← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 96

Sashe 13

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amma a zuciyar shi kuwa rayawa yake lallai wannan karon daga dukkan alamu tarkon shi zaiyi babban kamu,wanda yana ganin ta hanyar wannan Beran ne zai kai ga Asalin abin Farautar shi,
Gabaɗaya shiyansu Abbu zagaye yake da Camera ta ko ina har izuwa shiyansu na samar,wanda babu wanda ya san dasu face shi,
Wannan karon ya shirya wasan da gaske,

Sai dai kuma wannan halitta kallon ta kawai yake,amma tun ganin farko daya mata ya riga ya shaida ita waye,
Ya san yana da mantuwa akan abinda ya san baida amfani,idan kuma lokacin amfanin shi yazo yana tunashi,haka ƙwaƙwalwar shi take,dan haka tsaf ya sheda ta,wato dashi zata yi wasa ko,lailai bata san waye shi ba,amma a hankali zai fahimtar da ita ta yanda da ƙafar ta zata bar gidan,
Wani murmushin ya kuma saki yana buɗe idon shi,tare da fara ma Annabi kirari a zuciyar shi.

*this is just the beginning*

*Yanzun Aka Fara*
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*15*

*Na mai da Littafina mai suna a sama na kuɗi,tare da JAURO,idan kina son daya 300,dari uku,guda biyu kuma da Yar Tsanar Zinari tare da Jauro,dari biyar 500,ko wani daya dari uku*
*Hauwa Umar,Zenith Bank, 2284905309*
*ko katin waya na MTN,tare da turo shedar biya ta 08141644865*

*Not edit*

Jin an dafata tare da girgiza ta yasa ta dago kai a ɗan razane,

"Lafiya Biba tun dazun Ina ta magana amma kinyi zirfi cikin tunani,meke faruwa ne"

Ajiyar zuciya ta sauke me ƙarfi tana dafe kirjin ta,"Hmm,babu komai Nafisa,wai ina imagine ne a kan faruwar wani lamari mai tsayi,kin san kuwa a kan waye"

Girgiza kai tayi"A'a "

"A kan Young Ustaz"

Ɗan zaro ido tayi"Young Ustaz kuma?

"Eh,wai ina imagine ne yace ma Mam baya so na,bai yarda da ni ba,kinsan wani abin mamaki"

Nan ma girgiza kai tayi domin da tafara kulle mata kai,

"Wai har ina dab da barin wannan gidan bayan na kammala aikina,amma sai gashi kin tasheni daga mafarki na,naso ace naga yanda abin zai kasance," Kallon ta tayi"me yasa kika min magana?

"Ohh yi hakuri,dama nazo wucewa ne na hange ki anan,shi yasa na zo"

Matsawa tayi "zauna anan"

Zama tayi kusa da ita"na gode "

Jin an kara buɗe ƙofa an fito ne yasa ta kalle wurin,
Mutumin dazu ne dai ya kuma fitowa ya tafi,
"Waye wannan"

Kallon wanda ta nuna mata tayi"Yaya Shamsuddeen kenan"
"Amma ba'a giddan yake ba ko"
"A gidan yake,baƙi taɓa ganin shi a shiyar ku ba?
" A'a "
"To ai shima yaron Abbu ne,sai dai shi Mamar shi da ban ne,"
Cikin mamaki take jinjina kai,domin a list ɗin da aka bata babu sunan shi a ciki"to shi ina Mamar shi"
"Gaskiya ban sani ba amma dai a yanda naji sun rabu da Abbu"
"Me ya raba su?
Kallon mamaki take mata" Ya za'ayi in sani"
"Oh haka ne,never mind me,amma suna kama sosai da Ustazu,dan dazu ma na ɗauka shi ne,har na tafi mafarkin zaune"

Dariya tayi"mafarkin zaune ba,to bani labari akan mafarkin ki,"

Ita ma dariya tayi"kinsan wani lokaci mutum na zaune haka kurin zai kama imagining wasu abubuwa na faruwa,faɗa min halin Ustazu da yayanshi "

Wannan karon ma sai da tayi dariya"ɗan Allah Biba,karki ɓata ma young Ustaz din mu suna,wai ustazu"

Tabe baki tayi ba tare da tace komai ba,
Mai do fuskarta tayi ta kalle ta"ya cika girman kai,sai ya dinga kallon mutane kasa_kasa"

"La aikuwa Yaya Suraj bai da matsala,kawai dai kin mai rashin fahimta ne,kuma kinsan wani lokaci idan ba wai ka zauna da mutum bane baka sanin halin shi,daga shi har Yaya Shamsuddeen wallahi ba su da matsala,ɗan garama yaya Suraj wani lokaci zai dan maka magana,amma shi kuwa Yaya Shamsuddeen da wuya ki ganshi cikin gida,"

"Waɗancan ɗakunan kuma nasu waye"

Nuna mata take da hannu "kinga a gefen na yaya Suraj na Nuriddeen ne,sai na Ibrahim da Salman"

"Gidan akwai mutane har haka ne,su kuma ya'yan mutum ɗaya ne su?

" A'a,kawai dai bari na miki ƙwari_ƙwari,a yanda dai na sani,ita Kaka da kike gani Mijinta babban malami ne,a hanyar shi na zuwa wa'azi Sudan suka yi hatsarin jirgi ya rasa ran shi,
Tana da yara uku maza ɗaya mace,
Abba Al-Mustapha shine babba yana da mata daya mai suna Hajiya Rahama,suna da yara uku,Yaya Ibrahim,sai Aunty Hajjo wacce tayi aure yaranta biyu,sai karamar su Zainab,
Abba Al-Mustapha Custom ne.

Na biyu kuma shine Abbu Sufyan,na faɗa maki ya taɓa aure amma sun rabu da matar wanda suna da yaro ɗaya da ita,shine Shamsuddeen,daga baya kuma ya aure Malama Hafsat wacce ta haifa mashi yara biyu,Yaya Suraj sai ƙanwar su Amira,
Abbu Babban malami ne kuma ɗan kasuwa,shi kuma yaya Suraj duk da babban malami ne kamar mahaifin shi amma yana aiki ne da EFCC yana amsan Albashi mai tsoka.

Na uku kuma Dady Ahmad shi kuma Soja ne babba,bai cika zama a gida ba yaran shi biyar,Nurudeen,sai Aunty Atika wacce wata biyar kenan da akayi auren ta,sai Aunty maijidda,sai Salman da Bilki "

Na huɗun su kuma Goggo Hasiya,ita ta taba aure sai dai a yanda na samu labarin mijinta ya ɓace ba'asan inda yake ba,sai dai wasu na cewa guduwa yayi ya barta da ya'yanta,wasu suce sace shi aka yi,Allah kaɗai yasan gaskiya sai su,tana da yara biyu,Hadiza da Khadija, duk suna zaune ne a nan gidan ita da yaranta,sannan kuma kiyi hankali da ita dan masifaffiya ce na karshe,
Sannan ko wani shiya suna da ma'aikata,
Wannan shine labarin mutanen gidan,Halin su kuma a hankali zaki fahimce halin ko wanne daga cikin su,sai dai abinda zan faɗa maki shine kiyi hankali da Nurudeen da Ibrahim,domin ba kananan yan son aci duniya bane"

"Me kike nufi"
"Karki damu a hankali zaki gane me nake nufi"

Ajiyar zuciya ta sauke tana mikewa "kinga tashi mu tafi,gashi har after Nine O'Clock na safe,bari na je na fara shirin daura girki,na gode da labarin ki"
Dafata tayi "babu damuwa"
daga nan kowacce ta wuce ɓangaren da take aiki,

Har zata shige daki sai kuma ta dawo ta tsaya a tsakiyar falon tana kare ko'ina kallo,haka kurun zuciyar ta ke raya mata akan ta duba ta gani kar ya kasance tunanin ta na Camera ya zama gaskiya,

Kicin ta shiga ta dauko abin cire yanar gizo-gizo tare da dogon kujera,
Hawa tayi tana yi kamar mai cire kura amma kuma dubawa take yi,
A haka ta gama zagaye lungu da sako na shiyan sai dai ko alamun camera babu,
Ɗauko kujerar tare da sandar tayi ta shigo falon tana tsaki,"kai jama'a a duniya ba kada maƙiyi daya wuce zuciyarka,"

Jin muryar Ammi na kiranta ne yasa da sauri ta juyo tana amsawa,

"Je ki Ɓangaren Goggon su ki kira min Amira,ta zo ta tayani gyara dakin Abbu kafin ya iso dan yana hanya,ki ce tayi sauri"

"To Mam"
Fita tayi tana bin ta inda Nafisa ta nuna mata nan ne ɓangaren goggon su a dazu,
Tana isowa ɗan hanyar da ya raba shiyan Goggon da hanyar shiga shiyan Samarin gida ta kusa cin karo da Nurudeen,
Da sauri ta matsa baya tana rabewa gefe dan bashi damar wucewa,"Sorry ban kula da kai ba"

Murmushi yayi "koda ma kin bige ni kin bi ta kaina ai babu damuwa domin kin isa kiyi"

Ita sai bata bashi amsa ba,

Ba zato sai ganin shi tayi a gabanta yana daf da ita wanda har suna iya juyo numfashin juna,
Riƙo hannun ta yayi yana juyawa cikin wani irin salo irin na mazaje waɗanda suka kware wurin yaudarar zuciyar ƴan mata"Ya hannun naki Bib,da fatan ya dai na maki zafi"

Kafin ta buɗe baki ta bashi amsa ne suka ji taku a bayan su,
Shi dai bai juya ba,amma ita da sauri ta juya,sai dai ganin mai wutowa ne yasa ta dauke numfashi tana Freezing domin ba karamin bugawa zuciyar ta tayi ba,

Ko kallon in da suke bai yi ba,saima raɓawa ta gefen su da yayi ya wuce abun shi,
Da ido ta bi shi har ya ɓace ma ganin ta,
Ji tayi ya shafa fuskarta,"karki damu da wannan dutsen,shi bashida wata sha'awa a rayuwar shi,kar ki ji tsoro domin ba mu bane a gaban shi"

Cikin sauri ta ture shi baya tana matsawa sannan ta juya cikin sauri ta bar wurin,
Tana jin gabaɗaya zuciyar ta a jagule,
Tura kofar falon tayi tare da yin sallamah,wanda bai fito sosai ba,
Jin shiru ne yasa ta shiga cikin falon inda ta tarad wasu yan mata su Uku zaune sai hira suke cikin kwanciyar hankali ga kayan ciye-ciye a gaban su,
"Sannun ku,,Amira Ammi na kira"ta faɗa tana juyawa ba tare da ta jira jin amsar su ba,

Har ta kusa barin falon taji an daka mata tsawa tare da cewa" Ke jakar ina ce da zaki shigo mana falo babu sallamah,babu gaisuwa kawai sai ki faɗi abinda ke bakinki ki wuce kamar wata Tunkiya "

Cikin mamaki ta kalle yarinya da ke fadar wannan mummunan kalami a kanta wacce bata wuce tsaranta ba, wato Zainab,dama haka take da fadin Rai,

Nuna kanta tayi da hannun ta"da ni kike"dan ta juya gefe da gefe bata ga kowa ba,

Takowa tayi gaban ta "in ba dake ba da wa zanyi,wai me yasa ku ƴan aikin nan kuncika raina mutane ne,ko dan kunga ana sake maku"

Hadiza dake zaune ne tace "baƙi ga irin kallon da take maki ba"

Amira ce ta tafi "ku kuma da kanunan magana...

Kafin ta ƙarasa ne suka ji muryar goggo na fadin " Meke faruwa "tana karasowa inda suke.

Cikin shagwaba Zainab tace " Goggo wannan mai aikin ne muna zaune kawai sai shigowa tayi babu sallamah,sai ce mana tayi sannun ku,kamar taganmu a gadon asibiti "

"Ni dai matsamin ki ga in wuce" Cewar Amira"goggo na tafi Ammi na kira na"

Hannu kawai ta daga mata,
Kallon Biba take daga sama har katsa"ya sunan ki,awani bangare kike aiki,nawa ake biyanki "
Chapter 13 · 0% Book details