Sashe 69
Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali yake takawa har ya ƙarasa shigewa cikin ɗakin,
Littafin dake Aljihun shi ya ciro,
Shafa littafin yake kafin ya buɗe wani durowa mai numbobi wanda in baka lura ba zaka ɗauka ma abin zama ne,
Saka littafin a ciki yayi ya maida ya kulle,sannan ya shiga wanka,
Ya jima a banɗaki kafin ya fito ya saka kaya ya kwanta,dan tun a Asibiti yayi sallah kafin ya fito dan masallacin can suna riga na kofar gidan su Sallah,
Yayi ƙoƙarin ganin ya cire komai a ran shi kodan ya samu ya huta sosai ta yanda zai iya kula da ita kamar yanda Doctor ya faɗa,
Kuma Alhamdulillah yana kwanciya barci ne mai matukar nauyi ya ɗauke shi.
Jin yanda wayarshi ke ta ƙara ne yasa ya buɗe idanun shi da kyar wadanda sukai mashi nauyi,
Addu'ar tashi daga bacci yayi kafin ya mika hannu ya jawo wayar,
Kallon Screen din yayi,ganin sunan me kira ne ta saka ya dauki wayar yana sallamah,
Daga ɗayan ɓangaren amsawa tayi"kana ina?tundazu mun iso bamu gan kaba,gashi kaka ta damu"
"Ammi barci nake yi amma gani nan shigowa"
"Yauwa to maza ka tashi domin har ƙarfe biyar tayi"
Da sauri ya maida kallon shi kan agogon bango yana zabura,dan ko Sallah la'asar bai yi ba,
Cikin sauri yayi wanka domin ya kara samun karfin jiki sannan ya shirya cikin wani farin shadda wanda yasha maiko,ya gyara suman kanshi wanda sai da ya rage sama_sama saboda cika,
Yana idar da sallah fitowa yayi daga dakin yana jawo ƙofa,
Ji yayi ance"Yaya Suraj "
Juyawa yayi yana kallon me kira ba tare daya ce mai komai ba,
A hankali yake matsowa in da yake tsaye,hannu yakai a hankali ya dan taɓa shi"kai ne kuwa"ya fada kamar mai kokonto,
Mintsinin shi yayi a kafaɗa wanda hakan yasa ya saki ihu yayi tsalle ya rungume shi yana dariya yana faɗin "shine,wallahi shine ashe"
Dariya shima yayi wannan karo yana raba shi da jikin shi "Salman so kake ka karya ni"
Kuka kuma ya fashe da shi yana rike hannun shi"yaya Suraj,wallahi na ɗauka shi kenan ba za mu kara ganin ka ba"
Shafa kanshi yayi yana dan murmushi "to ba gani ba, me na kuka?
" Gani nake yi kamar mafarki nake yi"
Ganin ya fara tafiya ne yasa da sauri ya riƙe shi yana zaro ido"ina kuma zaka"
"Zan koma in da na fito ne"
"Ina kenan" Ya tambaya da sauri
"Duniya ta,domin dama mafarki kake yi" Dafa kafadarshi yayi"ya kamata ka farka haka nan in ba so kake ka bini ba"ya karasa faɗa yana zame hannun shi cikin da Salman ɗin,
Ganin kiran Ammi na ƙara shigowa wayar shi shine yasa da sauri yayi gaba ya bar shi nan tsaye yana tunanin shin da gaske mafarki yake yi ko kuwa idanun shi biyu.
Kai tsaye shiyan Kaka ya nufa inda suke zaune suna jiranshi.
Tun isan shi shiyan ya fahimce falon a cike yake,kasancewar yanda hayaniya ke tashi da muka yawan takalmar dake zube a ƙofar ɗakin,domin ita bata barin a shigar mata da takalmi falo,
Zame takalmin kafar shi yayi ya daga ƙaramin labulen dake rufe a kofa wanda yake shara_shara,bakinshi dauki da sallamah,
Kalifa yaron Aunty Atika shi ya fara ganin shi,dan yawanci hankalin su ya dauke ne a kan hiran da suke yi,
Jin yanda yayi ihun kiran sunan "Uncle Suraj" da yanda ya tashi da gudu ya nufo wurin shi ne ya janyo hankalin su dawowar kan wanda ke tsaye a bakin kofar yana dariya yayin da yake juyi da yaron a hannun shi,
Basu taɓa tsammanin sun yi kewarshi har haka ba sai yau da suke ganin shi,basu taba tsammanin dariyar shi na saka su nishaɗi ba sai yanzun da suke ganin shi tsaye a gabansu yana dariya,
Kai jama'a rayuwa kenan,yayin da wasu ke tsananin murnar ganin ka da ci gaban ka,to wani idan ya ganka ji yake kamar ya kashe ka,amma kuma a zahiri nunawa yake kamar yafi kowa murnar ganin naka(Allah kara bamu da makiyan ɓoye).
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*69*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Kamar dama jira su khadija ke yi ya sauke kalifa suka taso suma da gudu suka rungume shi,sai kuma Amira ta fara kuka,ganin haka ne yasa suma suka fara kuka,
Har yanzun dai murmushi ne a fuskarshi, "kukan na menene ba gashi na dawo ba"
Ƙara kan_kame shi suka yi,Kaka ce ta hau faɗa "yau ga ja'iran yara,so kuke ku yarda shi,ku sake shi muma mu samu mu ganshi mana"
Sake shi suka yi yayin daya cigaba da taku har gaban Kaka in da take zaune tana jin kamar ta tashi ta taro shi,sai dai ciyon kafa ya mata cikas,
Yana isa gabanta tsugunnawa yayi yana kamo hannayen ta ya sumbata"Kaka"
Hawaye ta shiga zubarwa "Allah mun gode maka da ka dawo mana da wannan yaron hannun mu lafiya ba tare da dubaran mu ba,Surajo Allah ya ƙara tsare ka,ya tona Asirin masu hannu a wannan lamarin"
"Amin Kaka,ya karfar ki?
" Ƙafa da sauƙi sai godiyar Allah "leken bayan shi take yi" Ina ita Habiba,ya banganta ba?
Shiru yayi bai iya bata amsa ba sai ma mikewa da yaki ya nufe in da Ibrahim yake ya mika mashi hannu,kafin ya ba Shamsuddeen sai Nurudeen,duk masabaha suka yi suna mashi barka da dawowa,
Idanun shi ne suka sauka a kan Maijiddarh wacce duk inda yayi take bin shi da ido,
Duke kan shi yayi kafin ya gaida su Hajiya Saude,da Goggon yara,duk Allah ya tsare suka mai,
"Yanzun Suraj shi kenan magana ta ƙare? Cewar Momy Saude,
" Ya ƙare mana,idan bai kare ba zaki ganshi ne a nan,ai duk munafunci irin na mutum bai isa yayi abinda Allah bai yi ba"kaka ta faɗa wacce dama kamar jira take yi,
"Ah ni fa bawai ina nufin wani abu bane,dama tunani nake yi tunda ya dawo kuma ni har yanzun ban gama bincike a kan wannan Yusuf din ba d......
Katse ta kaka tayi ta hanyar kara tambayar shi a karo na biyu" Wai ni Surajo na tambaye ka ina Habiba baka Bani amsa ba har yanzun"
Kallon Ammi yayi wacce ta mai magana da ido,
Juyawa yayi kan Kaka"ki yi haƙuri Kaka,tana Asibiti yanzun haka"
"Me ya same ta,Allah yasa ba hannun bane ya matsa mata?
Furzar da iska yayi cikin yanayi na dan damuwa yace" Ba hannun bane,domin yanzun haka aiki za'a mata zuwa anjima "
Dafe kirji tayi tana salati "wani irin ciyo ne haka ya same ta da za'a mata aiki"
"Jiya ne da aka fito koto,a yanda nake samun labari daga bakin durebanta wai taga wasu sun fito daga cikin koton sun shiga mota,to shine tace ya bi bayan su da ita,suna zuwa ta bar shi a waje ita kuma ta shiga cikin gidan,to bansan waye ta gani ta bi ba, ko kuma me ta ji a can,kawai dai sai gani yayi ta fito da gudu wasu na binta,ashe garin gudu sun samu nasaran buga mata ƙarfe a kai,"cewar Ammi
"Yaya to wasu mutane ne waɗannan? Sannan me tai masu"cewar Khadijah
"Koma dai me tai masu wannan karon sun zaɓi hanya mara bullewa"
"Idan har kasan ba zaka iya kula da ita har haka ba me na bari ta shiga cikin rigimarka? Nurudeen ya fada cikin yanayi na jin haushi,
"Kasan ko su waye ne?gaskiya ko su waye basu kyauta ba"
"Umm na sani" Ya faɗa yana sauke idanun shi akan Shamsuddeen, "Kaka zan fita zai dai zuwa anjima"
"Ka faɗa mana wani Asibiti ne sai mu je mu dubata" Cewar Goggo,
"A'a Goggo ki bari zuwa gobe sai kuje ku dubata saboda yanzun ko kunje ba za ku samu damar ganin ta ba"
"To ba damuwa Allah ya kaimu ya kuma bata lafiya"
Da Amin ya amsa yana fita.
Yana fitowa kai tsaye shiyan Ammi ya nufa,har ya kusa isa yaji daga bayan shi ana kiran kiran sunan shi,
Tsayawa yayi yana jiran karasowar ta,
"Ya aka yi Maijiddarh?
Matsowa tayi ta gefen shi ana ana dukar da kai" Yaya Suraj nayi farin cikin dawowar ka sosai"
"Na gode"
"Yauwa ya jikin Habiba?
" Da sauƙi Alhamdulillah"
Ganin tayi shiru ne kamar wacce bata da abun faɗa yace"ina iya wucewa"
"Eh,amma anjima zan zo Asibiti na dubata"
"Ok ba damuwa sai kin zo" Ya faɗa yana karasa shigewa cikin falon,
Da kallo ta bi shi tana jin tamkar tace ya tsaya,sai dai tasan a yanzun ba tada wannan damar,amma zata jira har zuwa sanda zata samu dama.
Yana shiga shiyan Ammi tsayawa yayi a babban falon su yana tsura ma hoton da sukayi gaba dayan su ido wanda harda Shamsuddeen a ciki,
Ji yayi daga bayan shi an dafa shi,
Juyowa yayi yana ganin ita ce ta rungume ta,
Ita ma rungume shin tayi tana Hamdala ga Allah maɗaukakin sarki,
Hannun shi taja suka shiga har cikin dakin ta sannan ta maida kofa ta rufe,
Zaunawa tayi saman gado yayin da ya zauna a kujeran dake gefen ta,domin baya taba yarda ta zauna mata a saman gado,duk da yasan ba nan suke kwana tare da Abbu ba.
"Shin an samu nasara kuwa?
Lumshe ido yayi ya buɗe" Ammi an samu fiye da baya"
Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi"kayi haƙuri Suraj na saka ka damuwa da yawa sanadin wannan aiki,sai dai ka sani dole sai ka sadaukar da wani abu kamin ka sami wani abun,
A lokacin dana samu karin bayani akan wannan shirin nasu hankali na ya tashi sosai,na rasa ta wani hanya zan bi domin tseratar da kai,ka yi hakuri shi yasa na juya wasan ta yanda basu yi tsammani ba,sai dai gashi ta sanadin haka the innocent soul is suffering,ina fatan zaka yafe min?