← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 96

Sashe 18

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin kuka ta ce "baki ga yanda jikin na yayi ba,kalli hannuna,! She is wicked women! What did I do to her! Me na mata,ni ba zan ƙara kwana a gidan nan ba,"ta faɗa tana dafe kanta tare da ɗan rintse ido" Ance gidan malamai akwai tsoron Allah,suna kyautatama kowa,ba suda zalunci,Ashe duka karya ne,su masu son kansu ne,na tabbatar da a wani wurin nake aiki da babu wanda zaimin haka,tunda nake a rayuwata ba'a taba marina ba,sai a gidan nan,ba'a taba duka na ba sai wannan so calling gidan malamai,Nafisa kalli yanda ta bata min jiki na,shikenan na zama mai tambo a jiki,ba zan zauna ba,na gama aikin I am out"

Gabaɗaya jikin su ne yayi sanyi,domin tabbas ba'a kyauta mata ba,kuma a yanda sunan su yayi kauri bai kamata a samu irin wannan shaidan daga cikin gidan su ba,

Ji tayi an yafa mata abu a jikin ta,wanda ya rufe ruf jikinta gaba ɗaya,
Dago ido tayi ta sauke a kan Ammi wacce ke tsugunne a gabanta,

"Idan har an zalunce ka,kana da damar da zaka faɗi abinda aka maka,amma suturta jikin ki ya zamo shine abu na farko daya kamata kiyi"ta faɗa tana share mata hawayen dake sauka saman fuskarta,

Aunty Maijidda ce cikin tsoro tace " Ammi jini"

Duk kallon inda ta nuna suka yi,farin hijabin da Ammi ta yafa mata ne ya fara jikewa da jini wanda yake ɗigowa daga cikin kanta,

Ammi na kokarin kai hannu saman hanta ne,taji saukar lallausar hannun shi biyu saman kanta wanda hakan yayi daidai da lunshe ido da tayi tana ganin wani duhu na gifta mata,
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*20*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Salati Kaka ta saka cikin tsoro,domin ko kaɗan bata son tashin hankali tana da saurin rudewa,"inna'lillahi'wa'inna'ilaihi rajiun,ya Ubangiji ka rabani da ganin bakin rana a rayuwa ta,yau me zan gani,kisan kai a gidan nan,"gaba ɗaya ta ruɗe tana kuma kokarin ruɗa su da kalamanta,
Ganin bata numfashi ne yasa cikin tsoro ita ma Ammi tace"Shamsuddeen bata numfashi fa"

Koƙarin ɗaukarta yake yace "Ammi ki kula da Kaka"
Ɗaukarta yayi yana ƙoƙarin barin Falon da ita,
Da sauri Nurudeen ya dakatar dashi ta hanyar faɗin "ina kuma zaka kai ta,baka ganin halin da take ciki?

Wani mugun kallo ya watsa mashi sannan ya kuma saka kai,
Kaka ce tace" Shamsuddeen dawo da ita nan Nura ya duba ta"
Cikin tsananin jin haushi ya dawo da ita ya ajiye ta a saman kushin ya juya ta bar falon,
Duk da kallo suka bishi,to me shi kuma ya bata mashi rai haka,
Kiran sunan shi da kaka tayi ne yasa shi dawo da kallon shi kanta"Sujaro zo ka dauke ta ka kai ta dakina"

Kallon wacce ake cewa ya ɗauka yayi yanda take wance babu numfashi,a hankali ya tako in da take kwance ya dauke ta ya shigar da ita dakin kaka,saman karamin gadon kaka ya kwantar da ita,
Aunty Maijiddarh ce data biyo shi a baya ta yaye gabaɗaya hijabin da Ammi ta rufa mata wanda ya gama baci da jini"Yaya Suraj ka dafe kanta inda yake fitar da jini"
Kauda kai yayi daga kallo ɗaya da yama jikin ta,dan sai lokacin yake ganin irin yanda fatar jikinta yayi,jin muryar Nurudeen yana ƙoƙarin shigowa ne yasa yaja zanin gadon ya rufa mata jikinta gaba ɗaya dashi,
"Ki danne mata wurin" Abinda ya faɗa kenan ya bar ɗakin,
Kai tsaye in da su Kaka suke ya tsaya ya mata magana,sai kuma ta kwalla kiran sunan Nurudeen wanda ya shiga dakin ko yana ƙoƙarin zame zanin da aka yafa mata,"Fito ga Hauwa'u ta zo,sai ta duba ta"

Yi yayi kamar bai ji me tace ba,sai da Maijiddarh tace"Kaka na magana "
Tsaki yaja ya fito falon yayin da ita kuma wacce aka kira da Hauwa'u ta shiga dakin,
Maijiddarh ita take ta taimaka mata har ta gama mata treatment sannan ta rubata Allurai da magunguna,
Duk suna zaune suna jiran fitowar ta,
Kai tsaye wurin da yake zaune ta nufa tare miƙa mashi ƙaramin takarda "yallabai an samu nasaran tsayar da jinin sannan na mata duk abinda ya kamata,wadannan magunguna da Allurai ne da za'a siya zan dinga zuwa na mata na kwana uku ne,sannan shatin jikinta ma zai tafi idan tayi amma da cream din dana rubuta,"

A maimakon ya karba sai kauda kai da yayi ganin duk yanda suka zuba mai ido,
Ganin bai da niyar karba ne yasa Ammi tace"kawo takardar "
Miƙa mata tayi cikin girmamawa,
"Allah ya maki Albarka yarinya,Bilki zo ki ɗauko kuɗi a daki na ki sallame ta mun gede sosai"cewar kaka,
Cikin rawar jiki Bilki ke kokarin tashi,sai ji suka yi matar tace" A'a Kaka ki barshi tsakani na da Suraj yafi nan,babu matsala Allah ya bata lafiya "
Da Amin suka amsa kafin ta masu sallamah ta fita,
Tashi suka ga yayi yabi bayan ta,
Ammi ne da Kaka suka shiga dakin,
Allah sarki baiwar Allah,a hankali take sauke numfashin wahala,gabaɗaya ta gama basu tausayi,
"Ki yi ƙoƙari ki bada a amso maganin da Alluran"
"To Kaka,bari na saka a kawo mata kaya saboda idan ta tashi"
"Haka ne"
Fitowa falo suka yi,
Salman ne yace"wai me ya haɗa ta da Momy Rahama?
Balki ce ta bashi amsa"wai rashin kunya tai mata,ai ni wallahi ba karamin birge ni tayi ba,dan yarinyar sam ba ta da kunya,haka fa taima goggo rashin kunyar nan,bata San Momy ba kyale ta zata yi ba"ta fada tana mikewa "tunda an gama game bari na ƙara gaba" Haɗa ido suka yi da Nurudeen wanda ya zuba mata harara,kasancewar ta raina shi shiyasa ko akai bata kawo shi ba saima dariya da tayi tana barin falon,
Kafin suma su watse,
Ranar a shiyan Kaka ta kwana tare da Nafisa,cikin dare ne wani irin zazzafar zazzaɓi ya taso mata wanda jikin ta har wani gab_gab_gab yake yi,yanda kasan wacce zata tashi,
Hakan ba karamin tsorata Nafisa tayi ba,gashi bata son ta tayar da kaka saboda ta san tana da hawan jini idan tana barci ba'a tashin ta,
Gabaɗaya ta rasa mafita, ta kuma san tabbas idan bata nime taimako ba komai na iya faruwa da Biba,
Wani shawara ne ya fado mata,dan haka da sauri ta shiga dakin kaka ta dauko wayar ta,
Tama rasa wata number zata kira dan Allah ya gani ba tayi Boko ba,ba zata iya tantance waye ta kira ba ko wa zata kira,
Dan haka number data gani a farkon wurin kira ta latsa ma kira,tana kallon Agogo,a lokacin ƙarfe biyu na dare,

Kira biyu aka ɗauka,jin muryar wanda yayi sallah ne yasa cikin rawar jiki ta kira sunan shi"Yaya Suraj kai ne? Ta tambaya domin tana buƙatar tabbatarwa,

Bai damu da bata amsar tambayar data mai ba sai ma jeho mata nashi tambayar da yayi"ina kaka?
"Tana barci"
"Lafiya kika kira?
" Biba ce ba ta da lafiya "ta fada da sauri jin yana ƙoƙarin ajiye wayar.
Dan shiru yayi yana tunanin ma wacce Biba,
" Na sani"ya bata amsa dan sai yanzun ya tuna tunda yasan dai a shiyan mutum ɗaya ce ba ta da lafiya,shi baimasan sunan ta ba sai yau.

"Yaya wallahi jikinta rawa kawai yake sosai gashi yayi zau,na rasa me zan yi,tsoro nake ji kar wani abu ya same ta"
"Ki jika towel da ruwan sanyi ki dinga Gogo mata a jiki"
"Yaya nayi hakan amma abin ya fi karfi na dan kamar zata yi jijjiga"
Shi mutum ne mai tausayi sosai dan haka mikewa yayi tsaye daga zaunen da yake saman darduma ya fito,
Kai tsaye shiyan su ya nufa,sai da ya ƙwanƙwasa sannan tazo ta buɗe mai ya shiga,
Nuna mashi Biba tayi wacce take kwance an jibga mata zannuwan gado a jiki,Lokaci-lokaci kuma takan zabura,kai basai ka taba jikin ta ba,ko daga yanayin ta kaɗai ya isa ta shaida maka irin yanda zafin jikinta yayi sama.
Yasan ba shida wani taimako da zai iya mata tunda ba aikin shi bane,wayar dake hannun shi ya danna kira wanda sai da ta mai kusan miss call takwas sannan ya ɗauka cikin muryar Barci,
Ce mai kawai yayi"kazo shiyan kaka ina jiran ka"ya sauke wayar a kunnen shi.
Jin an ambaci sunan kaka ne yasa da sauri ya wastsake ya saka dogon riga ya fito,kai tsaye shiyan na nufa,a buɗe ya samu ƙofar dan haka ahiga yayi,yana ƙoƙarin nufar ƙofar kaka,dan ba karamin ji da tsohuwar suke yi ba,shi yasa lamari in dai nata ne basa wasa dashi ko kaɗan,
Ji yayi muryar Nafisa ta ce"Yaya Nurudeen nan zaka wuto "
Bin bayanta yayi inda ya taradda Suraj a tsaye,kallon shi yayi,sai dai kafin ma ta mai magana ya nuna mashi gado da ido,
Cikin sauri ya karasa inda take kwance tare da yaye bargon ya dafa goshinta,
Kallon Nafisa yayi cikin dan yanayin bacin rai tace"garin ya kika bari jikinta yayi zafi har haka,ba kisan tana ita shiga Fit saboda high fever ba"

Ita dai bata ce komai addu'ar ta daya Allah yaba Biba lafiya,

Yaye duka bargon da aka rufa mata yayi"kara karfin AC"

Dan waro ido tayi ganin yanda take rawar sanyi sannan ace ta kara AC"rawar sanyi fa take yi"

Wani irin kallo ya wurga mata da sauri ta yi yanda yace tana kallo ikon Allah,

Allah yasa dazu kafin Ammi ta tafi sai da ta taimaka ta saka mata dogon wondo da riga shima dogo har kasa mara nauyi amma na barci ne,sai hula,to garin zaburan da take yi ne hulan ya zame wanda nan take suman duk ya baje saman filo,ya rufe mata fuska,
Suman baki ne wuluk yanda kasan ta shafa mashi dayis saboda baƙi,ga tsantsi da laushi,
Chapter 18 · 0% Book details