← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 96

Sashe 31

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tunda ta fita daga dakina bansan me ya faruba,sai kira daga Kaka,daga nan ne komai ya canja," Nan ya shiga bashi labarin duk abinda ya faru har zuwan shi nan.

"Amma Suraj a ganin ka waye ya dauki wannan hoton sannan har ya kai ma Kaka,kenan hakan na nufin bibiyar ku ake kuma wannan shiryayyen lamari ne?

" Tun daga farko shiryayye ne,sannan sanin waye mai daukar hoton bashi bane mai muhimmanci,daga shi mai daukar har wanda ya kai ma Kaka dukkan su yan aike ne,matsalar anan shine suna na da ya bata a gidan,ya cire duk wata yardar dake tsakanina da mutanen da nake kallo a matsayin nawa,ya saka mummunar fahimta a tsakanin mu,abinda ke min zafi Ammi! Idan da Ace Pa yana raye,ko kuma Grandma tana nan da hakan ba zai faruba,da ba akai wannan matakin ba,nima da ina da nawa ahalin,
Wani lokaci Farhan mutane suna da mantuwa,Amma babu komai lokaci ne zai tunatar dasu komai "

Dafa kafadarsa yayi"juriya shine ya kamace ka,ina fata ba zaka taɓa nuna gazawarka a idanun magauta ba?

Dan murmushi yayi"cikin juriya nake tsayin shekaru goma sha ɗaya,idan har zan iya z
Durewa na tsayin wannan lokacin me zai hana ni juriya har yanzun,na dai san duk abunda yake ma ba zai taba samu ba,"

"Hakan na nufin kasan waye kenan? To me yasa baza kaishi kasa ba lokaci ɗaya"

Wannan karon mamaki ne ya kama ni ganin irin murmushin daya saki,duk tsauri irin na mayunwacin Zaki,idan har zai yi farautar habin harin shi koda yana gabanshi dole ne sai ya fara dukar da kai kafin yakai cafka,"

"Kana nufin..

Katse shi yayi" Lokaci bai yi ba"

"To yanzun ya zaka yi da wannan auren?

Kallon Agogon dakin yayi wanda ya nuna ƙarfe biyar da rabi na yamma" Bayan sallah Magrib za'a daura,sai dai bansan yanda suka tsara abin ba,sai dai koma me suka shirya I will accept it,domin hakan ma wani mataki ne na nasara ta wanda su basu san haka ba amma ni na sani"

Cikin mamakin abokin nasa yace"me kake nufi da matakin nasarar ka,bayan kace baka son auren kuma ba sonta kake ba,ama ajiye batun so gefe,kasan ita din yar aikin makiyanka ce,ta yaya samunta zai zamar maka matakin nasara"

Dan karamin dariya yayi duk da bai fito ba haƙoran shi ne kawai suka bai yana "ka sa ido ka gani,domin yanzun ne Asalin wasan zai fara"

Shiru kawai yayi domin gabaɗaya ya rasa gane ina ya dosa,Sallamar Bala ne ya katse su,
Shigowa yayi da tire dauke da bowl na abinci da chokali sai goran ruwa da kofi,
Amsa Farhan yayi ya mai godiya sannan ya fita,

"Yaushe ruwan zai ƙare?ya tambaya.

" Zai kai ƙarfe takwas"

"Idan lokacin sallah yayi ka cire min idan mun dawo ɗaurin aure sai ka maida min"

Kallon mamaki yake mai"zaka je ne?

Bai bashi amsa ba sai ma cin abinci daya fara.

_________

Kaka ce ta shigo dakin rike da wani leda mai dan girma a hannun ta,ajiyewa tayi a gefen ta tana zama kusa da ita,
Ganin bata da niyar yi mata magana ne yasa tace"Kinji haushin hukuncin da muka yanke ne?

Dago idanun ta da suka kumbura tayi tare da girgiza kai"kawai dai auren ne bana so,dama ace korata kika yi da hakan yafi min"

Rike mata hannu tayi"na yarda da wannan hukuncin ne badan in cutar dake ba,na tabbatar da cewa wata rana sai kin yi alfahari da wannan hukun namu"

Shiru kawai tayi bata ce mata komai ba,
Mika mata ledar tayi"ki saka wannan kayan domin ƴan awoyi suka rage a ɗaura auren,sannan mahaifiyar ki ta iso munyi magana da A'i ba baza su jimaba zasu iso"

"Na gode"
"Allah ya Albarkaci rayuwar ki"

Dole ne idan har ina son kaiwa karshe na kwantar da hankali nabi komai a hankali, sai dai kuma hankalin nawa yaki kwanciya saboda rashin sanin wani hali Ummita ke ciki,ƙara share hawayen daya sauko mata tayi,wanda hakan ya jawo idanun suka kumbura sosai,
Da yar ta iya lallashin zuciyar ta sannan ta sauki lafiyayyen Les din da yaji aiki ta saka,a cikin kayan harda ƴan kunni da Sarkar wuya na zinari,sakawa tayi da takalmim,kayan ruwan Orange color ne da fari,shi yasa kayan ya bala'in yi mata yau,duk da yanda fuskantar babu ko da digon kwalliya amma ta fito yanda kasan ba ita ba,dan dinkin riga da zani ne Bubu irin na yarbawa wanda ake daura zanin a ciki,ɗaurin ɗan kwalin kuma data daura sai ta sauko da suman kanta ta baya,wanda har ya kusa gadon bayanta,
Wannan ne karo na farko da tayi shiga mai kyau mai kuma ma'ana tunda ta zo gida,
Zura ƙafarta tayi a takalmin wanda yake flat shoe ne fari da kuma madaidaicin mayafi fari,shi kuma a gefen kafardar ta na hagu ta rataya shi,sai turaren data feshe kanta dashi tun daga sama har katsa,

Jin yanda aka buɗe ƙofar aka shigo sannan aka maida aka kulle ne yasa ta dago kanta tana kallon ta,
Zama tayi kusa da ita cikin sauri ta ce "ina fatan ki zama mai wayau mai kuma rike sirrikan kanki,karki taɓa yarda da kowa koma waye,ki yi taka tsantsan sosai domin ta ko'ina za'a saka ido a kanku" Jin an murda kofar ana ƙoƙarin shigowa ne yasa da sauri ta canja magana"haba ke kuwa Biba wani irin kuka ne haka kika yi,kinga yanda idanun ki suka kunbura kuwa"

Wasu mata ne su biyu suka shigo ɗakin,mikewa tayi tana jawo wata acikin su"yauwa Maman Biba kinga yanda idanun ta suka koma kuwa "

Kallon matar da aka kira da Maman Biba tayi"Da kaganta kaga zubin yan duniya,sai dai ba tada wayewa sosai,tana isowa rungume Biba tayi"Haka kuma lamari ya kansance Habibatu,me yasa zaki aikata irin haka"ta faɗa tana saka kukan munafirci,

Ganin Goggo ta zo tayi tsaye ne yasa dole ta kakaro hawaye"Mama ki yi haƙuri ki yafe min,duk laifi na ne"

Ita dayar da suka taho tare nan ta shiga sharan hawaye harda fyace majina,

Ganin Goggo ta wuce ne yasa ta saki matar da sauri dan warin zufa take yi irin kuma mai ƙarnin nan,
Dan matsawa baya tayi kaɗan tana bata fuska,

"Ki ce min Biba ko Habiba,amma banda Habibatu"

Washe baki tayi"in dai baki so ai an gama,ni inama ni aka ba wannan aikin in auri dan gidan masu kuɗi ai da kullun da namar kaza zan dinga brush "ta karasa faɗa suna saka dariya.

Kaka ce ta saka Nafisa ta kawo masu lafiyayyen Abinci da ta saka aka shirya masu,nan suka shiga ci hannu baka hannu ƙwarya,

Jin Ana kiran sallah Magrib ne yasa gabanta faduwa,har aka idar da sallah tana zaune,ba ta iya tashi ta dauro Alwallah tayi sallah ba,ko a sujada kuka take yi,domin wannan lamarin so yake yafi karfin zuciyar ta,a tsorace take,ido rufe take niman wanda zata iya faɗa ma halin da take ciki,
Ta idar tana saman darduma sai ga A'i ta kuma shigowa tana rangaɗa guɗa tare da faɗin "An ɗaura,An ɗaura"

Maida kanta tayi ta haɗa da gwiwar ta tana karanto duk wani Addu'a da yazo bakin ta,jin irin yanda gabanta ke tsananin faɗuwa,abubuwan da suka faru da ita a baya suna ƙoƙarin dawo mata sabo a cikin ƙwaƙwalwar ta.

__________Acan waje kuwa wurin ɗaurin aure..

🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*33*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

A masallaci tun ganin lokacin kiran sallah ya kusa Abbu ya kira shi a waya,
Yana ɗauka yace"sai na tuna maka da batun ɗaurin aure "

Cikin sanyi murya yace"zan zo yanzun nan Abbu"

Ba tare da yace komai ba kuma ya kashe wayar,duk da yanda yaji muryar shi wani iri abin ya ɗan taɓa zuciyar shi,dan daga dukkan alamu kamar bai da lafiya,yana son Suraj sosai,domin yaro ne mai matukar biyayya,tunda suke dashi bai taɓa saɓa ma umurnin shi ba,ko yaci masa musu akan wani,kawai dai yau he is very disappointed akan abinda ya aikata,kuma dole ne sai ya nuna mai kuskuren shi a kan haka.

Kallon Farhan yayi dake ƙoƙarin cire mashi Drip,"ka fitar min da kayan da zan saka"

"An gama ran Ango ya daɗe"

Ba tare da yace mai komai ba ya tashi ya shiga banɗaki dan yayi wanka,yana gamawa ya dauro Alwallah gabaɗaya sannan ya fito,

Kujeran madubi ya ja ya zauna dan baya jin karfin jikin shi,mai ya shafa kawai sai turaren da ya feshe jikinsa dashi,
Kallon kayan dake ajiye saman gado yayi,ƙaramin tsaki yaja sannan ya buɗe durowa ta jawo wani farin Jallabi da farin hula ya saka,sai wani dan karamin Carbi daya riƙe a hannun shi,
Tsarki ya tabbata ga Allah,domin yanda kasan wani Balarabe haka ya fito,
Tunda yake saukowa daga sama ya buɗe baki yana kallon shi cikin mamaki,ganin yana ƙoƙarin wucewa ba tare da yace mai komai bane yasa da sauri ya tashi ya bi bayan shi "me haka zan gani Suraj,ina kayan dana fito maka dashi?

"Basu min ba" Ya bashi amsa a takaice,

Nuna shi yayi"ta ya za'a yi kaje ɗaurin auren ka da wannan kayan sai kace mai shirin zuwa bada sallah"

Buɗe mota tayi ya zauna a gidan baya ya jawo kofa ya kulle,

"To waye zai ja motar ba dai ni ba,ina matsayin abokin ango"

Ba tare da yace mai komai ba ya buɗe motar ya fito,kai tsaye motar Farhan dake parke a gefe ya kuma buɗe gidan baya ya shige,

Dafe kai yayi yana kallon motar,shi dai duk yanda kayi dashi sai ya bullo maka ta wata hanyar,
Buɗe wurin zaman direba yayi ya zauna ya ja motar yana gunguni,
Chapter 31 · 0% Book details