← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 96

Sashe 15

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga inda yake zaune a gaban karamin miro yana shafa mai ya amsa yana juyowa,
Shi kuma jin an amsa ne yasa ba tare daya jira komai ba ya shigo cikin dakin,
Sai kuma naga ya tsaya turus kamar wanda yaga wani abu,
Kallon Suraj ɗin yayi wanda yake ɗaure da Tawul iya kugu,jikin shi ba riga daga dukkan alamu kuma daga wanka ya fito,
Sai kuma ya kalli kan gado wanda yake a hargitse zanin gadon ya tattare ya koma gefe ɗaya,ga filalla duk sun yi gefe,dan daya gama gyara dakin ya rage saura gado,sai kawai ya wurga filallan a kan gadon kafin yaje ya dawo ba.

Ganin yanda yake ƙare ma dakin kallo ne yasa yace"Bismillah zauna,bari na saka kaya"

da sauri ya jirgiza kai"A'a ba zama zanyi ba,dama naga kofar ka a buɗe ne shi yasa na leko naga ko kana ciki"

"Ina ciki"

Juyawa yayi"to bari na tafi"har ya juya sai kuma ya juyo ya kalle shi "amma kuma" Ko tunanin ne yayi oho sai cewa yayi kuma"ba komai barshi "ya faɗa ganin yana kallon shi,ya juya ya fita yana mamakin wannan kuma wani irin sabon lamari ne yake shirin faruwa dasu kuma acikin wannan gidan kuma da wanda ba'a taba tunani ba,
Dole ya faɗa ma Kaka,ko kuma ya sanar da Abbu kafin abun yayi tsanani.....

*in Allah ya kaimu zanci gaba*
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*17*

*Na mai da Littafina mai suna a sama na kuɗi,tare da JAURO,idan kina son daya 300,dari uku,guda biyu kuma da Yar Tsanar Zinari tare da Jauro,dari biyar 500,ko wani daya dari uku*
*Hauwa Umar,Zenith Bank, 2284905309*
*ko katin waya na MTN,tare da turo shedar biya ta 08141644865*

Allah ya taimake ta koda ta shiga cikin falon babu kowa,cikin sauri ta shige ɗakin ta tana sauke ajiyar zuciya,ko ba komai ta godema Allah da dakin ya buɗe ba tare da mai dakin ya dawo ba,
Banɗaki ta shiga tayi wanka sannan ta canja kaya ta fito falo,zuwa lokacin an dan jima da idar da sallar,
Tana fitowa anan ta iske Ammi zaune tare da Shamsuddeen sai shi uban gaiyar wanda yake rike da carbi yana ja,shi kuma Shamsuddeen Amira na zuba masa abinci a plate suna dan hira da Ammi,

Tana zuwa tsugunnawa tayi a gabansu "Mam barka da Juma'a"sannan ta kalle su cikin dukar dakai tace" Barkan ku da Juma'a "

Dago kai Shamsuddeen yayi yana kallon ta,

"Yauwa barkarmu da rana mai falala,sai dai kuma ina kika je ne Babi tun dazu na aika cigiyar ki a cikin gidan nan sai dai ace ba'a ganki ba,ina kika je?

Wannan karon ba Shamsuddeen ba har ta shi kanshi da idon shi ke lumshe yana jan carbi sai da ya dakata na ɗan wasu lokutan dan jin ne zata ce,yayin da shi kuma Shamsuddeen ɗin yake satar kallon dukkan su,

Ba tare da dar ba tace"Mam kiyi haƙuri a lokacin da kika aikeni kiran Amira ne bayan na kirata ina hanyar shigowa saiga kiran Uwar ɗakina akan Mamata ba tada lafiya daga ƙauyen mu har an shigo da ita cikin gari yanzun haka tana Asibitin Koyarwa na Aminu Kano,
Mam kiyi haƙuri hankalina ne ya tashi shi yasa na tafi ba tare da izinin ki ba"ta faɗa tana share guntun hawayen daya zuba a idonta,

Idonun shi dasu rufe bai masan yanda akayi suka buɗe ba tsabar mamakin irin karyar da wannan ƴar yarinyar ta haɗa a lokaci ƙanƙani,sai tsintar idanun shi yayi a kanta,

Yayin data gefe ɗaya kuma Shamsuddeen ya kusa kamewa a zaune yana tunanin kodai ta manta dazun ya ganta tana fitowa ɗakin ƙanin shi.

"Subhanallah,ai ban sani ba dana hada ki da wani kuje tare,yi hakuri bar kuka,insha Allah mamarki zata samu lafiya da yardar Allah,
Yanzun ya jikin nata?

Jan majina tayi cikin muryar ban tausayi tace" Da sauƙi"
"Meke damunta ne har haka"

"Likita yace hawan jini ne ke damun ta"

"To ba komai kar ki damu,zuwa anjima Shamsuddeen in baka komai sai ka kai ta ku dubo Mamar nata"

Da sauri ya girgiza kai"A'a Ammi zuwa ajima zamu fita da Abbu ne sai dai ko Suraj"

Jiyowa yayi ya kalli yayan nashi yana bata fuska,wanda shi kuma da sauri ya kauda kai,

"To hakan ma yayi,kaga sai kuje kaida Amira ku gaida su"

Ba zai iya ci mata musu ba ko kaɗan,kuma ma bancin haka zai so ganin karshen mai ƙarya,"insha Allah Ammi,sai dai kimin hakuri zuwa bayan sallar la'asar sai mu je "

"Hakan ma yayi Allah ya kalmu"

"Na gode sosai Mam Allah ya biya ki,Allah yasa kifi haka"

"Amin kar ki damu,ɗauki ga bakin leda can ki kaima Kaka"

Ɗaukar ledae tayi ta fita tana sharan hawaye,

Girgiza kai Ammi tayi"yarinya abin tausayi"

Duk cikin su ba wanda ya bata amsa.

Tana fita kai tsaye shiyan kaka ta shiga inda ta same ta a zaune saman Babban darfuma ta mike ƙafa Nafisa na ja mata,
Cikin girmamawa ta gaishe ta tare da ajiye mata ledar a gefe,
"Ɗauka ki kai min ɗaki Biba"

"To Kaka" Ɗauka tayi ta shiga ɗakin,
Tsayawa tayi sake da baki tana kallon ikon Allah,wai dama har yanzun akwai irin wannan Gadon na mutanen da Mai Runfa,lah,ita da labarin shi kawai take ji bata taɓa gani ba,
Dakin gabaɗaya tsarin shi da kayan dake ciki duk na mutanen da ne,sai dai komai a tsare yake,kuma a tsaftace,
Akan wani teburi ta ajiye ledar ta fito tana murmushi,
Zama ta yi a gaban kaka tana tankwashe kafa,"Kaka nikan dakin ki yamin ƙyau sosai "

Kallon yarinyar tayi itama ta tana sakar mata murmushi "me ya burge ki a dakin tsohuwa?

Cire hannun Nafisa tayi daga kafar Kaka ta shiga matsa mata a hankali tana dannawa" Komai da komai,kinga ni kam har balle wannan gadon naki mai runfa,da kwanunaka,harda kyaryan mai kamar kwanu,kinsan wani abu?

Girgiza kai tayi tana jin daɗin matsar ƙafar da take mata,dan har tafi Nafisa iyawa,ta kuma san dai_dai inda yake ma mutum ciyo,"A'a saikin faɗa "

"Inda ace mijin da tan aura zai so irin waɗannan kayan ko,da nazo kin ɗan min naki na tafi dashi,ɗan Allah idan kin tashi kyauta da wannan gadon ki bani ina so kinji" Ta fada tana marairace fuska.

Dariya sosai Kaka ta saka ganin yanda ta wani marairace fuska ita a dole tana roƙo"in banda ke me zaki yi da kayan tsohuwa"

"Ni dai ina so kinji kaka,kuma kullun zan dinga zuwa ina danna maki kafa ina kuma tuna maki dan kar ki manta"

Dariya take tana jinjina wauta irin na yarinyar wacce cikin lokaci kankani ta shiga ranta,

Abbu ne suka shigo tare da Abba,suma da fara'a a fuskar su jin dariyar tsohuwar tun daga ƙofar falo,

Sallamah suka yi tare da shigo bayan kaka ta amsa,
Ganin sun zauna kusa da kaka ne yasa ta matsa tana gaida su,
Abba ne yace"wacece wannan "ya fada cikin sakin fuska dan shi yana da son wasa da yara.

" Sunan ta Biba ina jin baku taba haɗuwa bane,amma a dakin Ammin yara take,bayan tafiyar Abbu Sufyan ne na daukar ma Ammi ita saboda tsautsayin daya same ta"

"Godiya muke Uwar ƙwarai" Cewar Abbu yana murmushi,

Cikin jin na'uyin dattawan tace"Kaka na tafi sai anjima"

"To Ƴar Albarka sai na ganki,kar dai ki manta da Alƙawarin mu"

Dariya tayi kasa_kasa"ba zan manta ba"

Tana fita Abbu yace"to wani Alkawarin kuma aka yi"
Tana dariya ta sanar dasu yanda suka yi da Biba,aikuwa suma ba karamin darawa suka yi ba,daganan suka shiga hira kamar yanda suka saba duk Juma'a,a haka itama Goggon yara tazo ta same su,sai daf da sallar la'asar sannan suka fito shiyan su mazan suka tafi masallaci....

Tana fitowa shiyan kaka komawa tayi shiyan su,a kicin taga abinci a kula ta diba iya cikinta ta shige daki.
Sai da taci ta koshi sannan ta mike,juye_juye ta hauyi akan gadon,haka kawai ta rasa meke mata daɗi,ta rasa natsuwarta,komawa ƙasa tayi ta kwanta,sai dai nan ma haka ne,ji take kamar tayi ihu,abinda bata so tayi dai shi ne dole zata yi dan samun kwanciyar hankalin ta,in ba haka ba ji take kamar ta tube kayanta tayi yawo tsirara,
Jakkan kayanta ta ciro ta zazzage shi gaba ɗaya,daga can tsakan jakkan naga ta ciro wani dan sacet din magani wanda banga suna a jikin shi ba,guda daya naga ta cire tare da ballashi gida biyu ta saka rabi a baki ba tare data damu ba akan ta kora da ruwa,
Har wani jan numfashi take da saukewa tana wani lumshe ido yanda kasan wacce keshan wani abin daɗi,
Maida sauran tayi a kasan jakkan shi kuma ballin ta samu leda ta daure shi,harfa ta kusa gama mai da kayan kamar wacce aka tsikara ta kara zazzago kayan ta ciro ballin ta wurga abaki ta tattaune shi,goran ruwan da taci abinci shi ta dauka tasha sannan ta kara mai da kayan,
Komawa tayi kan gadon ta kwanta tana kallon sama yayin da taji wani natsuwa da kwanciyar hankali na sauko mata,a hankali ta fara lumshe ido tana budewa,ganin yanda dakin ya fara juya mata a hankali a hankali,
A haka ta kasance ita dao ba'a sume ba ita ba'a farke ba,har lokaci ya tafi.

Ganin an idar da sallar La'asar ne Ammi tace Amira taje ta sanar ma da Biba akan ta shirya yanzun Suraj din ya mata waya su same shi a bakin get.

Koda ta shiga dakin a kwance ta same ta,dan haka karasawa tayi inda take kwance tana tada ita"Biba,Biba,ki tashi wai Ammi ki shirya Yaya Suraj na get yana jiran mu"

A hankali ta buɗe idanun ta,waɗanda ba karamin nauyi suka mata ba,da kyar ta iya haɗo ɗan sauran hankalin daya rage mata"to ganinan zuwa"

Juyawa tayi ta fita ba tare data lura da halin da take ciki ba,
Chapter 15 · 0% Book details