← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 96

Sashe 25

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na'am Biba"
"Da zaran na kammala wannan aikin nawa,ba zan kuma yin wani aiki ba,zamu bar kasar nan mu je wani wuri in da babu wanda zai ƙara takura mana,in da ba zamu haɗu da wadanda suka san mu ba balle suyi threatened din mu"

"To Biba idan kina son haka ya kasance sai kin watsar da komai kin maida hankali kin cika aikin ki"

Share hawayen idonta ta kuma yi"zan yi haka,cikin satin nan duk hanyar da zanbi zan bi domin na kammala"

"Yauwa Biba,shi yasa nake son ki,saboda nasan zaki iya"

"Thank you for supporting me all the time,and encouraging me,you are my only Family in this world"

Daga nata ɓangaren ma share hawaye take yi,ta san halin Biba sarai,ta san matsalarta,kamar yanda ita ma ta san nata,Biba ta dauke ta ta maida ita danginta alokacin da take tsaka da niman taimako,ta bata muhalli,ta maye mata gurbin duk wani abinda ta rasa,
Sun maida junan su Ahalin juna,shi yasa ta riga tasan wannan wani irin rana ne a wurin Biba"ke ce farin ciki na,kuma gata na,dan haka ki yi sauri ki kammala ina jiran ki"

Jinjina kai tayi"sai munyi waya"tana gama faɗar haka ta sauke wayar.

Maida kanta tayi ta jinjinar da jikin iccen,idanun ta a lumshe,

Wani irin ni'imtaccen kamshe ne yake shiga hancinta,wanda ta tabbatar da a jikin mutum ɗaya kadai take jin wannan kamshen,
Tuna wanene yasa da sauri ta buɗe idanun ta,wanda cikin rashin sa'a sai a cikin nashi,

Yana tsaye a gefen ta ya zuba mata ido kamar mai nazarin ta,
Da sauri ta ɗauke kai dan ba zata iya jure kallon cikin waɗannan idanun shi ba,
Hannu tasa da sauri tana goge ragowar hawayen dake kwance saman fuskarta,
Tuna kwalin Segret din dake gefen tane yasa da sauri ta zabura tana daura hannun ta saman kwalin,
Ƙara dago ido tayi dan ganin ko yaga kwalin wanda bata fatan haka,
Sai dai har yanzun idanun shi na kanta ne bai dauke ba,
Kara kauda kai tayi a karo na biyu ta dauke kwalin Segret din cikin dubara ta tura a hijabin jikin ta,
Mikewa tayi ba tare data ce mai komai ba tana ƙoƙarin barin wurin,
Cikin muryar nan nashi mai ratsa kashi da barko taji yace"wannan ya zamo karo na karshe da zan kuma ganin inuwar ki a tanan ɓangaren "yana gama fadar haka ya juya yayi tafiyar shi cike da mamakin ta,shi fa ya fara zargin Something is not right about this girl,ya dawo daga masallaci ya shiga bayi domin yin wanka,amma gabaɗaya kasawa yayi saboda bayin shi dake warin hayaƙin Segret,domin windon a buɗe yake,
Yana lekawa shine ya hango ta.

___________Niger State.

Kusan mintuna biyar kenan yana tsaye a kanta amma bata San ma da zuwan nashi ba,
Dukawa yayi a hankali ya saka hannun ya amsa Album din dake hannun ta,wanda take kallo tana shafa hotunan ciki,

Dago kai tayi ta kalle shi,
Hannu yasa ya shiga share mata hawayen dake bin Fuskarta,"har tsayin wani lokaci zaki ɗauka kina zubar da hawaye Mama?

Dagowa tayi ta kalle shi da rinannun idanun ta"har zuwa sanda zata dawo cikin rayuwar mu,ko da ta dawo har sai na nime yafiyarta ta kuma yafe min sannan zan iya samun salama "

"Mama yau tsayin shekara biyar kenan,rabon da muga farin ciki acikin idanun ki,gashi sanadin yawan kukan da Kike yi idanun ki na son ya samu matsala,dan Allah Mama koda sau daya ne,ko da na rana daya ne muna son muga farin ciki a fuskokin ku,muna son muga dariya a faskarku"

"Abdulmajid" Ta kira sunan shi,
Rike hannun ta yayi"na'am Mama"

"Tun daga ranar da ƙanwarku ta saka kafa tabar wannan gidan ta tafi da duk wani farin ciki namu,kai ma ka sani,ko da nace zan ɓoye bakin ciki na nayi dariya a fili,to is feck,abu ne da bazan iya ba," Share hawayen ta tayi"yaune ranar zagayowar haihuwar ƙanwarku,yaune kuma naran da tayi aure,"idan da ace tana nan kamar shekarun baya,da tunda Asuba zata fara bi ɗakunan ku tana tayar daku akan sai kun bata gift na karin shakara,haka za ku korata waje ku saka sakata a ƙofar ku,amma duk da haka sai ta hanaku barci da buga ƙofa,har sai ta saka kun fito ba tare da dakun shirya ba,koda tayi aure ma haka sai dai tai ta damun ku da waya tunda Asuba,idan kuma kuka kashe wayoyin ku sai ta kirani tana korafi,"

Dariya yayi kaɗan shima yana share nashi hawayen,"wani lokaci idan na tuna soyayyar dake tsakanin mu Mama,sai naga kome yayi zafi bai kamata Salma tayi irin wannan nisan ba"

"Na tabbatar kuma saboda kun danne zuciyar ku ne shi yasa baku tafi kun barni ba,sai dai ku yi haƙuri domin wannan shine tawa Kaddaran," Ta karasa faɗa tana fashewa da kuka,

Rungume ta yayi ajikin shi yaya lallashinta sam baya son hawayen ta ya karu,dan haka ɗauko Album din da ya ajiye a gefe yayi ya buɗe "Mama kin ga nan hoton salma ne lokacin tana shekara biyu,a lokacin ta fara iya magana,kin tuna ba tada aiki sai na cizo,ko hannunka ka kuskure yayi hanyar bakin ta saita kai maka cizo,in kuma kaki yarda ta dinga kuka kenan tana binka"

Nan take ta shiga shafa hotun murmushi mai tattare da hawaye yana bin fuskarta,
Ko a cikin ya'yan ka Ubangiji kan jarabceka da son daya daga cikin su,wanda zaka ji duk kafi son shi,to su nasu gabaɗaya soyayyar akanta ne,domin ita kadai ce mace acikin su hudu.

_______Kano

🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*27*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

______________Kano.
Ganin ta gaji da zaman tunani ne yasa ta fito falo domin taya Amira yin girki,sai dai koda ta shiga kicin din kin yarda tayi ta bari tayi aiki, wai ta bari ta ƙara jin sauƙi,
"To ki bari na taya ki koda ƙyara ganye ne" Ta faɗa tana jawo kujeran kicin din ta zauna,

"So kike Ammi taimin faɗa?
" To ai tana ɗaki "
"Yauwa abunda za'ayi kawai shine ki shiga dakin Abu ki taya ni kyarawa kinga kafin ta sauko kin kammala"

Cikin sauri tace "na amince" Dan ji ta yi kamar ta kama kumatum Amira ta sumbace ta,

Nuna mata ɗan key din tayi"gashi nan ki ɗauka sai dai ki yi sauri"

Daukar makullin tayi,tana barin kincin din da sauri,cikin tsananin zakuwa da kuma Addu'ar Allah yasa ta dace,

Tunda ta shiga falon ta dafe Kwankwaso tana ƙare ma ko'ina kallo,ta ina zata fara,daga kan durowoyi ta fara bincike har karkashin kujeru,sai dai duk bata ga komai ba,tana yi tana share dakin tare da gogewa sama sama dan kar a fahimta,
Hannu tasa tana ƙoƙarin murda hannun kofar data gani,ta ji daddadar kamshin nan na tashi,
Bata juyoba taci gaba da murdawa ko Allah zai sa ya buɗe,
Daga bayanta ta ji ance"me kike yi"

Tsabar tsoratan da tayi batasan sanda ta yar da tsintsiyar dake hannun ta ba ta makale jikin bango tana dafe kinji,
Kallon shi take cikin jin haushi wai me yasa shi baya sallama ne,kawai sai dai kaji kamshin shi,

Ƙara jeho mata wani tambayar yayi"what ar you looking for?

Ba tare data bashi amsa ba ta raɓa ta gefen shi tana kokarin wucewa,hannun yasa ya kama gefen hijabinta kaɗan "fadamin me kike nima"

Kallon shi tayi ta kuma kalli hannun da ya riƙe ta dashi yanda kasan wanda ya rike kashi"gyaran daki nake yi "
Sake hijabin yayi,babu abinda daya kona mata rai irin yanda ya dauki abin goge hannu ya goge hannun shi gaba da baya ya wurga a wurin saka shara,wato yanda kasan wanda ya taba kashi,
"Nan ba wurin zuwan ki bane kina iya tafiya"ya faɗa yana nufar wurin kofar,tana kallo nan ma sai da ya ƙara gogewa sannan ya saka makulli,
Juyawa tayi ta fita daga falon gabaɗaya dan babu abinda ta samu,sai dai yau dinnan sai ta shiga dakin shi,domin ta ji abakin Amira cewa zasu yi wa'azi yau bayan Isha'i a masallacin kofar gida,dan haka yau kam damarta ce.

Daki ta koma lokacin ana daf da kiran sallah Magrib,wanka tayi ta saka doguwar riga na bacci iya cinya mai karamin wando a ciki,sai ta daura zani a sama,da hijabi,tana jira ayi sallar Isha'i sannan ta tafi,
Sai da ta tabbatar an idar da sallar Isha'i sannan ta fito,
Tana fitowa suka hadu da Nafisa a falo,rungume ta tayi"Biba ya jikin naki"

"Da sauƙi Nafisa"
"Kiyi haƙuri ban samu na koma na duba ki ba,ni ma Baba nane bai da lafiya shine na tafi duba sa"
"Ya jikin nashi?
" Yaji sauki dama wai Maciji ne ya sare shi a gona,amma Allah ta taimaka gidan mu suna bada maganin,sai zazzabi da yayi"

Kankame hannun ta tayi tana jin tsigar gikinta na tashi"waiyo Allah na tsani maciji,kinga ya jikin nashi"
"Yaji sauki sosai ko da na dawo,yauwa muje an aiko ni na kira ki ne"

"Waye?
" Goggo yara"
Sam bata son shiga tsabgar matar nan dan haka tace"me zan mata kuma?

"Kin ga ba ke kaɗai bace,ina ga zata sakamu aiki ne"

Turo baki tayi"duk ma'aikatan gidan nan,sai ni da Bani da lafiya?

Jan hannun ta tayi"dan Allah mu tafi kinga dare nayi"

Ba dan taso ba tabi bayan ta har shiyan Goggo,in da suka same ta a falo tana kallo,

"Yauwa Nafisa ku shiga dakin na ku duba min har kasan gado ni gabaɗaya ma na rasa meke motsi ne a cikin dakin,Allah dai yasa ba bera bane"

Dakin suka shiga suka fara dubawa,
Motsi taji ai kuwa ihu ta saka tana daka tsalle sai saman gado
Dariya Nafisa ta saka"kardar ke ma tsoron beran kike yi?

Leken kasa take yi"duba ta nan naji motsin abu"

Dariya ta kuma sakawa tana nuna ta"kinga leda ne na taka shine kika ji motsi "
Chapter 25 · 0% Book details