← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 96

Sashe 24

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ta girgiza mai,
"Me yasa ba zaki sha ba" Ya tambaya

Cikin kuka tace"bana shan shayi"

Nuna mata kofin dake gabanta yayi"amma wannan ba kalan shayin da kika saba sha ba,wannan yana ƙara lafiya dan haka ki daure ki sha a wuce wurin"

Girgiza kai take yi"dan Allah kar ka bari ya saka ni in sha mutuwa zanyi,dan Allah ka taimake ni"

"Is ok Baby I will help you"
Maida kallon shi kan Suraj yayi wanda gabaɗaya ma hankalin shi bai kansu yana kan aikin da yake yi a waya,

"Suraj wai me yasa kake son ka tilasta mata ta sha,tunda bata ra'ayi kamata tayi ka bar ta, ba kowa ke da ra'ayin shan shayi ba har balle irin wannan"

Ko kallon su bai yi ba,
"Suraj pls ka ajiye wayar nan muyi magana mana," Ya faɗa cikin roƙo dan yasan halin shi idan har yace zai mai garaje yana iya hassala shi,

"Me kake buƙata? Ya faɗa ba tare daya ajiye wayar ba,

" Dan Allah ka saurare ni dai"

Ajiye wayar yayi yana fuskantar shi"ok ina jin ka"

"Dan Allah ka bar ta ta wuce"

"Idan kana hada ni da Allah kana ƙara ja mata ne"
"Sorry na fahimta to ka bar ta ta wuce"

"Me yasa dana ce kowa ya dauko shayin ya ɗauka ita taki karɓa?

" Me kake nufi?

Ba tare daya kalle in da take ba yace"ka tambaye ta"

Kallon ta Nurudeen yayi"me yasa baki ɗauka ba?

"Bana shan shayi shi yasa"

"To kaji me take"

"Yauwa kai likita ne ai ko?

Jinjina kai yayi" Sosai ma kuwa"

"Zaka bari ta mutu a gabanka?ya faɗa yana nuna mashi Biba.

" Kai ina har abada,idan akwai hanyar da zan ceceta sai nabi dan ceto ta"

"That is good,dan haka ɗauka kisha yanzun kafin na nuna maki asalin waye ni ta yanda ba zaki taɓa manta hakan ba" Ya faɗa cikin tsananin daure fuska babu alamar wasa a ciki,

Kokarin magana yake amma sai cewa tayi"idan ba zaka iya jira a nan ta sha ba,ka jira ta a waje idan ta fito ka ceci rayuwar nata"
Jin abinda yace ne yasa yayi shiru kawai yana kallon su,
Yayin da ita kuma ta dauki kofi cikin kuka tana faɗin "i am Sorry" Sai dai ko kallon ta bai yi ba,

Kurba daya taima shayin ai da gudu ta mike ta shiga yarfe hannu ta rufe baki dan ta kasa haɗiye wa,
Duk da kallo suke binta,ƙoƙarin zubarwa take yi taji yace"idan har kika zubar zan ƙara maki wani "

Da kyar da rintse ido ta haɗiye,
Gaban shi ya nuna mata dole ta dawo ta tsugunna,a takaice ranar taga Azaban da tunda Allah ya halicceta bata taɓa tsammanin haɗuwa da irin sa ba,domin ko wani kurba daya ji take kamar zai tafi da numshinta da fatar bakinta harma da maƙoshin ta,
Tayi kuka tayi data sani tayi ban haƙuri amma bata taɓa tsammanin rashin imanin shi yakai nan ba,

Da Nurudeen ya nuna bacin ranshi sai cewa yayi idan ya kuma magana sai ya kara mata ruwan shayin domin ita da kanta ta haɗa abinda zai kashe ta,ko ƙarya na faɗa? Ya faɗa yana kallon ta yanda miyau ke dalala daga bakin ta,

Da sauri ta girgiza kai,Alamar haka ne,

"Dan haka idan ba zaka iya jira har ta kammala ba kana iya jira a waje"

Gaskiya ba zai iya ba,amma kuma ya tausaya mata,wata kila saboda bata san halin Suraj din bane shi yasa ta yi gangancin yi masa kutse,
Tashi yayi ya bar falon.

Bai damu da yanayin da take ciki ba sai da ya tabbatar ta shanye shayin dake cikin kofin tas sannan ya mike tsaye,dukowa yayi saitin kunnenta "ki tabbatar da ƙwarin gwiwar ki kafin aiwatarwa" Yana gama faɗar haka yayi ficewar sa ya bar ta nan tana fitar da numfashi da ƙyar,

Ko tashi bata iyawa sai da Nafisa da ke kofar gida taga fitowar shi shine ta shiga ta dagata,
Amma ina ko tashi bata iyayi,da talla_talla ta taimaka ta kaita shiyan su,dan ji take cikinta kamar ana busa mata wuta a ciki,
Ranar bata ga komai ba sai da daddare domin ranar a cikin bayi ta kwana,domin zawo mai azabar yaji ya kamata,tun tana yi tana iya fitowa har ta koma a banɗakun kawai take zaune,ko zaman ma sai dai tayi goho,tun tana iya hawaye har takai bata iyawa,domin abun sai ya haɗe mata ya zama Amai da zawo,
Kafin gari ya waye har ta zabge yanda kasan wacce tayi jinyar shekara,ko tashi bata iyayi,ita kanta Ammi data ganta da safe sai da ta tsorata,cikin gaggawa tasa akayi Asibiti da ita,a takaice sai da tayi kwana uku a Asibiti tasha ruwa leda Takwas,dan zawo tayi bana Arziki ba ko zama taba iyawa,
Duk numfashi daya cikin tsine ma Suraj take,in Allah ya yarda yace ta tabbatar da ƙwarin gwiwar ta kafin aiwatarwa to sai ta bashi mamaki,sai tasa yayi suman tsaye..
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*26*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Kaka ce tace Nafisa ta tsaya ta yi jinyar ta a Asibiti,ranar data cika kwana biyu kuma sai ga A'i ta zo a matsayin yar uwarta,ta karɓi jinyar har aka sallame ta,

Tana zaune kan gado A'i na haɗa kayan su a jakka ta kalle ta"kina buƙatar hutu dan haka na ɗaukar maki izini wurin Uwar ɗakin ki,idan kin ƙara jin sauƙi sai ki koma"

"Babu in da zanje ki mai dani can kawai,domin sai na ƙarasa aikin dana fara"

Ajiye kofin dake hannun ta tayi ta dago tana kallon ta"a haka ne zaki koma wannan gidan,Gara dai ki bari ki ƙara kwari in ba hakaba karasaki zasu yi"

Kauda kai tayi"ko da zan dauki hutu sai na tabbatar na rama abinda akai min"

"To wallahi in dai zaki bi shawara ta gara ki bar batun ramuwar nan,domin banga amfanin ta ba,wannan da kike gane tunda har ya iya tsallake tarkon ki ba tare da ko kwarzane ba ki tabbatar yana iya saukar da duk wani hatsari da jiji da kai irin na ƳAR TSANAR ZINARI"

"Zamu gani" Ta faɗa cikin kwarin gwiwa,

"Ki kalli yanda ya saka acikin kwana uku kika kusa rasa rayuwar ki,kin kuwa ga ma yanda kika koma,gaba ɗaya duk cikar fuskarki ya tsiyaye sai dogon hanci da idanu,to wallahi ki yi a hankali kar a fito mana da gawar ki"

Saukowa tayi daga kan gadon Asibitin "idan kin kammala haɗa kayan ki same ni a waje" Ta faɗa tana barin ɗakin,

Shiru tayi kawai ta bita da kallo,tausayin yarinyar take yi,domin ta tabbatar da bata san irin girman hatsarin da take saka rayuwar ta aciki ba,
Domin ba ita bace mace ta farko da VIP ya bama wannan aikin ba,ita ce ta shida,
Gaba ɗayan su sunyi aiki ne a sashi mabanbanta a cikin gidan,sai dai wahalhalun dake tattare da zama acikin gidan ke koransu,wasu basu ma samu damar koda magana bane da shi uban gaiyar,Ustaz,balle su samu damar nufar shiyan mazan gidan,acikin su ma akwai waɗanda ko ganin shi basu taba yi ba agidn, a haka kuma ko waccen su da kalar wahalar da zaisa su bar gidan,sai dai da sun fito da kwana biyu ake niman su a rasu sai bayan wani lokaci aga gawarsu,ba dan komai ba sai dan kawai sun san sirrin abinda ake hari,
To amma ita nata lamarin da ban ne tunda gashi har ta samu nasaran sanin wani abu,
Ta san ko da tayi nasara VIP ba zai taba barin ta ba,
Ajiyar zuciya ta sauke sannan da ɗauki jakkan ta fito,
Dole haka ta maida ita gidan ba dan tayi ni ya ba,
Ammi ce tace taje daki ta huta ta bata hutun kwana huɗu ta kara hutawa,
Sosai tai mata godiya sannan ta koma ɗaki,tana tunanin ta hanyar da zata dauki fansa dan ita bawai zata ƙyale shi bane,

Washegari tunda ta tashi,take cikin wani irin yanayi na rashin farin ciki da walwala,zuciyar ta gaba ɗaya zafi yake mata,har balle idan ta tuna yau wace rana ce a gare ta,
Ranar ko shiyan kaka bata shiga ba,sai wuraren bayan sallar La'asar sannan ta fito,ta bayan ɗakunan su nan ta je ta samu wuri ta zauna,

Fito da kwalin sigarin dake jikin ta tayi ta kunna daya,kafin wani lokaci har ta gama dashi ta kuma kunna wani,a haka sai da tasha kara biyar ba tare da taji komai na daga damuwarta ya rage ba,sabaninda da ƙara daya kawai take sha,

Tana ƙoƙarin kunna na shida ne sai ga kira ya shigo karamin wayar ta,dagawa tayi ta kara a kunne ganin me kira,
Sunan ta aka kira"Babi "

"Ummm" Ta amsa mata,
"Ina fata kina lafiya?
" Ummm"
"Ar you ok"
Share wayen daya zubo mata tayi da bayan hannun ta"yes I am fine"

Dan shiru ne ya ratsa tsakani kafin kuma tace"karki yi kuka,dan Allah kar kiyi shaye-shaye,don't forget were you ar,karki manta me ya kawo ki,nasan yanda kike ji yanzun saboda yau ne,amma karki bari tuna hakan ya raunata zuciyar ki,karki sha Sigret da yawa"

Dan jan majina tayi kaɗan "is really painfull,ji nake kamar zuciya ta zata buga,na kasa manta komai,na kasa anytime i remember is really destroy me,bana son ina tunawa amma it keep coming to my mind and ring is to my head,"

"Na sani,yanzun me kike yi?
" Just setting"
"Me a hannun ki?
Kallon Sigret din tayi"Segret "

"To ki maida shi cikin kwali sannan ki kashe wanda kike sha ki rike sai ki zubar in da ba za'a gani ba"

Kamar yanda faɗa mata haka tayi sai dai kwalin na ajiye a gefen ta,"Ummi ta"ta kira sunan ta,
Chapter 24 · 0% Book details