← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 96

Sashe 59

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan karon kalaman shi ya fara basu haushe "me a tattare da Salma da har zaka ce kai ba zaka yarda da Aurenta,na tabbatar idan kyau kake butaka to tana dashi,idan kuma kuɗi ne ko tarbiyya kaima kasan duk gidan su ka zo,ko me babban magana akan wannan lamarin"

"Babu wani babban lamari amma kasan shi aure abu ne na ra'ayi to ni kuma Allah bai Daura min wannan ra'ayi ba,kuyi haƙuri sannan ku ba ƙanwar ku haƙuri ta nime wani ta aura" Yana gama gadar haka ya tashi ya shige cikin gida ya bar su nan zaune a baranda,

Kallon juna suka yi suna jinjina wulakanci irin na Yusuf wanda basu taba tsammanin haka daga gareshi ba,sun dauka zai amshesu da hannu biyu sannan yayi farin ciki akan lamarin ya nuna jin daɗin shi,sai gashi ya nuna masu saɓanin haka,

"Tashi mu tafi"
Mikewa yayi suka fito sannan suka samu abin hawa ya maida su har ƙofar gida,

Suna shiga shiyan su zama suka yi a nan falo saman kushin in da Abdulmalik ke zaman jiran su,
Yana jin shigowar su ya tare su"Kun same shi? Ya kuke yi dashi? Dama soyayya suke yi ko?

Dafa kafadarshi Abdulmajid yayi"duk yanda kake tunanin abun ba haka yake ba"

Zaro ido waje yayi"kamar ya?

"Zauna kaji"
Nan suka shiga ba shi lamarin duk yanda suka yi da Yusuf din har wutowar su,"yanzun ban san yanda zamu yi da Salma ba,kasan ita matum ce mai tsayawa akan magana daya har balle a kan abinda take so,yanzun duk wani shawara da zamu bata ba ɗauka zatayi ba,"

"To me zai hana mu same Baba da maganar" In ji Abdulrahman.

"A'a yayi sauri Gara dai mu fara dai-dai ta kansu tsakanin shi da ita sannan mu shawo kan Mama tukun na kafin Baba"

"Hakan yayi, yanzun mu je mu kwanta kun ga har ƙarfe goma tayi gobe ma san abun yi"
Da wannan shawarar suka tsayar in da kowa ya shige ɗakin shi ya kwanta kowa zuciyar shi cike da nimar mafiya ma kanwar su.

Washegari ta riga kowa fitowa wanda ita kanta Mama sai da tayi mamakin fitowar ta,domin ba ta zata ba,
Cikin sakin fuska ta gaida Mama,wacce ta kasa yin shiru "what the occasion"

Dan dariya tayi kaɗan "babu komai Mama,kawai dai ina cikin farin ciki ne"

A tunanin ta ko ta hakura da maganar su na jiya ne dan haka tace"ai gara da kika cire shi a ranki domin hakan zai fi maki"

Girgiza kai tayi"A'a ban cire shi a rai na ba,kawai dai sun min Alkawarin taimaka min ne"

"Su yannin naki? Ta tambaya cikin mamaki,

" Umm "ta fada tana haɗa shayi,

Bata ce mata komai ba har sai da ta tabbatar ta karasa shan shayin ta sannan ta kalle ta" Bana son ki saka yakinin ki da yawa a kansu,domin haka zai iya cutar dake,abu na biyu ko da ni na amince ki sani mahaifinki ba zai taɓa yarda ba ballantana ni ma kuma ba zan taba yarda ba"

Ji tayi nan take duk wani kwarin gwiwa data tashi dashi Mama ta sare shi"me yasa baki son Yusuf,me yayi maki da kika tane shi har haka Mama
Yusuf fa is a normal gay,yana aiki a kamfanin Baba,ana biyan shi Albashi wanda na tabbatar da zai iya riƙe mu,to Mama me kuma ake buƙata,na tabbatar da idan da Ace tun farko bai da tarbiyya Baba ba zai taɓa yarda ya shigo dashi cikin gidan nan ba,ke ma kin sani"

Kallon ta kawai take yi tana kuma jinjina irin fahimtar ta da kuma yarda da tayi da mahaifinta,tabbas data san shi waye da bata faɗi haka ba,dan haka ba tare data bata amsa ba ta mike ta shige daki abunta,

Da kallo ta bita cikin mamakin abunda tayi,ta dauko magana sannan bata karasa ba ta wuce,
Dan haka tashi tayi ta bita daki,in da ta same ta tsaye da waya a hannu daga dukkan alamu kira take kokarin yi,

Kallon ta tayi"lafiya?

"Mama baki ce komai ba?

Zama tayi bakin gado" Me kuma kike son na faɗa maki Salma wanda zaki fahimce ni?

"Kin ce kar na ji kunya a duk lokacin da nake da wani buƙata ko niman taimako na zo na same ki a matsayin ki na mahaifiyata zaki taya ni samun mafita,amma sai gashi a karon farko kina kokarin jefa rayuwa ta cikin hatsari ta hanyar hana ni aure"

Dafe goshinta tayi ta dan murza tana busar da iska cikin tsanin damuwa da lokaci guda ya baiyana a fuskarta "ina maki gudun aikata wani babban kuskure wanda zai ta bibiyar rayuwar ki na tsayin har a bada Salma! Ina maki gudun tafka babban kuskure irin wanda na aikata a baya!ina maki gudun rayuwa mara tabbas,kokonta da bullewa Salma! Bawai ban fahimci halin da Kike ciki bane,kawai dai ina tsoron halin da zaki shiga ne,domin duk irin nunin da zan maki,ba zaki taba fahimtar komai ba domin idanun ki a rufe suke wanda ni kaina bana fatan abunda zai buɗe maki su har abada balle ki fuskanci abunda ke gaban ki,sai dai ki sani auren wannan yaron da zaki dauko ma kanki tamkar mutum ne ya faɗa rami sannan yaci gaba da haka ramin wai a kokarin shi na fitowa har wata rana wannan ramin yayi zurfin da zai fado ya danne shi,
Ni idan da ace wani kika kawo ba shi ba wallahi zan yi farin ciki dashi na kuma taya ki karbar shi,amma Yusuf har abada ba zan taba karɓar shiba,domin kokin aure shi ba zaki taba samun abunda kike nima ba"
Kama hannun ta tayi duka biyu ta haɗa wuri ɗaya"ɗan Allah ki fahimce ni Salma,ki canja wani zaɓin zan taimaka maki kin ji?

A hankali ta zame hannun ta a cikin nata"Mama ki yi hakuri duk yanda naso na natsu na fahimce ki na kasa,domin har yanzun baki ba ni wani kwakkwaran hujja ba da zai hana ni son shi,dan haka ki yi hakuri har yanzun ina kan baka na Yusuf shine zaɓi na"tana gama fadar haka ta tashi ta bar mata ɗakin "

Da kallo ta bita,sai dai wannan karon zuciyar ta cike yake da rauni ganin irin kuskuren da yarta ke kokarin tafkawa a rayuwar ta,sai dai ko zasu kai ruwa rana ne ba zata taɓa bari hakan ya faru ba....
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*59*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Ganin lokacin tashin Baba yayi ne yasa suka shiga dakin shi da sallamah,
Cikin farin cikin ganin yaran nashi ya amsa yana sakar masu murmushi,zama suka yi kan kushin "Baba muna da magana"

Ajiye Turaren da yake fesawa yayi ya dawo ya zauna a daya daga cikin kujerun da suke zagaye a dakin, yana fuskantar su,ganin yanda suka ba maganar da zasu faɗa Muhimmanci suka natsu,
Yasa yace"Ina jin ku"

Ajiyar zuciyar Abdulmajid ya sauke kafin ya fara magana "Baba Salma ta faɗa maka ra'ayin ta game da tafiya makaranta?

" A'a,wani abun tace maku ne?

"Ta samu Mama jiya da maganar cewa ita bata son tafiya karatu London ba tare da Aure ba,ina nufin wai aure take so"

Dan shiru yayi na dan wani lokaci alamun nazari kafin ya ce"tunda har ta zaɓi haka to ba matsala ba ne,da ace taje tana aikata wani abu bayan idon mu gara da ta faɗa kun ga sai ai mata abun da take so,in yaso sai su tafi tare da mijin ta,ko ba haka ba?

Kallon juna suke yi suna sakin murmushin nasara domin basu ɗauka lamarin na wurin Baba zai zo masu da sauƙi ba,"haka ne Baba"

"To dama tana da wanda take so ne,ko kuma ta tsayar?

" Eh tana dashi Baba,sai dai kuma data fadama Mama sai cewa tayi sai dai bayan ranta dan bata isa ta aure shi ba,"

"Wannan ai maganar banza ne,bayan yarinya na son shi kuma har ta faɗa,so take ta saka ta a wani hali ko kuma so take na mata auren dole,karku damu zan fahimtar da ita amma kan aure sai an yi tunda suna son juna,tukunna ma waye yaron,waye mahaifin shi?

" Baba ai ka riga ka san shi,Yusuf ne me zuwa nan gidan "

Dan jim yayi kafin kuma kamar wanda aka tsikara tace"ba dai Yusuf ba?

"Shi Baba"

Nan take wani irin zufa mai matukar sanyi ya shiga fito mai daga jiki ta ko'ina,hankalin shi ya tashi yayin da yaji wani abu ya tsaya mai a rai"ba dai Yusuf ba,dama amanata zai ci yana soyayya da ƴar tawa bayan duk abinda nake ma shi bai ishe shi ba"

Kallon tsoro da mamaki suke mai,sai suke ganin kamar ba shi ba,yanzun fa ya amince amma kuma yake yi kamar bai gane me suke nufi ba,

"Baba dama soyayyar bari daya ne"

"Kamar ya?

" Shi baya son ta ita ce ke son shi,dama so muke ka faɗa ma iyayen shi ko zasu shawo kan shi "

Wani irin ajiyar zuciya mai matukar ƙarfi ya sauke wanda yasa sai da suka kara shan jinin jikinsu da wannan lamarin,gashi har share zufa yake yi yayin da idanun shi suka yi ja "to tunda baya son ta ai ba dole bane,ba sai ta nime wani ba,ni ban damu ba ko ma waye ta kawo zan aura mata amma banda Yusuf"

"Baba amma fa yanzun ka nuna amincewar ka me ya faru,shin me yasa baku son ta auri Yusuf,ko dai akwai wani abu dangane dashi ne wanda ya kamata mu sani,?

Kara share zufan daya karyo mashi yayi" Kawai dai ku bata shawara tabi shawarar mahaifiyarta,ku tashi ku tafi sannan bana son na kuma jin irin makamancin wannan maganar a gidan nan on dai akanta ne da Yusuf "
Chapter 59 · 0% Book details