← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 96

Sashe 34

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin ta saki wani lallausar murmushi wanda ya baiyana fararen haƙoran ta suke jere tas dasu,sai kuma dimful wanda ya baiyana a gefe ɗaya na kumatun ta,
A hankali take takowa da takalmanta masu dan tudu har ta isa gefen da kushin yake tama kanta mazauni a wurin kafin ta juyo da kallon ta kan Farhan wanda yayi suman tsaye yana binta da kallo"Farhan ka faɗa mashi shin ya manta matsayi na ne a wurin shi,dan haka bai da hurumin faɗar haka"

Mai da kallon shi kan Suraj yayi"tace baka da hurumin fadar haka"

"Ka faɗa mata ta zaɓa wani ɗakin acikin ɗakunan duk wanda ya mata ta zaɓa,amma ba na son tazo inda nake"

Kallon ta yayi sai dai kuma ya rasa me zai ce mata,saboda yarinyar ba karamin kwarjini ta mai ba,
"Me ya faɗa Farhan"a zuwan ita bata ji me yace ba

"Ummm cewa yayi babu komai kina ina zama duk in da ya maki"

"Yauwa na gode Farhan"

Cikin sauri yace"yaushe na faɗa maka haka,ke tashi ki barmin daki"

Turo baki tayi ta tashi tana takawa kamar zata bar ɗakin,juyowa tayi tana dawowa baya kafin ta juyo da gudu ta nufo in da yake,

Ko da ya dago kai kafin yace zai motsa sai jinta yayi ta fado jikin shi,gabaɗaya suka zube saman gado a kwance ita tana saman kirjin shi,

Kokarin ture ta yake daga jikin shi sai kwantawa tayi da kyau yayin da kirjinta ke gogon nashi,
"Idan kayi ƙoƙarin ture ni zan yi abinda baka so"

Kauda kai yayi yana furzar da iska,"ɗaga ni"

Girgiza kai tayi"a'a "

"What do you want?

Dan shiru tayi kamar mai tunani sai kuma ta juyo da kallon ta kanshi,yatsa tasa tana zagaye fuskar shi dashi," Do you hate me that much?

"Fiye da yanda hankali zai ɗauka"

"Har haka?

" Ɗaga ni"

Sauke hannun ta tayi a fuskar shi "ni ma na tsane ka sosai,fiye da yanda ka tsane ne,sai dai ba yanda zaka yi dani domin na zama matar ka,dolen ka,kuma na zama bindin ka,duk inda zaka tafi tare zamu rika zuwa,ka saka hakan a ranka"tana gama fadar haka ta sauka daga jikin shi ta doshi hanyar da suka shigo ta fita,

Dakin dake gefen nashi ta buɗe,nan ma a kyare yake babu abinda babu,dan haka zama tayi nakin gado tana ƙara nazarin dakin.

Shigowa yayi yana dan kalle_kalle a ɗakin,"ta wuce ne?

"Zo ka mai da min drip"

Hannun shi ya kama yana duba inda zai samu jijiya "tana da kyau sosai,na ɗauka zan ganta kamar sauran yan aiki,sai dai ita na daban ce"

Bai bashi amsa ba sai ma mai da idanun shi da yayi ya rufe,

Ganin haka ne yasa shima ya ja bakin shi yayi shiru,dan ya sani idan har yayi haka ba kara wata maganar zai yi ba,amma dai maganar gaskiya shine ta wuce da tunanin shi,sam bai yi tsammanin haka ba,sai dai daga dukkan alamu ita din ba ƙaramar yar duniya bace,yarinyar idanun ta a buɗe suke,shi wallahi da zai samu irin wannan bai ga abinda zai sa yayi wasa da damar shi ba,sai dai yasan halin Suraj,zai kuwa so yaga yaya wasan nasu zai kasance da yarinyar dan ita kanta hatsabibiya ce,

Yana gama saka mashi ya mashi sallamah ya wuce a kan sai sun haɗu gobe.

Washegari da safe koda ta farka ƙarfe tara na safe saura,ta jima bata samu tayi barci irin haka ba,dan haka banɗaki ta shiga tayi wanka da kalolin sabulan wanka masu kamshi da ta gani,wanda hakan ne yasa ta jima a cikin banɗaki,
Sai da ta tabbatar ta cire duk wani dauɗa da dake jikin ta lungu da tsako sannan ta dauro Alwallah ta fito,buɗe durowar dakin tayi,babu komai a ciki sai kayan maza,cikin Jallabiyoyin shi ta jawo ɗaya haɗe da boxe size ta saka sannan ta yafa gyale tayi sallah,

Tana idarwa falo ta fito dan ba karamin yunwa take ji ba,
Kallon wurin da ake shirya abinci tayi,ganin manyan kuloli tayi shirye a wurin,dan haka jawo kujera daya tayi ta zauna sannan ta shiga jawo ko wanne gabanta tana dubewa dan ganin me a ciki,
Lafiyayyen farfeson kaza ta zuba wanda ya ji sinadirin kanshi da ɗandano,sai kunun kyada,
Bata jima da fara ci ba ta ji takun saukowar shi,kallo daya ta mai ta dauke kanta tana ci gaba da taunar tsokar kazanta,

Cikin sauri Bala dake biye dashi a baya ya karaso inda take"malama daga ina,wacece ke?me kike yi anan,daga zuwa kuma sai taba abin mutane "

Kallon ƙasa da sama ta mai"tashi min a kai karka saka na kware"

"Wacece ke"

Ajiye naman dake hannun ta tayi,sannan ta karaso inda yake tsaye cikin sakin fuska,
"Mijina Abin Alfahari na barka da safiya,ya jikin naka?

Kauda kai yayi yaci gaba da takawa zama yayi kan kushin," Bala"ya kira sunan shi,

"Idan kuna bukatar wannan abincin ka kwashe,idan kuma baka buƙata ka fitar min dashi"

"To me zaka ci uban daki na?

" Ka samar min abu mai sauƙi,wannan kuma zata zauna damu na ɗan wani lokaci ka bata abinci yanda ya kamata,"

Zama tayi kusa dashi tana daura kafa daya kan daya kamar yadda yayi"Bala ni matar mai gidanka ne,dan haka dole ka jirmama ni kamar yanda kake girmama shi"

Cikin mamaki yake kallon ubangidan nashi,da mamakin yaushe hakan ya faru,da kuma yaushe yayi aure,sai dai katse mashi tunanin yayi ta hanyar fadin"Barshi"ya yi fitar shi,

"Ina sauran ma'aikatan gidan nan?

" Suna shiyan su"
"Ina bukar ganin su yanzun nan"

Bata fuaka yayi dan ya lura kamar so take ta rusa masa gwamnatin shi a wurin ubangidan nashi,
"Yanzun suna kan aiki ne"

"Kaje ka kira min su idan kuma basu zo ba a bakin aikin ka"

Dafe kirji yayi"bakin aiki na kuma,ta nan fa nake samu nake ciyar da iyalai na "

"Ba sai ka koma bara ba,dama akwai wanda nayi alƙawarin zam nimar ma aiki,yama fika dacewa da aiki,ka ga yanzun ni ce mata gida sai yanda nayi da mai gidan"

Cikin rawar jiki ya juya "bari naje na kira su"

"Dawo muyi magana tukunna"

Dawowa yayi wannan karon harda tsugunnawa dan ya lura in bai yi hankali ba wannan yarinyar da bata wuce sa'ar kanwar shi ba tana iya mai sage_geduwa gara ya bita a hankali,

"Idan har ka yarda zaka min aiki zan kara maka albashi akan wanda ubangidan ka ke baka"

"Wani irin aiki,sai dai ki sani in har na cutar da ubangida na ne ba zan karba ba ko nawa zaki ba ni"

Dan murmushi tayi"kwantar da hankalin ka dan ni ma ba zan iya cutar dashi ba,sai dai na kare shi,aikin ka shine kawai duk lokacin da kaga zai fita ka sanar dani,in da hali ma har in da zai je "

Ji yayi hankalin shi ya ɗan kwanta"in dai wannan ne ba kida damuwa Hajiya "

"To kaje ka kira min su gani nan fitowa"

"To hajiya"

Bayan kamar mintuna goma sai gashi ya dawo"Hajiya suna ƙofar falo"

Mikewa tayi ta fito a tsaye ta same su suna jiranta,ba tare da damuwar komai ba ta masu sallah,

Amsawa suka yi cike da tunanin wacece ita,domin wannan ne karo na farko da wata mace ta shigo nan ɗin,
"Ni suna na Habiba,matar mai gidan ku,nasan zaku yi mamaki,amma ba abin mamaki bane dan jiya aka ɗaura mana aure da shi"

Ganin duk sunyi shiru suna mata kallon mamaki ne yasa ta ɗan daga kafaɗa ta "akwai mai abun fada?

Girgiza kai sarkin gida yayi" A'a Hajiya "

"Well to ni ina da abun faɗa,na farko bana son gulma da kananun magana,sannan ina son girmamawa,ma'ana a dinga bani girma na,na uku kuma ina fata zamu zauna lafiya tare da ku"

"In sha Allah Hajiya"

"To sai kumin introducing kan ku"

Babban cikin su ne ya matso gaba"ni suna na Sarkin Gida,kuma ni ne babban su mai kula da duk wani harka na cikin gidan nan,sai wannan Bala shine mai yi ma uban gida girki,sai kuma direba,da masu kula da tsakar gida ta tsaftar gidan "

"Hakan yayi kyau,dan haka kuna iya tafiya"

"Mun gode" Suka faɗa a tare,

Komawa cikin falon tayi ta zauna tana sauke ajiyar zuciya,wayarta dake hannun ta shiga dannawa tana kwada number Ummita ko Allah zai sa ta sumu,sai dai abu ɗaya kawai ake maimaita mata shine wayar a kashe take,
Tsaki taja cike da tunanin a wani hali take ci,gabaɗaya wannan yanayin yana hana ta samun natsuwa,

Ji tayi kararrawar kofa yana ƙara alamun ana niman izinin shigowa,
Tashi tayi ta buɗe ƙofar,
Kallon_kallo suka tsaya suna ma juna kafin Zainab ta buge kafadarta ta shiga ciki,sai Amira sannan Aunty Hajjo dake,
Da Bala da sarkin gida ne suka shigo dauke da wasu manyan Akwataiya guda shiga suka jera a tsakar falon sannan suka fita,

Mai da kallon ta kansu tayi,sun yi wani zaman taƙama a falon yanda kasan na gidan su,

Cikin sakin fuska tace "Aunty Hajjo ina kwana,Amira sannan ku da zuwa"
Sai dai duk cikin su ba wanda ya bata amsa,
Sherawa tayi ta shiga kicin ta dauki masu gorunan ruwa da lemu,

"Kin ga dauke mana a gaba dan ba mu maki kama da wadanda suke ni ma ba"

Ita fa ta lura da take taken su,ba su san duk wannan abun da take masu na marmari bane,amma ba komai a hankali zasu san juna,

Aunty Hajjo ce tace"wannan ba rigar Suraj bane kika saka"

Murmushi ta saki cikin jin kunya tace"da Asuba ne da muka yi wanka tare to shi ne ba ni da kayan da zan saka shine ya saka min nashi"

Gabaɗaya miyon bakin su daukewa yayi,wanka fa tace tare da Suraj din kuma har da saka mata kaya,kenan ba dai har yayi wani abu da ita ba,kai Namiji ba shida amana,

Ganin halin da suka shiga ne yasa ta saki wani shegen murmushi tana ɗan dago kai,
Sai dai cikin rashin sa'a idanun ta ya fada cikin nashi dake tsaye rungume da hannu yana sauraran abinda ta faɗa.

🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
Chapter 34 · 0% Book details