Sashe 61
Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hakan ne kuma ya kuma faruwa lokacin cin abincin rana,nan ma bata fito ba har suka kammala,kuma ko in da suke zama a falo suna kallo ta zo ta same su nan ma har suka gaji da zama suka fita basu ganta ba,
A lokacin cin abincin dare ne suna zaune har da Baba,Abdulrahman ya kasa daurewa,kallon Mama tayi"Mama wai Salma na gidan nan kuwa?
"Tana nan me ka gani?
" Naga duk yau ban ganta bane tun safe har wurin cin abinci "
"Kila bata jin cin abincin ne shi yasa ka ga bata fito ba"
"Amma daxu fa da rana na tambaye masu aiki suka shaida min bata ci abincin safe ba dana rana,kuma gashi na dare ma bata fito ba,kin San Salma tana da Ulcer " Cewar Abdulmajid,
Ba tare da Baba yace masu komai ba ya mike ya doshi dakin Salma,duk da kallo suka bishi,bayan kamar mintuna uku sai gashi ta fito cikin tashin hankali dauke da ita hannu kamar gawa tana jijjiga ta tare da kiran sunan ta,sai dai ina ko motsi bata yi sannan gashi duk jikinta amai ne,
Suma zabura suka yi suka bi bayan shi,amma ko kula su bai yi ba dan kafin ma su ƙarasa in da yake har ya saka ta a mota taja motar sun fita gidan,
Cikin tashin hankali Mama tace"Abdulrahman dauko min makullin mota yanzun nan"
"Mama yana hannun direba"
Cikin ihu tace"na mota na nace ka ɗauko min"
Ganin kamar shima a ruɗe yake yasa da gudu Abdulmalik yaje dakin ta ya dauko mata makullin,
Ita ta tuka su har Asibitin da suke zuwa ganin likita,
Koda ta isa ana ƙoƙarin Daura mata ruwa shi kuma Baba na tsaye ko kallon su bai yi ba,
Kokarin karasawa in da take suke ya dakatar dasu"ku dakata"
Duk tsayawa suka yi suna mashi kallon mamaki,
"Ina zaku je?wa zaku je dubawa?
Kasa bashi amsa suka yi,
" A lokacin da kuka tabbatar da bata ci abincin safe ba amatsakin na uwarta me ya kamata kiyi?sannan da kika ga bata fito ko da falo ba shima me ya kamata kiyi,har iyau bata fito cin abincin dare ba shima me ya kamata kiyi,?duk babu abinda kika yi saboda ba ita bace a gaban ki ko?
Hawaye ta fara,cikin sanyin jiki take kokarin yin magana ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu"ba kida wani uzurin da zaki fada min"
"Baba" Cewar Abdulmajid,
"Karka kira suna na,a da ina ɗauka ko bayan rai na zaku iya kula da kanwar ku ashe na yi kuskure,na yi kuskure ina ɗauka kuna mata ƙauna fiye da kanku,ban sani ba sai yanzun,amma ba komai kun ma kanku,domin tun da abin ya zama haka Gara kawai na aura mata Yusuf na mallaka masa wani kaso daga cikin dukiya ta tayanda zai iya kula min da ita ko bayan rai na"
Wani irin ihu Mama ta saka tana cakumo wuyar rigar shi,Inna'lillahi wainna'ilaihirajiun,domin abune da tunda suke tare da iyayen su basu taɓa ganin makamancin haka ya faru ba a gidan su,duk gaba ɗaya cikin tsoro suka ja baya,
"Wallahi ba ka isa ba,ba dai Yusuf ba,wannan ba zan yarda ba,so kake ka cuce rayuwar ta kamar yanda ka cuci nawa rayuwar! So kake ta kare wurin aikata aikin da zata din ga danasani!a da nayi tunanin ba zaka taɓa yarda ba tunda kasan komai,ba zaka taɓa bari ba,amma shine da kanka kake faɗin haka?ban taba sanin baka kaunata da zuri'a taba sai yau,kuma Salma yata ce Ni na haifa abuna dan haka ko da zata mutu ba zata taɓa auren wannan yaron ba"
"To ai kuwa zan ga uban da ya isa yasa a fasa,dan haka ki ma je gidan ku na sake ki saki daya"
Babu alamar tsoro ko dana sani sai ma ƙoƙarin ƙara shaƙe mai wuya da take yi"ba saki daya ba,Allah yasa kamin saki goma ba zan taɓa yarda da wannan auren ba"
"Tunda haƙa kika ce to na.... "
Cikin sauri Abdulrahman ya kulle mai baki yana fashewa da kuka tare da girgiza kai"dan Allah! Dan Allah Baba ya isa haka ba sai ka ƙara cewa komai ba"
"So kuke mu tsane ƴar uwar mu,wannan abun da kuke yi duk saboda auren wannan Yusuf din ne,abinda ba mu taɓa ganin kun yi ba sai gashi yau kun yi shi kuma a gaban jama'a,tir da wannan auren daga ita har shi Fuck them" Cewar Abdulmajid yana barin Asibitin domin dama shi zuciyar tsiya ne dashi,
Zame hannun tayi daga jikin shi tana kallon shi a karo na farko wanda sai lokacin hawaye ya sauko a idanun ta"kaji daɗi!yanzun ai kaji daɗi "tana gama fadar haka ta juya ta bar Asibitin tana tafiya tana sharan hawaye ba tare da ta damu da kallon ta da mutane ke yi ba.
Dogon tsaki yaja ba tare daya kalle su ba ya shige dakin da take kwance,
Jawo kujera yayi ya zauna yana shafa kanta,barci take yi tana sauke numfashin wahala,a zahiri ya furta "Allah kadai yasan iya wahalar da kika sha,in dai Yusuf ne sai dai tayi duk abinda zata yi amma sai kin aure shi,idan ya so sai...
Shiru yayi yana busar da iska ba tare da ya karasa faɗar abinda ke bakin shi ba,
A haka ya zauna da ita har sai da ta farka bayan barcin awa uku da tasha.
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*61*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
A hankali ta fara buɗe idanun ta da suke mata nauyi,ganin yanda yake zaune yana ɗan gyan-gyadi ne yasa ta kira sunan shi a hankali "Baba"
Buɗe ido yayi da sauri yana gyara zaman shi tare da ƙara riƙe hannun ta"sannu Salma,kin tashi?ya jikin naki?meke maki ciyo yanzun?
Dafe gefen kanta tayi tana ɗan lumshe ido "Baba kai na,kaina na ciyo"
"To bari na kira Doctor ina zuwa" Da sauri ya sake hannun ta ya fita,ba jimawa sai gashi ya shigo tare da wani Doctor dake bin shi a baya,
Dubata likitan yayi sannan ya dawo da kallon shi kan Baba"babu wani damuwa nan da lokaci kaɗan ciyon kan zai sauka,sannan zuwa anjima zaku iya komawa gida,sai dai a dai na bari tana zama da yunwa,sannan ta rage cin soyayyen abu"
"Insha Allah za'a kiyaye likita"
Ganin likitan ya wuce ne yasa ta kalle shi"Baba ina su Mama da Yaya?
Komawa yayi ya zauna"ki kyale su,yanzun ba su ba ne a gaban mu,ki fara samun sauƙi shine abu mai muhimmanci,sannan ba dai kina son Yusuf ba?
Jinjina kai tayi,
"To karki damu zan aura maki shi cikin satin nan matuƙar zaki iya haƙuri dashi"
Bata masan sanda ta saki laulausar murmushi ba"zan iya Baba,you are the best father in the world"
Murmushi shima ya mai da mata,yana raya abubuwa da yawa a ran shi game da wannan lamarin,
Shi ya zauna da ita har drip din da aka saka mata ya kare aka cere sannan aka sallame su,
Ko da suka koma gida bata tarad da kowa ba kuma bata damu ba,saboda ta san yanzun ba harkar ta suke shiga ba,kila ma sun kwanta ko,tunda a lokacin ƙarfe goma sha ɗaya na dare,
Sai da tayi wanka da ruwan dumi sannan ta kwanta kan gado tana sauke numfashi yayin da take jin wani irin farin ciki yana ratsa zuciyar ta,
Lumshe ido tayi tana tunanin irin rayuwar da zasu gudanar tsakanin ita da Yusuf,
Zuwa can kuma wani tunani ne ya fado ranta,shine me yasa take son Yusuf,ƙara lunkumewa tayi a cikin makeken gadon ta yayin da ta shiga tuno abubuwa masu yawa a kanshi,wanda idan da ace za ta zauna ta natsu tayi nazari data fahimce irin haukar data ke yi,sai sam ko kaɗan bata gani ba sai ma ƙara son kasancewa dashi da take ji yana ƙaruwa a zuciyar ta,
Da ire-iren waɗannan tunanin barci ya dauke ta.
Washegari da safe sai da ta makara wurin yin sallah Asuba,
Tana zaune saman darduma tana karatun Kur'ani sai ga Abdulrahman ya shigo dakin da sallah,
Ganin tana karatu ne yasa ya nime gefen ta ya zauna yana jira ta idar,
Addu'a tayi suka shafa tare,
Juyowa tayi in da yake zaune"barka da safiya Ya Abdul "
Duk da fuskar shi ya bayyana damuwar dake cikin zuciyar shi hakan bai hana shi ɗan sakar mata murmushi ba" Ya jikin naki?
"Naji sauki sosai"
"Allah ya ƙara maki lafiya"
Da Amin ta amsa,
"Kiyi haƙuri bamusan rashin lafiya kike yi ba,mun ɗauka kawai baki son cin abincin ne shi yasa ba mu je mun duba ki ba,ina fata zaki yafe ma yannin ki"
"Yaya har yanzun fa Mama bata zo ta duba ni ba,haka ma su Yaya,ta yaya zanji daɗi,a can Asibiti ina tunanin idan na farka zan ganku tare da ni,amma banga ko mutum ɗaya daga cikin ku ba,ban ji daɗi ba,ko dai kun tsane ni ne,kun dai na sona akan kawai na nuna zaɓi na"
"Ba haka bane Salma,kiyi haƙuri ke ma kinsa ko me kika mana ba za mu taɓa tsanar ki ba,kuma koda Baba ya kaiki Asibiti mun je,mun biku har da Mama,sai dai fushin da yayi ne yasa ya hana mu shiga mu ganki,shi yasa muka dawo gida"
"To amma Mama fa,kalli fa har gari ya fara haske amma ko lekowa bata yi ba"
"Ai bata kwana a gida ba"
" Oh tafiya tayi ta bar ni? Tana fada idanun ta na kawo ruwa,
"Ba tafiya ta yi ba,a jiya ne aka kira ta akan jikin Maman ta ya motsa,shine ta tafi ta duba ta"
Ya faɗa mata haka ne kawai domin ba zai iya ce mata saboda ita iyayen su suka sami matsala ba,
"Su yaya Abdulmajid fa?
" Zuwa anjima duk zaki gansu,sannan yanzun ki samu ki kwanta ki huta zuwa anjima sai mu tafi ki buda Mama"