← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 96

Sashe 64

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi tayi"eh"kallon Baba tayi daya zuba mata ido,domin shi ya fahimci inda zancen ta ya dosa,sai dai su yaran ba zasu taɓa ganewaba,sai dai ko kaɗan bai ga laifin ta ba,ƙoƙari take a matsayinta na uwa taga ta inganta rayuwar ahalinta,"ko ba haka ba Baban su? Ta faɗa tana tsare shi da ido,

Jinjina kai yayi"no need,kawai kome kuka haifa Allah ya albarkaci rayuwar su "

Da Amin suka amsa,
Daganan tashi sukayi domin su yi wanka su shirya su rakata filin jirgi,

Zuwa ƙarfe bakwai da rabi suka baro gida gabaɗayan su,har da Mama da Baba,dasu Aunty Hulaira yan rakiya,

A can suka sami Yusuf da ƴan uwan shi suna jiran isowar su,
Gaisawa suka yi cikin mutunci sannan Yaya Abdulrahman ya amsa Tikitin su ya shiga gudanar masu da komai har zuwa lokacin da jirgin su zai tashi,
A lokacin da zata wuce bata wani damu ba,sai lokacin data kalli idon yannin ta sannan ta fara hawaye,domin tasan zata yi kewar su,sai dai in sun kawo mata ziyara,amma ita da dawowa sai nan da shekara biyu idan ta kammala karatun ta,

Komawa baya tayi ta rungume su daya bayan daya tana,a kan Abdulmajid ta tsaya tana rike da hannun shi"Yaya kayi haƙuri "

Shima share hawayen shi yayi "we are all with you"

Rungume shi ta kuma yi"na gode "

Shafa kanta yayi"Allah ya albarkaci rayuwar auren ki"

Da Amin ta amsa ta kara rungume Aunty Hulaira da Mama har ma da Baba,kafin su shiga inda Asalin zasu shiga jirgi yayinda Yusuf ke rike da hannun ta,*Ban sani ba sallamar da nayi dasu a wannan lokacin na haɗa ne gabaɗaya har da farin cikina na bar masu a nan,yayin da na fara taka matakalar jirgi haɗe da wani mataki na littafin ƙaddaran rayuwata,tun daga wannan lokacin da ba zan taɓa mantawa da shi ba komai ya fara juyawa,a ranar Lahadi ƙarfe takwas daidai,*

Kujerana na kusa da nashi ne,dan haka hannun mu na cikin na juna domin shi wannan ne karo na farko daya taɓa shiga jirgi,ni kuma ba zan ma iya tuna adadin sau nawa na shiga ba,
A haka har jirgin mu ya sauka a birnin London.

Address din da Baba ya bani dashi nayi amfani na tare Taxi na faɗa masa ya kaimu,duk wannan abin yana riƙe da hannu na,saboda shi baisan gari ba,kuma zuwan shi na farko kenan wannan ƙasar,
Har bakin tangamemen Apartment din mu aka sauke mu,wuri ne ba kaɗan ba,dan gidan zai tasarma hawa goma sha biyar,dan lambar dakin mu shine na dari da goma sha uku,muna hawa na tara ne,
Dan Linta mukayi amfani zuwa sama,in da ƙofofi ne a jere wasu na kallon wasu,sai dai idan ka shiga cikin dakin zaka ɗauka wani duniya ne ka shiga,domin babu abinda babu,katon Falo da dakuna biyu wurin wanki da shanya,barandar shan iska,da kuma wurin girki,har da dan wani wuri da akayi domin hutawa,gaskiya dakin ya haɗu,komai akwai shi a cikin, ɗaki daya ta dauka sannan ta nuna mai nashi,"ga ɗakin nan,kayi wanka ka huta zan mana ordan abinci,zuwa gobe Monday zamu fara shiga School,domin mu karasa abinda za mu yi sai mu fara ɗaukar karatu"

"To Allah ya kai mu" Ya faɗa,
Juyawa tayi ta koma nata dakin data zaba,sai da tayi ordan abinci kafin ta shiga wanka,dan ɗakin akwai na'uran saka ɗumi adaki,

Bayan wasu mintuna ne karrawar kofar ya shiga ƙara,ita ta fito ta buɗe ta amsa abincin ta bashi kuɗin shi sannan kulle kofar,a saman Dinner Table, ta koma daki domin ta shirya,
Riga da ƙaramin wando ta saka iya cinya,a lokacin idan ka kalle ta ba zaka so ko da kyafta ido kayi ba,saboda yanda rayi matukar kyau yanda kasan wata Bebi,

Kwankwasa mashi kofa tayi haɗe da yin sallamah ta shiga ba tare da ta jira ya amsa ba,

A lokacin ya kammalawa saka gajeren wondo irin na maza wanda yake saukowa zuwa guiwa na shan iska,yana rike da Sinlet fari yana ƙoƙarin sakawa ta shigo,

Da sauri ya manna rigar a kirjin shi ya rufewa tare da kauda kai,"ki je ina saka kaya idan na gama zan fito"

Turo baki tayi tana ƙara matsowa inda yake"ai kai Mijina ne yanzun babu abinda zaka ɓoye min"
Amsar karamar rigar dake hannun shi tayi tana warwarewa,taimaka mashi tayi ya saka rigunan duka,"ni ba zan ɓoye maka komai na jiki na ba domin yanzun da daba daya bane"

Bai bata amsa ba sai ma cewa da yayi "mu je"
Tare suka fito suna zaune,ita ta saka masu a plate daya ta kuma hana shi saka hannu sai ma diba da take yi tana bashi a baki,tun yana ɗan kau kauda kai har dai ya zage yana karba,sannan shima yana saka mata a baki tana ci,
Sai dai abunda ya fara bata mamaki koda yake ta mai izini saboda ƙila lokacin shine na farko daya fara keɓancewa da mace,domin ko alamar burgewa ko jan hankali bata gani tare da shiba akan wannan shigar nata,ko a idanun shi bata gani ba.

🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*64*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Suna kammala cin abincin ta kwashe kayan ta kai kicin wanda zata saka ashara kuma ta saka,
Ko da ta fito baya falon dan haka dakin shi ta leka,yana kwance kan gado daga dukkan alamu waya yake yi,dan haka ita ma fitowa tayi ta koma nata dakin ta kira wayar Mama domin shaida masu sun sauka lafiya,

Bayan ta gama kiraye-kirayen wayarta ne ta kwanta daga nan barci ne mai matukar daɗi ya ɗauke ta,wanda ba ita ta tashi ba sai daf da magriba,cikin sauri ta ƙara yin wanka da ruwan zafi dan jikinta ya sake sannan ta jero sallolin da ake binta,a haka ta zauna har lokacin sallah Isha'i yati sannan tayi,
Jin karar TV tun Dazu ne yasa ta fito falon,
Yana zaune yana kallon Boll a wani tashar,

Zama tayi kusa dashi tana daura kanta a samar kafadarshi,"partner yunwa nake ji"

Zame kanta yayi daga jikin shi yana dan matsawa kaɗan "ki yi mana ordan abinci dan nima yunwa nake ji"

Ƙara matso shi tayi tana riƙe hannun shi,"shine baka tayar da ni ba?

"Naga kin ji daɗin barci ne shi yasa,"

"To bari na baka number su koda wani lokaci idan kana bukatar abinci sai ka nime su"

Hannun shi ya cire cikin nata yana mika mata wayar shi dake gefen shi,

Amsa tayi ta saka mai sannan tayi seving,
Lura da tayi kamar baya son tana taɓa shi ne yasa ta kyale shi,koda suka kammala cin abinci daki ya koma,duk yanda taso tajashi da hira,

Ita ma bata jima tana kallon ba ta kashe kayan kallon ta koma daki,

Ta dauka idan ta shiga daki zai biyo ta su kwana tare kamar yanda taga sauran sababbin ma'aurata ke yi,sai dai shi ko kofar ɗakinta bata jin ya taɓa,gashi kuma maganin da taje ta dinga banka ma cikinta wanda ta siya a ɓoye ya fara mata aiki,dan da kyar ma ta iya barci,

Washegari da safe tana idar da sallah dakin shi ta shiga,yana kwance saman gado yayi dai daya yana sharar baccin shi hankali kwance,ji take kamar ta fada kamshi ta rungume shi,
Ajiyar zuciya kawai take saukewa,
Jan bargon tayi tana kiran sunan shi a hankali,
Da kyar ta samu ya tashi"tashi ka shirya kasan yau zamu shiga makaranta"

Shi sam yama manta da wanin karatu,dan nashi bangaren kasuwanci zai karanta,amma duk makaranta daya ne sai dai kowa da Department din shi,

Tashi zaune yayi yana yamutse fuska "ki je ki shirya ganinan fitowa"

Fita tayi dakin tana jinjina nauyin barci irin nashi,
Wanka tayi ta shirya cikin doguwar riga na jallabiya baki sai karamin mayafi data naɗe kanta da shi,

Fitowa tayi riƙe da karamin jakka a hannun ta,dayan hannun kuma makullaine,
Cira wasu daga cikin shi tayi ta mika mashi"ga makullin dakin ka,wannan kuma na gida ne sai ka riƙe ɗaya,nima na riƙe data saura kuma zamu ajiye saboda tsaro,ko mantuwa "

"Ok" Kawai ya fada,

"Idan mun fita sai mu tsaya ka ci abinci"

Dagowa yayi ya kalle ta"ke fa "

Wannan ne karo na farko tun zuwan su jiya daya mata tambayar dake nuna alamun an damu da mutum,
Dan haka murmushi tayi"ni sai zuwa ƙarfe goma zan karya "

"Ok to nima ba wai ina karya da wuri bane,ki bari idan zaki cin abinci sai ki kira ni"

Jinjina kai tayi,

Koda suka isa katafaren makarantar tare da mutumin ba Baba ya hada su shi ya taimaka masu sukayi komai,sannan aka tura dan sako ya kai kowannensu Department din shi har kuma ajinsu,sannan aka nuna masu dakin karatu na ɗaliban,
Babu abun da yafi mata daɗi sai ganin cewar ƴan ajinsu basu da yawa basu wuce su goma sha ɗaya ba,

Kujeran ta a kusa da na wata yarinya me suna Suba yake,ita ƴar ƙasar Rasha ne,balarabiya,
Mika mata hannu tayi suka gaisa take fada mata sunan ta,da kuma garin su,ganin yanda tayi shiga kamar wata yar uwar su balarabiya,ta kuma yi mamakin jin cewar ita ƴar Nijeriya ce,

Koda suka kammala darasi ƙarfe sha biyu na rana,kallon agogon hannun ta tayi"lokaci ya tafi,ni zan wuce sai mun haɗu gobe"

Daga mata hannu tayi,"karki manta gobe ƙarfe biyu na rana muke da darasi"

"Insha Allah" Ta faɗa tana cigaba da tafiya tare da ciro wayarta a cikin jakka,number shi ta shiga kira,sai dai sai da yayi kara kusan sau uku sannan aka ɗauka,"kana ina ne"shine tambayar data fara mashi,

Dan shiru yayi kafin taku ta ji yace"ina wani wuri "

"Acikin makaranta? Ta kuma tambayar shi,

" A'a na bi wani aboki na ne zan karba abu a wurin shi,amma ba jimawa zan yi ba yanzun zan dawo,kin koma gida ne?

"A'a yanzun muka gama lecture,dama na kira ne na tambayeka ko kun kammala sannan kaci abinci?
Chapter 64 · 0% Book details