← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 96

Sashe 77

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ga mamakin ta sai gani tayi ya sakar mata murmushi yana mikewa tare da faɗin "kin tashi?
Kuma har yanzun idanun shi na cikin nata ne yaki bata damar da zata cire nata idanun saboda wani irin kaifaffen kallo ne yake jinfanta dashi mai kashe gaɓoɓi,

Tsayawa yayi a gabanta yayin da hannun shi ke zube a cikin aljihun shi,

Gani tayi yannin nata suna fita ɗaya bayan daya tare da jawo masu kofa,

Cire idanun nashi yayi cikin nata yana sassauta kallon da yake mata, zama yayi a gefen ta suna fuskantar juna daga kwancen da take,

Maida idanun nata tayi ta lumshe,
Babu zato taji saukar hannun shi yana zagaye fuskarta,yana kallon yanda take kara matse idanun ta,da gaske bata son buɗe ido ta kalle shi,

"Buɗe idan ki"

Turo bakin ta tayi tana motsawa a hankali sai dai baya iya jin me take faɗa,

"Ina son muyi magana"

"Kawai ka fada ina jinka"

Ji tayi wani irin sanyayyen sanyi mai haɗe da kamshi yana sauka a saman fuskanta,

A hankali ta fara motsa idanun ta kamar zata buɗe,sai kuma tayi kokarin juyawa gefe,sai dai ya riga ya saka hannun shi a gefenta ta yanda ko kaɗan bata da chance din juyawa,
Dole bude shanyayyun idanun ta tayi tana daurawa a cikin nashi tare da haɗe fuska,domin ta lura in bata nuna mai har yanzun a Biban ta take ba to ba ƙaramin raini bane zai shiga tsakanin su,😎

Kuma tsabar dai nimar magana duk da ta buɗe idon bai daina busa mata iska ba,abunma har da gaiya,dan ji take kamar zata shede,

Babu sallamar ko nimar izinin shigowa kawai ganin shi suka yi ya faɗo cikin dakin kai tsaye,yayin da waya ke makale a kunnen shi yana faɗin "zan dawo mana,in dai wannan ne karka samu damuwa do.......

Maganar ta makale ne cikin makoshin shi sakamakon....

Bai ma karasa tunanin dake zuciyar shi ba sai gani kawai yayi ya karasa dan tazaran dake tsanin fuskokin su wanda dama bai wuce inch daya ba,

Ita kanta sai da ta shiga Shock da daukewar numfashi domin abune da tunda take dashi bata taba tsammanin haka daga gare shi ba,

A nashi bangaren kuwa yaji irin shigowar da yayi,sai dai bai juya ba,bai kuma damu da sanin ko waye ya shigo ba,sai dai ko ma waye yasan darajar niman izini kafin shiga wuri,

Daura bakin shi kawai yayi saman nata ba tare da ya tsotsa ba,yayinda idanun su ke yawo a cikin na juna,

Bai masan sanda dankareren wayar dake a sakale a kafadarsa ya zame ya faɗi a kasa ba,ji kake tasss karan tarwatsewar wayar,
Ji yayi kafafunshi na minan gagaran ɗaukar shi,yayin da numfashin shi ke yi tamkar zai dauke sabar yanda zuciyar shi ke ci da wutar kishi,
Cikin zafin rai ya juya ya bar dakin tare da bugo kofar da ƙarfi,
Wanda har sai da ya jishi a tsakiyar kanshi,
Lumshe idanu yayi yana kokarin cire bakin shi daga nata,

Sai dai kuma nan take wani abu ya gefta zuciyar ta wanda yasa babu shiri ta buɗe bakin ta tana kamo lip din shi na kasa tare da sakala hannayen ta duka biyu a wuyan shi,tana kara ci gaba da tsosan bakin shi cikin kwarewa,yayin da idanun su ke cikin na juna........
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*78*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Wannan karon ma kamar waccan karon ne dan ko kaɗan bai da ba gudunmawa ba,sai ma hannun ta daya zame a hankali daga saman wuyan shi yana cire bakin shi a cikin nata,
Kallon sakon biyar ya mata sannan ya mike tsaye yana sai-saita natsuwarsa,

"Me kike son faɗa min a wancan ranar?

Kauda idanunta tayi daga cikin nashi" Duk abinda kake son sani ka duba a cikin waya ta "

Gani tayi ya zari Tissue paper dake ajiye ya shiga goge lips din shi dashi a hankali yana yi yana Kollon ta kamar yanda ita ma ta buɗe idanu tana kallon shi,

"Wannan ya zamo karo na karshe da zaki ƙara aikatamin haka ba tare da izini na ba"

Maganar tasa ta zo mata a bazata,tare da yanayin action din shi,bata taɓa tunanin yau har a kwai namijin da zaiji Kyankyamin haɗa baki da ita ba,har yakai ga matakin goge bakin,
duk da cewa duk Kiss din da take ma shi aciki babu wanda tayi masa domin nishaɗi,,duka da gaiya take yi masa su,duk da takanji shi a jikinta kasancewarsa lafiyayyen namiji,ko yanzun tayi masa haka ne kawai saboda ta san yanda baya son ta rabi jikin shi,sannan gashi har da kanshi dan ya kuntata ma wani shine yake iya daura lip din shi saman nata,shi yasa ta kara sa masa amma ba wai dan wani manufa ba sai dan kawai taga wani yanayi zai shiga,
Nan take taji zuciyarta ta raunana,yayinda kalamansa da Action dinsa suka mata zafi fiye da komai a wannan lokacin, har tana jin idanun ta na kawo hawayen bacin rai wanda bata basu damar sun sauka ba,

"Bana bukatar izinin ka domin aikata abinda nake so"

Kallon ta yayi yanda take kokarin shanye hawayen idanun ta,
"Ina Alkawarin da kamin a ƙoto?yau ina son ka bani takardar saki na,domin duk wani abu dake tsakanin mu ya riga ya kare tun a koto"

Jin yayi shiru ba shida alamun bata amsa ne yasa ta dago kai tana kallon shi,
Kauda kai yayi daga kallon ta yana dosar kofar fita"har yanzun da saura dan bai riga ya kare ba,"
Dafa hannun kofa yayi ya juyo yana kallon ta"nan da kwana biyu idan an sallame ki zaki koma wurin Ammi har zuwa sanda komai zai kammala,idan yaso daga baya sai nayi tunanin yanda zan yi dake"yana gama faɗin haka ya fita tare da rufo mata ƙofa,

Hawayen da take rikewa ne ya koma kuka jin abinda yace"wallahi baka isa ba,babu inda zan kona,garin mu zan wuce,baka isa kace sai ka yi tunanin yanda zakayi dani ba tunda ni ba kaya bane,kuma sai ka sake ni dan rainin hankali "ta faɗa cikin jin zafin abinda yayi mata yanzun,Allah ma ya sota ba kaunar shi take yi ba balle ta mutu da takaici,dan haka rabuwa dashi ya zama dole ko yana so ko baya so.

__________yana fitowa ɗakin ajiyar zuciya ya sauke,yana dan yatsine fuska,dakin da suke zaune yayi noking tare da sallamah,

Amsawa suka yi yayin da Abdulmalik ke yar dariya kasa_kasa,
"Yayan mu me kake ma dariya?

Kafin ya bashi amsa sai gani kawai suka yi ya shigo a harzike har wani huci yake yi,

" Kai karamin dan iska ne,domin a iskan cin ma baka taka kara ka karye ba,har ni zaka nuna ma salon duniyanci?ni!!!!

Giran ya dage yana mashi kallon kai kuma wanene "Malam daga dukkan alamu kana da ƙarancin ilimin addini,da tarbiya"Juyawa yayi in da suke" Ni zan wuce sai mun yi waya"

A tare suka mai addu'ar Allah ya tsare,

Ganin da gaske kokarin gefta shi yake yi ne yasa cikin kasa dai-daita fushi ya finciko shi baya"ina kake tunanin zaka je,"kafin yace zai bashi amsa sai jin saukar naushi yayi a gefen cikin shi,from no where,

A tsaye yake amma bai san sanda ya dafe wurin ba yana dukawa,domin nan take yaji wani irin jiri na daukar idanun shi tare da raɗaɗi,

Cikin tashin hankali da gigita sukayo kanshi suna ƙoƙarin daga shi,sai dai ya kasa mikewa tsaye sosai yana dafe da gefen cikin shi,

Lafiyayyen Mari Abdulrahman ya sauke mashi yana cakumar kwalar shi"ban taba sanin har yanzun ba kada hankali ba sai yau,so kake ka kashe shi?

"Idan na kashe shi sai me?me zaku iya yi?ka sani gabaɗayan ku a tafin hannu na kuke,?

Ganin yanda su Abdulmajid suka tallaboshi suna ƙoƙarin zaunar dashi kan kushin ne yasa ya nuna shi da yatsa" A haka kuke tunanin zai iya da kanwarku da take harija?a haka?naushi daya ne fa na masa amma duba yanda ya zama kamar wanda na ma dukkan mutuwa,"fisgar kanshi yayi daga hannun Abdulrahman yana ƙara kallon shi yanda yake sauke numfashi yana dan rintse idanu "ka sani kafin ka san komai na jikin ta na riga ka sani,kuma Salma har yanzun ni take so ba wani raggo irin ka ba,bari ma na faɗa maku abinda baku sani ba,tun wancan lokacin a shekaron biyar da suka wuce na maida auren mu da Salma,tun kafin ta gama iddah k......

Basu san tashi shi ba domin hankalinsu nakan wannan mummunan zancen da yake kokarin bijiro da shi,
Sai ganin shi kawai suka yi shake da wuyan Yusif din,wanda yaji nan take numfashin ahi na ƙoƙarin barin gangar jikinsa,

Buga bayan shi yayi da jikin bango yayin da yake mashi kallon sama da kasa,"na lura har yanzun you are stuck in that fucking five years,sannan ka sani wannan ya zamo karo na karshe a rayuwar ka da zaka ƙara fadin irin makamanciyar wannan maganar a kanta,

Ganin da gaske kokarin suma yake yi ne yasa suka cire shi a hannun ahi,nan take ya shiga tarin wahala yana shafa wuya,bai taba tsammanin yaron yanada karfin da zai iya shake mai makoshi lokaci ɗaya yaji kamar zai mutu ba sai yau,shi kadai yasan irin shakar da yasha,shi kaɗai yasan irin wutar fitinar da ya hango a cikin idanun yaron,

Ganin ya kara mikewa kamar zai yi kanshi ne yasa cikin sauri ya buɗe ƙofar dakin ya fita,yana shafa wuya,

Kara zaunar dashi Abdulmajid yayi suna kallon yanda yake huci dan yau mutumin ba karamin kona mashi rai kalamanshi suka yi ba,wallahi ba shi ba da yake yi dan ita,har ta da ita sai ya hukunta,kyaleta kawai yake yi amma bari ta ji sauƙi,

Dafa kafadarshi Abdulmalik yayi"dan Allah ka yi hakuri ka sassauta ma zuciyarka ko dan lafiyar ka,kaga yanzun ma jini na fita ya kamata muje a duba wurin in ba wata matsala"

"Haka ne,"
Chapter 77 · 0% Book details