← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 96

Sashe 42

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*42*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Ranar haka ta kwana duba Ammi,sai dai duk shigan da zata yi a zaune zata same ta saman sallaya,
Ganin haka ne yasa itama ta dauro Alwala ta shiga yin Nafila har zuwa ƙarfe uku na dare sannan bacci ɓarawo ya ɗauke ta,
Washegari da safe tana idar da sallar dakin Ammi ta shiga,har yanzun tana zaune saman sallaya,zama tayi a gefen ta tana jira ta kai karshe,sai dai ganin har yanzun ba ta da niyar tsayawa ne yasa ta dafa hannun ta tare da kiran sunan ta"Ammi"ganin bata dago bane yasa ta kuma kiran sunan ta,wannan karon ido kawai ta dago ta kalle ta da shi ba tare data amsa ba,kuma har lokacin tana jan carbin,
"Tabbas kina cikin tashin hankali irin wanda ba zai taba faɗuwa ba,duk yanda zamu shiga cikin tashin hankali ba zai kai rabin wanda kike ciki ba,dukkanin mu mun sani babu ta wani hanyar da zamu saka wannan lamarin yayi sanyi irin ta hanyar Addu'o'i da rokon Allah,
Ke mahaifiyarsa ce,addu'ar ki a gare shi ba zai taɓa faduwa kasa banza ba,sai dai kuma be kamata ki yi ta yanda zaki iya cutar da kanki ba,ke din tamkar bango ce a gare shi,idan kuma har kika faɗi to dame zai jingina,
Ammi faduwar ki tamkar nasarar ce a gare su,zuciyarki ta zamo tamkar na dutse shine zai nuna jaruntar ɗan ki,
Duk da ban zauna dashi na wani lokaci ba,sai dai na fahimta shi mutum ne ba mai tsoro ba,mutum ne mai juriya da tawakkali,na tabbata zai jure,zai kuma kai ga inda yake da burin kai wa,
Ya kamata ki samu ki yi wanka sai ki ci abinci ki kwanta ki huta,domin sai Kanada lafiya da kuzari sannan zaka iya fita filin daga har ka gabza faɗa"mikewa tayi"Allah ya kawo mana mafita "har ta kai bakin ƙofa zata fita taji tace" Allah ma ya riga ya kawo mana mafitar"

Cikin tsananin mamaki ta juyo tana kallon ta,domin rabon da taji tayi magana tun kan a tafi asibiti,da sauri ta dawo gabanta ta tsuguna"Ammi ina mafitar?menene mafitar?

Ajiye carbin dake hannun ta tayi ba tare data fuskance taba tace"Kece mafitar "

Zaro ido tayi"ta yaya aka yi na zama mafitar wannan lamarin,ni bansan komai ba"ta faɗa gabanta na faduwa cikin tsoro,don kar azo Ammi ta riga tasan komai,Alhalin itama mafitar take nima,

Ganin yanda kamar hankalin ta ya tashi ne yasa ta rike mata hannun "ba abinda kike tunani nake nufi ba,kawai dai ki yarda da ni ke kaɗai ce wacce zaki iya taimakon shi,ki kaɗai ce wacce zata iya fito dashi,"

"Ammi ta yaya zan yi haka,wallahi bansan wannan hanyar ba,ban San hanyar da zanbi ba,"

"Kin sani,sai dai duhun da ya lulluɓe maki idanu shi zai hana ki ganin wannan hanyar,duhun daya lulluɓe maki zuciya,shi zai hana ƙwaƙwalwar ki buɗe maki hanyar,
Sai dai zan yi haƙuri na jira har zuwa lokacin da duhun zai yaye,haske ya baiyana,har zuwa sanda zaki ƙara karɓar kanki a matsayin yanda kike,har zuwa sanda zaki karɓi kaddaranki a yanda ta zo maki,
Zan jira har wannan lokacin"

Shiru tayi kawai tana kallon Ammi,domin ko kaɗan bata fahimci me take nufi ba,bata fahimci ina zancen ta ya dosa ba,sai tsintar kanta tayi da kara cewa "yaushe ne wannan lokacin zai zo da kike faɗa?

" Ni ma dai ban sani ba,amma na tabbata ya fara matsowa,duk da irin nisan da yayi,karki takura ma kanki da tunanin kalaman da ba zaki taba fahimta ba,sai dai kawai a bu daya zan faɗa maki,idan wannan lokacin yazo,amsar da kanshi zai bibiye ki ba ke zaki bibiye shi ba,
Tashi ki tafi zan kwanta na huta kamar yanda kika buƙata"

Mikewa tayi jiki a sanyaye ta bar dakin,ita kam koma me Ammi ke nufi ba ta sani ba,amma ta san duk rintsi baza ta taba bari ta mutu a hannun wani ba,to sai dai in haka Allah ya tsara mata,

Kyaran gidan ta fara kafin ƙarfe bakwai ta kammala komai har ta haɗa abin ƙari,
Jin ana ta ƙwanƙwasa kofar falo ne yasa da sauri ta fito ta buɗe,
Bankade ta tayi "wannan ai iskanci ne mutum naji ana buga kofa amma bai iya fitowa ya buɗe ɗan isa,to Allah dai yasan mun san asalin mutum"

Ita dai bata ce mata komai ba,amma kuma tana mamakin canji irin na Amira,ta san a da ba haka suke ba,amma tunda ta auri yayanta shi kenan yarinyar tabi ta tsaneta,karamin tsaki taja dan yanzun ba ita ɓace a gaban ta,

Daki ta koma dama abinci take ci,tana kammalawa ta haye kan gado ta kwanta,taso ta ɗan yi bacci,sai kuma ta jawo waya ta shiga Facebook,gara ta duba taga ya ake ciki game da lamarin,
Har yanzun dai ko ta ina labarinsa ne ke zagayawa,
Anan ne ma take gani ashe yarinyar yar Chief Judge ne,
Mahaifinta babban Alkali ne akasan,ba Musulmi ba ne,mugun mutu ne,wai yarinyar watan ta hudu bata gida,sun nime ta basu ganta ba,ta samu matsala da mahaifiyar ne shine tayi fushi ta bar gida,,
A yanda Uwar ke kuka take faɗa kenan a wani dan Video da ta gani ta buɗe,wai sai an daukar mata haƙƙin yarta,sai sun kashe shi ba zasu taba yarda ba,shi kuma mahaifin yana fadin sai inda karfin shi ya ƙare,zai ga kuma wanda zai tsaya ma yaron,domin yarinyar su biyu kawai suka haifa,daga yayanta Namiji sai ita,"
Mutane kowa nata fadin Albarkacin bakinsa,
Tayi matukar mamaki yanda taji mutane da yawa sun yarda da lamarin sai tsine mashi suke suna Allah wadai da mutum irin shi,har da cewa ai duk dama kyan ɗan maciji ne da dashi,kai ga dai maganganu nan dai wanda kallon su kaɗai zai iya hardasa ma mutum bugawar zuciya,

Dan haka sauka tayi kawai a online ɗin tsabar haushi ma sai goge Facebook din tayi gabaɗaya daga kan wayar ta,
Bata san Me yasa mutane suke haka ba,basu san farkon labari ba,sai kawai su tashi su fara bada tsakiyar labari ba tare da sun jira sun ga ƙarshen ba.

Jin an buɗe ƙofar an Leko ne yasa ta dago tana kallon kofar,haɗa ido suka yi "wai kije shiyan Kaka ana nimanki a can" Tana gama faɗa ta jawo kofar ta kulle,

Kallon agogo tayi,har ƙarfe tara na safe tayi,ashe dai ta ɓata lokaci a online,
Mikewa tayi ta saka Hijabin ta ƙaramin sannan ta fita,
Tunda tayi sallamah ta ɗaga labulen gabanta ke faduwa,domin mutanin gidan suna cikin falon har ta da Ammi,
Samun wuri tayi ta zauna gefen Ammi bayan ta gaida su,har da kaka,

"Mustapha kira Abbu Sufyan muji ya ake ciki" Cewar kaka,

Amsawa yayi ya saka wayar a amsa kuwa,
Sai da yayi kira biyu sannan ya ɗauka,
Sai ga muryam Abbu ya baiyana,amsa sallamah yayi,kafin su gama gaida juna,"ga Mama"ya faɗa yana mika ma Kaka,

Tana amsa yana ƙoƙarin gaida ita ta dakatar dashi"ina Surajo?ya yake?yana cin abinci kuwa?

"Mama,wallahi tun ƙarfe bakwai da muka samu muka iso har yanzun sun hana mu ganin shi,sai yawo da hankali suke mana,sai turamu ofisoshi suke yi,
Yanzun haka wai sai mun ɗauki lauya sannan zamu iya ganin shi,to munma ce su samar mana lauya amma sai cewa suka yi su badu da wani lauya a ƙasa,sai dai mu samu da kanmu,to yanzun dai abinda muke cike kenan,dan akwai wani abokin mu da muka yi karatu tare,to danshi Lauya ne,yanzun haka yaron yana hanya zai iso sai musan yanda za'ayi"

Share hawayen ta tayi"Allah sarki yaron kirki,Allah ya bashi karfin zuciyar cin wannan jarabawar,Allah yasa komai yazo maku da sauƙi "

"Mama ki dai na kuka,kin san dai abinda likita yace,dan haka addu'ar ku kawai muke buƙata"

Jan majina tana"Allah ya maku Albarka"

"Amin yauwa ina ga gashi ya iso bari muyi magana duk yanda ake ciki zaku ji"ya fada yana sauke wayar,

" Wani gaskiya Allah zai nuna bancin wanda ya nuna mana yanzun,ina ce ko sati ɗaya ba'a cika ba da aka gama rigima akan Auren shi,wanda shima Allah ne ya tona mai Asiri kika gani da idanun ki,da yake Maijiddarh ba tada rabon shan wahala da ganin bakin ciki sai gashi an fasa an daura da Farkan shi,to yanzun ya aikata halin shi a in da Allah ya tona mai Asiri,sannan ku faɗi haka,wama yasan da haka yake yi duk yawon Wa'azin da yake yi,gaskiya Allah na gode maka daka nuna min komai a baiyane Asirin da ake ɓoyewa ya tonu,d..........

Saukar Marin da taji a fuskarta ne yasa ta dafe kumatunta tare da dago idanunta dan san ganin wani isasshe ne mai zarra da zai mata haka,

Kowa na falon tsit sukayi suna mashi kallon mamaki,domin abune da ba'a taba yi ba acikin gidan,balle har a gaban kaka kuma bata ce komai ba,

Cikin tsanin mamaki ta kira sunan shi"Mustapha ni ka mara?

"Kwarai kuwa an Mare ki,ko zaki rama ne?

" To me na maka zaka Mare ni,kan na faɗi gaskiya,idan har ni kun iya rufe baki na zaku iya rufe na mutanen dake waje suna magana ne,ko kuwa zaku dinga binsu da duka ne?

"Koma me zamu yi dasu babu ruwan ki,amma ke kuma muna da yanda zamu yi dake,ban taɓa sanin rashin mutuncin ki ya kai har haka ba Saudat sai yau,ace a gaban Uwata,a gaban Mahaifiyar Yaro kike fadin haka dan ba kiɗa imani da hankali" Ya karasa faɗa a tsawace cikin bacin rai,

"Haba Abba me yasa zaka Mari Momy bayan kowa nan yasan maganarta gaskiya ne,ya aikata,idan da ace be aikata ba da hakan be faru ba,ga abu a zahiri babu sharri a ciki amma ku baku son ku gani" Mi kewa yayi ya riƙe hannu Hajiya Saude data dafe kumatu "Momy tashi muje"mi kewa yayi tabi bayan ɗanta suka fita,yayin da itama Aunty Hajjo tabi bayan su ta fita,
Chapter 42 · 0% Book details