← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 96

Sashe 9

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*11*

*Na mai da Littafina mai suna a sama na kuɗi,tare da JAURO,idan kina son daya 300,dari uku,guda biyu kuma da Yar Tsanar Zinari tare da Jauro,dari biyar 500,ko wani daya dari uku*
*Hauwa Umar,Zenith Bank, 2284905309*
*ko katin waya na MTN,tare da turo shedar biya ta 08141644865*

Dariya matar ta fashe dashi,"ai kuwa haka dai zaki daure kiyi tunda kin riga kin zo,batun girki kuma karki damu yanzun akwai takardar girke-girke kala-kala sai a siya maki ki tafi dashi,dan ina ganin haka zai fi sauƙi "

Shiru kawai tayi mata dan gaba ɗaya ranta a jagule yake,ta yaya kamar ita ace wai aikatau zata,kuma a gidan Malamai,ya za'a tasake,dan gaskiya ba zata iya daina shaye-shaye ba,ga wasu kaya kamar na gidan yari wasu manya-manya dasu,
Ajiyar zuciya ta sauke tana karewa dakin kallo,

Matar ce wacce ko sunan ta bata sani ba tace"bari na saka a kawo maki abinci"

Girgiza kai tayi"ki bar shi kawai dan yanzun zan tafi ne"

Kallo mamaki take mata"zuwa ina?

"Hotel zan kama,ranar da zan tafi aiki zan zo,tunda kin ce sai nan da kwana biyu"

Taɓa baki tayi,dama tasan hakan na iya faruwa tun daga ganin farko data mata, "babu matsala,bari na kira mai Adaidaita na ya kai ki"

"Ok "kawai ta ce mata,

Bata wani jima ba sai ga mai Adaidaita ya iso,ita matar ita ta faɗa mashi sunan Hotel ɗin da zai kai Biba,wanda yana kaita tun daga ganin tsarin ginin tace bai mata ba ya canja mata wani,
Aikuwa lafiyayyen Hotel ya kai ta,wanda anan ta sauka kuma taimashi biya mai ƙyau,ta bashi sakon akan ya faɗa ma matar in da ta sauka.

_______Tunda ya dawo daga Wa'azi Abuja kwana biyu kenan bai ƙara fita ba,sai Abbu da ya tafi Jos wa'azi.

Yau tunda ya dawo masallaci sallah Asuba ya zauna a shiyan Kaka inda anan suke karatun safe zuwa ƙarfe bakwai kafin su tashi sannan ayi shirin Boko,

Tunda ya shigo ko wacce ta kama kanta,daga wacce ke turo baki har masu gyangyadi duk natsuwa suka yi,
Samun daya daga cikin kushin din falon yayi ya zauna yana jan carbi,yana kallon yanda Malamin su ke biya wa ko wacce,da kuma yanda suke biyawa,
Sai da lokacin da suke tashi yayi kafin malamin ya masu addu'a,
Ɗaya bayan daya suke gaida shi suna fita,bai amsa ba sai dai ɗan gyada masu kai da yake yi,har suka gama fita,

Daya daga cikin jerin ƴan matan da suka fita su uku ne ta dafe kirji tare da sauke a jiyar zuciya,

Duk kallon ta suka yi"lafiya kuwa Zainab "

Lumshe ido tayi ta buɗe "ke dai bari Sis Bilki wallahi duk sanda naga Yaya Suraj sai naji gabana yana faɗuwa,ban san me yasa ba,amma wallahi bala'in kwarjini yake min"

"Lah Ashe bani kaɗai nake jjn haka ba,sai dai wani lokaci haushe yake bani saboda bai sake mana fuska,kullum fuskar shi a haɗe,in dai ba an nuna shi a TV bane yana wa'azi shi ne wani lokaci zaka ga yana murmushi,amma fa su mama cewa suka yi wai yana da fara'a,ni dai bana gani,kufa?ta faɗa tana kallon su.

" Hadiza kenan,to bari kiji,ko jiya naga yana ma Khalifa wasa yaron Anti Hajo,mune dai ya rai na,insha Allah sai ya haɗu da mata dai-dai dashi,wacce zata zaunar dashi tace yayi ta dariya shi kaɗai "cewar sis Bilki.

Gabaɗayan su dariya suja kwashe dashi kamar wasu sababbin mahaukata,dan maganar Bilki ba karamin dariya ya saka su ba,
" Ba Amin ba Bilki,ke a tunanin ki a kwai maccen da zata iya juya wannan,balle har ta kawo mashi hauka,haka ma baki ji abinda yace ma kaka bane a ranar daya dawo,wai shi har yanzun bai ga maccen data iya motsa zuciyar shi ko da kaɗan bane,kin ga ko akwai matsala,ni dai kam zan so naga Allah ya nuna min wannan yarinyar data motsa zuciyar shi,ta saka shi kuka ace,sai mu ga Young Ustadz yana rokon asoshi,"

Nan ma wata Uwar dariyar suka fashi dashi Zainab harda faduwa sabar dariya,
Daga bayan su suka ji ance "idan kun gama gulmar sai ku bani hanya in wuce"

Da sauri suka zabura tare da juyawa suna kallon ta suna matsa mata,

Ganin zata wuce ne yasa da sauri duk suka riƙo mata hannu "Aunty Maijidda baki dai ji me muka faɗi ba ko?

Kallon su tayi daya bayan daya yanda duk suka riƙe ta tare da Zuba mata ido suna jiran su ji me zata ce,
" Naji mana?

"Me kika ji?Hadiza ta tambaya.

" Komai da komai,ina nufin tun daga farko har in da kuka tsaya,yanzun ku sake ni bari naje na sanar dashi domin ya fara Addu'ar niman tsari a kanku"

Ƙara cakume ta suka yi suka shiga roƙon ta akan ta rufa masu asiri ba zasu sake ba,

"Ok,ok naji ku sake ni,amma duk sanda na karajin kun ma Suraj irin wannan addu'ar ni da kaina zan faɗa mashi"

"Insha Allah ba za mu sake ba"

"To ku sake ni mana na wuce"
Duk sake ta suka yi ta wuce tana girgiza kai,tana jinjina zancen yaran a zuciyar ta,domin gata nan zaune a gida har yanzun ta kasa aure tana zaman jiran shi amma shi ko kallon ta bayayi,kuma kowa a gidan ya sani,
Shi kuma yi yake kamar bai san da halittar ta ba acikin gidan,dan haka bata fatan ma a samu macen da har zata motsa masa zuciya,dan a wannan lokacin bata san wani irin hali zata shiga ba,ko kuma me zata iya aikatawaaikatawa ba.

Tashi yayi ya shiga cikin ɗakin kaka in da take zaune tana jan carbi,zama yayi kusa da ita ya na tankwashe kafa"barka da safiya tsohuwa"

Saida takai karshe sannan ta ajiye carbin "Surajo da fatan ka tashi lafiya?

" Alhamdulillah"

"Allah ya maka Albarka, ya nuna min auren ka"

"Amin tsohuwa"

Hararanshi tayi"sai kace yana da niyar yi"

Ɗan murmushi yayi "ina da niya mana Tsohuwa," Mikewa yayi Abbu yasa ni aikin duba masa wani littafi bari naje,"

"In ajiye maka abin kari"

"No A'a dan zan fita ne kuma ba zan dawo da wuri ba"

"Allah ya tsare,amma ka tabbar ka karya da wuri dai"

Murmushi kawai yayi ya fita.

Dakin shi ya buɗe ya shiga ajiye carbin hannun shi yayi a inda yake rataye sharbi,
Dakin da yake ajiye littatafai ne ya shiga sannan ya fara dudduba littafin,sai dai baya wurin,dirowoyin dakin ya fara jawowa yana dubawa nan ma baya ciki,
Tsayawa yayi yana tunanin to ina ya ajiye littafin,
Fitowa falo yayi ya jawo wani karamin durowar dake gefen kushin,
Tsayawa yayi yana kallon abunda ke ciki wanda shi yana manta dashi,
Hannu yasa ya dauko pos din harda wayar,

Samun kanshi yayi da zama kan hannun kushin din,haka kawai zuciyar shi ke raya mashi ya kunna wayar,
Dubawa yayi yaga wurin kunnawa sannan ya kunna,
Kafin ya kawo ne ya buɗe pos ɗin,wanda ATM card dinta ne da aka rubuta Habiba Abdulmajid,sai master card,da kuɗi a ciki yan dubu daya daya,wanda bai damu daya kirga ko nawa bane, wani karamin kwali ya gani ɗan madaidaici,ciro kwalin yayi wanda yana buɗewa sai ganin karan Sigari yayi a ciki,wato Taba,ya jima yana jujjuyawa tare da tunanin yanzun mace ce ke shan wannan abin,tunda dai gashi a jakkanta ya gani,kafin ya maida komai a cikin jakkan ya rufe,

Duba wayar yayi babu wani key da aka saka mata,wurin App ya fara dubawa wanda babu wani App a wurin sai irin wanda waya ke zuwa dashi,sai kuma WhatsApp da Facebook, ko TikTok babu a wayar,
Komawa baya yayi ya shiga wurin hotuna,

To ni dai bansan me yake gani a wurin ba ko kallo sai dai ji da nayi yana sauke numfashi akai-akai,sai kuma naga da sauri ya fita wurin yana kashe wayar gaba daya tare da mai su in da ya dauko,
Mikewa yayi ya buɗe firig tare da daukar goran ruwa mara sanyi sosai yashi,
Kafin ma ya ajiye goran hannun shine yaji wayar shi na vibration a Aljihu,
Yana dubawa ne yaga sunan kanwarshi,ɗauka yayi wanda kafinma yakai ga yin sallamah yaji kukanta da ihunta,
Cikin sauri yashiga tambayarta lafiya,meke faruwa,

"Yaya, Suraj dan Allah kazo part ɗinmu da sauri Ammi ta zame ta faɗi,kuma ta kasa tashi"

Bai ma gama sauraron abinda take fadaba tunda yaji tace Ammi ta faɗi ya fita cikin sauri wanda har yana dan haɗawa da sassarfa ya nufi part ɗinsu.

Koda ya shiga falon yaga basu ciki,har zai haura sama yaji kamar kuka a kicin,dan haka can ya nufa,
Ta samu ta mike da kyar hannun ta na cikin na Amira sai dai ta kasa ajiye kafar a ƙasa sai cije baki take yi,
Da sauri a karasa in da suke yana rikota "Subhanallah,Ammi sannu,ba ki dai ji ciyo ba?

Cije baki tayi" Suraj kafa ta,zafi yake min bana iya ajiye ta "
Tsugunnawa tayi ya duba kafar wanda yake na hagu ne,Babban yatsar kafar yayi ja har ya fara kumbura,

Yana mikewa kawai sai ji Ammi tayi ya dauke ta kamar wata yarinya yana tafiya da ita,
"Suraj sauke ni,so kake ka kada ni "

Bai kulata ba sai da ya fito da ita falo ya zaunar da ita kan kushin,sannan yace"Ammi bari na kira me kyaran kafa dan kamar kin samu targade ne"

Kyara zama tayi tana jinjina mai kai"amma kar ka sanar da Abbu ku dan hankalin shi na iya tashi"

"Insha Allah"ya faɗa yana zaro wayar shi a Aljihu.

Wata number ya kira wanda bai jima yana ƙara ba aka ɗauka,sallamah kawai yayi yace" Idan ba damuwa ina buƙatar ganin ka a gida yanzun,"ban ji me aka ce mashi ba sai ajiye wayar da naga yayi ya koma wurin Ammi yana mata sannu,

Kallon Amira yayi wacce ke hawaye"me ya faru a kicin ɗin?

Share hawayen idon ta tayi "Yaya man gyaɗa ta taka shine ta zame"

Cikin mamaki yace"man gyaɗa kuma,garin ya man gyaɗa ya zube har ta zame,ko dai gangancinki ne"
Chapter 9 · 0% Book details