← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 96

Sashe 22

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk da ta ji yace ke,amma hakan bai sa ta juyo ba,sai ma cigaba da taku da ke yi,

Zainab ce tace"ke Biba baki jin Yaya Suraj na magana"

Juyowa tayi ba tare da tace komai ba,hakan ne ya tunzura shi,domin ba abunda ya tsana irin yayi magana a kyale shi,dan ne zuciyar shi yayi,ya nuna ta da yatsa"zo ki dauke wannan abun a gaba na"

Ba ita kaɗai ba har ta kaka kallon mamaki take mai,
"Ni fa na dama da hannu na, na kuma ajiye maka"

Kallon kaka yayi"daga yau in dai har kina son ki ba ni abu na ci ko na nasha,to kar ki ƙara barin masu aiki su taɓa,ko da kuwa ɗauko min ne,"

"Me yasa" Ta tambaye shi mamakin ta na ƙaruwa, domin abune da bai taba yi ba,

Kallon ta yake ido cikin ido"Saboda kazamai ne,and I hate it"

Nan take ta ji idanun ta sun cika da hawaye,domin babu wani cin fuska daya wuce wannan,a kalle ka ido cikin ido a kira ka da kalmar da ko haɗa hanya ba ku yi da ita,wato ƙazanta,ganin baida niyar dauke idanun shi a kanta ne yasa ta ɗauke idonta a kanshi,tana ƙoƙarin haɗiye hawayen ta,domin ba zata taba bari su zubo anan ba,

"Amma Suraj naga daga Biba har Nafisa duka su suna da tsafta sosai,na yarda da tsaftar sune shi yasa ma suke zaune tare da mu"

Mi kewa yayi tsaye yana ƙara daura idon shi akan fuskarta"ki ƙara binciken ta "yana gama faɗar haka ya bar falon,

" Waye zan ƙara binci ka"cewar kaka tana kallon shi yana barin falon,sai dai bai bata amsa ba ya wuce.

Juyo da kallon ta kan Biba tayi wacce ke tsaye tamkar wacce aka dasa"me ke faruwa "ta tambaye ta,

Girgiza kai kawai tayi ta juya ta koma dakin Nafisa,
Duk da kallo suka bita,kafin kuma ta maida kallon ta kan kwanun Furan ta,
" Mejiddarh zo ki ɗauka kusha tunda shi wanda akai ma gwanin ta ba'a burge shi ba "

Riƙe baki tayi"ni! Wallahi Kaka bana sha,haka kurum,tunda kika ga Yaya Suraj ya faɗi haka shi yasan abinda ya gani,kinga na ma wuce"ya faɗa tana ƙoƙarin barin falon,

"Zainabu zo ki ɗauka Kuje kusha"

Dariya suka saka "a'a tsohuwa ki dai sha abin ki"
"To yanzun ni ya kuke son nayi da wannan Furan?
Ai tuni duk sun fita sun bar ta cikin Mamakin su,to amma me shi Surajo yaje nufi ne,

Fitowar Biba ne yasa ta dago tana kallon ta,
Dukawa tayi kaɗan" Kaka na wuce sai da safe"

"Zo ki zauna Biba" Ta faɗa tana nuna mata kusa da ita,

A hankali ta tako ta zauna kusa da ita ta zauna in da ta nuna mata,

"Ki yi hakuri da halin Suraj,shi haka yake,sai dai ina son ki san shi mutum ne mai matukar sauƙin kai,bai cika shiga harkar da ba nashi ba,balle na masu aiki,wannan shine karo na karko da ya taɓa faɗar haka,shi mutum ne mai matukar kyankyami,bansan me ya gani tattare dake ba haka wanda ya saka shi fadar haka,amma dan Allah koma menene ki yi ƙoƙari kiyayewa kin ji?

Hadiye hawayenta tayi"insha Allah kaka zan kiyaye "

"Yauwa Allah ya maki Albarka"
"Amin,sai da safe"
"Allah tashe mu lafiya"

Tana shiga daki ta saka sakata,
Fadawa tayi kan gado tana fashewa da kuka,tunda take a rayuwar ta ba'a taba mata irin makamanciyar wannan abun ba sai yau,babu wanda ya taba faɗa mata haka,a kowani rana tana wanka sau uku a rana,ta goge baki sau uku,a jikinta ba ta barin ko da digon suma ne,in dai batun tsafta ne sai dai ta nuna ma mutum ba dai a nuna mata ba,kayan wanka ta ma odar take yi daga Indiya,amma shine wannan Ustazun saboda baya tsoron Allah zai kalli cikin idanun ta ya fada mata bai yarda da tsaftar ta ba,wannan abu yafi komai bakanta mata rai,kallon idanun ta da yayi,
Insha Allah sai ta shayar dashi madaran mamaki,ta yanda zata ga yaya zai yi da rayuwar sa a wannan lokacin,
Ranar haka ta kwana cikin baƙin ciki, da Alwashi.
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*24*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Washegari haka ta tashi cikin rashin walwala,a haka ta kammala aikin ta na gida,ranar ko shiyan kaka bata shiga ba tana dakin ta,sai da rana ta fito tayi girkin rana,tana kammalawa ta jira in da ake jerawa,
Ammi ce ta kira ta dakin ta,
Amsawa tayi tana shiga dakin da sallamah,wani kwali ta nuna mata da kuma makulli,"dan Allah dauki wannan kwalin da makullin ki buɗe dakin Abbi ki ajiye wannan a falon sa,yau ƙafan nan so yake ya takura min"

Ai ji take gabaɗaya ta nime bacin ranta ta rasa,har ma bata san sanda ta saki wani murmushi ba,"to Ammi"

Har takai hannu zata ɗauka sai suka ji sallamar shi,amsawa Ammi tayi,tana faɗin "yauwa ga ɗan Albarka nan ya shigo,kinga barshi Biba bari nasa kawai yakai min"

Nan take taji wani kololo ya sauko ya mata saye,wannan fa shi ake kira anga samu anga rashi,
"Ammi bari nakai maki kawai" Ta faɗa tana addu'ar Allah ya bata sa'a ta amince,
"Jeki abinki ai kina ƙoƙari Allah dai ya maki albarka"

Kasa amsawa ma tayi ta fita tana barin dakin cikin tsananin jin haushin shigowar shi,gabaɗaya ya bata mata jin daɗin ta,
Dan haka inda suke ajiye su Omo ta nufa ta dauki wani gora da naga an rubuta Fresh a jiki ta buɗe ta zuba da yawa a cikin bokitin da suke morping daki dashi,ta zuba ruwa kaɗan,sannan ta saka mopa ta fito falo da sauri,
Ta dai-dai ƙarshen matakala tana tsamo mopa ko matsewan kirki bata yi ba ta saka a ƙasan wurin ta shiga kogewa,ta yanda sai da ta tabbatar wurin ya juku yanda take so sannan ta maida kayan in da ta dauko ta koma gefe ta tsaya ta naɗe hannu,

Tunda ya fito daga ɗakin Ammi ta kure shi da ido tana taunar yatsanta a hankali,Allah_Allah take kawai ya sauko,
Jikin shi ne ya bashi ana kallon shi,duk da ya saba da kallo domin ba baƙon shi ba,amma yasan a gidan ba mai mai irin wannan kallon mai shiga jiki,dan haka dan juyawa yayi ya kalle ta inda yake jin nan din ne,ai kuwa idanun shi ne suka sauka a kanta,sai dai kuma hankalin ta bawai a kanshi yake ba akan takun da yake yi yake,bin inda idanunta ke kallo yayi,kafin ya dauke kanshi,
Faɗi take ai Gara kai ma ka karye ko zan samu damar cika aiki na in huta,
Kirgawa take yi saura huɗu,saura uku,saura biyu,saura d....

Ɗan ƙara ta saki tana yarfe hannu jin zafin cizon da tama yatsar ta,tana faɗin kash,ganin a maimakon ya faɗi sai wucewa yayi cikin tafiyar nan nashi na kasaita,

Kallon shi tayi ta kalli wurin,to kodai ba ta saka da kyau bane,
Cikin hanzari ta karasa wurin domin dubawa,sai dai tana saka ƙafa sai ji tayi tayi baya zuuuu ta zame sai gata tayi zaman yan Bori,
Ba ƙaramin zafi taji ba wanda yasa ta saki ƙara,kokarin mikewa take yi,sai dai ta kasa mikewa dan data yunkura sai santsi ya kuma kwasanta,
Jin motsi a bayanta ne yasa ta juya,sai ganin shi tayi tsaye rungume da hannu yana kallon ta,
Hannu ta shiga miƙa mai,alamun ya taimake ta,
Takowa ya fara yi a hankali har ya iso in da take,kallon sakon biyar ya mata da hannun da take mika mashi ya kada kai ya wuce abin shi,
Yaune karon farko da bakin ta ya fara furta sunan shi a gaban shi,"Suraj! Suraj,yaya Suraj! "Sai dai ko juyowa ya kalle ta bai yi ba ya yayi wucewar shi,
Faɗi take" Mugu,waiyo Allah mazaunai na,"ta faɗa tana dafa duwawun ta,da rarrafe ta samu ta bar wurin,tana masa Allah ya isa,dan bai faɗi ba shine yasa ita ta shige,ta faɗi.
Haka ta koma kicin ta kuma hado ruwa ta zo ta goge wurin kar wani ya kuma zamewa tunda wanda ta haɗa ma gadan ya tsallake,amma wallahi bawai ta hakura bane sai ta rama,dan yanzun suka fara,
Dafe ƙwanƙwaso tayi tana fadin wash tare da yamutse fuska.

Da yamma da kyar take iya mikewa a haka tayi girki,har Ammi na tambayar ta ko lafiya me ta same ta ne,sai cewa tayi zamewa tayi a banɗaki,

Nafisa ce ta zo shiyan su wai Kaka na kiran ta,dama lokacin shirin wanke-wanke take yi,dan haka Ammi tace ta tafi ta bar wanke-wanke Amira zata ƙarasa,

Suna fitowa,taga yanda aka ƙawata harabar tsakar gidan harda Docuration akai mai da su Balan_balan kore da Ja,wurin yayi kyau saboda ya samu wadataccen haske, haɗu da su Hadiza tsaye ita da Zainab sun sha kwalliya yanda kasan wadanda zasu gidan biki suka yi,
Ko kallon banza basu ishe ta ba,suka wuce abin su,sai ma Nafisa ce data gaishe su,ita ko kallon arziki basu ishe ta ba,
Kallon Nafisa tayi"yau me za'ayi a gidan nan ne?

Dariya tayi "ai yau karin shekaran Yaya Nurudeen da kuma Aunty Maijiddarh,dan a wata irin daya aka haife su,shi yasa suke yi a tare"

Cikin mamaki tace"dama gidan malamai haka ana celebration na Birthday?

"To su dai suna yi sai dai ba ko yaushe ba,suma da kika ga zasu yi kangara gare su,kuma iyayen su sun daure masu gaba da baya shiyasa,"

Taɓa baki tayi"shi yasa naga waɗancan masu kama da Ungulun sun sha kwalliya "
Dariya sosai Nafisa ta fashe dashi,domin ba karamin dariya abun ya bata ba,wai masu kama da Ungulu,

A zaune take saman kushin tana kallon wa'azi a TV,zama tayi kusa da ƙafafunta a ƙasa,"barka da dare Kaka "
Juyowa tayi"shine yau baki shigo kin duba ni ba ko Habiba,ko dai fushi kike da ni?

Ɗan dariya tayi"A'a Kaka,dama ina shirin na kammala aiki na na shigo ne sai ga kiran ki"
Chapter 22 · 0% Book details