← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 96

Sashe 45

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙarfe takwas da rabi ta masu ne a filin jirgi,dan haka lokacin nayi jirgin su ya tashi,
Cikin lokaci ƙanƙani suka sauka a garin Legas inda Abbu da Dady ne suka tare su,
Daki daya aka sauke ta ita da Nadiya a babban Hotel din da suka sauka,sai kuma su kowa daki dai daya.

🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*45*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Misalin ƙarfe Hudu na yamma,
Zaune suke a wani matsakaicin falo,mai ɗauke da jerin kujeru kamar na Dinner table mai zagaye da kujeru shida,
Su biyar ne zaune a kan kujerun,daga dukkan alamu akwai wanda suke jira,
Hira suke yi jifa_jifa a tsakanin su,
Jin an buɗe ƙofar an shigo ne yasa gaba ɗaya suka maida hankali kan kofar,ganin wanda ya shigo ne yasa gabaɗaya suka mike tsaye,
Daya daga cikin sune ya karasa inda yake cikin dariya suka rungume juna,
"Barka dai Abokina"

"Shine Dazu ka nuna kamar baka sanni ba"

"Kayi haƙuri kasan irin yanayin da muke ciki a yanzun,dole komai sai munyi da taka-tsantsan,"

"Hakane kuma"

Jawo mashi kujera yayi ya zauna,

"Naji yau kwana uku kenan da kuka iso"

"Eh haka ne,kasan dole mu riga kowa isowa"

Daya daga cikin sune yace"Shugaba har yanzun fa yaron yaki yayi magana "

Murmushi mutumin yayi wanda ba zan iya shaida fuskar shi ba saboda ƙarancin haske na ɗakin,"ba zai taɓa magana ba"kallon wanda ke gefen shi yayi"Chip baka da abin faɗa ne?

Gyara zama yayi"ni kuwa nake da abin faɗa,domin na sadaukar da yarinya ta domin ƙaruwar mu,kuma ni har yanzun ban ji bayanin da nake son ji"

Daya daga cikin su ne ya kuma cewa"amma dai ai ba aikin banza kayi ba,domin ba karamin kuɗi ka karɓa ba akanta,kaga kenan zamu iya cewa tsiyan yarka muka yi da makudan kuɗi kuma ka saka hannu ka karɓi abin ka "

"Ku me yasa baku sai da naku ya'yan ba,ka sani duk da kuɗi na karɓa ba karamin Alfarma na ma kungiya ba,Shugaba matsayin da aka min alƙawari?

"Ina nan ina aiki akai Ade Bayo,ka kwantar da hankalin ka in dai matsayin Minista ne zaka yi shi,kai dai kawai ka mai da hankali akan batun shiga kotunnan da za'ayi jibi"

"Shi kenan Shugaba"

Kara tambaya yayi yana juyowa kan wanda Dazu ya kira da abokin shi,ji nake murya shi tamkar na tabajin jin shi a wani wuri,"ya ake ciki batun lauyoyi?

"Har yanzun dai ba'a samu wanda zai tsaya masu ba,domin mun toshe duk wannan hanyar,wannan karon abunda muka yi shekaru muna shiryawa shi muke kokarin muga mun kammala a wannan karon,sai dai wannan yaron yana son ya nuna mana taurin kai"

Dan dariya yayi"baka tsoron Mahaifiyar ka da matar ka su gane?

Shima dariya yayi"ba zasu taba ganewa ba,dama ita ai dan haka tun farkon aka aure ta "

Duk shekewa da dariya suka yi,
Sannan daya ya kuma cewa"jibi ne shiga koto,chep hukuncin kisa gaba ɗaya zaka yanke mai"

"Idan ya yanke mai hukuncin kisa ba tare da faɗa mana komai ba to ya zamu yi kenen"

"Karku damu Zinariya dab take da karasa aikin ta ba tare data sani ba"

"Ya zamu yi da ita?

" Zuwa gobe zamu kara fahimtar da ita karfin mu,dan haka ku kwantar da hankalin ku cigaba da gudanar da komai kamar yanda muka tsara,"

Duk mikewa suka yi cikin girmamawa"to Shugaba"

"Sai mun haɗu a kotu"ya faɗa yana barin dakin suna rake mai baya.

____________daki ne mai matukar duhu wanda mutum ko tafin hannun shi baya iya gani,ta gefe ɗaya kuma baka jin komai sai karan saukar duka,ta ko ina kake ji,
An dau lokaci mai dan tsayi kafin kuma naga an bubbude windojin dakin gabaɗaya lokaci ɗaya haske kuma ya baiyana a ɗakin,

A tsaye nake rakube a jikin bango amma tsabar firgita bansan sanda ya yanke jiki na faɗi ba,ganin abinda ke tsaye a gaba na,

A tsaye yake a tsakiyar ɗakin yayinda hannayen shi ke daure duka a baya a tsakale a wani ƙarfe,
Gabaɗaya jikin shi a farfashe yake wani wuri ya tara jini har yayi baƙi,duk fatan jikin shi a fatfashe yake babu kyan gani kasancewar shi farin mutum,fuskar shi gefe ɗaya ya kumbura haka gefen fuskar shi,ya rame fiye da tunani a kwana uku kawai,ya fita kamannin shi,idan aka faɗa maka wannan Suraj ne wlh kana iya musawa,

Dago idanun shi yayi wadanda suka canja kala,daga asalin kalan da suke ya daura a kansu,

"Ka faɗa mana komai muna iya sake ka kaci gaba da rayuwar ka"

Murmushi yayi wanda ba shida daɗin kallo sannan ya tofar da miyau gefe mai tattare da jini"har abada "

Ɗayan ne ya sauke numfashi"ko dama baka faɗa ba dab muke da samun abunda ka daɗe kana ɓoyewa "

"Ba za ku taɓa samu ba"

"Oh haka kake gani?to shikenan kaci gaba da wahalar da kanka,yanzun haka cikin kawa biyu komai zai kammala"

Dariya dai ya kuma yi"ita din Mage ce,bata isa ta shiga dajin da damisa kaɗai yake iya shiga yayi shawagi acikin ta ba,ku dai na daura yardar ku da imanin ku a kan haka,domin babu abinda zata iya yi"

"Haka kake gani ko,zamu baka mamaki"

"Ni ma kuma zan baku mamaki"

Kallon juna saka yi cikin mamaki to me yake nufi shi da yake kulle "me kake shiryawa?

" Abinda kuka zo tambaya kenan?

Dafashi wanda na ji dazun sun kira da Shugaba yayi"mu je kawai,kai kuma zamu ga iya inda taurin kan naka zai kai ka"ya faɗa yana jan hannun shi suka bar wurin,tare da kullo ƙofa.

Sai da suka shiga mota sannan ya kalleshi cikin damuwa"me wannan yaron ke nufi?

"Kaga karka damu,so kawai yake ya saka mana kokonto a ziciyarmu"

"Kasan yaron hatsabibin kanshi ne,shi yasa na ɗan fara damuwa"

"Tada mota muje babu abinda ya isa yayi"

Taka mota yayi kuwa suka bar wurin.

_______________suna fitowa daga dakin wurin cin abinci suka nufa na cikin Hotel ɗin,anan suka ci abinci suna dan taba hira,
Ganin shigowar Pa da Dady ne yasa da sauri ta tashi ta karasa inda suke,

Tana dan kiran sunan Dady,
Tsayawa sukayi ta karaso "Dady yaushe zamu tafi ganin Suraj din?

Ɗan jim yayi kafin yace" Kin ga wallahi har yanzun akan abunda muje aiki kenan yata,babban matsalar ma shine rashin loya,shi yasa har yanzun bamu samu damar ganin shi ba"

"To yanzun Dady babu wani abinda za'a iya yi?

" Ina fa,sai dai mujira mugani zuwa jibi,"

Pa ne ya miko mata wani ATM"Kim ga karɓi wannan ki rike a hannun ki,anjima kaɗan ku shirya a kwai wani yarona a nan garin zai zo ya kaiku ku ga gari sai ku dan shi iska ke da Nadiya,karki wani saka damuwa a ranki "

Amsa tayi tana murmushi,duk da ba wannan bane a gabanta amma ko ba komai ta ji daɗin yanda ya nuna mata kulawa "mun gade Pa"

Komawa tayi ta zauna inda suke da Nadiya tana nuna mata katin.

Ranar tunda mutumin ya fita dasu basu suka dawo gida ba sai ƙarfe goma na dare,shima ita ta matsa su dawo saboda ta gaji,
Suna dawowa wanka tayi kawai ta kwanta dan tun a can suka ci abinci,
Nadiya ce ma ta dauki kayan shaye-shayen ta fara,

Har baccinta ya fara nisa dan lokacin ƙarfe sha biyu na dare ta ji wayar ta na ƙara,
Ba tare data duba waye ba ta dauka ta saka a kunne ba tare data ce komai ba,

Ji tayi ance "Biba kina jina?

" Ummm "ta faɗa cikin yanayin barci,

" Duk abinda kike yi yanzun nan ki baro shi ki taho Abuja,domin kuwa yanzun haka rayuwar Ummita na gagarumin hatsari,tana cikin gidan ki a ɗaure,ba lallai bane takai har zuwa lokacin da zaki iso,amma abu ɗaya shine ko gawarta ki samu nasarar gani,domin idan har suka san kin san inda take kafin ki iso sun dauketa a wurin,karki maimaita maganar a fili domin ana iya jinki"

Wani zabura tafi har tana fadowa daga saman gadon,"hello! Hello "amma ina tuni an kashe layin,
Jikinta har rawa yake yi wurin ƙara kiran number amma wayar ma ce mata yake wai the number is not exist,
Gabaɗaya babu abinda ke mata Ringin akai irin rayuwar ta na cikin haratsari,mutuwa,da kuma kalmar gawa,
Dafe kirjinta tayi,tana ambatar sunan a fatar bakinta Ummita,

Duk irin tambayar da Nadiya ke mata ganin yanda hankalin ta ke tashi kin bata amsa tayi,tunanin mafita kawai yake yi awanni lokacin,ta san cewa idan har tace sai da safe to lallai lokaci zai kure mata kamar yanda yace,
Dan haka ta riga ta tsayar da zuciyarta kome zai faru ko nawa zata kashe yau sai ta isa garin Abuja,
Cikin sauri ta cire kayan dake jikinta na barci ta saka doguwar riga na jallabiya ta dauki karamin jakka,
Kallon Nadiya tayi da tayi zurum tana kallon ta"idan an kira ki akan ina nake,ki ce masu an kirani Babban Yayana yayi hatsari ya mutu,na tafi"

"Da gasken hatsari yayi"

Kokarin fita take yi"eh"ta bata amsa tana fita tare da jawo mata ƙofa,

Ta san garin Lagos sosai dan ba bakonta bane,
Dan haka tana fita mashin ta tara ba tare tayi ciniki dashi ba ta faɗa mashi sunan garejin da zai kaita,dan ta san a can ne kadai zata ita samun motar da zai kaita duk in da zata je,

Cikin lokaci kankani suka isa saboda irin gudun data saka yayi,saboda dare ne akwai sauƙin abin hawa,
Dubu biyu zata bashi amma dubu biyar ta bashi tayi wucewar ta,

Ofishin Shugaban garejin taje ta mai magana akan ta son direban da zai kaita Abuja cikin ƙanƙanin lokacin,

Dubu talatin suka ce,amma ga mamakin su sai cewa tayi in dai zai yi sauri ta bashi dubu Sittin,
Cikin lokaci kankani aka haɗa ta da lafiyayyen mota da ma kuma wanda zai kaita bayan ta masu transfer,
Chapter 45 · 0% Book details