← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 96

Sashe 39

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A'a har yanzun da nake baki labari babu labarin waɗannan mutanen,sai dai kuma wasu na zargin idan Kakan nashi ta tashi zata San wadanda suka aikata mata haka"

To me wannan me muhimmanci da aka sata,su waye kuma suka aikata wannan aiki,
Mai da kallon ta kanshi tayi"yama sunan garin da kakan nashi take"

"Tana can dai ƙasashen turawa,ba kin ce kuna waya ba,hala bai faɗa maki bane?

Dan murmushi ta kakaro" Ya faɗa mun kawai manta sunan garin nayi,yauwa bayan Kakan shi babu wasu yan uwa dake zuwa nan din a wancan lokacin?

"Eh kawun shi ne ko waye,kamar dai kanin Kakar shi ne naji yace a wancan lokacin shine yazo sau daya,kuma bai ƙara zuwa ba?

Da sauri ta mike tana turo mashi akwatin gaban shi," Ka dauki akwatin duka,duk abinda bai maka ba ka zubar"ta faɗa tana barin wurin,

Tsabar daɗi har da rawar murna sai da yayi,

Tana shiga daki da sauri ta jawo durowa ta falli takarda ta dauki Biro,
Rubutu ta fara kamar haka,
Kakan shi,sai kuma sata,alamar tambaya ta saka a wurin,to me aka sata,wani irin abu ne haka,sannan su waye suka aikata satan,

Shiru tayi ta shiga dogon nazari,to ita yanzun wannan takardar da aka ce ta dauko me amfanin shi,tabbas takardar ba gida bane,ko kamfani,takarda ne,wani irin buɗe ido tayi kafin a fili ta furta"ba dai yana da Alaka da wancan satan ba"girgiza kai tayi"inaa hakan ba zai yu ba,"har gitsa suman kanta tayi"Ya Allah me yake faruwa ne,shin wani irin aiki nake yi,wa kuma nake ma aiki,"sai dai fa idan har zargin ta zai iya kasancewa gaskita takardar nada Alaƙa da wancan aikin to shi kuma VIP kenan koma waye shi yana da masaniya a kan komai,
Ajiyar zuciya ta sauke,kai hakan ba zai taba yuwa ba,ai shi wancan aikin ma shekara goma sha daya,kenan da suka yi fashin,
Ita kuma wannan aikin nata data fara har auren bai wuce wata biyu,dan haka ba yanda za'a yi hakan ya faru,
Sai dai koma waye VIP sai ta binciko shi duk inda yake a duniya,haka koma menene waɗannan takardun suma sai ta bincikosu domin ta nan ne kawai zata iya samun duk wani amsoshin da take buƙata,kuma shine makamin duk wani yaƙi da zata gabza har ya kai ta ga duk wanda take son gani,
Sai dai babban matsalar shine ta yaya zata iya yin haka,ta ina zata samu wannan takardar.
Jin karan da wayar ta keyi ne ya dawo da ita daga dan gajeren nazarin da take yi,
Ganin me kira ne yasa gaban ta faɗuwa,dan cikin sauri ta ɗauki wayar tana karawa a kunnen ta,
"Me kika samu" Abu na farko da aka fara faɗa kenan daga ɗayan ɓangaren,

"Ina Ummita?

" Me kika samu? Ya kara maimaitawa,

Ta lura idan ba har ta bashi amsar tambayar shi bane ba zai taba amsata ba, "har yanzun ina kan bincikawa,amma ban samu komai ba har yanzun,sai dai ina ganin kamar waɗannan takardun basa cikin wannan gidan"

Tsaki taji an ja"to me nufinki a tunanin ki,shi din ya fiki wayau nisa ba kusa ba,sai dai ina da tabbacin duk wayau shi yana da lago,shi zaki nimo ki yi amfani dashi har ya kai ga faɗa maki in da suke,domin shi kaɗai yasan in da suke"

"Ta yaya zan yi haka?

" Ke matar shi ce kin fini sanin haka,na baki nan da kwana biyu,idan banji labari mai daɗi ba kome ya biyo baya sai ki yi maraba dashi,domin nima banda isasshen lokacin"

"Ummita fa?

" Nan da kwana biyu zaki ganta"

Kafin tace wani abu har ya katse kiran,to me yake nufi da nan da kwana biyu zata ganta,
Ita kan ta shiga uku,kwana biyu kam ya mata kaɗan ta ina zata fara,
Mikewa tayi ta nufin dakin shi,gara ta fara binciken dakin ko zata samu wani abu,
Tama yi tunanin zata ga dakin a rufe,sai dai a buɗe yake dan haka shiga tayi ta fara duba duk wani lungu da sako na dakin wanda tayi kusan awa biyu ba tare da taji ta gaji ba,har addu'a take akan Allah yasa ta samu wani abun,sai dai kamar yanda ta hargitsa dakin haka ta kyara dan ba abinda ta samu ko me kankantarsa,
Fitowa tayi ta jawo mashi kofa ta zauna nan bakin ƙofa,gabaɗaya ta rasa meke mata daɗi,ta rasa wani kalan tunani zata yi,a haka dai ta ƙarar da wannan ranar batare da yanke me ta kamata tayi ba,

Washegari da safe,ƙarfe goma wayar dakin ya shiga ƙara babu kakkautawa,
Cikin gigin bacci ta dauka tana karawa a kunne,
Muryar Bala taji yana fadin"Hajiya ki sauko kin yi baƙi "

"Ohh Bala barci fa nake yi"

"Ki yi hakuri ki sauko domin yan uwan Ubangida na ne suka zo,kamar ma harda iyaye"

Kashe wayar tayi tana jan tsaki, sannan ta shiga banɗaki tayi wanka cikin gaggawa ta saka doguwar riga na Atamfa wanda yaji aiki,

Tunda take saukowa daga saman bene suka kureta da ido,yayin da kamshin turaren ta ke sanar dasu isowar ta gare su,

Cikin jirmamawa ta shiga gaida su,duk da wasu sun amsa wasu basu amsa ba,
Ganin an kawo masu ruwa da abun motsa baki ne yasa ta zauna ita ma a daya daga cikin kujerun falon,

"Sannun isassah,muna saman kushin kina sama babu ko ɗan girmamawa"cewar Hajiya Rahama,

Hararan gefe tayi" Momy ai yanzun kin san level ya ƙaru "

Duk buɗe baki suka yi suna kallon ta"ah lallai level ya karu,baƙauye ya karo wulaƙanci "

"Sosai ma kuwa Goggo tunda gashi Baƙauyen ne ya samu nasarar shiga gidan sarki"

Duk sun gane inda ta dosa,dan haka mikewa suka yi "zamu tafi ina Suraj,ko shi yafi ƙarfin fitowa ya gaishe mu"

"Barci yake yi domin jiya da daddare yayi aiki ya gaji,bamu yi bacci da wuri ba"

Daya bayan daya suka fita suka bar falon ba tare da sun kuma ce mata komai ba,lallai ashe ita din Kura ce mai lulluɓe da fatan Akuya,jiya sun ga Video da aka mata a wurin wa'azi,shine kaka ta haɗa su taimasu faɗa akan ba su je sun dubo Suraj din da matar shi ba,amma ji amma da yar iska ta faɗa masu,

Ita kuma suna fita taja ƙaramin tsaki,domin ita wallahi ko kaɗan bata su take yi ba,
Wani tunani ne ya faɗo mata dan haka cikin sauri ta tashi ta shige daki,durowa ta buɗe ta shiga duba Asalin Jakkan kayanta ta dauko ta zazzage,
Wannan wasiƙar data taɓa satowa a ɗakin shi ta dauko,
Jikinta har rawa yake yi wurin lalubar number shi,kira biyu ya ɗauka ba tare da yace komai ba,

"Na samu wani abun" Ta faɗa da kwarin gwiwa,

"Ina jinki"

"Wasika ce dana samu a dakin shi,"

"Akan inda takardar yake ne?

" A'a sai da an ruba *Hadarin dake sararin samaniya yayi baƙi kirin,kuma daf yake da saukar da baƙin ruwa mai mugun dafi, da fatan za'a shirya ma ƙwaryar taran shi* abinda ke cikin wasikar dana samu kenan,

Dariya taji ya sheke dashi kafin yace"ai kuwa ruwan ma yafara sauka sai dai bansan ko da wani irin ƙwarya zai iya taran shi ba"

"Me kake nufi"

"Koma me nike nufi daga nan zuwa gobe zaki ji"

"To Ummita fa"ji tayi ya kashe wayar dif yayin da take jin sautin dariyar shi a ranta,haka kawai kuma sai taji gabanta na faduwa kafin wani irin tsoro ya shige ta," Me yake nufi?me zai faru a gobe?ita fa ta lura kamar daga jiya zuwa yau ta rame tsabar fargaba,ƙoƙari tayi ta cire abun arai,sai dai duk yanda tayi ta kasa sai ka ƙara shiga fargaba da take yi,

Ganin ta kasa jurewa ne ya ta fito daga falon tana kira Bala,

Da sauri ya karaso "Hajiya gani" Ya faɗa cikin girmamawa dan tun kyautar data mashi ya shiga kara girmamata,

"Kana da lambar Ubangidan ka na kasar waje?

" A'a ba ni da shi sai dai Sarkin gida ba zai rasa ba saboda ko wani abun ya taso"

"Yi sauri ka kiramin shi"

Har zai fita sai kuma ya juyo"amma baki da number ne Hajiya?

"Ohh kai dai da wannan tambayar,to numbobin waya tane suka goge"

Dan dariya tayi"ok ok na gane,in ba haka ba ai da sai nayi mamaki"ya karasa faɗa yana fita,

Tama kasa zaune ta kasa tsaye,ganin ya jima ne yasa ta fita dan gara ta bishi ta amsa da kanta,dan gani take kamar ko wani dakika ta kara kamar barazana ce a gareta,
In da tasan sarkin gidan ya cika zama nan ta nufa,yana ganin ta ya mike yana amsar takardar da yake mika ma Bala,
"Hajiya da kanki,ai da sai ki bari na zo"

"Kaga sauri nake bani number"

Mika mata takardar yayi"wadannan sune numbobin da yake amfani dasu guda uku,
Daya na Paris ne,dan yace a kwai aikin da zai tafi yi a can,amma ban san ko yaje ba,in dai yana can to zaki ga number dana rubata Paris,sai biyu kuma na Germany wanda idan yana can shima yafi amfanin da layukan,kuma idan yana nan ma wani lokaci yana amfani da dayar"

Da sauri ta juya tana fadin "na gode"

Daki ta koma har da saka key,sannan ta zauna ta shiga loda number ta farko a wayar,
Har ta kammala tana ƙoƙarin danna kira wani tunani ya fado mata,to yanzun idan ma ta kira shi me zata ce mai,me zata faɗa mashi,me kenan take kokarin aikatawa,
Da sauri ta sauke hannun ta daga kan wayar,amma kuma kaso casa'in na zuciyar ta ba karfafa mata guiwar koran shi,
Ta ma rasa me zata kama,shin ta kira ko karta kira.

*fans Yar tsanar zinari na niman shawara,shin ta kira Suraj ko karta kira shi*.....

🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*40*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*
Chapter 39 · 0% Book details