← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 96

Sashe 47

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Ina da takardun zama cikakkiya Lauya,sai dai License di na yayi expire,ina buƙatar inyi sabon Registration wanda ba ni da lokacin,
Sai dai taimako daya zaka iya min shine a matsayin ka na Babban Ministan birnin taraiya ka saka Amin Ragester cikin awa daya sannan a dauke ni a matsayin lauyar Gwamnati,ta hakan ne zan iya tsaya mashi domin ni babu abinda zan rasa yanzu"

"Dama kin yi karatu har haka ne?

" Nayi karatun lauya a kasar London,nayi Digree na daya dana biyu duka a can "

Buɗe baki yayi yana kallon ta cikin mamaki,domin bai taba tunani ba,"ina takardun naki suke?

Wayar shi ta ɗauka ta saka number Google Account dinta ta fito mai da su,mika mashi tayi "gashi nan,sai ka tura masu suyi printing"

Amsa yayi yana kallo kafin ya gado yana kallon ta,cikakkiyar result ne mai dauke da shedar kwarewarta a kan Lauya,"Me yasa naga sunan *UMMU SALMA ABDULLAH*

Lumshe ido tayi"Asalin sunan kenan "

"Kina nufin asalin sunan ki kenan"

"Umm"

"Biba kuma fa"

Ɗaga kafaɗa tayi,"ka yi ƙoƙari a kammala min komai zuwa ƙarfe bakwai zan wuce"

Dariya yayi yana jin son yarinyar na ƙara tasiri a zuciyar shi,yanzun da yake gab da sanin ita wacece"zan saka a kaiki da ƙaramin jirgina "

"Na gode,ka saka a samomin duk wani abunda nake buƙata zan rubuta maka list,zan zauna anan kafin na tafi"

"An gama Hajiya ta," Ganin tana ƙoƙarin shigewa daya daga cikin dakin ne yace"to ko ɗan Kiss ba zan samu ba?

"Har yanzun da igiyar auren shi a kaina ka bari idan an warware"ta fada shigewa cikin dakin tare da turo ƙofa,

Murmushi yayi kawai ya tashi yana barin gidan,

Tana kulle kofar faɗawa tayi kan gado tana fashewa da kuka tare da tura kanta cikin filo,
Ada tayi Alkawarin ba zata kara amfani da duk wani abu ɗaya danganci Salma ba,saboda ta tsani ta tuna baya,bata kaunar ta tuna wandanda suka yi silar kawota duniya saboda babban zunubin da suka aikata ma rayuwar ta,taso tayi nisa da komai ta ci gaba da tafiya har abada,sai gashi sanadin wannan aikin yana ƙoƙarin mai da baya,bayan ma sosai irin wanda ta fara mantawa da kaman sa,
Bata son ta ji suna ko mai irin nata saboda gudun wancan rayuwar,

Jin wayar shi data karɓi daya yana ƙara ne yasa ta duba,shi ne ke kira akan ta turo masa list din dan har an fara mata aikin takardun ta,
Dan haka cikin sauri ta rubuta komai ta tura mashi,sannan ta tashi ta shiga banɗaki dan tayi wanka kafin ya aiko mata da kaya ta wuce,
Zuciyar ta cike da ƙuduri da kwarin gwiwar ɗaukar fansa.
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*47*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Kafin ƙarfe shida na yamma ya kammala mata komai na tafiyar ta an kammala hada mata License nata,sannan ya saka jirgin shi ya dauke ta,wanda ƙarfe takwas ta masu ne garin Lagos,

Bata yarda ta sauka a Hotel din da su Abba suke ba,wani ta kama da ban ta kammala shirin ta sannan ta nufe babban Headquarter da taji yake,

A babban offishin su aka sauke ta kasancewar ta nuna masu I D card din ta na matsayin cikakkiyar lauyar gwamnati sannan zata tsaya mashi,
A lokacin ma Ogan su na gida aka fada mashi,sannan tace tana buƙatar ganin wanda zata kare,

Koda suka faɗa mashi dariya kawai yayi"maza ma sun kasa sai ita,ku barta ta shiga"

Ai kuwa kira suka yi aciki aka fito dashi karamin falo in da suke ganawa da lauyoyi ko kuma iyalan su,

Tunda ta shigo wurin take kallon ko ina da kuma irin jami'an tsaro dake wurin,har aka mata iso aka buɗe mata ƙofar shiga in da yake,

Tunda ta shiga take kallon wanda ke zaune fuskarshi na kallon gefe,
A hannun shi da suke kumbure idanun ta suka fara sauka,hakan yasa karfin takunta fara raguwa,har ta iso in da yake zaune,
Ganin bai juyo bane yasa ta kira sunan shi a hankali dan son tabbatar wa"Suraj"

Juyowa yana daura idanun shi a kanta,

Da sauri ta dafa kujerar dake kusa da ita,
Kamar yanda take kallon shi haka shima yake kallon ta,banbancin shine ita kallon tsoro take mai,
Ganin ba ta da niyar natsuwa ne yasa yace"Idan baki da karfin gwiwar gurewa me na baiyana?

Tabbatas shi ne,
Ji tayi hawayen da take ƙoƙarin rikewa ya sauko,
Da sauri ta share da bayan hannun ta,cikin karfin hali ta jawo kujeran dake kusa dashi ta zauna,

"What have they do to you?

" Tambayar da kika zo ki min kenan?

Ganin yanda yake magana da kyar ne yasa ta kasa jurewa ta kifa kanta da kujeran wurin tana fashewa da kuka"ba zan taɓa yafe masu ba!ba zan taɓa barin su ba"ta faɗa cikin kuka,

Bai dakatar da ita ba dan haka sai da tayi kuka sosai har sai da taji zuciyarta ya ɗanyi sanyi sannan ta tago,idanun ta sun yi jawur sun kumbura,saboda yinin da tayi tana yin kuka,

"Why are you crying?

" They killed my friend,she is my everything "

"Waye lauyar nawa?

Share hawayen idanun ta tayi wandanda suka kasa tsayawa," Ni ce"

"Akwai hatsari a aikin ba zaki iya ba"

"Na riga na rasa abinda nake karewa,babu wani abunda yayi saura wanda zan rasa"

"Wannan hawayen yana nufin gazawa,rashin juriya"

"Na yau ne kawai"

"To ki saka su tsaya"ya faɗa yana kallon yanda take ƙoƙarin ganin ta Dakar da hawayen ta hanyar shanyewa amma ta kasa,because the more she tried the more hawayen ke kara saukowa,

" Ko wata fitar numfashi da aƙwai sauki mai tarin yawa a cikin shi,
Kula da ciyo mai matukar zafi ba abu ne mai sauƙi ba,
Kada ki yi ƙoƙarin kunna wuta akan abinda zai iya kona ki,sannan kaɗa ki rike takobin ki domin yanka fure kawai,
A sanda zaki iya iyo a cikin babban Teku,kada ki bari ruwan hawaye ya rufe maki idanun ki,domin kina iya nitsewa"
Mikewa tsaye yayi"sai mun haɗu a Kotu gode "yana gama faɗar haka ya juya ya bar wurin cikin dingishi wanda yake yi yana dafe gefen cikin shi,

mikewa itama tayi tana sai saita kanta sannan ta fito cikin wurin ta wuce bayan ta masu sallamah,

Hotel din data sauka ta koma,tana shiga daki wayar ta na ƙara,koda ta duba sunan Ammi ta gani,dan haka ɗauka ta yi,sallamah taimata,ita ma ta amsa,

"Gobe za'a shiga koto"

"Hakane Ammi"
"Kin samu ganin shi?

" Eh"

Dan shiru tayi na wani lokaci"Abbu yace har yanzun basu samu ganin shi ba,sannan basu samu tsayayyen lauya ba"

"Zan tsaya a matsayin lauyar shi"

Ajiye carbin dake hannun ta tayi,"ya amince?

"Ban damu da amincewar shi ba"

Jin sautin murmushin ta tayi,"Allah ya bada sa'a "

"Me yasa baki yi mamaki ba?
" Saboda Nasan zaki iya"
"Baki yi mamakin kasancewata lauya ba?me yasa baki tambaya ba?
" Saboda akwai wasu abubuwan da har mu mutu bamu isa mu san su ba,
Allah ya kare ki,ya kuma saka Ayi walƙiya mai matuƙar haske,abin da ke cikin duhu ya baiyana"

Shiru tayi ta kasa cewa komai,maganar su na matuƙar daure mata kai daga na Uwar har na ɗan,shima bai yi mamakin kasancewarta lauya ba,haka bai tambaye komai akai ba,it seems like sun san wani abu game da ita,

"Ammi"ta kira sunan ta

" Na'am "

"Shin kin san koni wacece?

Sai da tayi ɗan jim kamar ba zata amsa ba sai kuma tace" Na sani Ummu Salma,na sani tun farko,har ta abinda ke kanki baki sani ba game dake,"ajiyar zuciya ta sake"ina da duk wani amsa da Kike nima,sai dai yanzun ba lokacin da zan amsa maki su bane,abu na farko da zaki yi shine Ceto rayuwar ɗa na,idan har kika dawo min dashi lafiya na miki alkawarin sanar dake abin da baki sani ba"

"Amma shi ya sani?

"Bai sani ba,babu wanda ya sani,"

"Wacece ke? Ta tambaya domin ji take kamar bada Ammin take magana ba,a ina ta santa,har ta san Asalin sunan ta,ji take kamar numfashi kawai take yi amma wasu mutane ne ke sarrafa rayuwar ta,
" Me yasa kika karbe ni a matsayin mai aikin ki bancin tun farko kin san ko ni wacece?

"Ki yarda dani Ummu Salma,ba zan taɓa cutar dake ba,ke dai kawai ki yi yanda nace,domin rayuwar ku a yanzun shi yafi komai muhimmanci"

Hawaye ne ya shiga bin idanun ta,meke faruwa da rayuwar ne,jan majina tayi tana ƙoƙarin sai ta kanta "Amma kin san da mutuwar Ummita?

" Dazu nake samun labari,very sorry for you lost "

"Me yasa zasu mata irin wannan kisan,me yasa" Ta karasa faɗa tana fashewa da kukan data kasa riƙewa ta tsugunna a nan ƙasa tana faman rusa kukan,
Hannu tasa ta dafe kirjin ta "ba zan iya daurewa ba,zuciya ta zafi take min kamar an kunna wuta,a duk lokacin dana tuna shi kenan na rasata har a ba da ji nake kamar na mutu ni ma,
Rayuta kadai ta rage min a yanzun amma ji nake kanar ita din ma tana hannun wasu ne su ke juya min ita,
Yaya zan yi,me ya kamata nayi domin dawo da komai,sai dai komai ya riga da ya bar hannu na,duk da haka bana jin zan iya barin koma waye ke da saka hannu akan wannan lamarin,ina nufin ko waye shi"

"Rayuwar ki tana hannun Allah ne da hannun ki ba hannun wani ba,ke kike da damar da zaki juya taki rayuwar Salma,ko wani abu da ki kaga ya faru da bawa to yana da dalili,ko wani dan Adam kuma yana da nashi tarihin mai ƙunshe da abubuwan mamaki da darasi,kamar dai naki,
Ina maki fatan nasara akan wannan tseren,idan har akwai abinda kike butaka kina iya tuntuɓa ta"tana gama faɗar haka ta yanke wayar.
Chapter 47 · 0% Book details