← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 96

Sashe 91

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*wannan shafin na sadaukar dashi ga yan group din Yar tsanar zinari,da Moonlight writers,sai group din Fakiri,wadanda na kira da wadanda ban samu na kira ba,ina matukar Alfahari da ku*

*Love you all* 😘

🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*90*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

*Sadaukarwa ga*

Mummys Girl
Maman Amira(Kaduna)
Maman masoyi
Hassana Muhammad
Ummeeh
Maman Ummi
Khadija Barau
~Chawa
Madame Anass
Nana Aisha
Maman Abdul,

Na sadaukar da wannan shafin gare ku,Allah ya Albarkaci rayuwarku dana Ahalinku.

Ko da ta koma falo har ma'aikatan gidan sun kusa kammala gyaran falon,dan haka kai tsaye dakin da Ammi ta sauka ta shiga,

Tana ganin ta kuwa ta mika mata hannu,amsa tayi ta zauna kusa da ita,
"Ya jikin naki?

Dan dukar da kai tayi" Naji sauki sosai Ammi"

"Alhamsulillah"

Dan shiru ne ya ratsa dakin na sakon ni,kafin tace"ki yi hakuri haka Allah ya kadar ta ba zaku haɗu ba "nan ta shiga yi mata nasiha mai matukar sanyaya jiki,tana kara tsoratata akan tsoron Allah da bauta masa,cire damuwa da maida komai ba komai ba,muhimmancin hakuri," Ina fata zaki yi aiki da abinda na faɗa maki?

Share guntun hawayen ta tayi tana jin yanda zuciyarta ke sanyi tana kara samun natsuwa"na gode sosai Ammi insha Allah zan yi iya ƙoƙari na"

"Allah ya maki Albarka,ya baki zuri'a na gari"

"Amin"cikin sanyin murya tace" Ammi ina Abbu,kin koma Kano ne,yasu Kaka?

Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi,"ayanda naji Kaka tana kwance a Asibiti,amma jikin da sauƙi yanzun,Ashe tun randa ake shari'ar Nurudeen ya kwasa ya tura ma mahaifiyarshi,shine ita muka ta je ta nuna ma Kaka,wacce nan take ta yanke jiki,ita ma Goggon yara sai da aka saka mata ruwa saboda hawan jinjin ta ya tashi,jin Yayan ta ne ya kashe mijinta"

Dan zabura tayi "ya mutu ne?

Dafa kafadar ta tayi" Bayan sun kamashi da shekara uku shine ciyo ya kama shi wanda yayi sanadin rayuwar sa"

Duk da bata sanshi ba,taso ace ko da sau daya ne ta gan shi,

"Karki damu,nasan me kike tunani,Goggon yara macece mai sauƙin kai,sai dai tana da faɗa,baka sanin sauƙin ta sai ka zauna tare da ita,yanzun haka ta san komai game dake,sannan ashirye take data karɓe ki a mayin ya,a cewarta ke baki aikata mata komai ba,kuma ba laifin ki bane da kika zo duniya a haka,itama tayi kuka sosai tace kuma in nima mata gafarar ki,duk abinda tayi maki ki yafe mata"

Girgiza kai tayi"ni dama ban rike ta ba Ammi,kuma bata min komai ba,na gode da karbata da tayi,ina mata jaje da fatan Alkhairi "

"Hakan da kika yi shine dai-dai Salma,domin Allah yana son masu hakuri,
Shi kuma Abbu yanzun haka yana gidan yari,domin washegarin dawowar ki suka turo shi nan tare da kwararrun hujjoji,yanzun haka an yanke mashi hukuncin rama gidan yari har karshen rayuwar shi tare da aiki mai tsanani,Salma gabaɗaya ya bata rayukan ahalin nan,idan kin je gidan yanda kika san babu mutane saboda rashin kwanciyar hankali da farin ciki"

Katseta tayi"Ammi kin je ne?

"Naje na duba Kaka,na tabbatar mata da ta kwantar da hankalin ta ni ban rike ta ba a rai na,kawai wanda yayi laifi ne ake hukuntawa,domin abinda yayi ba irin wanda za'a iya yafe mashi bane,ya aure ni bayan raba ni da mijina da yayi,yasan komai sannan ya tsaya yana cuta ta,yana da mata amma bai taba fada min ba,abubuwa marasa dadi Salma,ina matukar son mijina amma haka sukayi amma da kishi na suka raba mu,suka kuma kashe min su,ta yaya zan iya yafe ma mutum irin wannan,tsayin shekarun dana zauna dashi na zauna ne cikin kunci,rashin tabbas da dana sani tun farko,to amma ya zan yi,dole in jira har zuwa lokaci,lokacin daya dace"busar da iska tayi"na gode ma Allah da komai ya zo karshe,dazu da muka yi waya da Goggon yara tace zuwa gobe za'a sallami Kaka,mu kuma zuwa gobe idan anyi sadakar uku zan koma London saboda Mama"

Ji tayi jikinta yayi sanyi idanun ta sun taru da hawaye "Ammi amma dai zaki dawo ko?

Riko hannun ta tayi" Acan zan zauna saboda Ummi,ita ma tana buƙata ta,sai dai tunda kuna nan zan dunga zuwa lokaci-lokaci in duba ku,sannan ga waya zamu dinga yi kullun karki damu"ta faɗa tana rungume ta.

Ranar bata ƙara saka shi a ido ba har ta kwanta kwanta bacci,
Cikin magagin bacci ne ta ji wayarta na kara,sai dai saboda gajiya da kuma rashin son yin magana a waya da daddare yasa kawai ta kashe wayar ba tare data duba mai kira ba.

Washegari ne da karfe goma na safe aka gudanar da Addu'ar sadakar uku na Baba wanda aka haɗa da na bakwai din Mama,

Bayan kammala Addu'ar sai da suka kammala sallamar baki sannan ya kira ta awaya dan yana son zai wuce ne,ganin ba'a ɗauka bane ya kira layin Ammi,bugu biyu ta dauka da sallamah,

Amsawa yayi yana faɗin "Ammi dan Allah in akwai wani kusa dake ki kice a faɗa ma Salma ta kira ni a waya"

"Babu kowa kusa dani,sai dai in ni zanje na faɗa mata"

Dan murmushi yayi"wane ni na aiki Abin alfahari na "
Itama murmushi tayi"na maka uzuri,yauwa ƴar albarka kaga gata ma ta shigo"
Yana jin sanda ta mika mata wayar tana faɗa mata ga mijin ki zai yi magana dake,

Amsar wayar tayi tana barin dakin,sannan ta saka a kunni,
"Hello"

"Ki same ni a dakin Abdurrahman"

Kallon wayar tayi ganin ga katse,karamin tsaki taja tana komawa ta kai ma Ammi wayar ta,

🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*91*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Kamar yanda ya faɗa a dakin Ya Abdul-rahman ta same shi,sanye yake da ƙananan kaya a jikin shi,ta lura ya ɗan yi rama,hannun shi na rike da waya kamar ko wani lokaci,
Zama tayi kusa da shi "barka da safiya"

"Kin tashi lafiya"

"Lafiya qlau"

Ajiye wayar yayi yana fuskantar ta"yau zamu wuce "

"Umm haka naji Ammi ta ce"

"Yaushe zaki dawo"

Dan shiru tayi tana dauke idanun ta a kanshi,"na riga na faɗa maka bazan koma ba,dan Allah ka sauwake min"

Ba tare da ya kuma ce mata komai ba ya tashi ya fita,

Da kallo ta bi shi,ita ba taga wani dalili da zai saka yaki rabuwa da ita ba,tunda ba wai sun shaku bane,koma dai ne zai yi sai dai yayi amma fa ba zata taba komawa rayuwar shi ba,
Itama tashi tayi ta fita,

Ranar ma sai a bakin Aunty Hulaira taji cewar ya wuce,
Dan ita Ammi sai da akayi sallah Azahar sannan ta wuce,saboda zata kwana a Abuja gobe tabi jirgi zuwa London.

Kwana biyu da yin sadaka baƙi na nisa dana kusa duk suka gidajen su,gida ya rage daga ita sai Aunty Hulaira sai kuma mazan,
Kaka ce tace bata yarda Aunty Hulaira ta barta ta zauna a gidan ita kaɗai ba sai dai su dawo Bosso,dan in tana can ita kadai hankalin ta ba zai taɓa kwanciya ba,
Suma su Abdulmalik sun yi na'am da hakan,
Ita kuma sam ba ta so haka ba,tafi buƙatar zama ita ja dai akan zama da Kaka,dan ita Allah ya mata surutu ne,to amma ya ta iya dole ta tattara suka kwasa zuwa Bosso,

Yau tsayin kwana biyar kenan da komawarta gidan kaka,wanda yake dai-dai da sati ɗaya rabon da suyi waya dashi,ranar sadakar uku,

Jin yanda Kaka ke kwalla kiran sunan ta ne yasa dole ta tashi ta fito tana turo baki,
A bakin kofa ta tsaya ba tare da ta iso inda suke zaune saman tabarma ba"gani"

"Ai na ganki,wai ke meke damun ki ne,ace ayi mutum baya sakewa da mutane kullun shi kenan ƙunshe a ɗaki kamar Daudauwa,maza zo ki zauna ki sha iska,irin haka ba shi ke sakawa kafa mutum ya nukushe ba?

Dariya Aunty Hulaira ta saka" Haba Mama sai kace wata tumatur ko Kankana"

"Yo me marabin su da ita"

"Kin ga Salma,zo ki zauna kisha iska qyale Mama"

Takowa tayi ta zauna saman tabarmar "ni wallahi na gaji da zama haka"

"Au duniya ta zo karshe,wato dai faɗa mana kike kin gaji damu gidan mijin ki zaki koma"

Zaro ido tayi"ni da Kaka ba haka nace ba,Aunty Hulaira ni fa kishi ga tsakani ni da Kaka,dan na lura tunda nazo gidan nan ba ta da aiki sai ja na da faɗa "

Hannu ta saka ta rufe baki,dan wannan fadan nasu yafi karfin ta,

"Uwata an kai maki karata banji duka ba"

"Umm,ina zuwa bari naje nasha ruwa"ta fada tana barin wurin,dan wannan faɗar na Kaka da Salma in sun fara sai su saka ka rasa abin faɗa,

Ganin ta wuce ne yasa ita ma tashi ta bar ta zaune duk da tana jin irin kiran da take mata,

Tana shiga daki taji wayarta na ƙara,ko kafin ta karasa ta dauka wayar ya katse wani kiran ya ƙara shigowa,dauka tayi na nazarin number,saboda number na kasar waje ne,
Tasan kila Ammi ce,dan haka ta dauka da Sallamah,

Jin shiru ne yasa ta kuma maimaita sallamar,tana kara tattara natsuwarta,domin haka kawai taji jikinta na bata ba Ammi bace,sunan shi da zuciyarta ta kama ne yasa tace"idan har kasan ba kada ƙwarin gwiwa magana me na kira?

Daga cikin wayar tana jin yanda ya sauke ajiyar zuciya,kafin ya amsa mata sallamar,
Chapter 91 · 0% Book details