Sashe 44
Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ranta fa ya fara ɓaci da wannan rashin kunyar na yarinyar"Amira,ko kinki ko kinso ni din matar yayanki ne,idan baki karɓe ni ba wannan damuwar ki ne tunda yayanki ya karɓe ni ya kuma haɗa shimfida dani,uwarki ta karɓe ni,idan kin ga dama ki kaimata wayar idan kin ga dama karki bata,wawuya Stupid"tana jin lokacin da zata sauke wayar ana tambayar keda waye ke waya,ta sauke wayar tana faɗin ai Gara na karasa lalata alakar dake tsakanin mu na san cewa bama shiri gabaɗaya,
A can ɓangaren kuwa,ji tayi ranta ya bala'in baci har balle ce mata wawuya da stupid ɗin data yi,gashi ta sauke wayar balle ta rama ko za ta ji sanyi,
Jin tambayar da Ammi ke mata ne yasa idanun ta cika da Hawaye ta mika mata waya"Habiba ce,wallahi Ammi sai nama yarinyar nan rashin mutunci,cemin da tayi wawuya harda cemin stupid "
"Ta birgeni,dama ta haɗa maki da Doluwa tunda baki gane komai ba"
"Ammi!"
"Yes na,oya tashi ki barmin daki bana son surutu"
Cikin jin haushi ta tashi ta bar dakin tana turo baki,
Girgiza kai kawai rayi tana ƙara kiran wayar Habiban,
Ɗauka tayi da sallamah tana gaida Ammi,ita ma amsawa tayi,sannan tace"kin kira bana kusa"
"Eh Ammi dama baki aka yi kuma sun ce zuwa anjima na kawo su wurin ki,so karki ganni da baƙi shi yasa na kira ki"
Dan murmushi tayi"na gode Habiba,amma su waye?
"Kanin Kakar Suraj ne da yaran shi,"
"Kanin kakar Suraj?
" Eh"
"Kin tabbata"
"Eh to ni dai yanda Bala ya faɗa min kenan,sannan na taba ganin hoton shi tare da na Kaka"
Shiru ne na ɗan wani lokaci ya ratsa wayar wanda har sai da tayi tunanin ko kiran ya katse ne ta shiga fadin Hello,
Jin ta sauke numfashi ne yasa tace "ok sai kin zo"
"To Ammi"
Sauke wayar tayi tama tunanin yaufa ta so taje Wudil,amma ba komai taje gobe.
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*44*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Koda suka kammala cin abinci kwanciya suka yi domin su samu su huta,
Sai zuwa yamma sannan suka shirya,Direba ya jasu har gidan su Ammi,a falon Kaka akai masu masauki,sannan Ammi tazo suka gaisa,cikin mutumtawa,
Kuka Pa ya saka yana yabon Suraj da harshen turanci,ita sam bata ma taɓa tsammanin kaka na jin Turanci ba sai yau,in da take ta bashi haƙuri tana kuma tsanar dashi halin da ake ciki,
Cewa yayi Gobe zasu tafi Legos din suje su samu su Abbu dan asan halin da ake ciki,
Babu zato ta ji Ammi tace"sai ku tafi tare da Habiba dan ko ba komai ya kamata tana kusa"
Cikin sauri ta kalle ta,sai dai kauda kai tayi tana jiran ta ji me kaka zata ce,
Kamar zata musa sai kuma tace "to ba damuwa sai su tafi tare"
Ita wallahi ba haka taso ba,dan haka tashi tayi tace masu tana zuwa ta koma shiyan Ammi tayi zamanta,
Sai da zasu wuce ne Ammi ta saka aka kirata sannan suka tafi,
Direba na sauke su ta amsa makullin mota tana kokarin shiga,budurwar da suke kira da Nadiya ce tace "zaki kuma fita ne?
" Eh"ta bata amsa,
"Zanje " Ta faɗa tana ƙoƙarin zagayawa ta shiga mota,
Da sauri ta tada motar"Sorry ana jira na ne yanzun zan dawo"ta faɗa tana fita daga gidan,tunda abun ya zama haka gara ta tafi duk dare ta dawo,
Da Marp ta yi amfani ta tafi Wudil,
Ranar ba ita ta dawo ba sai ƙarfe kusan sha-biyu na dare,dan ba ƙaramin wahala tasha ba,
A matukar gajiye ta shigo gidan kai tsaye ɗakinta ta buɗe wanda tana tura ƙofar hayaƙi ya fara turnike mata fuska,
Ƙara hasken wutar dakin tayi tana kallon ta cike da mamaki,
Tana zaune a kasa ga kwalin sigari a gabanta ga kullin wiwi irin yanda suke yin shi kamar taba da kuma ƙananan kwalaben giya masu ƙarfi da tsada guda biyu,sai shan abinta take yi cikin kwanciyar hankali,
Ganinta kuma bai saka ta fasa abinda take yi ba,
Ɗan dariya tayi"Sorry Beb na bata maki daki ko?
Shigowa tayi ta faɗa kan gado tana sauke ajiyar zuciya"no is ok"
"Thank you"
Bata ce mata komai ba sai lumshe ido da tayi tana nazarin maganar da suka yi da Dattijon Mutumin,wanda ya riga ya san da zuwanta,to ta yaya akayi ya san cewa zata zo,tuno irin maganar da suka yi ne yasa jikinta ƙara yin sanyi,
Wannan wani irin aiki ne take yi,abun yana kama da ba mutum ɗaya take ma aiki ba,
Wannan wani irin rikici ne ta jefa kanta a ciki haka,
Jin warin Sigari ta wurin kanta ne tasa ta dago ido tana kallon ta,
Mika mata wanda ke hannun ta tayi"wannan yana rage damuwa "
Tashi tayi ta sauko katsa ta zauna kusa da ita sannan ta amsa ta fara zuka cikin kwarewa,
Dariya ta saka cikin jin daɗi ta shiga faɗin "Ashe ke ma kin iya har haka?
"Nama fi nan"
"Bari kiga irin yanda muke sha a garinmu"
Wani irin wasa da hayaƙin take yi sosai,
"Gaskiya naku na daban ne,"
"Sosai ma kuwa,kuma ina shanye kara shida zuwa takwas a rana"
"Kai amma kinsan yawan shanta yana kawo illa"
"Ban damu ba,sai dai ina shan maganin da bazata min illa ba"
"Haka ne,"
"Kefa?
" Me kenan?ta tambaya,
"Guda nawa kike sha a rana,Kwali daya ko biyu"
Dariya tayi "ina bai wuce sau daya a sati ba,ina kiyaye lafiya ta"
"Amma dai ke matsoraciya ce,to wannan fa?ta fada tana mika mata wiwi,
Girgiza kai ta yi" A'a bana shanta ita da giya "
"Me yasa?
" Kawai dai"
"Ki gwada mana?
" A'a ke dai sha kawai"
"Kina shekara nawa kika fara shaye-shaye?
"Goma sha-biyar"
"Wow that was so early"
Jinjina kai tayi "sosai ma"
"Ni sai da na kai 20 years,kuma wani saurayi na ya koya min gashi yanzun mun rabu dashi, he break my heart,ban cin ina son shi sosai"
Shafa bayan ta tayi "Sorry ai haka suke ƴar uwa they easily break our heart,ni ma akwai wanda nake so sosai,i eving Love him more than my life,ban taba son wani ba irin yanda nake son shi,but in the end sister,he break my heart more than the way glass use to be break in to pieces,irin yanda bazai taɓa haɗuwa ba har abada,he disappointed me,but babu komai"
"Akwai"
Girgiza kai tayi"babu"
"Idan babu why are you Crying"
Shafa kumatunta tayi,ita san bata masan tana hawaye ba,dan murmushi tayi tana share hawayen ta"babu komai,na bar su da Allah "ta faɗa da Hausa wannan karon dan dama da turanci suke magana,
" Har yanzun kina son shi?
Shiru tayi tana sauraron bugun zuciyar ta"ƙila"
"Me hakan ke nufi?
" Ban sani ba tukun na"
"Ke mutuniyar kirki ce,in faɗa maki wani abu?
Lumshe ido tayi ta buɗe tana jin yanda zuciyar ta ke zafi" Ina jinki"
Dan matsowa tayi Kusa da ita dai_dai kunnen ta"Be careful with my Father and brother"
Razo ido tayi tana shirin yin magana ta daura mata hannu a baki,tare da nuna mata ƙofa da hannu,
Bin hannun tayi da kallo inda idon ta ya sauka akan inuwar mutum,
"Suna iya kashe mutum,na taba gani kuma suka ce idan na faɗa zasu kashe ni,kema ki yi a hankali"ta raɗa mata a kunne kuma
Gabanta ne ya shiga bugawa da karfi,ita ma cikin raɗa ta tace" Yaushe zaku tafi?
"Ban sani ba,kin ga manta dasu,ni dai wallahi kin min i Love you" Ta faɗa da ɗan karfi cikin alamar fitar hankali
Kwantar da ita gefe tayi"kwanta ki huta"tashi tayi ta nufi bakin kofa duk da har lokacin tana ganin inuwa a wurin,tsoro take ji sai dai ba zata fasa zuwa dubawa ba,
Tana bude ƙofar sai dai ba kowa a wurin,dan lellekawa tayi nan ma ba kowa,maida ƙofar tayi ta rufe ta koma ta kwanta bayan ta kashe wutar dakin ta kwanta gefen Nadiya,
Agogon wayar ta ta duba ƙarfe biyu na dare har da rabi,
Lumshe ido tayi,ji take zuciyar ta kamar an ɗauko dutse mai matuƙar nauyi an Daura mata,abubuwa ne da yawa ke mata yawo a cikin zuciyar ta,
Idan ta tuna maganar ta da Wannan dattijon,da kuma hiranta da Nadiya har zuwa kalamanta na karshe sai ta rasa gane ina ne Asalin hanyar daya kamata tabi,sai ta tsince kanta acikin duhu irin wanda Ammi ta faɗa har kuma take mata fatar yayewar shi,to sai dai ta rasa koda ƙaramin hasken da zai haska mata hanya domin taimaka mata wurin niman madaidaiciyar hanya,wanda zai iya bullar da ita,har ta kaita ga fita tarkon da take ganin tamkar ɗana mata shi akayi da gangan aka kuma sakata aiki a kanshi,
A wannan daren bacci barawo ne kawai ta samu damar sace zuciya irin nata mai cike da sake sake.
Washegari koda ta tashi ƙarfe bakwai har ta wuce,dan haka wanka tayi sannan tayi sallah ta tayarda Nadiya da ƙyar,
Fitowa tayi ta ba Bala sako akan ya amso abin kari,sai dai ma har ya riga ya gama girkawa,
Pa ne kawai zaune a falo,dan haka cikin girmamawa ta gaishe shi,amsawa yayo cikin sakin fuska,har ma yana tambayarta ƙarfe nawa jirginsu zai tafi,
"Ƙarfe tara"ta bashi amsa,
" To kiyo kokarin saka Nadiya ta shirya da wuri karta bata mana lokacin "
Da to kawai ta amsa mashi sannan ta koma daki,
Samun ta tayi har ta kammala wanka tana saka kaya,
Zama tayi kusa da ita,"barka da safi Nadiya "
Murmushi ta sakar mata"barka,da fatan kin tashi lafiya "
"Lafiya,na ma zata baki tashi ba"
"Ina son in ga Suraj shi yasa na tashi da wuri,"
"Idan kin kammala ki fito mu ci abinci"
"A'a kuci kawai ni bana cin abinci da safe haka"
"Ok"ta fada tana mikewa,