← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 96

Sashe 21

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin diran motoci a harabar gidan ne yasa ta tashi daga kwancen da take ta buɗe wundan ɗakinta wanda zata iya hangan harabar gidan duk da yayi nisa sosai ba zata iya tantance mutanen dake wurin ba,
Motoci ne guda biyar wannan karon,sun ɗan jima daga bisani kuma taga sun guya sun bar gidan,
Komawa tayi ta kwanta,tana aiyana ƙila ya dawo ne,
Ganin har ƙarfe shida tayi ne yasa ta tashi ta fito daga shiyan su,kamar zata nufa shiyan kaka,sai kuma ta juya tayi hanyar Boys Quetta,
Tasan wannan lokacin duk mazan gidan basa nan,dan haka daga tsayen da take ta kunna wutar Sigari ta saka a baki,kyakkyawar zuka ta masa tana busar da hayaƙin tare da lumshe ido,
Duk da tasan ba ko yaushe take sha ba,amma a ƙalla a sati tasha sau biyu,to kuma gashi tunda ta dawo ko sau daya bata sha ba sai yau,shi yasa take jinta a sama,

Tunda ya nufo sashin su yake jin warin Taba,abinda yafi tsana a rayuwar shi,ko kaɗan baya so,
Mamaki ne ya kamashi domin bai taba tunanin a gidan a kwai mai shanta ba,dan bai taɓa jin makamancin warinta ba,
Duk da duhun Magriba ya gabato amma yana iya hanyan ko ina na wurin,

Idanun shi ne suka sauka a kanta,yanda take busa hayaƙin sama cikin ƙware da kuma yanda ta riƙe a hannu,wannan shi zai tabbatar maka da cewar ita din ba yar koya bace,
Gabaɗaya ya kasa yarda da abinda yake gani,Mace! To yana dai ji a labarai,

Jikinta ne ta bata kamar ana kallon ta daga ta wani wurin,dan haka da sauri ta shiga juye_juye,sai dai bata ga kowa ba,
Ajiyar zuciya tasauke ta yarda karan sagarin ta murje da ƙafa,kafin ta bar wurin.
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*23*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Komawa shiyan su tayi,sai da aka yi Sallah Isha'i sannan ta fito zata shiyan Kaka,
Ta kusa shiga shiyan ne ta ji an finciko ta anyi baya da ita an jin gina ta jikin bango,
Kasancewar wurin akwai ƙarancin haske hakan yasa bata gane ko fuskar waye ba ne,sai da ta ji muryar sa yana sun sunan wuyanta,cikin muryar da zai nuna maka irin shaukin da mutum ke ciki yace"Baby na ina kika tafi kwana da kwanaki,sannan kin dawo kin kuma hana ni ganin fuskar ki"

Oh sai yanzun ta dago muryar shi,kauda fuska tayi,domin bata son ta nuna mashi halinta,in ba haka ba,wlh da in ta rike shi sai ya gudu da kafar shi,"Nurudeen bana son haka"ta faɗa tana ƙoƙarin barin wurin,
Riƙe mata hannu yayi yana ƙoƙarin jawo ta baya "akwai maganar da nake son na faɗa maki"

"To sake ni sai ka faɗa min"
"Kina da kyau"
"Na sani" Ta bashi amsa kai tsaye,
"An taba faɗa maki"
"Sosai ma"
Murmushi yayi"wannan ba abin mamaki bane idan aka yi duba da cancantar ki"
Kafin ta bashi amsa ne suka ji daga bayan su wani sanyayyan murya yace"Excuse me "

Ganin wanda yayi magana ne yasa gaba ɗayansu shan jinin jikin su,saboda shi rike yake da hannun ta,cikin sauri ya sake ta,yana matsawa gefe,ita ma haka,amma shi gogan ko a jikin shi,sai ma raɓawa da yayi ta gefen su ya wuce ya bar su da kamshi,
Ganin ya shige shiyan Kaka ne yasa da sauri ta juya ta bar wurin,dan Gara kawai ta koma shiyan su,ita bata san Me yasa a duk lokacin da zasu haɗu basa haɗuwa da sa'a ba,yanzun ba sai ya mata kallon mara da'a ba,
Wani zuciya nata ne ya bata amsa kai tsaye,dama da'a gare ki,nan take ta saki murmushi,domin rabon ta da wannan kalmar shekara biyar kenan daya wuce.
Tana shiga daki faɗawa tayi kan gado tana lumshe ido,kome take tunani?Allah kaɗai yasan abinda ke gudana a zuciyar ta,daga bisani kuma sai naga kamar hawaye na gangarowa daga idanun ta data lumshe,sai dai kafin na tantance sai gani nayi ta kifa fuskarta cikin filo,sai kuma a hankali shesshekar kuka ke tashi,wanda idan ba wai ba ka saurara sosai bane ba zaka taba tsammanin ana yin shi ba,ita wannan ba komai bane a wurinta face abinda ta saba komai tsayin dare sai yishi,in dai wannan kukan ne,
Jin alamar kamar za'a shigo ne yasa da sauri ta gyara natsuwar ta,tana goge fuska da sauri,
Amira ce ta shigo da sallamah"Biba wai inji Ammi ki fito ki yi wanke-wanke an kama"

Mikewa tayi"ok gani nan tafe"
Cikin natsuwa take aikinta har ta kammala yanda kasan ba ta da wani damuwa domin fuskarta a washe yake,
Ba ta yarda masalarta ko damuwarta ya nuna a fuskar ta,abu ne mai wuya,
Wannan tsakanin ta da zuciyar ta ne.
Tana kammalawa daki ta shige ta kwanta,dan ta kammala aikinta na yau sai kuma gobe idan Allah ya kaimu,

Washegari ma bayan an idar da sallah ne ta fito ta shiga gyaran gidan sannan ta daura break Fast,Waina da Miya tayi,wanda ya ji kayan haɗi,
Koda ta kammala har takwas ta wuce,dan haka daki ta koma tayi wanka,dan tana idar da sallah suke gaisawa da Mam,
Daukar na kaka tayi ta kai mata,
Koda ta dawo bata lura dashi zaune ba,sai da Ammi ta ce"Biba zubo ma Suraj Waina"

"Ammi wa yayi Waina? Ya tambaye ta,
Kasancewar tasan yana matukar so,cikin murmushi tace" Biba tayi,kuma gashi yayi laushi yanda kake so"

Daukar wayar shi dake gefen shi yayi yana mikewa"Ammi ki ce ta barshi kar ta zubo,yau bana jin cin waina "

Kallon mamaki take mai,domin tasan yanda yake son waina ko ya ko shi ne sai ya dauki guda daya ya saka Albarka,
"Yau kaine baka jin cin waina?
Murmushi ya sakar mata" Bari na tafi na gaida Kaka Ammi,zuwa anjima zan shigo"
Jin jina kai tayi,tana binshi da kallo,
Ita dai tana kicin tana jinsu,
Koda yaje shiyan Kaka ma haka ne ta faru,domin tana mai tayi ita ma ce mata yayi baya jin cin masa,

Ta gaji da zama ita kaɗai,gashi duk yaran gidan sun tafi makaranta,dan haka fitowa tayi ta zauna ta gefen Barandar su,ganin kamar rana yana son ya takura mata ne yasa ta canja wurin zana zuwa ta takanin shiyan Goggo da Hajiya Rahama,daga inda take zaune tana iya hango duk mai shiga da kuma wanda zai fita,
A karamar wayar dake hannun ta take buga game,duk da ba wai daɗin shi yake ji ba,
A hankali ta fara jin sautin murya na tashi,cigaba da buga game ɗin ta tayi,iska ne ya kwaso magana ya faɗa kunnen ta,wanda wannan kalmar ce tasa ta natsuwa ta ajiye wayar hannun ta"gabaɗaya ya tare min numfashi,baƙin ruhi ne dashj,ba zai taɓa bari mu ci galaba akan shi ba,"

Ɗayan da suke magana mai sanye da dogon hijabi har katsa ne ta ji tace"kome yake taƙama dashi,wannan karon abin ba zai taba zuwa yanda zai yi tsammani ba,domin sai yayi kuka da idanun sa yana niman cito,alokacin da babu wani Mahaluki da zai yarda da shi,"

Tabbas wannan ba muryar mace bane kamar yanda take ganin mutum sanye da hijabi,Namiji ne,amsar da zuciyar ta ya bata kenan,amma yanda yayi shirin mata har da nikabi ba zaka taba kawo hakan a rai ba,
To su waye,dukkanin su sun juya mata baya,bata gane wacce macen ba,amma daga dukkan Alamu a gidan take,
Ganin jamar zasu juyo ne yasa da sauri ta bar wurin ta koma inda ta taso,zuciyar ta fal da tunani,to waye abin harin su,gaskiya akwai masala koma waye suke hari,ita dai gara tayi ta gama ta koma inda ta fito,dan zaman gidan sam baya mata daɗi ko kaɗan.

Tana kallo har mai hijabin yazo ya wuce,ta jima a wurin kafin ta tashi ta koma shiyan su dan locin yin girkin rana yayi,

Da yamma tana kammala aikinta shiyan Kaka ta tafi wurin Nafisa,dan ta gaji da zama ita kaɗai,sun sha hira tare da Kaka kafin a kira sallah,su suka shige dakin Nafisa har aka yi Isha'i,
Suna jin sanda jikokinta suka fara zuwa gaishe ta,wasu su zauna wasu su wuce,
Hadiza ce take ba Zainab labarin wani India film data kalla jiya,gabaɗaya sun karaɗe falon da surutu,
Fitowa tayi domin ta ɗaukar ruwan sha,ta buɗe firig kenan ta ji falon ya dauki wani irin shiru yanda kasan ba mutane a cikin shi,sai kuma ta ji sanyayyar muryan nan dai yana sallamah,
Sai da Kaka tayi dariya kafin ta amsa,
Shigowa yayi ya zauna a gefen ta,
Cikin zolaya tace "wai ya naji shiru ne kamar ba mutane a falon"
Dago shanyanyun idanun shi yayi ya sauke a kansu,yanda duk suka natsu,
Mai da duban shi yayi kan Kaka"Me ya faru?

Gabaɗaya sun cika ni da surutu,nayi magana sunce wai suyi shiru kamar babu mutane,to yanzun bansan me ya faru ba naga duk sun natsu kamar babu kowa ma a nan"ta karasa faɗa da murmushi,

Aunty Maijiddarh ce cikin salon yanga da makale murya tace"Kaka ai hira suke taya ki"

"Ke kuma me ya samu muryar ki na ji ta kamar a shaƙe,ko mura kike yi ne"cewar kaka tana tambayar Maijiddarh domin tasan yanzun dai ta gama magana da muryarta lafiya amma yanzun yanzun kuma ace ya shaƙe,

Da yake su ƴan mata ne shi yasa nan take suka fahimci abinda ke faruwa wato make murya tayi,dan tana gaban shi,
Ai kuwa mantawa sukayi suka shiga kyalkyata dariya,Zainab harda dukawa "kai Aunty Maijiddarh harda make murya kuma,wallahi ko kyau bai maki ba"

Ɗaukar ruwan dake gaban kaka yayi ya ƙafa a kai yayi Bismillah ya shanye,

"Biba ɗauko ma Surajo Fura a firij ya sha tunda ya shigo"

Amsawa tayi da to sannan ta buɗe firig din da har ta rufe ta jawo kwanun dake ɗauke da lafiyayyen fura da aka dama shi da Kindirmo,

Tana daukowa ta kawo gabanshi,sai da ta duka sannan ta ajiye,
Har ta juya baya sai ji tayi yace "ke"
Chapter 21 · 0% Book details