← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 96

Sashe 46

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda suka kama hanya mutumin ke zuba wani uban gudu da ita yanda kasan zasu tashi sama,ta san gudun da suke yi ya wuce kima amma ita bashi bane a gaban ta,burinta daya kawai ta ganta a Abuja,
Cikin hukuncin Ubangiji sai gashi ƙarfe biyar na Asuba ta masu a cikin garin Abuja,ita take ta nuna mai hanya har ƙofar gidan ta,
Tana fita cikin tsananin sauri ta ɗauki makullin gidan inda suke ajiyewa ta buɗe ta buɗe,
Na falo ma haka sannan ta shiga,
Kunna wutar gidan tayi gaba ɗaya ko ina ya dauke da haske sannan ta shiga duba ɗaki ɗaki tana kiran sunan ta.
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*46*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Duk in da take tunanin zata ganta a cikin gidan ta duba bata ganta ba,
Cikin sanyin jiki ta dawo falo ta zube anan kasa tana fashewa da kuka,
Ummita tamkar kwarin gwiwar ta ce na cigaba da rayuwa a wannan lokacin,tana son Ummita domin sun yi rayuwa da ita na amana,tausayi,da daraja juna,
Bata da wani wanda take gani a matsalin dangi irin ta,itace Ahalinta,
Idanun ta ne ya sauka a kan labulen da isaka ke kadawa yana dagawa kaɗan kasancewar ta bar kofa a buɗe,
Kamar hannun mutum take gani,

Da gudu ta tashi ta ita wurin tana kiran sunan ta tare da yaye labulen,

Wani irin ihu ta yanka wanda tun daganan sai ganin duhu tayi ya mamaye mata idanu,daganan kuma bata ƙara sanin meke faruwa ba,

Bayan awa uku,a hankali ta fara buɗe idanun ta tana kallon silin din dakin,
Shiru tayi tana sauraren ƙaran Ac dake tashi,ƙoƙari take ta tuna abinda ke faruwa da ita,
Wani irin zabura tayi da karfi saura kaɗan ta fado sai ji tayi an riƙe ta"ki yi a hankali karki ji ciyo"

Juyowa tayi ta kalli Nos din dake riƙe da ita"ina ne nan,ina Ummita "

"Ki kwantar da hankalin ki nan kina Asibiti ne"

"Asibiti? Ta maimaita,

" Eh"
Da sauri ta sauka daga kan gadon tana cire Butterfly needle da aka saka mata Drip dashi ba tare data damu da zafin da wurin ke mata ba,
"Ina Ummita"

Rike mata hannu tayi mu je na kaiki,"

Har ofishin Doctor ta kaita sannan ta mai bayani,
Tashi yayi daga kan kujeran da take,yana nuna mata hanya"mu je "

Tana biye dashi ya juyo yace"ya kike da ita"

"Yar uwa tace"

Shiru yayi kamar ba zai ce komai ba sai kuma yace"iyayen ku fa,dama jira muke ki farka"

"Duka sun mutu ba mu da kowa sai mu kaɗai" Ta faɗa mashi dan bata son ya kuma mata wani tambayar,

Tura ƙofar dakin yayi ya shiga tana biye dashi sai dai dakatawa yayi kafin su karasa ciki,"naso ace naga wani babba naku,sai dai kin ce ba kuda kowa wanda hakan ke nufin ke zan ma bayanin komai "

"Ina Ummita?

Numfashi ya sauke" Ina mai baki haƙuri akan rashin da ki kayi,domin sakamakon gwaje-gwaje ya tabbatar mana da cewa yau tsayin kwana biyu kenan ma da bata raye,saboda rashin Oxygen,shi yasa ma har ta fara kunbura,

Sam ita bata ma fahimce me yake nufi ba"ina Ummita "ta ƙara maimaita mai,dan ji take kamar kalam shi na dazu ba da ita yake yi ba,

Lumshe ido yayi ya buɗe yana matsa mata a hanya" Tana ciki"

Bata ma jira ya ƙarasa faɗa ba ta shige cikin dakin da sauri,

Kallon gadon dake cikin dakin tayi wanda shi kadai ne a tsakar dakin,akwai kamar mutum kwance a sama sai dai an rufe shi da farin kyalle kamar da gawa,

Ta jima tsaye tana kallon gadon kafin a hankali ta fara takawa har ta isa ta wurin kan,
Hannu tasa ta yaye zanin da aka rufe fuskar dashi har katsa,
Tun daga suman kan take kallo har zuwa yatsar ƙafa,

Jin yanda jikinta ke rawa ne yasa ta tsugunna a gaban gawar tana jin yanda hawaye ke diga daga idanunta zuwa katsa,
Wani irin kuka ta fashe dashi mai ƙarfi tana riƙe hannu ta,"Ummita!"ta shiga kiran sunan tana kuka mai matukar girgiza zuciya,ba-zata taba manta maganar da sukayi da ita na karshe ba in da take cewa *ke ce farin cika na,kuma gata na,dan haka ki yi sauri ki kammala ina jiran ki*
Rungume hannun ta tayi a kirginta"Ummita ke kika ce zaki jira ni,me yasa zanzo yanzun na tarar da gawar ki,why?me yasa,shin baki san ni ma kece farin ciki na ba,me yasa zaki tafi ki barni"kuka take yi sosai tana jin wani irin duhu na mamaye zuciyar ta,wani irin zafi take ji gabaɗaya jikinta har katsan zuciyar ta,
Shi kenan Ummita ta mutu kenan ba zata sake tashi ba,ba zasu sake rayuwa wuri ɗaya ba,ba zata sake mata magana ba,yanzun da waye zata dinga zuwa aiki,
Kallon gawar tayi,"wani irin mutuwar azaba kika yi yar uwata "ta faɗa tana daura kanta saman kirjin ta,

Nos din ce ta zo ta daga ta tana rungume ta," Fatar jikinta bai da karfi saboda zafi,ki yi hakuri yanzun haka ƴan sanda na kan bincike akan ta"

"Dan Allah ki taimake ni ki ƙara dubata ko dai bata mutu ba,ina son na faɗa mata zan mai da ita gida wata rana,ina son tayi rayuwar farin ciki kamar kowa,me yasa zata tafi yanzun"ta ƙarasa faɗa cikin tsananin kuka tana dafe kanta" Nayi dana sani akan komai,me yasa lokacin da zan tafi da kika ce zaki je ban tafi dake ba,"komawa tayi wurin gawar ta shiga jijjigata "Ummita,dan Allah ki tashi,please don't live me,me yasa zasu ce kin mutu,I can take it,na rasa kowa nawa,a lokacin da nake farin cikin samun ki nake murnar zan rayu a matsayin me yar uwa me yasa zan rasaki ke ma,?
Share hawayen ta tayi" Kin ce na daina kuka,me yasa zaki tafi,ni yanzun na zama ni dai kenan,Ummita "
Ji tayi lokaci ɗaya numfashin ta yana ƙoƙarin daukewa kuma,
Ganin zata faɗi ne yasa Nos din dake gefe tana taya ta kuka tayi saurin riƙe ta,
Da taimakon likitan aka ƙara mai da ita kan gado,
Alluran barci mai ƙarfi sukai mata wanda dole zata jima tana yi dan tana buƙatar hutu,
Duk da haka kafin barcin yafi karfin ta sai kiran sunan Ummita take yi,
Gaskiya sun tausaya mata sosai,domin ta saka yarinyar a rai,

Ba ita ta ƙara tashi ba sai ƙarfe biyar na yamma,ta jima a kwance idanun ta biyu,wato abinda zasu mata kenan,ta masu aiki tsayin shekaru shine zasu biyo mata ta wannan hanyar,
Tabbas wannan karon sun kai makuran su,kamar yanda bata san waye su ba,haka basu san wacece Biba ba,amma yanzun sun taso da guguwar da ba zasu iya tarewa ba,sai ta baiyanar dasu a idon duniya ɓoyewar da suke yi sai ta baiyana,
Yanzun da ita zasu fara Yaƙin ba da Suraj ba,sai ta zame masu ɗan haƙƙin data rai na,
Mikewa zaune tayi sannan ta sauko daga saman gadon tana zura takalminta,
Tana buɗe ƙofar Nos din na ƙoƙarin shigowa "Miss ya jikin naki?

" Da sauƙi dan Allah ki ara min wayar ki"

"To ba damuwa"

Cirowa tayi ta mika mata wayar,komawa tayi cikin dakin ta zauna bakin gado,
Number data san yafi kiranta dashi ta tura masa sako kamar haka:*Naga saƙon ka na gode,ni kuma ku jira nawa zuwan*

Goge saƙon tayi tayi sannan ta saka wani number wanda Ringin uku aka ɗauka,
"Biba ce"

"Biba" Ya faɗa da mamaki kafin da sauri yace kuma"kina ina ne,tunda muka rabu a Legos ban ƙara ganin ki ba,na kira Ummita number ta baya shiga,Biba yaushe zamu haɗu,akwai aiki a katsa fa"

"Mu haɗu yanzun zan zo gust house ɗin ka"

"Wow to sai mun haɗu ina jiran ji,ko na zo na ɗauke ki ne?

" A'a gani nan zuwa"ta kashe wayar,

Mikewa tayi ta fito ta kai ma matar wayar ta"zan wuce amma ba zan dawo yanzun ba a saka gawar a Matuware "

"Ki tsaya to ki karasa karɓar treatment di ki"

Girgiza kai tayi"ina da abin yi"tana gama faɗa ta wuce,

Tana fita Adaidaita ta hau ta faɗa masa in da zai kai ta,
Suna isa me gadin ne tasa ya ba mutumin kuɗin shi,sannan ta shiga ciki,
Gidan ba baƙon ta bane dan haka kai tsaye cikin falon ta shige,
Da sauri ya taso ya rungume ta ya ɗaga ta sama yana juyi da ita yana dariya,

"Ka sauke ni Mansour"

Sauke ta yayi yana rungume da ita,kokarin sumbatar ta yayi ta kauda kai tana zame wa daga jikin shi,samun wuri tayi ta zauna a daya daga cikin kujerun falon,

Zama yayi kusa da ita "Beb meke faruwa naga kamar baki cikin farin ciki"

Dago fuskantar yayi cikin tashin hankali yace"me ya samu idon ki?kin yi kuka ne?me ya faru,waye ya taɓa ki?

Kuka ta fashe dashi tana faɗawa jikin shi,gabaɗaya ta gama tayar mai da hankali saboda irin kukan da take yi,"Ummita ta Mutu,they kill her"

Da sauri ya dago ta"me kike nufi da ta mutu?

Sake shi tayi tana kyara zama"wani aiki ne na karɓa mai matuƙar rikitarwa,"nan ta shiga bashi labari har na auren da tayi a cikin aiki da kuma abinda ke faruwa da shi da kuma ita,"yanzun haka ana su shirin gobe za'a shiga koto,idan har na bari suka samu nasara akan shi to kamar akai na suka samu,so suke su kashe mu bayan kammala komai,sun hana a samu lauyar da zai tsaya"

"Zan samar maku lauya Biba,sai dai nayi baƙin cikin wannan auren,amma dai in komai ya wuce kuka gama wannan rigimar zaki dawo mana ko?
Dan Allah ya gani yana bala'in son yarinyar,

" Bana son shi,dan haka zan rabu dashi"

"Bari na kira shi yazo ya same mu"

"A'a bana buƙatar wani Loya,zasu iya mai barazana kamar yanda suka saba,wannan karon kuma ina son na fito masu ne a zahirin koni wacece"

"Me kike nufi?
Chapter 46 · 0% Book details