a matsayin wanda take so wanda ni bansan in da ta haɗu dashi ba,wato Abbu Safwan,nasan zata fuskanci matsala daga wurin dangin mu,amma da taimakona ta aure shi,duk da har raina ba wai ina kaunar shi ba ne,
A ranar da aka ɗaura auren su a ranar aka sace Suraj...

🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*83*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Hankalin mu ya kai kololuwa wurin tashi,lungu da tsako yan sanda nima suke sai dai babu labari,Kakanshi ne yace ai mu kwantar da hankalin mu ayi trackin din Suraj ta hanyar zoben dake hannu shi wanda ya bashi a matsayin kwatar karin shekara,
Da wannan muka yi amfani wurin gane in da suka kai shi a cikin wani sohon gini na wani unguwa,ba karamin fafatawa akayi da yan sanda da barayin ba kafin su samu nasarar dauko shi,inda suka kashe mutum biyu cikin barayin,suka kuma kama mutum daya,
Da ka tambaye shi dalilin kama Suraj din sai cewa yayi suma kwangilar sace shi aka basu,kuma basu san wanda ya saka su ba,abinda da yasa kuma suka karɓi aikin saboda na kuɗi ne masu yawa aka saka a kan duk kungiyar data samu sa'ar sato shi,
Wannan bayanin nasu yasa Hafsat ska kuka tare da roƙo na akan dan Allah na basu Suraj su tafi dashi Nigeria,ba zan iya hana ta ba saboda ina matukar son ta,duk da muma na jin yanda zamu rabu da jikan mu,ta gefe ɗaya kuma ga mahaifinsa,sai dai shima ko ba komai Hafsat kanwa ce a gare shi,zai iya yin komai domin faranta mata,shi yasa ko da na faɗa masa hukuncin daya yanke bai Musa ba,domin dama shi ba mai jayayya bane a gare ni,
Dan haka a washegari ranar suka wuce dashi,

Sai da tayi wata biyar hudu sannan muka kwaso muka zo dubata har da Abdul basit,a gidan da muka saka aka yi mana ana muka sauka,
Munyi farin cikin ganin ta ita da Suraj cikin farin ciki da ƙoshin lafiya,gata kuma har Allah ya azurta ta da samun ciki,
Mun kai wata biyu a garin sannan muka koma London,bamu kara dawowa ba sai ta haihu,
A gaka rayuwa ke tafiya mana sai dai kuma shi Abdul basit yaki yarda ko kadan yayi wani aure,idan yaga na damu sai yace mai nike buta aduniya daya jika,kuma gashi sun bani shi da Hafsat,in yi hakuri ahi ba zai iya aure ba tunda har Hafsat bata iya zama dashi ba,to babu macen da zata iya zama dashi,
Haka kuma idan nace to ya fada min gaskiyar lamarin shi da ita,nasan shi ba mai niman mata ba ne,me ya faru,sai yace shima bai sani ba,amma yaji daɗi da nuna yardar da nayi dashi,Hafsat kuma bai san in da ta samu waɗannan hotuna ba,sai dai yasan komai dadewa gaskiya zata yi halinta ko yana raye ko baya raye,idan ya faɗi hakan na kan kwabe shi da fadin ina zai je ya bar ni,

Wani narar Alhamis da ba zan taba mantawa ba,
Abdul basit ya shigo garin daga Airport zuwa gida aka dauke shi,sannan aka kira mu akan in har muna son ɗan mu dole mu amso wannan Diamond din mu kawo gida,idan kuma muka daka faɗa ma Jami'an tsaro to tabbas zasu kashe shi,

Dan mu yafi mana komai da muka mallaka,dan haka cikin rawar jiki muka je Banki bayan dogon cike cike muka amso sannan muka dawo gida, sai dai kafin mu shiga ciki sai ga kira daga Hafsatkamar ba zan ɗauka ba,sai kuma na dauka,cikin Kuka take shaida min Abbu Safwan yaci amanar mu,tambayar ta na shiga yi akan wani amana ne yaci,na daiji ta ambaci sunan Abdul basit daganan mijina ya karɓe wayar ya kashe tare da faɗin yanzun ba lokacin wannan maganar bane, ,muna shiga falo anan muka same shi daure da saman kujera sun masa jina jina,yayin da fuskokinsu ke sanye a cikin bakin safa,
Mutum shida ne,sannan muryoyin su ba asalin nasu bane sun yi amfani da abin canja murya,
Cikin kuka na isa gare shi ya rungume shi una kuka,ina kuma rokon da su kyale mu ga abinda suke bukata nan,sai dai cikin rashin imani babban su yana karbar akwatin Diamond din a hannun Usman ya harbe shi a tsakiyar goshi,
Wani irin razanannan ƙara na fasa,sai ina ƙoƙarin barin jikin Abdul basit naji ya kira suna na,abu ɗaya ya faɗa min shine Ummi Suraj,kafin ya karasa shima sai saukar harbi naji a jikinshi ta ko'ina,na ruɗe,na rasa wurin waye zan tafi,shi wurin mijina da nake ganin shi kwance acikin jini babu rai,ko kuma wurin dana da yake zaune cikin jini wanda yake zuba kamar an yanka dabba,
Kamar yanda nake kallon idanun Abdul basit dake kallo na a haka har idanun suka lumshe alamun rai yayi halin sa,
Na rasa hankali na domin sai kiran sunan su nake yi,da wannan suka yi amfani wurin ganin sun buga min ƙarfe a ciki a maimakon harbi,a cewarsu ba zasu yi asaran bulet din su ba wurin karasa ni, wannan ma kawai ya ishe ni,nan suka wuce suka barni,ba tare da sun san Allah ya yi ba zan mutu a hannun su ba,sun kashe min miji da dana a gaban ido na,sai dai kuma duk da haka na gane mutum data a cikin su,wanda yake tunanin idan yayi badda kama ba zan iya shaida shi ba,sai dai ina rokon Koto da kafin na faɗi waye wannan ina son ba ma Hafsat dama ta fito ta faɗi abinda ta sani game da wannan lamarin.

Kowa ka gani a cikin koton jikin shi yayi sanyi yayin da dayawa a cikin su hawaye suke yi na tausayin matar,ta ɗayan bangaren kuna idan ka juya zaka ga waɗansu sai sharan zufa suke yi,duk sanyi irin na garin,domin basu taba tsammanin irin wannan ranar zata zo masu da wuri ba,acikin bazata,

babu wani tashin hankali da ya wuce irin wannan kisan a gaban idan ka,har balle a ce mutane masu muhimmanci a gare ka,

Nan daya daga cikin Alkalan yace Hafsat ta fito,
A hankali Ammi ta fito wacce idanun ta sun yi jajir saboda kuka dan tunda Grandma ta fara bada labari take kuka domin tuna irin zama na amana da suka yi da Abdul basit da irin soyayyar da ya nuna mata,ita ce zata masa laifi amma dan kawai a zauna lafiya shi zai bata haƙuri ya haɗa harda lallashi,ko kadan baya son abinda zai taɓa ta,ba zata taɓa yafe ma duk wani mai hannu a cikin kisan shi ba koda waye kuwa,share hawayenta tayi tana tsayawa a kan stage,

"Kamar yanda Ummi ta faɗa kun san komai daya faru har aure na da Abbu Safwan,A lokacin dana kira Ummi a wannan ranar naji wani sirri dan gane dashi wanda ya tashi hankali na har na kasa daurewa na kira ta,
Abinda ya faru kuwa shine na kammala girki rana shi kuma yana dakin shi wanda tunda nake dashi ban taba shiga dakin ba,idan na tambaye shi me a cikin ɗakin n sai yace min ai takardu ne kawai a ciki,ni kuma ban kawo komai a raina ba,
To naje faɗa mashi cewar na kanmala abinci shine na samu tana cikin wannan dakin kuna kofar a buɗe take,dan haka ba tare da tunanin komai ba na kutsa kai,dai-dai lokacin shi kuma yana waya yana faɗin,
Ku kashe Abdul basit din,domin na lura har yanzun hankalin ta na kamshi,karku damu da batun takardun domin nasan ita da ɗanta sun san inda takardun yake,zan ci gaba da lallabasu har su kawo min shi cikin hannu na,
Sai kuma ya kuma cewa ai wannan dalilin ne yasa nake matukar girmamaka Oga,domin cikin ruwan sanyi ka saka ta rabu da mijinta ta hanyar hotunan karya,gashi yanzun ka aura min Jari domin ita din jari ne a gare ni,ai in faɗa maka ko yanzun kasuwa ta tashi dan koli yaci riba,

Jikina na rawa na juya na bar dakin ina kuka shine na fita ta baya cikin tsananin tashin hankali na kira Ummi dan in shaida mata,
Na fara mata magana shine ta kashi wayar na kira na kira kuma ban samu ba,nan na tsugunna ina ta rusar kuka na rashin sanin abin yi,

Daga baya na naji ance"kin gane gaskiya kenan ko?
Chapter 83 · 0% Book details