← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 96

Sashe 62

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jinjina kai tayi"to yaya"
Daganan sallama ya mata ya fita.

Sai zuwa ƙarfe goma ta tashi,sai dai har yanzun basu shigo ba,amma ga kulolin abinci nan a jere an ajiye mata,
Kaɗan ta iya ci kafin ta fito daga ɗakin,
Kallon ƙofar Mama tayi dake a buɗe,kamar ta shiga kamar kar ta shiga,tayi kewar su,tana son ganin su,
A hankali take takawa har ta isa bakin ƙofar sannan ta ɗaga labule ta shiga,
Dakin ba kowa a ciki gashi a gyare,kofar banɗaki ta buɗe shima a bushe yake alamun ba'a yi amfani dashi ba,

To ina Mama ta je ne,ko dai tana falo ne ko kocin,

Fitowa tayi ta nufi kicin,sai dai bata ciki sai ma'aikata,
Kallon daya daga ciki tayi"Mama Ladidi ina Mama na?

"Wallahi tunda safe dana zo ban ganta ba,ni ma na duba dakin ta dan na gaishe ta sai dai bata ciki"

Ba tare data ce mata komai ba ta nufi dakin Baba,sai da tayi sallamah ya bata damar shigowa sannan ta shiga,
Zama tayi a gefe shi yana turo baki,
"Me ya faru" Ya tambaye ta,

"Baba ina Mama taje ne tunda safe haka?

" Tana gidan su"

"Gidan su ta maimaita"

"Ummm"

"Ko dai kaka ce ba tada lafiya"

"Kila" Ya bata amsa a takaice,

Mikewa tayi"bari na bita na duba jikin kaka "
Bai bata amsa ba sai ma cewa da yayi"ki dawo da wuri "

"To Baba" Daganan fita tayi ta koma daki ta shirya kafin ta saka direba ya kai ta gidan kakannin ta dake Bosso,
Gidan su da gidan sarki bai da nisa daka wuce Bosso clinic sai gidan,

A ƙofar gidan ta haɗu da Yaya Abdulmajid zai fito,
Kallon ta yayi yana tsayawa"Ya jikin naki?
Ya tambaya fuskar shi babu walwala,

"Na ji sauki" Ta faɗa tana raɓawa ta gefen shi ta wuce,dan haushin shi take ji,

Da sallamah ta shiga cikin gidan duk suna zaune a dakin Kaka,daga dukkan alamu hira suke yi,dan har da kanwar Mama Aunty Hulaira,

"A'a lale da zuwan babbar mace"

Turo baki tayi tana zuwa kai tsaye wurin Aunty Hulaira ta zauna a jikin ta"ina kwana Mama Hulaira "

Dariya tayi tana shafa kanta"lafiya qlau Ummu Salma,ya karatu?

"Yau naga iya shege,yanzun ke ko Uwar ki ta isa ta shigo nan ba tare data gaida ni ba balle ke Salamatu"cewar Kaka,

Gwalo tai mata tana makale kafaɗa" Ba dai zan gaishe ki ba tunda ba wurin ki na zo ba,ina Mama ta?

Cikin jin haushi tace"gata nan na makala a wuya "

Dariya Aunty Hulaira ke masu"ku dai duk in da kuka haɗu baku gajiya da faɗa "

Cikin shakwaba tace"Aunty Hulaira ina Mama?

"Ta je Unguwar Biri tun dazu gidan Aunty Hadiza,na san ba zata jima ba zata dawo tunda ta jima da zuwa"

Kallon kaka tayi"wai me yasa ake kiran unguwar da unguwar Biri,ko dai Birai ne a unguwar?

"Ki bari idan Uwarki ta dawo sai ki tambaye ta"

"Aunty Hulaira,kin ga kaka tana zagi na ko?

" Dan mai garinku ba sai ta rama maki ba"

"Da zaran Mama ta dawo wucewa zamu yi,dama so kike ki ba mutane wahala shi yasa kawai kika kwanta wai ba kida lafiya"

"Ta yaya zata koma babu inda zata je har sai mahaifinki mai taurin kai ya janye maganar auren ki"

Buɗe baki tayi cikin mamaki tace"ba dai yaji Mama tayi ba?

"Ai wannan yafi yaji tunda tun a asibiti ya dirka mata saki daya dan ta faɗi gaskiya"

Dafe kirji tayi"saki!shi Baban nawa ne ya saki Mama?

"Oh!to ai sai kiyi,jiya kin ganta a gida ne?

Girgiza kai tayi,

" To dama jira nake ki zo naji dalilin da saboda wani banzan soyayya naki zaki raba auren iyayen ki da aka gina shekara ishirin "

Jikinta ne yayi sanyi sosai,domin bata taba tsammanin lamarin ya kai har haka ba.
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*62*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Share hawayen dake bin idanun ta tayi"ban taba tsammanin lamarin zai kai haka ba tsakanin Baba da Mama,ni son tsakani da Allah na ke ma Yusuf kaka,ba wai soyayyar sha'awa bace ko ta wani abu,Allah ne ya Daura min,gashi ta sanadi na auren iyaye na yana ƙoƙarin rabuwa,idan har haka ya faru ba zan taɓa yafe ma kaina ba"

Ganin yanda take kuka ne yasa Aunty Hulaira ta jawota jikinta"ya isa haka ba laifin ki bane,haka Allah ya tsara kuma duk abinda Allah zai tsara mana zai same mu ba mu isa mu kauce masa ba,so wannan ma mu ɗauke shi a matsayin haka"ta faɗa tana share mata hawaye,

"Shi yasa na ga su yaya suna jin haushi na"

"Yo ba dole su ji haushin ki ba sun ga kina ƙoƙarin sakawa a saki Uwar su"

"Kaka dan Allah ki kyale yarinya ta huta kin ga ba lafiya ne da ita ba,"

Tabe baki tayi"ku dai kuka sani,
Wai ni kan Salamatu in tambaye ki?

Bata bata amsa ba sai ido data Daura mata wanda hakan ke nuna tana jinta,

"Shi wannan yaron da kika nace ma anya ba Asiri ya maki ba"

Aunty Hulaira ce tace "Asiri kuma Kaka?

" To ki duba ki ga,in ba aikin asiri ba ta yaya za'a yi ace yarinya ta bijirema kowa,bata jin shawaran kowa saboda shi,ki duba ki ga fa har auren uwarta take kokarin kashewa amma baki ji tace ta fasa ba,ko kin fasa?
Ta faɗa tana tambayar ta

Ita fa wannan tsohuwar mugun surunta ke sakawa bata son zuwa gidan,cikin jin haushi tace"ba Asiriba kome zaki ce ina son Yusuf kuma ba zan fasa ba,sai dai zan roki Baba Mama ta dawo"

"Wai shi din ma ɗan gidan uban waye ne?

Aunty Hulaira ce tace" A jiya dai Aunty Fatima ta ce min yaron aikin Baban ta ne,shi ya samar mai komai har ta gidan da suke ciki,to yanzun haka a jiya yace zai ɗibar mai kaso mai yawa a cikin dukiyar shi wanda zai dinga kula da ita Salmar"

Abin mamaki,sai gashi nan take kuwa tsohuwa ta shiga washe baki"ai to in haka ne kenen abun ma da sauƙi tunda ba cikin talauci da kunci zaku zauna ba,tunda mahaifin naki ya ji ya gani zai iya, to in banda ma abin Fatima me na tayar da hankali har haka,bari to zo ai kuwa yanzun zata tattara ta bar min gida"

Sallamah suka ji sannan lokaci ɗaya tana tambayar"wa zai bar gida?

"Ke mana,domin ni yanda kika min bayani ina daukar yaron matsiyaci ne ashe ubanta yace zai masu komai"

Ita ba ta san sai yaushe bane idanun Kaka zasu dawo dai-dai akan kuɗi,gabaɗaya rayuwar ta idan kana son faranta mata to ka dauko harkar Arziki,duk har da saboda wannan shegen son kudin nata ta jefa ta cikin wannan yanayin da take ciki,

Mai da kallon ta kan Salma tayi"bi yo ni"

Tashi tayi tabi bayan ta zuwa ɗakin kaka data shiga.

Tana zaune kan gado,nuna mata kusa da ita tayi alamun ta zauna a wurin,
Zama tayi tana kallon fuskar mahaifiyar nata wanda a ɗan tsakanin kwana biyun nan ta rame sosai,sai dai ita bata lura ba sai yanzun,

"Ummu Salma" Ta kira sunan ta,

Kanta a duke ta amsa da "na'am" Domin kunyar haɗa ido take da ita,saboda gashi saboda ita auren ta na ƙoƙarin mutuwa,

"Dado kanki ki kalle ni"

Girgiza kai tayi hawaye na kara sauko mata"Mama dan Allah ki yi hakuri,ban San abinda ya faru tsakanin da Baba kenen ba saboda ni"

"Koma me ya faru dani wannan ba damuwarki bane,tsanina dashi ne,ni tambaya nake son na maki wanda zai kasance tambaya ce ta ƙarshe tsakanina dake a kan Yusuf"

Dagowa tayi tana kallon mahaifiyar nata,

Jinjina mata kai tayi"Ummu Salma"ta kira sunan ta a natse

Sai dai bata iya amsawa ba saboda yanda zuciyarta ke bugawa dan bata San wani irin tambaya mahaifiyar nata zata mata ba,

"A yau kina da damar da zaki sauya Kaddaranki,ki sauya rayuwar ki gabaɗaya,idan har zaki jure ma zuciyar ki kibar zabin ranki,ki dauki dayan ɓangaren," Ta faɗa tana kallon ta,

Ganin har ƴan mintuna sun shuɗe ne yasa tace"kina ji a ranki kin zabi Yusuf kenan?

Nan ma shiru tayi,

"Ki faɗa min abinda ke ranki Salma ba zan maki dole ba,kuma na maki alkawarin duk hukuncin da kika yanke a wannan lokacin to na karɓa"

"Mama kiyi haƙuri har yanzun na kasa cire shi a raina"

Nan take wani hawaye mai matuƙar zafi ta sauko daga cikin idanun nata,yayin da ta ji zuciyarta ya mata nauyi Kamar an daura dutse,

Cikin sauri ta dafa hannun ta"Mama kuka kike yi dan na zaɓe Yusuf,Mama k.....

Yatsa ta saka mata a baki alamun tayi shiru,tana girgiza mata kai,"Salma sai yau na tabbatar da Allah baka taɓa mashi wayau ko dubara,na yarda da hakan tunda gashi tsayin shekaru muna ta kokarin keɓe ku daga irin wannan amma sai gashi sai da Allah ya jarabcemu ta hanyar da bamu yi tsammani ba,"

"To Mama me yasa kike kuka?

" Ba zaki taɓa gane me yasa nake kuka ba Salma sai nan da lokaci mai karasowa,domin kuwa lokacin yazo,karasowa kawai ya rage,lokacin zaki fahimci abinda nake maki gudu,lokacin zaki fahimci illar hanyar da kika zaɓa,yayin da babu hanyar juyawa baya,kuma babu Alkalamin da zai goge haka daga cikin rayuwar ki da ƙwaƙwalwar ki,abinda nake ma gudu kenan Salma,ranar da zaki kasa jurewa,ina matukar tsoron amsar da zan baki,shi yasa tun kina da sauran dama nake roƙon ki daki janye batun wannan yaron"

Ganin irin yanda mahaifiyar nata ke hawaye wanda ke nuna asalin tsoron ta ne yasa ita ma nata hawayen kara yin yawa"Mama ki yi haƙuri "

Shafa kanta tayi"Allah ya maki Albarka,ya baki haƙuri da juriya a duk halin da kika tsinci kanki"

"Amin Mama"

"Shi kenan tashi mu koma gida,dama nayi magana da Baban ku ko"

"Da gaske zaki koma me Mama?
Chapter 62 · 0% Book details