Sashe 94
Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin da gaske tafiyar zai yi ba tare da ya ce mata zai siyo ba yasa tace"ka siyo min Balango"
"Idan har kina so ki tashi muje,"
"Ki tashi mana ai babu nisa da kun siyo sai ku dawo" Cewar kaka,
Allah ya gani tana son cin Balango,dan tun safe dashi ta tashi a rai,
Ba tada zabi mikewa tayi tana takawa a hankali tana dan rmatse ido,saboda hawa tsaunin da suka yi duk ƙafarta ciyo yake yi ya mata tsami,dan har dingisawa take yi,
Shiya buɗe mata gidan gaba dan ta shiga,amma sai ki tayi ta bude gidan baya ta shiga ta zauna,
Girgizar kai yayi ya buɗe mazaunin direba ya shiga ya tayar da mota,
Yana hawa babban titi ya dawo wayar shi,ta dai ji alamun yana magana amma bata San Me yake faɗa ba,
Jiyowa dan wai gawa baya kaɗan yayi"ina ake sai da Balango?
"Wurin masallaci Juma'a"
Cigaba da tuki yayi,sai dai maimakon ya karasa sai kwanan Sitadiyon Junshon ya bi kai tsaye Asibitin Loko ya shiga da motar,
Kallon shi take yi tana kallon Asibitin,
Buɗe mata kofar yayi "fito"
"Me zamu yi a Asibiti?
" Ni zaki raka saboda bana jin daɗi "
Kamar ba zata ce komai ba sai kuma ta fito tabi bayan shi,
Ofishin Babban likita suka fara shiga gaisawa suka yi da mutumin"Ustadz Suraj ko?
"Eh"
"Barka da zuwa,muje Malam"
Shi ya masu jagora har babban ɗakin da ake Sikainin,
Da kanshi ya ƙyara gadon yanda zata ji daɗin kwanciya,
Nuna mata gadon yayi"Madam Bismillah "
Kafin ta gama tantance me yake nufi sai ji tayi ya dagata cak ya kwantar saman gado,
Zaro ido tayi tana ƙoƙarin sauka da sauri ya mai da ita"please"
"Me za'a min?
Hannu ya tura cikin hijabin ta yana sakawa cikin rigarta tana jin yanda yake shafa cikin ta," So nake duba min meke cikin nan"
Kara yunkurawa tayi"da izinin wa,ni dai sake ni in tashi"
Dan marairaice fuska yayi"dan Allah Bebin,ba wani abu bane dubawa ne"
Likitan ne yace"Madam ba wani abu bane dan Allah ki bari a duba"
Komawa tayi ta kwanta tana kauda kai,
Tana ji ya daga hijabin ya daga rigar ma,sannan ya kara zamo da siket sakar marar ta,
Shafa marar yake yana tunanin anya abinda kaka ta faɗa gaskiya ne kuwa,saboda sam cikin ba shida alamun akwai abu a ciki,saboda yanda yake shafe,
"Malam ka dan cire hannun ka a wurin"
"Oh Sorry" Ya faɗa yana murmushi,
Nurse ce ta shafa mata wani dan mai a wurin mai sanyi sannan ta daura wani ɗan na'ura tana zagaye marar dashi,
Jin an danna kasan maran da dan ƙarfi ne yasa ta saki ƙara dana matse hannun shi dake cikin nata,dan tun da aka fara ta ne matsar ido kasancewar tana dan jin zafi,
"Ki mata a hankali mana"cewar likitan
" Sorry,sannan "ya shiga fada yana shafa hannun ta,
Goge mata ciki tayi sannan ta saukar mata da riga" An gama Madam"
Tashi zaune tayi tana kokarin sauka ya kama ƙafarta yana matso da kujeran shi gaban gadon ya Daura kafar saman cinyanshi,
A hankali ya shiga matsa mata kafar yana dan daddannawa,
Ba ta ci musu ba saboda kafar damun ta yake yi,
Mai da kanta tayi ta kwantar tana lunshe ido dan ba karamin daɗi matsar kafar ke mata ba,
Cikin burgewa likitan ke kallon su yana yan rubuce rubucen shi a wani takarda har ya kammala,
Mika mashi yayi"Malam Suraj gashi an kammala "
Karba yayi yana godiya,tare da warware takardar,
Tun daga sama ya fara dubawa komai lafiya har zuwa wata cikin wanda ya nuna wata sati takwas da kwana biyar,
Tunda ya fara karanta yake murmushi har ya kammala,tashi yayi ya rungume ta,dan tuni har ta fara gyangyadi,
Ture shi take kokarin yi"me haka ka sake ni"
Sake ta yayi yana dariya"na gode sosai da wannan kyau da Allah ya Bani ta sanadiyar kiina rokon Allah ya sauke ki lafiya"
Ba tare da ta kula shi ba ta sauka tana saka takalmin kafar ta,
Ɗaukarta yayi kamar wata karamar yarinya,ba tare da ya damu da kallon su da mutane ke yi ba ya gaba da ita,ta san ko tace ya sauke ta ba sauke ta zai yi ba dan haka bata tsaya wahalar da bakin ta ba,
A gidan gaba ya saka ta ya mai da marfi ya rufe sannan ya shiga ya tayarda mota,
Sai da suka kai in da ake sayarda Balango sannan yayi parking ya sauka ya shiya da waya kuwa dan na dubu goma ya siya,
Har suka isa gida bata ce mashi komai ba,
Ganin sun shiga Zauren gidan tana ƙoƙarin shigewa ne yasa ya dakatar da ita,dan yasan in dai har ta shiga ba fitowa zata yi ba,
"Bebin ki shirya mu koma gida gobe,dan Allah ki ba ni dama na kula dake da Baby na dake tare dake har a bada"
Fisge hannun ta tayi daga cikin nashi"ba zan taba komawa gidan ka ba,bana son ka na faɗa maka kamar yan da baka sona,ina haɗa ka da Allah daka sake ni Suraj,Nasan ka san girman Allah "
"Wallahi ban taɓa maki karya ba Salma,Allah shine shaida na,amma ban taba faɗa maki cewar bana son ki ba,ina matukar son ki,ina kaunar ki"
Katse shi tayi"me yasa sai yanzun zaka faɗa min?me yasa tun dama baka faɗa min ba?ko dan yanzun kasan cewar ina dauke da gudan jinin ka shi yasa?
Girgizar kai yayi"A'a Salma ba haka bane,ni a tunani na faɗa maki hakan bai da wani amfani,nuna maki soyayya shine yafi,dan Allah ki Bani dama na nuna maki wannan soyayya ta hanyar kulawa da rayuwar ki,ki Bani dama na killace na nuna maki asalin waye ni,ki Bani wannan damar"
"Ba zan iya ba,kafin ka tafi gobe ka aikomin da takardar saki na"kokarin wucewa take yi ya riko ta,
Kasancewar yanda jikin shi ke rawa saboda tashin hankali daya tsince kanshi yasa tana ture shi yayi baya saura kaɗan ya faɗi,
Ji yayi an riƙe shi,bai damu da ya juya ba yayi kokarin kara binta,sai dai riko shi aka kuma yi hakan yasa ya juya,
Abdulmajid dake tsaye idanun shi sun yi jawur ya matso gaban su ba tare da wata_wata ba ya dauke ta damari sai da kusa kifuwa a kasa,
Zabura yayi yana ƙoƙari taro ya dakatar dashi da hannu"ka tafi gida Suraj,gode zamu yi magana "
"Marinta fa ka yi Abdulmajid,ba ita kaɗai ɓace,me yasa zaka Mare ta?
" Na sani,amma ka tafi,ina son nayi magana da ita a matsayi na Yayan ta ne"
Dafe goshin shi yayi,yana kallon yanda take kuka dafe da kumatun ta,jin kukan yake har cikin zuciyar shi, "idan har danni ne na yafe mata duk abinda tace,kuma ban yi fushi ba kamar yarda banji haushi ba,dan Allah kamin Alkawarin ba ko goshin ta ba zaka kuma dungura ba"
"Na maka Alkawari"
"Na gode" Ya faɗa yana barin gidan,sam zaciyar shi babu daɗi akan wannan marin da aka mata.
A nasu bangaren kuwa yana ganin wucewar shi ya juyo kanta..........
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*94*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
A nashi bangaren kuwa yana ganin wucewar shi ya juyo kanta,
"Kin bani kunya!ban taba tunanin har yanzun ba kiyi nadama abubuwan da suka faru da rayuwar ki ba sai yau!ban taɓa tunanin son zuciyar ki ya kai nan ba sai yau!mijin ki!mijin ki fa kike kallon idanun shi ki ce mashi baya ki son shi ya sake ki!Ashe iatigfarin da kike yi na karya ne!tuban da kike ikirarin kin yi ashe duk na fadar fatan baki ne!tunda gashi ko kadan baki nuna ma Allah godiya ba akan baiwar samun rahamar da ya maki,tunda gashi har kina da bakin da zaki kalli mutumin da Allah ya halarta maki zama dashi kina fadin ya sake ki!Wa'iyazubillah,kalmar da Al'arshin Ubangiji ke girgiza aduk sanda aka ambace shi,sannan kike fadin mijin ki ya sake ki,wallahi Salma ba ki da godiyar Allah,na tabbatar da idan bawan Allah nan ya sake yi ba zaki taba samun ko da mashin shini bane balle a kai ga batun Aure,kuma sai Allah ya jarabceki akan hakkin shi,"busar da iska yayi yana huci"idan har yanzun zuciyar ki na kan Yusuf ne to ki cire,domin wannan karon idan har kika zabe shi to babu mu babu ke har a bada,tunda baki San Alkhairin dake tare da ke ba,wallahi salma ki gode ma Allah,biyo ni ki ga wani abun mamaki"
Tunda ya fara magana take kuka,bin bayan shi tayi har bakin motar shi ta bude ta shiga kamar yanda taga shima yayi,
Har cikin motar Kuka take yi tana ƙara jin tsanar kasancewa da Suraj a rayuwar ta,in dai tun yanzun taraiyarsu zai zamar mata barazana a rayuwa to gaba bata San Me zai faru ba,
Gani tayi sun shiga cikin Asibitin General Hospital Minna,
Yana yin parking suka fito,ita dai tana biye dashi har cikin wani word suka shiga in da kana dosan dakin wani irin karni da wari da za fara ji,duk da tsafta irin na Asibiti,
Tsayawa yayi a bakin kofa ya ciro Nose marks ya mika mata "saka a hancin ki"
Amsa tayi ta saka sannan suka shiga dakin,
Tun da suka saka kafa taji kanta ya sara,ganin mutane kwance tamkar masu ciyon kanjamau sabar rama da kashin jikin su daya fito,wasu ko numfashi kirki basu iya yi,ga wari na masifa dan ko majinyaci daya baya tare dasu,
Abakin wani gado suka tsaya,in da wani tsohon mutum ke kwance yana fitar da numfashi da kyar ko riga babu a jikin shi,wallahi har tsoron kallon fuskar shi take yi yanda fuskar ya rame kana iya ganin duk wani kashi na fuskar,ga ido da yayi zuru_zuru,
Cikin sauri ta riko hannu Abdulmajid tana dan komawa ta gefen shi,
Nuna mata mutum yayi"kinsan waye wannan?
Girgiza kai tayi,
"Kara kallon shi da kyau ki gani"