← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 96

Sashe 33

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon Abbu Sufyan yayi"dazu banji daɗin kalamanka ba sam Sufyan,kai a matsayin uba kake a wajen shi,shi kuma yana maka kallon mahaifi,amma ka bari bacin rai ya rinjaye ka,ka faɗa maganar da sam bata dace da bakin ka ba,ka kushe shi da zuri'ar shi,ka aibantashi a gaban ɗan ka,yayin dashi kuma ka yabe shi da kasancewar shi jinin ka,karka manta ko kai bakafi karfin Allah ya jarabceka ka,ina so kuma ka tuna waye Mahaifin Suraj wacece Kakar shi da kuka kira da jikin yahudawa,kai kanka kasan waye ita,idan da Ace tana kusa,wane kai Sufyan,sai dai kawai kaci Albarkacin Auren mahaifiyar jikanta,Kaka kema kin sani,amma ɗan ƙaramin kuskure ba tare da dogon bincike ba idanun ku sun rufe,a gaskiya kun ban kunya,ba kaɗan ba,ban taba tsammanin a gaban mahaifiyar yaron zaku iya fadar haka ba tamkar ku kuke taimaka mata kamar ta dogara daku,bayan a ko wani lokaci idan taga dama tana iya rabuwa da nan ɗin,idan kana taƙama aƙwai yarinya a tsakanin ku,to kamin ta same ta sai da ta sami wanin ta,"mikewa yayi"ni na tafi sai da safen ku,yauwa kaka ki saka ta fito tabi mijinta dare na yi dan na lura kamar ma ba lafiya gare shi ba"yana fama fadar haka ya fita ya bar su nan zaune cikin tarin nazari,

Kaka ce tayi kiran sunan Nafisa dake dakin kakan tana kyara mata wurin kwanciya,
Cikin sauri ta zo ta tsugunna "ki ce ma Habiba ta fito mijinta na jiranta"

"To kaka"

Ajiyar zuciya Abbu Sufyan sa sauke tare da mikewa "Mama sai da safe"

"Allah ya tashemu lafiya"
Tare da Dady suka fita kowa yayi nashi shiyan,

Kai tsaye dakin ta ya nufa bakin shi dauke da sallamah,
Har yanzun a zaune take saman darduma sai dai ba komai take yi ba,daga dukkan alamu nazari wani abu take yi,
Zama yayi kusa da ita ya yaro hannun ta,
Murmushi ta sakar mai kamar babu komai a zuciyar ta,"barka da shigowa"

Bai iya bata amsa ba sai dukar da kai da yayi yana tunanin ta ina zai fara"kiyi haƙuri"

"Akan me?ta tambaye shi,

Jin abinda tace ne yasa ya dago kai" Dan Allah kiyi haƙuri akan abunda ya faru dazu,bai kamata na faɗa abinda na faɗa ba"

Girgiza mai kai ta yi,fuskarta a sake tana Daura hannun ta saman nashi,cikin tabbatarwa wanda ya hakan ke sashi shiga shakku tace"A'a,ya ya wuce,ba kayi kuma ko wani kuskure ba,ka tunatar dashi ne matsayin shi a gareka,ba kayi kuskure ba is normal thing"

Baki ya buɗe yana ƙoƙarin yin magana ta sanya mashi yatsanta a baki alamun yayi shiru "karka damu da sai ka ban haƙuri,wallahi har cikin raina ban rike ba,kuma na gode maka a bisa haƙuri da kayi dashi na tsayin shekaru har izuwa yau daka aurar dashi,na kuma gode da kuka bashi damar matsawa ko zai kara fahimtar rayuwa,domin yanzun shi ba yaro ba ne,na gode"

Rungume ta yayi a jikin shi,sai yanzun yake ainahin danasani akan kalamansa na dazu,yaso ta nuna bacin ranta ta yanda zai bata haƙuri a wuce wurin,amma sai gashi ita ke bashi haƙuri ta bar shi da nauyin zuciya,
"Ki bani dama ta ƙarshe"

"Har abada ni matar ce idan ba ka yanke Alakar dake tsakanin mu ba,da kanka,ka kwantar da hankali ka har yanzun kallon uba yake maka"

Babu yanda ya iya da ita amma She make him fill guilty,in sha Allah da kanshi zai gyara abinda yake ƙoƙarin batawa.

*_________* tana zaune kan gado bayan ta gama sauraren duk bayanin da suka tattauna a kai sa ga Nafisa ta shigo,
Kallo take kare mata daga sama har kasa "Masha Allah Biba,yanda kikasan kamar ba ke ba,gaskiya ke yar sa'a ce gashi daga zuwa aikin kin yi ram da daya daga cikin yaran gida,dan Allah ni ma ki ban sirrin" Ta faɗa fuskarta dauke da farin ciki,

"Wai ba cewa akayi ki kira ni ba?

" Umm haka ne,kin ga taso Angon ki na waje yana jiran ki,"

Ganin ta taso tana kokarin fita ne yasa ta jawota baya"ke tsaya ba haka ake yi ba"Mayafinta dake a kafadarta ta dauka ta yafa mata a kai ta sauko dashi far ya rufe rabin fuska,"wai ina Maman ki da yar uwarta?

"Sun wuce"

Dan budo ido yayi"ta yaya zasu wuce basu tsaya sun kai ki ba?

"Mu a garin mu Ango shi kaɗai yake tafiya da Amaryarsa ba tare da kowa ba,"

"Wow gaskiya abun yayi kyau,to amma ni dai muje sai na rakaki har bakin mota"

"Aukuwa na gode muje"
Tare suka fito,
Wurin Kaka ta tsugunna tana mata sallamah"karki damu mun riga munyi magana da ƴan uwan ki kuma sun faɗa mana Al'adun ku,shi yasa na ce ki fito ki bin angon ki,sannan batun kayan sawarki na ba Teloli su uku domin ayi saurin haɗawa zuwa gobe,in sha Allah za'a kawo maki kayan Lefen ki"

Nan ma godiya tayi mata,

"Tashi kije yana jira Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a ta gari"

Wannan karon kam bata ce Amin ba dan bata buƙatar ko fatan haɗa zuri'a da shi,dan ba wannan bane a gabanta,

"Kaka bari na raka ta wurin mota sai na nawo"

"To hakan ma yayi"

Tashi suka yi suka fita tana riƙe da hannun ta "Biba dan Allah duk dadin da kika samu karki manta da ni,tunda yanzun kin zama matar manya"

"Dan Allah karki dame ni da wannan maganar sai kace wacce zasu tabbata tare"

"Me kike nufi,tare zaku tabbata tunda mijinki ne"

Girgiza kai tayi"ba zaki gane ba"
Ganin sun isa bakin motar ne yasa dole tayi shiru,

Kallon Farhan Nafisa tayi dake jingine a jikin mota"dan Allah wani mota zan saka Amarya?

Da hannu ya mata nuni da wani karuwar Jeep baka dake ɗan nisa dashi kaɗan,

Nufar wurin suka yi yana bin wacce fuskarta ke lulluɓe da kallon nazari,dan daga dukkan alamu doguwa ce sai dai ba can ba,sannan siririya nan ma ba sosai ba,tana da shef sosai duk da a lulluɓe take,to ko ya fuskarta zai kasance tunda yaji abokin nashi yace tana shan sigret,ko ma dai ya take nan ba da jimawa ba zasu haɗu.

Buɗe mata gidan baya tayi"ki shiga nan ki zauna,sai da safe ni na tafi"

"Na gode Nafisa ba zan kuma manta dake ba"

Cikin jin daɗi ta ce"ai kuwa na gode"sannan ta ja mata kofa ta rufe,

Kyara zamanta da kyau tayi tana sauke ajiyar zuciya tare da cire mafayin dake lulluɓe a kanta,

Wani irin fitinannan kamshi ta ji yana tashi a cikin motar wanda ta saka ta lumshe ido ta buɗe,
Jin kamar numfashi a gefen ta ne yasa da sauri ta kalli wurin,

Yana zaune idanun shi a lumshe yana jan carbi,yayin da yayi tamkar bai san da mutum a gefen sa ba,

Kallon shigar dake jikin shi tayi tana tabe baki,wato da Jallabiya yazo ɗaurin auren shi,ɗan ƙaramin tsaki taja wanda bata yi tunanin ya fito ba,

Kamar mai ciyon baki taji yace"wannan ya zama karo na karshe"

Da ba dan ta kwantar da hankalin ta ba da bata fahimce me yake nufi ba,magana a gutsurew ba tare da an kai ƙarshen shiba,

Farhan ne ya buɗe mazaunin direba ya shiga yana daɗin "Amarya baki laifi ko da kin mari ango"

"Ba dai irin wannan ba"

Jin abinda tace ne yasa ya dan saki dariya kaɗan,"ke dai faɗi gaskiya Amarya,kin ga dai ga angon naki nan zaune a gefe yana ji,ko zaki gwada?

"To kai ɗin me zai hana ka kwada na baka baki"

Wannan karon ko dariya yayi sosai"lallai za'a je dake,to ya kuma muka ji da jama'a?

"Alhamdulillah"

"Allah ya baku zaman haƙuri,"
"Amin"

Tayar da motar yayi suna barin harabar gidan"suna na Farhar "

"Ni kuma Biba"

"Nice to meet you" Tunanin bata jin Turanci yasa da sauri yace yi haƙuri "ina nufin naji daɗin haɗuwa da ke"

"Karka damu ni ma haka"

Daganan basu kuma cewa komai ba har suka iso Sultan road,
Kamar dazu babban Get din da kanshi ya buɗe suka shiga sannan ya kulle kanshi,

Daga kai tayi tana kallon gidan wanda gabaɗaya kusan rabin shi da Glass aka yi shi,ba karya ya haɗu,ta faɗi hakan a zuciyar ta,domin ita a wurin ta ba wannan ne karo na farko data fara ganin ire-iren wadannan gidajen ba,tunda tayi zaman kasan waje kuma ta zagaya kasashe da dama,

Ganin uban gaiyar ya fita ba tare da ya ce mata komai ba yayi gaba yana taku dai daya kamar bai son yi,
Taji an buɗe mata ƙofar "fito Amarya"cewar Farhar,

Fitowa tayi" Na gode "
"Mu tafi ciki kafin ya kulle ƙofar"

Ita dai bata ce masa komai ba tabi bayan shi har cikin madaidaicin falon,
Ganin ya doshi sama ne yasa tabi shi har cikin dakin,

A zaune suka same shi a bakin gado dafe da kai,

Jin takun tafiyar na mutane biyu ne yasa ba tare daya dago ba yace,
"Me ta shigo min a daki "

"Me kake nufi?

" Kace ta fitar min a daki"ya fada wannan karon yana daura idanun shi akanta,

Wanda hakan yayi dai-dai da zame kyalen kanta data kuma yi gabadaya ta rike a hannu,
Hakan yayi sanadiyyar baiyanar kyakkyawar fuskarta da yake ƙyalli ba tare da ko digon ƙwalliya ba,haka kuma lallausar sumanta dake kwance a gadon bayanta saboda kalar ɗaurin dankwalin da tayi,
Ita ma tana daura nata idanun a cikin nashi......
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*35*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Chapter 33 · 0% Book details