← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 96

Sashe 60

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sanyi jiki da kokonton iyayen nasu suka fito daga dakin Baba yayin da suka samu Mama a falo zaune tana kallo a zahiri,amma idan ka fahimce ta da kyau ba kallon take yi ba kawai idanun ta ne a kan TV,
Duk zama suka yi kusa da ita,yayin da Abdulmalik ya dafa kafadarshi ta,"yin dogon nazari yana haifar da damuwa Mama"

Juyowa tayi tana ɗan lumshe ido"kanwar ku ke ƙoƙarin haifar ma da rayuwar mu da damuwa gaba ɗaya "

Matsowa Abdulrahman yayi cikin damuwa"Mama dan Allah ko dai akwai abunda kuke ɓoye ma na ne game da Yusuf ke da Baba banda baku son mu sani?

"Me ka gane Abdulrahman,shin wani abun ya faru ne?

" Mama munje mun samu Baba da maganar Yusuf da Salma,da fari ya yarda ya amince kafin sanin Yusuf take so,amma daga jin shine taje so,shima ya tashi hankalin shi ya nuna rashin yardar shi,Mama ko dai Yusuf yaron Baba ne bamu sani ba?

Kallon yaran nata take yi yanda duk suka tsira mata ido suna jiran karan bayani,
Girgiza kai tayi"Shi ba ɗan mahaifinku bane,domin mahaifinku ba shida wani ɗa a duniya,kuma na tabbatar da mata basu gaban shi,
Kawai dai akwai dalilin da yasa bamu amince da wannan auren ba,sannan ɗan Allah karku tambaye ni domin ba faɗa maku zan yi ba har abada kamar yanda shima mahaifin naku ba zai taɓa yarda ba har da shi kanshi Yusuf ɗin,domin shi yasan dalilin,
Abu na gaba shine kusan yanda zaku shawo kan kanwar ku ta bar wannan maganar ta canja wani"tashi tayi ta koma daki ta turo ƙofa,

Cakuɗe gashin kanshi Abdulmajid yayi"ohhhh,this doesn't make sense,kai na ya dau zafi,so nake na san wannan dalilin"

"Ni ma haka wallahi" Cewar Abdulmalik,

"Ku tashi mu je mu sami Yusuf tunda Mama tace ya sani sai mu rokeshi ta faɗa ma na"

Da haka suka bar gida,sai dai ko da suka je gidan su Maman shi ke shaida masu ya fita sai dai ba zai jima ba, dan haka suka zauna zaman jiran shi,
Ya ɗauki kusan awa daya kafin ya dawo,ko da ya gansu bai wani nuna zumudin zuwan nasu ba kamar sauran lokutan da suka saba zuwa har ya rasa ina zai ajiye su,

Jan kure yayi ya zauna yana miƙa masu hannu suka gaisa,"kun jima da zuwa ne?

"Eh amma ba sosai ba"

"Ai da kun kira ni"

"No ba damuwa tunda gashi ka dawo" Cewar Abdulrahman

"Da fatan kuna lafiya" Ya tambaye su, dan wannan karon dukansu su uku ne suka zo,

"Lafiya ƙalau,dama dai akan maganar jiya ne Yusuf,sai dai abin mamaki kamar yanda kace iyayen mu ba zasu yarda sai gashi hakan ne ya kasance dan har yanzun dukansu sun ƙi amincewa saboda wani dalili nasu wanda mu ba mu sani ba amma kuma kai kasani,shine muke rokon ka ko zaka iya faɗa mana ne yasa dukka suka ki amincewa da kai,menene dalili "

Ɗan dariya yayi wanda ya basu mamaki domin basu ga wani abun dariya ba acikin wannan maganar"shi Baban da Maman naku basu faɗa maku ba? Ya faɗa yana Daura kafa daya kan daya,

"Sun ƙi faɗa shi yasa muka zo ko zaka faɗa mana"

"Ai ba zasu iya faɗa maku ba,domin sirrin su ne"

"Dan Allah ka faɗa mana,menene wannan sirrin Yusuf" Cewar Abdulmajid cikin zakuwa,

Girgiza kai yayi"Umm umm,domin ƙwaƙwalwan ku da zuciyar ku ba za su iya ɗauka ba,May be ma zuciyar dayanka yana iya bugawa,dan haka"Let the sleeping dogs lie"(abar kaza cikin gashin ta)

"A'a Gara dai a fige ta"

"Kun ga ni iyaye na ada talawaka ne,saboda iyayen ku ne muka samu rufin Asiri har muka samu muhalli na kuma samu abun yi,ƙila shi yasa suke ganin rashin dacewar na aure ƴar su,ni ma kuma bai dace na aure ƴar mai gida na ba,kun ga gara dai da kasance ayi Cut your coat according to your clothes(dai_dai ruwa dai_dai tsaki) ku samar mata wani kawai "

"Wannan ba hujja bace Yusuf,kuma baka faɗa mana har yanzun ainahin dalilin ba"cewar Abdulmalik,

Ajiyar zuciyar ya sauke,yana mikewa tsaye" Kun ga ku tashi"

Duk kallon shi suke yi cikin rashin fahimta,

"Ku tashi mana"

Mikewa tsaye suka yi suna jira su ji me zai ce,

"Wannan ya zamo karo na karshe da zaku ƙara takowa gidan mu da sunan yi min maganar wata mace,bana ra'ayin ta,bana ra'ayin ƙanwar ku,bana sonta a takaice,ina fatan kun fahimta,dan haka ku zo ku fita" Ya fada yana nu a masu hanya,

Cikin tsananin jin zafin wulaƙancin da ya masu Abdulmajid ya shako wuyan rigar shi "kai har kayi kyau da arzikin da zaka ce baka son kanwar mu,in banda rigima da rashin sanin ciyon kai irin na Salma me zata yi da jaki mara hankali wanda bai san abun arziki ba irin ka,ko an faɗa maka muma muna son ka ne,ko kuma muna son ƙanwar mu ta aure mutum irin ka,daga yau idan ka ƙara ganin mu a ƙofar gidan ku duk abinda kaka dama ka mana,Stupid"ya faɗa yana ture shi gefe,
Bayan Abdulrahman ya samu nasaran cire hannun shi a wuyan Yusuf din wanda yake ta faman shafa makoshi da tari dan ba karamin shaka yayi mai ba,dama ya sani ko lokacin da yake zuwa gidan su duk cikin su babu wanda ya kai Abdulmajid zuciya,

Ko kallon su bai yi ba ya juya fuuu ya fita a gidan,dama wannan karon da mota suka zo dan haka buɗe gidan baya yayi ya shiga ya zauna yana hadiyar zuciya,dan babu abinda yafi bashi haushi irin yanda ya fito a gaban fuskar su yace baya son Salma,wannan abun ya ƙona mashi rai,
Ko suka iso suka shiga mota ba wanda yace ma ɗan uwan shi komai har suka isa gida,
Ya rigasu sauka a motar dan haka gani suka yi kai tsaye ya shige cikin gida,
Da sauri,suma bin shi suka yi,sai dai kafin su isa garya shige dakin Salma ya turo ƙofa,
Dole sai komawa falo suka yi suka zauna suna zaman jiran fitowar shi,

A zaune ya same ta tana danne_danne a waya,
Tsayawa yayi a kanta yana huci,
Dago kai tayi tana kallon shi,sai dai bata ce mashi komai ba,

"We need to talk"

"What happen"

"Ba zaki aure wannan yaron ba"

"Wa kenan?

" Wanda kike so"

Yusuf "

"Koma waye ba zaki aure shi ba,yanzun kam ina bayan su da Baba"

"Yaya" Ta kira sunan shi tana mamakin me ya faru daya hassalashi haka,

"Ido na fa ya kalla yace min baya son kanwata,wani irin cin fuska ne yafi haka,idan har kina ganin girman mu da darajan mu a matsayin mu na yannin ki yi ki fitar harkar yaron nan,in aure kike so akwai mazajen da suka fi shi komai wallahi zamu tsaya miki har sai kin aure shi,na maki aikawari"

Kallon shi take ido cikin ido"me zai hana kamin wannan alƙawarin wurin ganin na aure wanda nake so?Yaya ba wai ina son Yusuf bane dan in canja ra'ayi a kanshi a ko wani lokaci,A'a kawai ina son shi ne domin na aure shi,kayi haƙuri kome zaka ce ba zan canja ra'ayi ba"

"Hakan na nufin kin zaɓe ki bijire mana akan shi?kin zaɓe shi kenan a kan mu?
Ya faɗa yana kallon ta,

Lumshe ido tayi ta buɗe tana kokarin yin magana ya katse ta" Tunda haka kike zaɓar ma rayuwar ki shikenan,mu dai ba zamu maki mugun fata ba saboda ke kanwarmu ne,amma ki sani ko me ya biyo baya a tsakanin ki da shi karki nufo mu"yana gama faɗan haka ya juya ya bar ɗakin,

Tabe baki tayi tana faɗin "what ever"

*Ban sani ba ashe hakan da nayi tamkar na caka ma ciki na wuƙa ne* .

🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*60*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Tun daga wannan lokacin kowa na gidan ya fitar harkarta,babu mai shiga lamarin ta,kuma hakan ba wai ya dameta bane,abinda zai ba mutum mamaki shine duk wannan haukar da take yi bata taɓa tunkarar Yusuf din da maganar soyayya ba,
Tun abun baya damunta tana ganin kamar na dan lokaci ne har abun ya fara damunta,domin tunda take a rayuwar ta bata yini daya ba batare da tayi magana da yannin taba,gashi yanzun idan har suna cin abinci ta fito to kowa tashi yake ya bar mata wuri,haka kuma idan har suna zaune suna hira ta shigo to duk nan take zasu haɗe fuska babu mai ƙara magana kuma har sai ta gaji da zama ta tashi,ko kuma su sudinga tashi dai daya,

Wannan abun da suke mata ba karmin ciyo yake mata ba,dan haka a kwana na uku sai taki fitowa karin safe,har suka kammala bata fitowa,Lokaci-lokaci suna kallon ƙofar ɗakin ta,sai dai ba wanda yace komai har suka kammala suka tashi,

Da lokaci girkin rana yayi Mama ta fito ta shiga kicin,kallon kulolin abincin tayi,kiran mai masu wanke-wanke tayi ta nuna mata kayan"me yasa ba'a wanke waɗannan kayan ba,tun na karin safe bayan kin San ban son ajiye kayan wanke-wanke?

Dukar da kai matar tayi cikin girmamawa"Ummu Salma ce bata fito taci abinci safe ba,shi yasa na bar shi ko zata fito "

"Ta zo ta ci? Ta kuma tambaya,

Girgiza kai tayi" A'a bata fito ba"

Ɗan shiru tayi kafin ta kuma kallon ta"amma kin je kin mata magana kuwa?

"Eh naje na mata magana amma sai cewa tayi na fita ba zata ci ba"

Tabe baki tayi"cikin ta,idan yunwa ya dame ta ai ta fito"har ta juya sai kuma da sauri ta kara juyowa "amma dai lafiyar ta glau ko da kika shiga?

" Eh lafiyar ta kalau domin tana zaune ne a falo tana danna waya"

"Ki dafa shinkafa fari da wake da miya,amma a miyar kar a saka Nama,a dafa kwai sai a ɗaura a sama"

"To Hajiya an gama" Matar ta faɗa cikin girmamawa,
Chapter 60 · 0% Book details